burinki ki zama mai faɗa a ji a faɗin ƙasar Tunisia ne to ɗaya daga cikinsu zaki buƙata........"
Kara kwaɓe fuska ta yi tare da wurgawa Aunty tata wani irin kallo mai kama da zargi. "Gaskiya Aunty kanki baya kawo wuta sam sam, ni fa ba ce maki na yi ina son in auri wanda zai yi mulki a nan gaba ba, so nake na haifi wanda zai yi mulki a nan gaba, kina tunanin ko na auri ɗaya daga cikin ƴaƴan King zan samu yadda nake so ne? Gaskiya Aunty sam baki tunani mai kyau, ai ko na auri magajin kakkarfar kujerar izza buƙatata bata biya ba, dan dai ke da kanki kin san ƴaƴansa ba masu juyuwa bane, baki isa ki juyasu yadda ranki yake so ba! Amma idan kika auri uban kika haifi naki ƴaƴan, ko ba yanzu ba nan da shakaru 20 zuwa da 25 zaki zama yadda kike burin ki zama, zaki zama mai karfin iko, a duk lokacin da aka ce ɗanki ne a saman wannan the most powerful seat ɗin, sannan ya sanya powerful Crown a kansa, ai kinga daga nan zaki murza kambunki son ranki a faɗin ƙasar, amma idan kika biyewa ƴaƴan nan nasa sai su ce maki basu son sarauta kamar dai Yah Abbas, kin ga shi ma ya ce maki baya sha'awar sarauta, to nasan ƴaƴansa ma yadda suke shararrun ƴan bokon nan ba wani mulki da za su yi, shiyasa bana son na auri magajin mulki, nafi son na haifi magaji wadda ko ya ce baya son ya yi mulki zan tursasa shi dole ya yi, sannan shi Jahiz da kike magana kada ki manta bashi da gadon mulkin nan a yanzu, dan King yana da yara, da bashi da yara ne sai kaninsa ya hau kujera........"
Kallon tsab Mammie ta yi mata. "Lallai Aliyah kin girma, waye ya ce maki Jahiz bashi da gadon mulki? Yana da shi mana, idan su Ramish suka kekashe ƙasa suka ce basu da ra'ayin mulkar ƙasar Tunisia ai dole idan King ya tsufa Jahiz ya karɓesa tun da Abbas baya ra'ayi".
Cike da rashin respect a maganar tata ta furta. "Aunty koma dai menene ni magajin nake son haifa, magajin da ko baya son mulki zan tursasa shi yi dan cinmma burina, dan haka ni King Zuhair ne burina, shi nake son aura!".
"Aliyah King Zuhair ya fi karfinki, Jahiz shi ne zaɓin da na yi maki, dan haka ki dai'na maganar King!!".
Cigaba da wurga mata kallon zargin ta yi, a ƙule ta ce. "Aunty saboda kema kina da burin auran King Zuhair ɗin shi ne kike son hanani ko? To ki bari mana kowacce ta gwada sa'arta, a cikinmu duk wadda ta samu nasarar mallakarsa ai shikenan duk ɗaya muke, ni dai ba zan hakura da burina kuma muradina ba"............... Tashin sense, lallan yanzu KINGDOM OF POWER zai kama da wuta, na ce ba my people's mu gayawa Aliyah wacece Momma ne ko dai mu bari ta Momma ta gwada mata karfin jinin Modarawa?🤔 Tab kuna tunanin da Momma King ya fara aura ma zai kara aure ne? Ai da ba wannan magana kuma kun sani, hmmm Hajiya Aliyah momma kam dai'dai take da zamaninki, ga Mama a gefe, sannan ga mummy, uwa uba ga su Ramish, wai kuna tunanin su Ramish zasu yarda King ya auri wadda suka girma ne?🤔 Gaskiya akwai rikici a wanan gida ba kaɗan ba.
"Aliyah ni kike gayawa ina son auran King Zuhair? A yaushe muka yi hakan dake?". Ta yi maganar cike da mamaki tana kuma zaro idanun.
"Kina mamakin ya aka yi nasan burinki ne Aunty? To bari ki ji ranar da kika je gida ina jinki ke da mama kuna magana a kan ke dama ba Yah Abbas kike so ba, King Zuhair kike so, dan burin mulki kike da shi, kuma ko za'a mutu ko za'ayi rai, ko rai nawa zaki iya salwantarwa domin ki auri King ki haifi maganin Crown of Kingdom of power!!".
Kara zaro idanu sosai Mammie ta yi, bata taɓa tunanin bayan mahaifiyarsu akwai wadda tasan da wannan magana ba, sirrinta ne kuma burinta!.
"Aunty ki dai'na yin mamaki fa, kuma ki dai'na ƙoƙarin hanani mallakar abin da zuciyata take so, Crown na kingdom of power rawani ne da kowani basarake yake burin samunsa, kujerar mulkin kingdom of power kujerace da jiga jigan sarakuna masu karfin iko suke fatan su zauna a kansa, masarautu ba adadi ne a ƙarƙashin wannan masarauta, duk wani karfin ikon mai karfi a faɗin ƙasar nan dama maƙota ƙasashe duk a ƙarƙashin King Zuhair suke, a haka kike son nayi wasa da wannan dama? Sanin kanki ne fa shiga in da King Zuhair yake ma ba ƙaramin abu bane, ke kanki kin san ko da yatsa ka nuna gate na farko na shigo cikin masarautar nan sai an datse maka hannu, duk wani karfin iko da isa tana nan! Wlh kamar yadda kika ce ko rayuka nawa zaki iya salwantarwa domin ki mallaki King, ni ma hakance, zan iya aikata komai dan na mallakesa, dan haka da ni dake lokacin buga wasa a tsakaninmu ya yi, kowacce ta gwada sa'arta kawai....." E lallai akwai cakwakiya ba kaɗan ba!.
Tana kai karshen maganar ta miƙe fuuu abayar jikinta na ja a ƙasa ta nufi waje, bata zame ko'ina ba sai family part ɗin King, kai tsaye wajen mummy ta nufa, dan ita mummy ƴar baruwa na ce, kowa nata ne, kowa ya zo gidan hannu bibbiyu take tarbansa, shiyasa suke sonta, tana da hakuri haɗi da kawaici, ainahin mahaifiyarta ƴar Nigeria ce, kuma ita ba yar kowan kowa ba ce, tana da taimakon mutane da kuma saukin kai sosai, ba kamar Mama da Momma ba, ku kunsan Momma tana da kyan zuciya, wargi ne kawai bata ɗauka! Iadan ka kawo mata ba dai'dai ba yanzu zata nuna maka cewa jinin Modarawa ne yake gudu a jikinta. Mama kuma sai ka rasa me matar nan take so a duniya, sai bala'in masifar tsiya, ga ɗan banzan kishi na masifa.
Da kallon mamaki Mammie ta bi Aliyah har ta kurewa ganinta, mamaki da al'ajabi ya hanata yin magana, tunani take yi wai yaushe Aliyah ta girma da har take cewa su ƙara ko wacce tata ta fisheta?. Ita ma fa Mammien ba wata babba bace take wani cewa yaushe Aliyah ta girma, Aliyah ɗin ce fa mai bi mata a wajen haihuwa, kada ku manta Sarina ce ƴarta ta farinta, so ita ma ba wata babbar mace can can bace, iyayi ne kawai.
Wayarta ta ɗauka tare da miƙewa ta nufi cikin bedroom ɗinta tana faɗin. "Dani kike yi Aliyah, yaushe ma aka haifeki da har zaki ce mu ƙara akan muradina? Ke har kin isa ina son abu kuma a yunwace nake da na cinma burina a kansa ki ce kema kina son shi? Wlh ba'a haifeki ba! Tsab zan gyara maki zama, zan gwada maki banbancin shekaru..."
Ta kai karshen maganar tata tana zama a gefen bed ɗin nata, dai'dai lokacin kuma wadda take kira a waya ya ɗauki kiran. "Misalin karfe 1 dare mu haɗu a in da muka saba haɗuwa". Shi ne abin da ta gayawa wanda ta kira ɗin. Tana gama faɗin hakan ta katse kiran tare da buga uban tagumi tana tunani.
(Ni kam na ce uncle Abbas da King sun ga ta kansu, shi yanzu uncle Abbas kenan ya Mammie zata yi da shi tun da ta ce yayansa take so? Shi kuwa King yaga ta kansa kowa son shi yake yi, bawan Allah bai ma san ana yi ba, momma ki shirya ga kishiyar karfi da yaji na dole nan Aliyah tana zuwa, zaki tashi daga amarya 😅 Mama kuma kishi zai karu😅 family part ɗin King zai kama da wuta, 🔥 mummy baiwar Allah dai babu ruwanta, da rabon za'ayi yaki ba kaɗan ba, da rabon su Ramish zasu yi kisan kai ko na ce kashe kashe😅 hmmmm KINGDOM OF POWER kuma yanzu nasu wasan zai fara🔥 ina commander ZAFAR sai ku shirya, ni dai bari na tafi Nigeria gidansu Zainab dan jin ya ake ciki).
GIDANSU KHADIJAH 😥💔
Hakura maman Zainab ta yi ta karɓi wannan ɗaki da Hauwa ta zaɓa mata, a ciki ta kwana, bakinciki kamar zai kasheta, ta fara danasanin zuwanta sabon gidan nan, dan bakinciki kala kala Hauwa take kunsa mata, tsabar mugunta dan ta kuntata mata ma da daddare tasa baban Zainab ya sanyata ta yi masu girkin dare, har da gaya mata kalar abincin da take son ta girka masu Hauwar ta yi.
Idan ran maman Zainab ya yi dubu to ya ɓaci, amma haka ta daure ta yi girki tare da taimakawar su Khadija, ita kuwa Hauwa tun yamma da ta gaya mata ga abin da zata yi masu, suka ci wanka ita da baban Zainab ɗin suka nufi kasuwa, ta tasa shi a gaba wai sai dai su je ya karɓi komai nasa daga hannun Sadiq, haka ya shirya suka tafi, maman Zainab ta yi girki tare da su Khadija.
Sai can wuraren karfe 9 na dare su Hauwar suka dawo, a lokacin maman Zainab sun kammala girki ta zubawa su Khadija sun ci nasu, ita ma ta ɗan tsakuri kaɗan ta ci, bakinciki ya hanata cin abincin na kirki, so kaɗan ta tsakura.
Tana gama cin abincin bayan sun yi sallar mangariba da isha'i ta wuce ɗakinta ta kwanta, su Khadija ma suka wuce nasu da Hauwa ta basu suka kwanta, Zainab ta yi addu'ar barci ta kwanta, ita kuma Khadija ta ɗauro alwala, dan kwanciya bai ganta ba iyayenta suna cikin masifa.
Maman Zainab tana kwanciya sai ga kiran Sadiq ya shigo cikin wayarta, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi da ganin kiransa. Ɗauka ta yi cike da fargaba. A hankali ta yi sallama kamar mai jin tsoron wani abin ko wadda bakinta yake ciwo.
"Assalamu alaikum Maman Zainab na manta ban gaya maki ba ni fa ina hanyar Kaduna, da farko massages naso in tura maki, amma sai dai nace bari kawai na kiraki". Cewar Sadiq ɗin.
A zabure ta miƙe zaune a tsakiyar gadon, zaro idanu waje ta yi. "Sadiq me zaka je yi a Kaduna? Kuma sai ka tafi baka sanar da ni ba? Yanzu da ka tafi ya kake son na yi da rai'na? Da waye zan yi shawara? Waye zai rage mun raɗaɗin da yake damuna a rai'na?! Ina kake son na sanya rayuwata na ji daɗi? Mutuwa kuke son nayi ne?". Tana magana wasu zafafan hawaye suna biyo ƙuncinta.
"Ki yi hakuri maman Zainab, dole ce tasa na tafi, amma kinsan ni ma ba zan so rabuwa dake a irin wannan hali da kike ciki ba, shiyasa nace maki da farko sms naso in yi maki ba kira ba, saboda kada na ji kukanki, da ina turo maki sms zan kashe wayata, amma ki yi hakuri Allah yana tare da ke!!".
"Sadiq to me yayi zafi da zaka tafi ka barni? Kana da wata ƴar uwa a duniyar nan biyu na ne? Ko dai ka dai'na sona ne". Cikin raunin murya haɗe da karyewar zuciya ta yi maganar.
"Ko ɗaya maman Zainab, ban dai'na sonki ba, yama za'ayi na dai'na sonki? Ai ba zai yiwu ba, yanayi ne yazo da dole na yi nisa dake, idan ba haka ba zan iya aikata kisan kai wadda kema kanki ba zaki so na yi hakan ba, ba zan iya jurar cin kashin da suke yi maki ba, baban Zainab ya zo kasuwa da yamma, ya karɓi komai da komai nasa, mun yi lissafi da shi da Hauwa, komai ya fita yadda yakamata, kuma mun yi a rubuce yasa hannu na sa hannu a kan na mayar mashi da komai ɗinsa, shi ne naga ya dace na koma gida in je in kula da mama".
Magana ta gaskiya ba hakance tasa Sadiq ya bar garin Kano ya kama hanyar Kaduna ba, abin da yasa shi ne, wani irin mummunar cin mutunci baban Zainab da Hauwa suka yi mashi a kasuwa, ga lissafi sun yi dallah dallah amma Hauwa ta ce da baban Zainab karya ne ya saci wasu kuɗaɗen, wai ba zai yiwu ace iya wannan ribar kawai aka samu a shagon ba, gudun irin haka fa yasa Sadiq ɗin yake ciyar da su maman Zainab ɗin da kuɗinsa, harta su maman Haidar idan suka zo kasuwa a kan basu da abincin ci daga aljihunsa yake cire kuɗin ya basu, duk dan kada ya taɓa naira biyar ɗin baban Zainab, amma da yake Hauwa makirace, kuma tana jin haushin marin da ya yi mata, sai da ta sa baban Zainab ya ci mutuncinsa a bainan nasi, ya yi mashi kaca kaca, shi kuma Sadiq ga shegen zuciya kamar ɗan kuturu, hakan yasa ya haɗa kayansa ya nufi gidan iyayensa in da zai bugi kirji yace ya isa a can, har police Hauwa ta ce baban Zainab ya kira su zo su tafi da Sadiq ɗin, da kyar masu shagunan kusa da su suka bata hakuri ta hakura, mata kamar wata kanwar shaiɗan. Wannan shi ne a takaice abin da ya faru a tsakaninsu da yasa Sadiq ɗin ya bar Kano, yaki gayawa ƴar uwa tasa gaskiya ne kawai dan baya son ya ɗaga mata hankali, baya son kara mata zafi a kan zafi, shiyasa ya ce mata sun yi lissafi lafiya lou!!.
Sosai maman Zainab ta rinƙa kuka, sai hakuri yake bata ita kuma tana yi mashi magiyar ya dawo dan Allah, daga shi sai su Khadija take gani ta ji daɗi a rayuwarta, sune kaɗai suka rage mata, sune kaɗai farincikinta a yanzu.
Duk magiyar da ta yi mashi ya kafe a kan lallai shi ba zai dawo ba, ta yi hakuri kawai, daga ƙarshe dai ya bata hakuri tare da kashe wayarsa ya yi switch off ɗinta mai gabaɗaya dan ma kada ta sake kiransa.
A wannan daren dai sai da barci ya kasance ɓarawo ya saci maman Zainab, nan ma har wuraren karfe 2, bakinciki da ɓacin rai ya hanata rintsawa baiwar Allah.
Washegari da safe haka ta farka idanunta a kumbure luhu luhu, saboda kuka da ta sha ga kuma rashin barci, tana farkawa ta fito kuma Hauwa ta ce lallai lallai ita zata yi masu kayan ƙarin kumallo, rai a ɓace ta ce ba zata yi ba, baban Zainab ya ce ta yi ko ranta ya ɓaci.
Danne zuciyarta ta yi ta girka ba dan ta so ba, yau dai su Khadijah basu je school ba, dan basu taho da uniform ɗinsu sabon gidan ba, ga shi yau jumma'a, so basu taho da uniform ɗin da suke amfani da shi ranar Friday ba.
A takaice dai babu daɗi suka yi ƙarin kumallo a gidan, duk wanda ka gani ransa a cunkushe banda Hauwa da take cikin farinciki, ranta fes, sai daɗi take ji tana kuntatawa maman Zainab.
Da misalin karfe ɗaya na rana tana zaune a parlour ita da su Khadija, Zainab tana kallo a Tv, Khadija kuma ta buga uban tagumi kamar yadda mamanta ta yi.
"Mama ina kawu Sadiq ne? Ba zai zo gidan nan bane?". Cewar Zainab.
Wani irin ƙululun bakinciki maman ta ji ya taso mata. "Khadija tashi ki je ɗakina ki ɗauko mun wayata bari na gwada numbersa ko yanzu kam zata shiga, tun safe nake gwadawa bata shiga".
Da to Khadija ta amsa mata.
Bata kai ga miƙewa ba sai ga Hauwa da baban Zainab sun fito. Yana shirye cikin wata haɗaɗɗiyar shadda chocolate color, ya yi kyau sosai, da alama masallacin jumma'a zai je, ita ma Hauwa ta ci kwalliya cikin abaya brown color.
Gaisuwa Khadijah ta ɗagawa baban nata, a takaice ya amsa ba tare da ya bi ta kanta ba ko ya ɗaga idanu ya kalleta ba. Zata wuce cikin kenan ya ce. "Khadija ki shirya Hauwa ta ce lallai yau a ɗaura aurenki da Haidar bayan mun sauko sallar jumma'a, dan haka ki shirya su Maman Haidar zasu zo su ɗaukeki".
Wani irin kuka Khadijan ta fashe da shi mai matuƙar tsuma zuciyar mai sauraro, da gudun gaske ta afka cikin ɗakin maman nata, wani irin jan numfashi da take yi cikin kuka sai ta baka tausayi, kamar zata haɗiyi zuciya. Da gudu Zainab ta tashi ta bi bayanta.
Ita kuwa Hauwa wani irin murmushin mugunta take ta faman saki. Miƙewa tsaye maman Zainab ta yi, cikin wata iriyar murya da ba zaka iya fassara halin da take ciki ba ta furta. "Baban Zainab kada ka yi wannan kuskuren, wlh billahi Haidar ba zai aura mun ƴa ba, kada ka bijiro da abin da zai sanyaka yin danasani, wlh a kan farincikin ƴaƴana na yarda komai ya faru, zan iya barin maka gidanka a kan wannan aure".
Hauwa ce ta ce. "To me laifi dan yarinya ta auri ɗan uwanta na jini? Kyamar dangin nasa kike yi ne? Amma kuma ke kin haɗa jini da shi ko?......"
Cikin ɗaga murya tare da zafin rai haɗi da ɓacin rai maman Zainab ta ce. "Hauwa ban kasa dake ba, a wannan gaɓa idan kika saka mun baki a maganata zan ci uban, wlh wlh wlh idan kika sake saka baki a maganar nan babu uban da ya isa ya dakatar da ni daga sumar dake a cikin gidan nan, sai na yi maki dukan uwar ala tsine, ke sai na yi maki abin da wlh ke da kanki ba zaki iya gane kanki ba, kin san halina bani da full stop idan aka kureni, in dai ba so kike hajiya ta haifi wata Hauwar ba, ki sake saka mun baki shegiya mai kama da kazar mayu".
Juyowa ta yi ta kalli baban Zainab ɗin. "Honey ka tafi masallaci abinka, kada ka dakata kowa, idan an ɗaura auren ka kirani ka sanar da ni". Cewar Hauwa. Ta yi hakan ne kuma dan tana tsoron maman Zainab, tana tson sake yi mata magana, amma tana da bakin yin magana da baban Zainab ɗin kam ai, a ranta kuma ta ƙuduri niyar yau sai an ɗaura auren nan ko dan taga ya maman Zainab zata yi.
Kai Hauwa dai anyi sheɗaniya makirar mace.
Sa kai baban Zainab ɗin ya yi zai wuce ya fita ba tare da ya ce