x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 338

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
da kama, mugu yana yin galaba a kan mutun ne ta hanyar suffar tausayi, tabbas akwai masu bukatar a tausaya masu ɗin, amma kuma wake ɗaya yake ɓata gari, tabbas na tsani na ga mutun ya zo mun da suffar ban tausayi, dan haka na yanke hukunci, mu ba zamu taɓa taimakon kowa ba a rayuwarmu, mu kaɗai zamu zauna, ko da kuwa me zai faru!!".

Ta kai karshen maganar tare da miƙewa da nufin ta fice daga cikin ɗakin, da alama ranta ya ɓaci sosai, dan kuwa gabaɗaya yanayin face nata ya sauya.

Dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa. "Mamma but why? Ki gaya mun dalilinki na ji, if the reason is so......".

Katse shi ta yi ta hanyar cewa. "Kamran ni ce nan na haifeka ba kai ka haifeni ba, babu wani dalili, bani da wata dalilin da zan ce maka ga shi da yasa bana son kowa ya raɓemu, kada ka sake jefo mun wata tambayar kuma!!".

Tana kai karshen maganar ta fice daga cikin ɗakin da sauri.

Idan ransa ya yi dubu, to ya ɓaci, meyasa Mammansa take yin hakan ne? Furzar da iska mai zafi daga bakinsa ya yi yana wani huci.

Wani irin dunƙule hannunsa ya yi tare da kaiwa jikin bangon kogon dutsen wani irin naushi. Nan take hannun nasa ta fashe sosai, saboda dutsen yana da masifar karfi.

Sake kaiwa dutsen naushi a karo na biyu ya yi, kuma dukka da wannan hannu da ta fashe a karon farko, ga jini har ya fara malala, jajir jinin nasa, tamkar ba jikinsa bane ba, tamkar baya jin zafi haka ya sake kaiwa dutsen naushi a karo na uku, yana yi yana huci kamar wani kububuwa.

Da gudu Mamma ta dawo cikin ɗakin, a ruɗe take faɗin. "Kamran ka fara halin nan naka ko? Ka bari mana".

Sake dunƙule hannun nasa ya yi a karo na ukun zai kai naushi wa bangon.

A dubu ɗari ta rike hannun nasa tana faɗin. "Ya isa haka mana".

Ƙoƙarin kwace hannun nasa ya fara yi, sai dai ina ya kasa kwacewa. Da hannu ɗaya ta rike shi, amma ya kasa kwacewa, dan Mamma fa jarumar macece ba raguwa ba, akwaita da karfi sosai.

Ganin ba zai iya kwace hannun nasa bane yasa ya yi ƙoƙarin miƙewa ya fice mata daga cikin ɗakin.

Riƙo shi ta yi da kyau tana faɗin. "Haba my son, what's all this meaning for?".
Ta yi maganar cikin sanyin murya.

Sai huci yake yi yaki ya yi magana, ga hannunsa dake ta famar malalar da jini, yatsarsa ta tsakiyar nan ma kamar ta karye ne ko dai ta samu targaɗe, domin kuwa gata ta kumbura suntum.

Rungumarsa Mamman ta yi tana ɗan bubbuga bayansa alamar rarrashi, kamar zata yi kuka take faɗin.

"Kamran wai sai yaushe zaka dai'na wannan halin naka ne? Meyasa kake son ganina a cikin ɓacin rai ne? Meyasa kake damuwa da al'umma? Meyasa kullum akan jama'a muke samun saɓani da kai? Baka taɓa ɓata mun ba, baka taɓa kin bin maganata ba, baka yi mun musu, baka ce mun a'a, komai nace to kawai kake cewa, but why a wannan karon ma a kan jama'a ba zaka ce mun to ba? Why?".

Har wa lokacin bai iya ce mata ko uppan ba, bayan wannan huci da yake yi babu wani abin kuma da yake fitowa daga garesa, ya dai kwantar da kansa shiru a saman shoulder ɗinta, ya lumshe idanuwansa kamar mai jin barci, zuciyarsa ce take tafasa mashi tamkar an ɗaura dalma a wuta, hakan ce ma ta hana shi iya buɗe baki ya yi magana, wannan abin yana mugun damunsa, yana kuma taɓa mashi zuciya, meyasa Mammarsa bata son ya yi taimako? Ga shi dai tana da kyakkyawar zuciya a gare shi, amma kuma ko mutuwa a gabanta wani bare yake yi ba zata taimaka mashi ba, kuma ba zata taɓa bari shi ya taimaka mashi ba, to meyasa? Ga shi shi kuma Allah ya yi shi mutun ne mai bala'in son taimako, baya burin yaga wani bawa a cikin damuwa bai taimaka mashi ba, amma Mamma sam bata son hakan, ko zai yi taimako sai dai y yi a ɓoye kada ta sani, idan ta sani sai sun samu saɓani sosai.

Nasan zaku so jin wanenen KAMRAN, to ku kasa kunne kuji ɗan kaɗan daga cikin labarin wanene shi.

Su dai mazauna wannan dajin ne na tsawon shekaru, kusan ma za'a ce a nan aka haifi Kamran ɗin, su biyu kawai suke yin rayuwarsu, daga shi sai Mamma, suna rayuwa ne cike da so da kaunar juna, Mamma tana bala'in kaunar ɗan nata, Mamma mace ce jaruma mai tafasasshiyar jini, bata da tsoro ko kaɗan, a shekarun baya lokacin da Kamran yake ƙarami har faɗa da damusa ta taɓa yi, Allah ya bata nasara kuma ta kashe damusar, sam bata san menene tsoro ba, bugu da kari mace ce mai magana guda ɗaya, tana da tsayawa a kan maganarta kuma, duk wuya duk daɗi baya sa Mamma ta juya baya a kan abin da ta yi niyya, abin ban mamaki tare da ban sha'awa a rayuwar tasu kuma shi ne, Mamma mace ce mai bala'in ilimi ga tarin baiwa da Allah ya yi mata, duk wasu abubuwan da yake a cikin gidan ita ta kera kayanta, a matakin karatu ko mai degree ba zai nuna mata komai ba, tana karanta da Kamran sosai, a yanzu yana matakin Ss 2 a makarantar tata da dake karantar da shi, yana da ilimi na wuce misali, ga baiwa da ya gada daga wajen Mammar tasa, sai dai kuma yafi Mamma zuciya, duk da take mace jaruma mai zuciya, to wlh ya ninkata, dan idan ransa ya ɓaci kamar yadda kuka ga ya yi yanzu, ya rinƙa buga hannunsa da jikin dutse har ya ji ciwo, to haka yake yi idan ransa ya ɓaci. Dole ce tasa yake yin hakan, domin ba yadda zai yi da Mamma, mahaifiyarsa ce, ko murya bai isa ya ɗaga mata ba, so dole idan ransa ya ɓaci ya nemi mafita, kada ya je ya haɗiyi zuciya ya mutu a banza, ga shi shi mutun ne da bai iya danne zuciyarsa ba, hakan tasa yake yin irin wannan abin na buga hannunsa da dutse ya jiwa kansa ciwo dan ya samu zuciyarsa ta yi sanyi.

(Ba wani a kusa bare ya sauke ɓacin ran a kansa😅 Mamma dai ita kaɗai ce😅 dole nan gani nan bari😅 ba yadda zai yi da ita)

A kowace safiya Mamma da Kamran suna gabatar da training na motsa jiki, a tare suke yin komai, ita ce malamarsa mai koya mashi faɗa, duk wasu dabarun yaki da salon faɗa ta koya mashi, ga shi daman kakkarfar mutun ne shi, sabon jini mai tafasa, hakan yasa Mamma take matuƙar Alfahari da shi.

Wannan shi ne kaɗan daga cikin tarihin Mamma da kuma Kamran. Nasan kuna da tambayoyi da dama a kansu, ni kai'na ina da waɗan nan tambayoyin, dan dole ne rayuwarsu akwai tambayoyi! Amma koma me, lokaci ne zai nuna mana!.

Ta jima a rungume da shi tana jiran zuciyar tasa ta ɗan yi sanyi. Ba ita ta sake shi ba har sai da ta ji ya dai'na wannan hucin, sannan ta sake shi tare da miƙewa ta nufi waje.

Jingina bayansa da jikin ƙogon dutsen ya yi yana sauke numfashi a hankali hankali.

Jim kaɗan Mamma ta dawo hannunta a ɗauke da wani kwando irin na itacen ayaba da ake sakawar nan, kwando ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ƙasashen Arewacin duniya sun fi yawan amfani da ita wajen zuba kayan miya ko kuma fruits.

A in da ta tashi ta koma ta zauna tare da riƙo hannun nasa. Wani farin audiga mai ɗan girma ta fitar daga cikin kwandon, fari tas da shi. Jinin hannun nasa ta fara goge mashi tana yi mashi sannu.

Lumshe idanuwansa ya yi kamar bai ji me ta ce ba.

Bayan ta goge jinin ne ta ɗauko wani purple abu a cikin wani ɗan ƙaramin mazubi wanda ta kyara kayanta da itace, ta yi kamar kwanon sha da marfin, gwanin birgewa, da alama Mamma likita ce.

Wani audiga ta gutsuro tare da ɗan dangwalo wannan purple abin, sannan ta fara goga mashi a wajajen da hannun nasa ta farfashe. Sai sannu take ce mashi, saboda tasan abin akwai bala'in zafi sosai, amma shi kuwa yadda yake zaune tun farko, ko motsawa bai yi ba, kuma bai nuna wata alama da zata nuna cewa ya ji zafin abin ba, ya dai ɗaure fuska tamau kamar hadari.

Bayan ta gama saka mashi wannan abin ne ta mayar da abin cikin kwandon, sannan ta ɗauko wani ɗan ƙaramin audiga tare da wani ganye da ta kwaɓa da wani magani, shima yana cikin wani ɗan mazubi ne wadda ta kyara kayanta.

A gefe guda kusa da ita ta ajiyesu kafin ta riko yatsar nasa da ta kunburar. Duba yatsar ta fara yi dan ta gani karayace ko gocewar ƙashi.

Ta ɗan ɗauki lokaci da a kallah zai kai 5 mins tana ɗan jujjuya yatsar kafin ta saki hannun nasa, sannan ta miƙe ta nufi waje.

Duk abin da take yi mashi yana ji har cikin ransa, amma saboda dakiya da jarumta sam bai nuna alamar kamar yasan tana taɓa shi bama.

Hannunta ɗauke da wani kyakkyawan mazubin ruwa da ta kyara da itace ta dawo cikin ɗakin. Ruwa mai zafi ta ɗebo a cikin wannan mazubin, sai tashin tiririn hayaki ruwan yake yi.

A kusa da shi ta zo ta ajiye ruwan kafin ta wuce wajen ajiye kayansa. Wani ɗan karamin towel na sakar zare ta ɗauko, fari kal towel ɗin.

A in da ta tashi ta koma ta zauna tare da sake riƙo hannun nasa, sai kara kumbura hannun nasa yake yi sosai da sosai, ba karya ya bugu kam.

Ɗan dai'dai tsakiyar yatsar ta riƙo ta fara ɗan jujjuyata daga kasa kafin ta ja da karfi.

Har lokacin bai nuna wani alama ta yana jin abin da take yi ba, saboda tsabar jarumta da juriya, ya dake tamkar bai san ta rike hannun ba.

Bayan ta ja sai ta ɗauki wannan ɗan ƙaramin towel ɗin ta saka shi a cikin ruwan zafi, sai da ya ɗauki zafi sosai, ta sa hannu babu ko tsoro ta ciro towel ɗin, da zafinsa yana tiririn hayaki ta matse ruwan jikin, ko kaɗan ita ma babu alamar tsoro ko jin wani yanayi mara kyau a tattare da ita.

A saman hannun nasa ta kai towel ɗin ta fara ɗabba mashi wajen. Haka ta cigaba da yi har sai da wannan ruwan zafin ya yi sanyi.

Abinku da fararen fata jikin madara, nan take daga ita mai rike towel ɗin da hannunta har shi da ake ɗabbawa hannu dukkansu hannayensu ya yi jajir tamkar ya tara jini ne a wajen, sai dai duk da haka babu alamar kamar sun ji zafi ko wani raɗaɗi a saman face nasu.

Wani irin mai mai sanyaya ciwo ta shafa mashi. Har cikin ransa ya ji sanyi sosai, bandeji ta ɗauko ta ɗaure mashi hannun nasa.

Har lokacin kuma bai buɗe idanuwansa ba, yana dai ji ta gama mashi komai tsab, sannan ta miƙe tare da ɗaukar kayayyakin da ta shigo dasu dukka ta fitar da su.

Tana fita ya gyara ya kwanta a saman bed ɗin nasa tare da ɗaura hannunsa guda a saman face nasa yana tunanin maman twins ɗin nan, shi dai har ga Allah matar ta shiga ransa, kuma ya kuduri niyar koda Mamma bata so sai ya rinƙa taimakawa matar a ɓoye, dan shi yana da tausayi sosai, yana da zafin zuciya da kuma faɗa sosai kamar Mamma ɗin tasa, sai dai kuma akwai shi da tausayi da son taimakawa jama'a.


*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*

🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥


🔥💔𝑨 𝒕𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝒉𝒆𝒂𝒓𝒕𝒔 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒔𝒕𝒐𝒓𝒚, 𝒅𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚 𝒐𝒃𝒔𝒕𝒂𝒄𝒍𝒆, 𝒂𝒏𝒅 𝒓𝒐𝒎𝒂𝒏𝒄𝒆💔🔥



𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)






🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 1/7/2024.....✍️📚🌹






🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








E____________4🔥







*DOMIN NEMAN KARIN BAYANI KU NEMENI TA WANNAN NUMBER 08161390581*






Jim kaɗan Mamma ta dawo cikin ɗakin hannunta ɗauke da wani kyakkywar mazubi da suke zuba abinci, tamkar plastic plat haka ta kera kayanta, Mamma ba dai basira ba, daga kanta an rufe kofa, jajirtattiyar mace ce, hazika mai kaifin basira da ƙwaƙwalwa, ga tafasasshen jini na jarumta tamkar wata ƴar commander mayaka.

Sai tashin tiriri abincin nata yake yi, ya sha kayan kamshi na ganyayyaki masu inganci da karawa jiki lafiya, komai nasu fresh ne, dan komai na cikin wannan daji babu busasshen, ɗanyu ne, su corry leaf, carrots, green beans, peas, eggplant, spinach, cabbage, cucumber, tamator da dai sauransu, komai nasu fresh ne, hakan yasa abincinsu yana da matuƙar kyan gani a idanu ga kuma ɗanɗano mai daɗi a baki, akwai wani ɓangare daga cikin dajin in da Kamran ɗin yake ɗebo masu gishiri, basu da maggi, saboda kowa yasan a wannan dajin dai babu in da zasu samo maggi, amma kuma a cikin gayyayyakin da suke amfani dasu da akwai waɗan da suka fi maggi ɗanɗano mai daɗi, hakan yasa abincinsu yake da ɗanɗano na musamman, sannan dama already su basu san menene maggi ba, dan kunga a wannan daji suka taso, so ɗanɗanon da suka saba da shi tun farko, basu da wani sama da shi.

A saman katakon ta ɗaura plate na abincin, da akwai wani kyakkyawar cup mai ɗauke da wani irin red tea, shayi ne da ya ji gayyayyaki masu kara lafiya da inganci, ganyen shayin nasu ne yake red color tamkar ganyen shayin da jama'ar Arewacin duniya suke amfani da su. Ga wani gasasshen nama da yake ta tashin tiriri da kamshi, namar nan ta gasu sosai, dan sai da ta sanya yawuna ya tsinke.

Suna da wadatatcen nama sosai a gidan nasu, domin Kamran jarumin namiji ne sadauki kuma mafarauci, shi yake farauto masu nama duk bayan kwana biyu, sai mamma ta dafa ta kuma soya da man namar, idan tana so kuma tana iya ajiye ɗanyen ta hanyar saƙala shi a jikin wasu itatuwa wadda ta dasasu a cikin madafinta, wato in da take girki kenan, kasancewar a koda yaushe tana cikin yin girki yasa wannan nama da take ajiyewa baya yin komai, sai dai baya wuce kwana ɗaya suke yin amfani da shi, dan in ya wuce haka zai lalace.

Haƙiƙa rayuwarsu gwanin birgewa ne, musamman yadda suke da kayayyakin ci na morewa, ga fresh fruits ɗin nan kala kala, wata fruit ɗin ma sai dai ka ganta amma baka san suna ba, saboda ba a ko'ina aka cika samunta ba, mafita yawancin abubuwan da suke cikin wannan dajin, abubuwa ne da yafi yawaita ta ɓangaren Arewacin duniya, so ba'a ko'ina ake samunsu ba. Wannan cima mai kyau da suke samu ne yasa jikinsu yake da bala'in kyau, sai ka gansu kamar waɗan da suke rayuwa a wani hamshakin Daula mai cike da kayan more rayuwa, ka gansu wasu luwai luwai da su gwanin ban sha'awa.

A kusa da shi ta zo ta ajiye wannan kayan abinci da ta ɗebo kafin ta zauna a gefensa.

Cikin wannan sanyayyar muryar tasu ta fara ambatar sunansa a hankali hankali.

Kasa kasa kamar mai ciwon baki ya amsa mata ba tare da ya buɗe idanuwansa ko kuma ya ɗago kai ba.

"Stand up and eat your food".

Ta faɗa tana ƙoƙarin cire mashi kyakkyawar hular sakar da yake a kansa, dan ta kallah yana haɗa zufa, da alama hannun nasa ne ta fara jiƙa yasa yake wannan uban zufar, kowa dai yasan yadda gocewar ƙashi take, koba ki taɓa yi ba nasan kin taɓa jin labari, zafin bala'i ke gare shi, kawai dauriyar bala'i da taurin zuciya ce gare shi yasa bai nuna alamar kamar yana jin wani abu da ya danganci zafi ko ciwo ba.

"Mamma i can't eat anything now, i want to sleep, because am feeling sleeping".

Ya bata amsa can kasan maƙoshinsa.

Nisawa ta yi tare da miƙewa ta fice daga cikin ɗakin ba tare da ta ɗauki kayan abincin ba, ta bar mashi su a wajen, da alama kuma ranta ya ɓaci.

Fita daga cikin kogon mai gabaɗaya ta yi, a saman tsaunin ta zauna saman wata dutse tare da buga uban tagumi tamkar mai tunanin wani abin.
Daga yanayinta alamu sun nuna tana a cikin damuwa, dan face nata gabaɗaya ya canza, jikinta ya yi sanyi, tamkar ba ita ba, da alamu Kamran ya taɓo mata wani part da bata da buƙata ne a rayuwarta.

Ta yi nisa cikin duniyar tunanin data lula, tamkar daga sama ta ji an kwanto a saman bayanta, ya kuma zuro kyawawan fararen hannayen nan nasa ta saman wuyarta yana sauke numfashi a hankali hankali.

Shiru ta yi bata motsa ba kuma bata ce mashi ko uppan ba.

"Am so so sorry Mamma". Ya faɗa in a low voice.

"Sorry for what Kamran?".
Ta yi maganar tare da kai hannunta tana shafa hannayen nasa da ya zuro mata ta saman wuyar tata.

"I knew kin ji babu daɗi, kiyi hakuri my Mamma".

Juyowa ta yi ta rungumesa tana faɗin.

"Is okey my son, ni ban ji babu daɗi ba, kuma bana fatan wata rana ta zo wanda zaka sa naji babu daɗi, kai ɗin ɗan albarka ne, a ko'ina kake kana tare da albarkata, yanzu je ka ɗauko abinci kazo mu ci".

Manna mata sumbata a lallausan kumatunta ya yi kafin ya miƙe ya nufi cikin gidan nasu, dan gidansu za'a ce tun da a nan suke rayuwarsu, kuma rayuwa ce kamar kowa suke yinta, sun fi wasu masu rayuwa a cikin gari ma jin daɗi da ƴanci, dan su babu ruwansu da
End Ads