shi Khadija yake so, kuma ba komai ne yasa ya kafe sai ita yake so ba face surar jikinta, Zainab yanzu take girma, halittar jikinta bai bayyana sosai ba, su tula tula duk basu ciko sosai kamar yadda yake so ba, ita kuma Khadijah sai dai muce Masha Allah, komai ya ciko, abinku da jahili mara ilimi, tula tulanta da shape nata ne kawai suke ɗauke mashi hankali, sune a gabansa, dan ko wayarsa ka karɓa banda hotunan mata masu tula tulanta breast manya manya babu abin da zaka gani, yana sha'awar hakan sosai, ita kuma Khadijah akwaisu sosai, shi ne yasa ya nace dole sai ita yake so, kayan takaici! Dama ace son Allah da annabi yake yi mata ne, da sai ace to da sauki, amma saboda surar jikinta yake sonta kuwa kunga akwai babbar matsala, yana iya mayar da ita karamar bazawara, dan ba hankali ke gare shi ba, mutumin da ko karatun sallah bai gana iyawa ba, sai dai ba bi jam'i a masallaci, ai kunga babu abin da ba zai iya aikatawa ba, dama kuma ba ganin Mahaifiyarta da mutunci yake yi ba, abin dai sai dai mu saka Khadijah a addu'a.
❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥
Zaune suke a parlourn, Maman Zainab kamar kullum ta gama shirya masu abincin darensu a tsakiyar parlourn, sun yi sallar issha suna zaune suna jiran Baban Zainab. Yanzu an kara gyara parlourn sosai, arziki ya ci uban na da, dan baban Zainab mutun ne mai taimako, hakan tasa arzikinsa yake kara bunƙasa sosai.
Zainab tana kallon labarai a kan KINGDOM OF POWER a news, a duniya yarinyar nan tana son wannan masarautar sosai, musamman idan ana magana a kan KING ZUHAIR ABDUL MALIK da ƴaƴansa, abin yana ƙayatar da ita.
Ita kuma Khadijah ta buga uban tagumi tana tunanin maganar da suka yi da Haidar ɗazun a kan cewa wai yanzu yakamata ta rinƙa kai mashi abinci ɗaki ne, bai kamata ya rinƙa zuwa da kansa yana ɗauka ba, dan saura ƴan watannin da basu fi 8 ba su rubuta waec and neco, suna rubutawa kuma sai aurensu, irin shi ya fara jin kansa a angon nan.
To kawai ta amsa mashi da shi, domin idan ta tsaya yin dogon magana da shi ma ko kuma ta ce zata yi mashi gardama, ƙaramin aikinsa ne ya mareta, Mamansu kuma bata da bakin magana, idan ta yi magana to ta jira isowar maman Haidar ɗin da tawagarsu gidan, tsabar bakin ciki wani lokaci ma ji Maman Zainab ɗin take yi kamar ta haɗa kayanta kawai ta bar gidan, amma idan ta tuna cewa idan ta bar gidan dole zata bar su Khadijah ɗin a gidan, ta gudu kenan bata tsira ba, ai gara mata ma ta zauna da su, dan kada ta tafi wani abin ya haɗo Haidar da Khadijah ya zo ya yi masu ba dai'dai ba, dan ba hankali ke gare shi ba.
Wannan dalilin kawai yasa take hakuri ta cigaba da zama cikin takurar wannan balaƴaƴƴar wato Maman Haidar, shi ma baban Zainab sam baya jin daɗin abin, amma yana can yana ta faman neman mafita ta yadda zai lallaɓa mahaifiyarsa ta hakura da zancen auren, su bar Khadija ta kawo mijinta wanda take so, kullum suna cikin zuba addu'a sosai.
Sallamar Aunty Hauwa ce ta katse masu abin da suke yi a in da dukkansu suka kai kallonsu kofar shigowa, amma ban da Khadija da kanta yake kallon ƙasa ta buga uban tagumi, da alama ma bata ji sallamar Aunty Hauwa ɗin ba.
Hannunta ɗauke da manya manyan ledoji ta shigo cikin parlourn. Da murna Maman Zainab ta tarbeta tana faɗin
"Daga ina kuma Hauwa da wannan uban kayan?".
Da yake yanzu Aunty Hauwa fa ta zama dillaliya, saye da sayarwa take yi, har gida mata suke kawo mata kaya irin kamar mace ta yi suna an tara mata atamfofi tana son ta sayar, sai ta kaiwa Aunty Hauwa ta saya da sauki ta bata kuɗin, sannan ta fitar ita kuma ta sayar a sabo, ba abin da bata saya ta kuma sayar, har da su gadaje second hand, su kujeru dukka.
A tsakiyar parlourn ta shirge niki nikin kayan tare da zama a saman sofa tana mayar da numfashi, tamkar ba matar aure ba ta wani yafo ɗan mayafin da ko kafaɗunta basu gama rufewa ba.
"Wlh daga gidan wata dillaliya nake, na je ne nan na kwaso wasu manya manyan zannuwar gado, shi ne na ce bari na kawo maki ko zaki saya". Cewar Aunty Hauwar kenan.
"Kai Hauwa akwai ki da neman magana, ai kin san ni komai baban Zainab ne yake saya mun, kin taɓa ganin na sayi wani abin da kuɗi na ne?".
Girgiza mata kai Aunty Hauwar ta yi alamar a'a bata taɓa gani ba.
"To kin gani, shi ne nan mai sayan komai, zannuwar gado duk bayan wata biyu yana zuwa mana da sabbi daga kasuwa".
Ɗan taɓe baki Aunty Hauwar ta yi kafin ta furta kun ji daɗinku ai.
Murmushi maman Zainab ta yi tare da faɗin. "Gaskiya kam mun ji daɗi, kema ai kina jin daɗi, sai kasuwancinki kike yi kina tare kuɗaɗe".
"Hmmm kasuwanci ko wahala? Yanzu duba fa sai da na fita na je na kwaso kayan nan da kai'na, ke kuma fa? Kina zaune a gida babu in da kike zuwa, baki shan wahalar nema, baki shan rana, sai dai duk abin da kike so ayi maki, ai kinga ni dake akwai banbanci, ku ne masu jin daɗi, Allah dai yasa mu adanshinku".
Kara faɗaɗa murmushinta Maman Zainab ta yi. "Zainab ba zaku gaishe da Aunty Hauwa ba ne? Ki kawo mata ruwan sanyi ta sha".
Ɗan turo baki gaba Zainab ɗin ta yi tare da miƙewa ta nufi wajen fridge, tana yi wa Aunty Hauwar sannu da zuwa. Ruwa mai sanyi roba ɗaya ta ɗauko mata tare da wani kyakkyawar plastic cup. A gabanta ta zo ta ajiye mata, sannan ta juya ta nufi cikin ɗakinsu.
Miƙewa ita ma Khadijah ta yi, ba tare da ta kalli in da Aunty Hauwa ɗin take ba ta yi mata sannu da zuwa kafin ta sa kai ta wuce ɗakinsu.
"Maman Zainab wai menene yake damun Khadijah ne? Yau na ganta wata iriya da ita, sam bata da walwala". Cewar Aunty Hauwar, ta yi maganar kuma tana zuba ruwan da Zainab ta kawo mata a cikin cup dan ta sha.
"Hauwa kenan ke da kin san komai, maganar nan ne dai na aurenta da Haidar, wai ina kika baro su Khalid ne Hauwa?".
Sai da ta sha ruwan da ta zuba a cup ɗin, sannan ta amsa mata da cewa. "Su Khalid suna gidan kakarsu, amma kema maman Zainab wlh da laifinki, yaushe zaki tsaya suna yi maki irin wannan cin kashin? Sai na yi maki magana sai ki ce ai yayyunsa ne ba kannensa ba, to su yayyun nasa idan suka yi ba dai'dai ba ba'a gyara masu zama ne? A ina kika taɓa jin irin wannan? Ki zauna ki yi shiru kina ji kina gani za'a lalata maki rayuwar yarinya, kefa haka kike, tun muna makaranta ma ni nake tare maki faɗa, sai ki yi shiru ki bari kowani kare da doki yana takaki son ransa, ni wlh ba zan ɗauki wannan iskanci ba, shiyasa ma nake kara godewa Allah da ya bani yara dukka maza babu mace a ciki, dan na huta da waɗan na rigingimun". Ta kai karshen maganar alamar ranta ya ɓaci.
"Hauwa ke ba zaki gane bane, wlh ni ba zan iya fito na fito da mahaifiyarsa ba, saboda kinga babban Zainab bai cancanci na yi koda musu ne da mahaifiyarsa ba, shi zaki duba, yana yi mana komai dan ya sanya mu cikin farinciki, a gaskiya ko ba dan ma haka ba ni ba zan iya tsayawa ina fito na fito da mahaifiyarsa ba ko na yi mata rashin kunya, ba zan iya ba, dan uwa uwace ko mai lalacewarta".
Girgiza kai Aunty Hauwar ta yi. "Ai nima ban ce ki yi fito na fito da mahaifiyarsa ba, ita wannan Maman Haidar ɗin zaki gyarawa zama, ita zaki takawa birki, cin kashi ya yi yawa, suna zaginki a kan kin tara masu ƴaƴa mata a goda, ga shi har Yanzu shiru baki sake haihuwa ba sai dai ki ci ki kwanta sai kiɓa kike yi, sannan kuma saboda basu da kunya sai su dawo suna neman auren ƴar taki da kika tara masu a gida wa ɗansu? Kuma duk da suna neman auren ƴar taki ma basu dai'na ci maki mutunci ba? A haka kuma kike tunanin zaki zuba masu ido? Ai wlh basu isa ba, bari zaki yi rana ɗaya idan Maman Haidar ɗin ta zo ta nemi kawo maki rai'nin wayo, a nan ne zaki taka mata birki, ki karta mata jar warning mai zaman kanta, hakan zai sanya ki ɗan huta, haba abin ya yi yawa mana".
Tana magana tana wani kara ɓata rai.
"Hauwa ba zaki gane bane, misali yanzu idan na yi wa maman Haidar magana cikin ɗaga murya ma, wlh to ki jirayi zuwan kakansu, dan sai ta je ta kwashi karya da gaskiya ta gayawa mahaifiyar tasu, ita kuma zata sako hijabi ta zo nan ta ci mutunci na fes, kullum sai ta ce zata sanya baban Zainab ya sake ni, ni kuma a yadda su Zainab suka taso yanzu suke ƙoƙarin zama ƴan'matan nan zamana dasu shi ne mafi a'ala a gareni, a yanzu nisa da su babbar haɗari ne a gareni, kinga yanzu suke tashen girma, yanzu ne suke buƙatar kulawata sosai, dan haka gara na jure na cigaba da hakuri na zauna da babansu har izuwa lokacin da zan kaisu ɗakin mazajensu lafiya, daga nan sai na san abin yi".
Ta kai karshen maganar tamkar zata yi kuka, idanuwanta sun ciko tab da kwallah, abin gwanin ban tausayi, takura sam bashi da daɗi a rayuwar nan.
Aunty Hauwa na ƙoƙarin yin magana suka tsinkayo sallamar baban Zainab ɗin a bakin kofar shigowa parlourn, sun dawo ne daga masallacin sallar issha.
Jin sallamarsa yasa Aunty Hauwar ta miƙe tsaye tana faɗin.
"Zamu karisa maganar idan kin zo gida ko kuma idan na sake zuwa, yanzu dai bari na wuce dare ya yi, kuma kinga unguwar nan taku sai a hankali, kada wani ya bugeni ya kwashe mun kaya".
Tana magana tana tattare kayan nata, haka ta jidesu ta nufi waje. Dai'dai lokacin kuma Baban Zainab ya shigo cikin parlourn.
Kamar yadda kuka sani ne, ko sannu bai ce wa Aunty Hauwar ba, yasa kai zai wuce, dan haka yake.
Cikin sauri ta ɗaga mashi gaisuwa, ya sha dakakkiyar shaddarsa ɗinkin mutunci, yanzu kuɗi sun fara zama mashi zamzam, wani katafaren gini ma yake ta faman gina masu, hawa ɗaya ce gidan, idan ya kammala zasu koma can abinsu, sai dai kash dangi sun sako shi a gaba a kan ya kara aure tun da Maman Zainab taki ta sake haihuwa, Maman Haidar har da wani cewa sun gaji suna son sake ganin yara ƴan dogwai dogwai a gidan. Ɗan adam kenan, ba'a iya mashi.
A takaice ya amsa mata gaisuwar tata tare da sanya kai ya wuce ciki abinsa.
Har bakin kofar gida Maman Zainab ɗin ta rako Aunty Hauwar, yau ma kamar kullum sai da ta bata dubu ɗaya wai ta hau mashi.
Karɓa ta yi tare da zuba mata godiya. Daga haka suka yi sallama, Maman Zainab ta wuce ciki, ita kuma Aunty Hauwar ta nufi waje.
Tana fita Sadiq bawan Allah ya fito daga cikin ɗakinsu ya zo ya rufe kofar gidan tare da kalewa da sakata, sannan ya koma cikin ɗakin nasu.
Haidar sai faman sanya kaya yake yi shi a dole zai fito tsakar gida su yi hira da Khadijah, ita kuma sam bata son yin hira da shi da daddare, dan kullum sai ya rinƙa ƙoƙarin taɓa jikinta, tsabar jahilci sai ya ce ai ita ƙanwarsa ce kuma aurensu ya kusa.
A kule take ce mashi ya bari sai anyi auren tukun nan, haka dai take fama da shi, baiwar Allah, ga shi ta kasa iya gayawa babanta abin da yake yi mata su ɗauki mataki, ta rasa ina zata saka kanta, mamanta ta yi so silent over. Shiyasa wani lokaci shiru shiru ma bashi da daɗi sam.
Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI.
A saman sofa baban Zainab ya zauna yana jiran shigowar maman daga rakiyar Aunty Hauwa da ta yi. Bawan Allah tunaninsa duk yana wajen yadda zai yi da mahaifiyarsa, ga jikin tsufa, idan ka fara yi mata magana duk sai ta bi ta rikice ta ce wai an zageta, haka take yi, ta tsufa sosai, dan a ƴaƴanta Baban Zainab shi ne wajen na shidda, and dukka mata ne ƴaƴan nata shi ne kawai namiji, uku daga ciki sun rasu sun bar mata jikoki tana tare da su, wani lokaci ƴaƴan suna wajen kakarsu ta wajen ubansu kenan, wani lokaci kuma suna wajenta, yanzu daga maman Haidar, sai wata mai bin Maman Haidar ɗin takwarar Zainab, sai babansu Zainab, sune manyan da suka rage, sai kanana mata guda biyu da duk suma sun yi aure suna ɗakin mazajensu, so a takaice dai tsohuwa ce sosai kakar tasu, shi ne yasa take a birkice sosai.
Baki a ɗauke da sallama Maman Zainab ta dawo cikin ɗakin, kusa da shi ta zo ta zauna tana yi mashi sannu da dawowa daga masallaci.
Ƙaƙalo murmushin dole ya yi kafin ya ce. "Ina su Khadijah? And ina kayan da na dawo da shi daga kasuwa?".
"Suna ciki, kayan ma na kai ɗaki".
Ta bashi amsa tana miƙewa tsaye, ɗakinsu Khadijah ɗin ta nufa domin ta kirasu su zo su ci abincin dare.
Da fitowarsu kallo ɗaya baban ya yi wa Khadijah ɗin ya kawar da kallonsa, har ƴar rama ta yi.
A in da suka saba zama a nan suka zauna.
"Khadijah ɗauki abincin su kawu Sadiq ki kai masu". Cewar mamanta, da yake bata san abin da yake faruwa ba, bata san cewa Haidar ɗin yana son keɓewa da Khadijar dan ya rinƙa taɓa mata jiki ba.
Cikin sanyin murya a takaice ta ce. "Zainab ta kai masu pls Mama".
Babansu ne ya amsa da cewa. "Yeah nima abin da zance kenan, Khadija ba zata sake kai masu abinci ba, ita ma Zainab ɗin daga yau idan ta kai masu shikenan, su zo su rinƙa ɗauka da kansu!".
Ya yi maganar ne cikin umarni, babu wasa a tattare da shi, hakan yasa Maman Zainab ɗin ta amsa mashi da to In Sha Allah hakan za'ayi.
Turo baki Zainab ta yi kamar zata sa ihu, dan ita fa a duniya ta tsani zuwa koda kofar ɗakinsu ne, bare ma idan kawu Sadiq baya nan, sai ta ji kamar ta yi ta zunduma ihu idan aka aiketa koda ɗaukar abu ne a cikin ɗakin, bata son ganin Haidar, amma ya zata yi? Dole ta miƙe ta zuro hijabi kafin ta ɗauki ƙatuwar kular abincin tare da plates ta nufi waje da shi.
A bakin kofar ta tsaya ta kaiwa kofar ɗakin kauri da kafa kamar shi ne ya yi mata laifi, yadda kuka san kofar ne ya sakata dole ta kawo abinci.
Daga ta cikin ɗaki Sadiq bawan Allah ya ce. "Zainab ba? Ai nasan sai ke ce zaki buga mana kofa irin haka, to sannu da ƙoƙari ƴar neman rigima......"
Bai gama rufe baki ba Haidar da yake tsaye wajen mirror ya karɓi zancen cikin faɗa da cewa.
"Ai wlh Zainab sai na koya maki hankali a gidan nan, ba ke baki da hankali ba? Yanzu mu sa'anninki ne da zaki zo ba sallama ki hau dukan mana kofa? Bari na same ki a waje sai na sharara maki Marika". On a serious note ya yi maganar.
Murguɗa mashi baki ta yi dan tasan baya ganinta, sannan ta ce. "Kawu Sadiq ga abincinku nan in ji mama".
Har suna haɗa baki shi da Haidar wajen magana, shi Sadiq ya ce ta ajiye a waje bari ya zo ya ɗauka, shi kuma Haidar ya ce to uban waye take so ya zo ya karɓa? Waye sa'anta? Ta kawo ciki ta ajiye.
Banza ta yi da Haidar ɗin kamar bata ji me ya ce ba, dan dama ita Zainab haka take, yadda kuka san me za'a ce ne, ta iya mannin hauka ta mayar da mutane ƴan iska, idan ka yi mata maganar da bai yi mata daɗi ba kuma kana da matsayin da ba zata iya ramawa ba kamar dai yayan nasu, sai ta mayar da kai ɗan iska, ta yi kamar ma bata ji me ka ce ba, kamar ma bata san kana yi ba, idan kuma tasan tana da halin ramawa, to wlh bata barin kota kwana, tsab zata solleka soso da sabulu. Yanzu ma abin da ta yi kenan, ta ajiye abincin a kofar ɗakin tare da murguɗa baki kamar Haidar ɗin yana ganinta, sannan ta watsa masu daƙuwa da yatsunta biyar yadda kuka san suna ganinta, kofar ɗakin ma fa a rufe yake, amma haka ta tsaya tana huce haushinta a waje, abin gwanin ban dariya.
Bayan ta watsa masu dakuwar ma bai yi mata ba, sai da ta dunƙule hannu ta yi alamar zata kai haushi tana wani watso harara da waɗan nan fararen idanuwan nata kamar na mage.
Muryar Haidar ne ya katseta da cewa. "Ke ba zaki kawo mana abincin bane kina tsaye a waje?".