x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 99 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 294001 words
  • 297000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 417

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
juyawa suka yi ido huɗu da wani murtukeken kumurcin maciji bakin kirin da shi kwance a kusa da dutsen da Kamran yake zama idan ya zo. Macijin yana da girma sosai da sosai, ga shi bakin kirin.

Wani irin ihu ta kurma tare da miƙewa tsaye. Ihu da ta yi yasa macijin girgiza jikinsa ya kuma miƙe daga kwanciyar da ya yi, sannan ya yi wani irin kananannaɗa kamar ba lafiya ba, wannan maciji kamar ba maciji ba.

A guje ta miƙe tare da rugawa wajen ƴar uwarta, hannunta ta riƙo tana faɗin. "Tashi mugudu Sweetie, mun shiga uku maciji a ɗakinmu". Da karfi ta yi maganar cikin ihu.

Ai a dubu ita ma Sweetien ta miƙe, hannunta Pretty ta riƙe gam suka nufi waje da gudu. Ai kuwa macijin yana ganinsu ya rufa masu baya.

Da gudun gaske suka fito cikin ramin, sai jan hannun Sweetien take yi, baiwar Allah bata iya ganin komai sai yadda aka yi da ita. Gudu suke yi basu san ina suka nufa ba, shi kuma macijin da kyar ya fito daga cikin ramin, saboda hawace tana yi masu wahala, ko da ya fito babu alamarsu a arear, habawa Pretty sarkin tsoro tuni ya ja Sweetien suka bar arear wajen. Waige waige snake ɗin ya fara yi kamar yadda macizai suke yi idan suka bi mutun ko idan zasu yi mugunta. Ya fasa kai tare da ɗago kan yana nemansu.

Ganin babu alamarsu a wajen ne yasa ya kwantar da kansa ƙasa ya fara bin cikin ciyayi suuuuuuuu ya tafi.

Su kuwa gudu suke yi babu kakkautawa, basu fa san ina suka dosa ba bayin Allah, sai fincikar Sweetie pretty take yi suna tiƙar uban gudu.

Basu fargaba sai ganin wata bakar damisa suka yi a gabansu. Wani irin birki Pretty ta ja har sai da Sweetien ta kusa faɗuwa, a hankali ta fara ja da baya da baya. Suna ta zuba uban haki Sweetie ta tambayeta lafiya suka tsaya?.

Ƙasa iya yin magana ta yi, dara daran idanunta na'a kan hakwaran wannan damisa da yake ta faman buɗe baki. Ai bata san lokacin da ta saki fitsari a jikinta ba, zuuu fitsarin ya ganganro ƙasa, tana son ta yi kuka, amma ta rasa ina kukan nata ma ya tafi, wani irin kakkarwa jikinta ya fara yi kamar wadda sanyi ya kama, ji take yi shikenan yau kwananta ya kare.

Sai yau ta tuna da addu'ar da mun ɗinsu ta koya masu na idan sunga miyagu zasu cutar da su, sai dai ta ƙasa iya furta addu'ar ma. Sambatun Sweetie na tambayarta lafiya ne ya dawo da ita cikin hayyacinta.

Kuka ta fashe da shi mai tsananin sauti tare da cewa. "Sweetie mun mutu yau, damusa ce a gabanmu, baki ji gurnaninta ba? Mun mutu yau kam!". Tana kai karshen maganar ta kara sautin kukan nata.

Sweetie na ƙoƙarin yin magana kirjinta na dukan uku uku duk da ita bata kalli damisar ba, bata san ya take ba, amma ta tsorata, tana ƙoƙarin tambayarta damisar Kamran ne wato Rocky. Bata kai ga yin maganar ba damisar ta daka wani uban tsalle ta haykewa Sweetien wanda hakan yasa ta zube ƙasa hannunta dana Prettyn ya rabu, Prettyn ta saketa dan dole ta faɗi ƙasa a gefensu ita ma.

Ƙoƙarin capko wuyar Sweetien damisar ta yi, baiwar Allah bata gani sai ƙoƙarin kwatar kanta take yi, tana ta buge buge da hannunta.

Ganin hakan yasa Pretty ta miƙe tsaye, zuciyarta tafasa yake yi kamar an ɗaura dalma a wuta, jikinta na tsuma, da taga yadda Sweetie ke buge buge da hannu da kafa, ga shi jikin damisar ya rufe jininta ba'a iya ganinta sai hannu da kafar da take ta bubbugawa a ƙasa tana neman yadda zata kwaci kanta.

Ganin haka yasa Prettyn ta yi tunanin ko damisar cin namar Sweetien take yi, ta kara tsorita over! Jikinta na tsuma tana tsotace, nan take ta ji wani karfi ya zo mata, zuciya ba zata iya gani a kashe mata ƴar uwa ba, da wani irin mahaukacin gudu ta nufi damisar, ita kanta bata san ta nufe shi ba, jini ba wasa ba, tashin hankalin kada ƴar uwarta ta mutu ne yasa ta nufi damisar ba tare da saninta ba, bata san tana da karfin zuciya har haka da zata iya tinkarar damisa ba har sai da taga Sweetien a gaɓar mutuwa. Wani irin kukan kura ta yi ta haye saman bayan damisar ta fara kai mashi duka da ƴan hannayenta da basu wuce a kama a karya ba, duka take kai mashi har da su cizo, tana yi tana sambatu a kan ya rabun mata da ƴar uwarta, kada ya kasheta, wlh ita kaɗai kawai take da shi a duniya.

(Ni kam na ce ko yaushe damisa yasan duniya bare har yasan yar uwa kuma yasan ita kaɗai kike da shi a duniya? Jama'a ku taya jin abin da Pretty ke gayyawa damisa fisabilillahi 🤌 Allah sarki, duk wata zuciya mai imani ne ba zata ɗauki ganin a kashe mata nata a gabanta ba, barema su da suka taso a tare, basu da kowa, kullum suna manne da juna, suka kwanta ciki ɗaya kuma suka sha nono lokaci guda, ai fin haka ma Prettyn zata aikata)

Baiwar Allah ihu take tamkar maƙoshinta zai ɓalle, komai rashin imanin zuciya ta gansu a wannan hali sai ta tausaya masu. Wani irin girgiza damisar ta yi sai ga Pretty ta faɗo ƙasa tim.

Ɗago kai damisar ta yi daga kan Sweetien tana kallonta, duk ta farfasawa Sweetie wuya da faratunan hannunta, sai dai bata kai ga tsinke mata maƙogoro ba, har yanzu akwai rai a jikinta.

Ihu Prettyn ta sake kurmawa ganin jinin dake malala daga wuyar ƴar uwar tata, da karfi ta miƙewa tsaye, cikin dakiyar zuciya da ita kanta bata san tana da shi ba sai yau data ga bone, da Sweetie ta mutu gara mata ta rinkari koma wace iriyar masifa ce. Wani katon itace dake kusa da ita yashe a ƙasa ta ɗauko, idanunta ya rufe sosai, gadan gadan ta nufi damisar, a lokacin kuma damisar ta mayar da kanta kan Sweetie tana ƙoƙarin lamusheta.

Da karfi Prettyn ta daddage ta bugawa damisar itacen a kai. Hakan yasa ta ɗaga kanta sama ta saki wani uban gurnani mai tarwatsa ƙwaƙwalwale masu sauraro. Ita kanta Pretty sai da ta jefar da itacen ta sanya hannu ta toshe kunnuwanta, tare da runtse idanunta ta ɗan yi baya.

Wani irin dip da ta ji a kusa da ita ne yasa ta yi saurin buɗe idanunta. Damisar ce a gabanta, ta baro kan Sweetie ta tinkarota, shi ne ta yi tsalle daga kan Sweetien ta diro a gabanta hakan yasa ta ji wannan dip ɗin.

Sai a lokacin kuma ta dawo cikin hankalinta ta gane ashe fa damisa ce a gabanta, duk buga mata itace da ta yi bata cikin hayyacinta ne, tsoron rasa ƴar uwarta yasa ta yi duk abin da ta aikata. Yanzu kuma da ta juyo ta kanta sai ta fara tunanin mutuwa zata yi, nan take ta fara hawaye.

Cikin takun ƙatsaita damisar ta tunkarota. Habawa kafa me naci ban baka ba? Da wani irin mahaukacin gudu ta juya ta nufi barin wajen, da gudu damisar ta rufa mata baya, gudu take kamar walkiya, kamar zata tashi sama, tana gudu kuma tana ihun a kawo mata ɗauki.

(Gaskiya duk da sun ban tausayi a wannan waje, kuma na yi kwallah, amma wlh sai da Pretty ta sake bani dariya😅 dan ni kaɗai naga irin gudun da take yi kamar walkiya😅 Allah sarki gudun cetan rai😥💔 ko in da take kawa bata sani ba, yi take kamar zata fire sama kawai)

Ita kuma Sweetie jin damisar ta bar kanta ne yasa ta miƙe jini ba ɓulɓula daga wuyar tata, ta kai hannu ta rike wajen tana kuka gwanin ban tausayi, ga shi bata iya gani, haka ta bazama cikin dajin nan tana layi tana kiran sunan Pretty, kuka take yi sosai gwanin ban tausayi, sai kutsawa cikin dajin take yi ba tare da ta san ina ta nufa ko in take takawa ba.

Hanyar yamma ta nufa dan neman Prettyn tana kuka, ita kuma Pretty ta yi gabas ne, so kwata kwata ma basu haɗa hanya ba. Bata yi nisa a lalluɓen hanyar da take yi tana tafiya ba sai ga wasu jiga jigan zaratan matasan maza da mace ɗaya masu ji da lafiya sun sha gabanta, dukkansu sanye suke da fararen kaya tas except macen, kumma dukkansu suit ne a jikinsu, macen kuma wani irin kaya ne mai kama dana mayaƙa ta sanya, macece da a shekaru ba ba zata wuci 22 years ba, mazan kuma zasu iya haura 30 haka. Face ɗinsu da wani irin bakin fenti na zanen bakar damisa, ba zaka taɓa iya gane su wanene bane, maza ne majiya karfi madaka katti. Su goma ne cif sai macen. Daga sama har ƙasa su da gani kasan daga wani ɗaular suka fito, dan babu harkar karanta a tattare da su, sun jiku da naira, sai dai kuma babu alamar imani ko ɗigo a tattare da su, sannan babu annufi a kan fuskokinsu, duk yadda aka yi waɗan nan basu ƙunso alkhari ba!! Dan daga ganin yanayinsu kasan babu lafiya!.

Macen cikinsun lafiyayyar mace ce wadda da kallo ɗaya zaka yi mata kasan e lallai ta karɓi horo iya horo bana wasa ba, macece amma damtsen hannunta kamar na Assistant commander wato HOORAIN, daga ganin wannan mayakiya ce ko dai wani abin makamancin hakan. Macen ce ta matso ta ɗauki Sweetie cak ta saɓa a saman shoulder ɗinta, da alama nemanta ne ya kawosu cikin wannan daji, duk yadda aka yi sun san face ɗin Sweetien kuma ita suke nema, dan suna ganinta babu wata wata suka nufeta, duk yadda aka yi ita ce dalilin zuwansu wannan dajin. (Da alama Sweetie ce zata kai mu ga RAWANIN ZALINCI)

Gaba da ita macen ta yi, waɗan nan zaratan mazan suka rufa mata baya, da alama itace shugabansu, kuma itace karama a cikinsu, duk sun fita shekaru, amma yadda suke yi mata biyaya sun yi mubaya'a zaka gane e lallai duk yadda aka yi ta fisu matsayi. Gata jajircecciya, daga gani jininta a tafashe yake.

Tafiya suka yi da Sweetien ta hanyar da suka fito, sai sambatu take yi tana kiran sunan Kamran da kuma Pretty, Allah sarki bata ma san wanene ya ɗauketa ba. Su kuma sam babu wanda ya ce mata ko sannu a cikinsu, kuma ba kayan mayaƙa ne a jikinsu ba bare muce mayakan da suke nemansu su da mum ɗinsu ne suka kamata, ko dai su ne suka sake yin ɓadda kama da fararen suit? To lokaci ne zai nuna mana koma su wanene.

A ɓangaren Pretty kuwa, tana tsaka da tikar gudu wannan damisa ta daka wani uban tsalle da nufin ta sauka a kanta, sai dai bata kai ga yin hakan ba Kamran ya shiga tsakaninsu, dan kuwa hanyar da Pretty ta biyo hanyar kogonsu ne, yana zaune a saman dutsen a waje suna hira da Mammarsa ya jiyo ihu tun daga nesa, ko ba'a gaya mashi ba yasan ita ce, dan muryarta hadda ya yi mata. A ɗari ya miƙe Mamma na kiransa amma ina, ko kallonta bai yi ba, da gudun gaske ya nufi in da ake ihu, to kun ji yadda aka yi.

Ai kuwa yana shiga tsakaninsu damisar ta sauka a kansa, rigizib ya zube ƙasa. Habawa hayke mashi damisar ta yi, kokawa da ita ya fara yi yana ƙoƙarin kwatar kansa, ita kuma damisar da waɗan nan shegun faratu nan nata duk ta farfashe mashi fuska, so take ta damki maƙogwaransa ta tsinketa ta kashe shi.

Ita kuwa Pretty da bata san ma da cewa Kamran ya zo ba, cigaba da tikar gudunta kawai ta yi tana ihu, a tunaninta damisar na binta, gudu take yi sosai har ta bar yankin mai gabaɗaya, ta yi nisan kiwo.

Kamran kuma gabaɗaya damisar ta gama da shi, ko motsin kirki baya yi, duk ta farfashe mashi fiska jini na malala, tana ƙoƙarin capko wuyarsa da bakinta dan ta ƙarisa kashe shi kwatsam ba zato ba tsammani sai ta ɗaga kai sama ta kurma wani irin gurnanin azaba sakamakon wani irin kaifaffen wuƙa da Mamma ta caka mata a ciki.

Wani irin gurnani ta saki take da girgiza jikinta. Mamma dake tsaye a dake kamar wata commander mayaka ta fara kalla.

Ko alamar tsoro babu a fuskar Mamma, tana tsaye cikin jarumta, ko shakkar damisar bata ji ba, zuciyarta tafasa yake yi, wani irin bakinciki ta ji na jiwa ɗanta ciwo da damisar ta yi, burinta kawai ta zo su gwabza ta kashe banza, dan ita ba yau ta fara faɗa da damisun dake cikin wannan dajin ba, kafin Kamran ya girma ta sha gwagwar maya kafin su shafa mata lafiya, so Mamma ta wuce tunaninku, ita kaɗai tasan wacece ita kuma me yake ranta.

Kanta damisar ta yi cikin zafin nama. Ai kuwa bata yi wata wata ba ta sunkuya ƙasa tare da daba mata wata kaifaffiyar wukar a wuya wajen maƙogwaranta. Kun san damisa da zaki taurin rai ne da su, basu mutuwa ta daɗi, dan haka suka fara kokawa da Mamma babu kakkautawa.

Ganin haka yasa Kamran ya lallaɓa da kyar da makyarkyata ya miƙe, yana ta layi ya fara nufar hanyar da take ta kudu domin neman Pretty, bawan Allah shi bama ta rayuwarsa yake yi ba, Pretty ce kawai a ransa. Ita kuma Pretty gabas ta yi, Mamma kuma na faɗa da damisa tana ƙoƙarin ƙarisa kashe ta, yau Rocky baya nan, su suke kwatar kansu da kansu, Allah sarki ga Sweetie dai an tafi da ita, ko su wanene?............ Wai yau ina wannan jarumin mai irin idon su Pretty wanda yake kawo masu ɗauki kullum ne?😥💔


To wannan shi ne sanadiyar rabuwar waɗan nan bayin Allah da suka shafi tsawon lokaci a tare, Sweetie, Pretty, Kamran, shin zasu sake haɗuwa? Ya Kamran zai yi idan aka ce yau babu Pretty? Anya zai iya cigaba da rayuwa? Kun san kaunar da take a tsakaninsu fa! Shin Kamran zai je neman babansa? Wanenen ma shi? Wacece Mamma? Ina mum twins ta tafi ta barsu a cikin wannan dajin? Su waye su Pretty? Suwaye suke neman rayuwarsu? Su waye suka biyo mamansu time da take da cikinsu? Meyasa su kaɗai ake da buƙata ban da mamarsu? Meyasa lokacin da aka biyota waɗan da suka biyota cikin nata kawai suke da buƙata? Ina babansu? Ina baban Kamran? Waye wannan jarumi mai irin idon Prettyn?

DUBAI. Menene makomar Leesharh? Shin asirinta zai tonu? Maganin me Ramish ya sha? Shin zai cutu da gaske?. Idan Allah yasa Leesharh ta gama aiki shin masu nikaf zasu cika alkawarin da suka ɗaukar mata na haɗata da babanta kuma su mayar da ita kasarsu? Shin da gaske Leesharh ita ta kashe mahaifiyarta? Idan ita ce menene dalili? Wacece ita ma? Ya makomar tsakaninta da Obaid a yanzu?

GIDANSU KHADIJAH. Menene makomar maman Zainab? Baban Zainab ya mutu? Ina Hauwa? Idan baban Zainab ya mutu ya maman Zainab zata yi? Zata tsira kuwa? Kisan kai ta yi kenan? Hukuma zasu barta?.

KINGDOM OF POWER. Nan ba sai na yi magana ba, cakwakiyar dake ciki ya wuce tunaninku, abin ya wuce zatonku.

Shin da gaske Sweetie ce zata kaimu ga RAWANIN ZALINCI? Suwanene waɗan da suka ɗauketa? Ina kuma zasu kaita?.

Amsoshinku yana step two, yanzu zamu afka cikin labarinmu, kada ki bari a baki labari, labari ne da yazo da salo na daban, zalinci, cin amana, hainci, cutarwa, zanba cikin aminci, tauye yarda, tauye hakki, cin hakki, cin zarafi, mugunta, keta, da kuma zazzafar soyayya mai cike da kaddarori haɗi da nasarori da kuma fafutukan cikar buri. 500 Naira kacal kuɗin karatun littafin RAWANIN ZALINCI from step one to end, da 500 naki zaki cigaba da karatunsa cikin aminci da kwanciyar hankali, trust me ba zaki taɓa yin danasanin karanta littafin RAWANIN ZALINCI ba, zaki ilmantu matuƙa, zaki nishaɗantu matuka, zaki wa'azantu matuƙa, ku kunsan yadda alƙalamina yake, akwai tarin abubuwa a tattare da shi, ba sai na ɓata bakina wajen sake gaya maku ba.

Duk wadda ta shirya biyan kuɗin karatun littafin RAWANIN ZALINCI zata tura kuɗinta ta wannan account ɗin 1882812910 Musa Fatima Zahra access bank. Sai ta tura mun shaidar biya ta nan. 08161390581, kina biya zaki afka cikin tafiyar nan, ayita dake, kada ki yarda a baki labari!!.

TAƁA KA LASHE STEP TWO🔥💔😥


KAMRAN AND MAMMA.

"Kamran idan ka sake magana a kan babanka zaka mutu, mutuwa kuma mafi muni a rayuwa, kamar yadda ka taso baka san kowa ba, sai ni, to haka zaka riƙe ka manta da duk wasu tunanin banza".

"But Mamma why? I want to know my father ko da kuwa hakan ce zata zama sanadiyar numfashina na karshe, just tell me where's he? Ni zan je in da yake koda kuwa ya fi wuta zafi dole na tunkaresa!! Na kusancesa!!".

Tsawa ta daka mashi mai sauti, cikin fusata, idanunta sun kaɗa sun yi jajir, jijiyon kanta har wani mimmikewa suka yi, da alama ranta ya kai kololuwa wajen ɓaci, har wani huci take yi kamar zakanya. "Kamran ina gaya ma zaka yi mutuwar walaƙanci in dai ka sake yin magana a kan babanka! Kai ba mutun ne kamar kowa ba! Kai ba kamar sauran mutane kake ba! Kai na daban ne, farautarka ake yi kamar yadda ake karautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana! Zaka mutu idan ka fita! Zaka mutu kamar dabba! Dan haka ka tsaya a in da na tsayar da kai!!".

"Mamma i can't! I can't gaskiya! Idan kuma kina son na bi maganarki so tell me who I am?! Where's my father and my family?! Why are you hiding our life anytime?! Am tired! Am tired Mamma! I want to see my father and my family, cos I can't stay with you again! Tafiya zan yi na nemo babana and Prettyta even wannan shi ne ganina dake ta karshe!".

Tashin hankali kenan, ɗan tsokaci a tsakanin Mamma da Kamran kenan, menene dalilin Mamma na hana shi sanin tarihin babansa bayan ya buƙaci sani? Waye shi? Ina mahaifin nasa yake? Meyasa take cewa zai mutu idan ya sake yin magana a kan babansa? Meyasa?!!.

SWEETIE.🔥

"Ɗago idanunki
End Ads