x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 337

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ya rungumosu sosai a jikinsa.

Ƙasan wata katuwar bishiyar mangoro ya je ya kwantar da baby's ɗin, Allah sarki wannan baby mai tsallara ihun shi ma ya yi shiru a yanzu, da alama dama sanyin ruwan saman nan ne tasa yake wannan uban kuka haka, shi kuma ɗayan dai shiru bai motsa ba har wa yau.

Ganyen bishiyar manya manyan ya karyo tare da shunfuɗawa a ƙasa kamar katifa, sannan ya ɗaura baby's ɗin a kai, ya kuma karyo wasu ganye ya rufa masu a saman kayan nasa da ya kudundunesu.

Da sauri ya juya ya koma wajen ramin, a lokacin ita kuma matar ta yi iya ka bakin ƙoƙarinta ta maida kayanta jikinta da ta cire, ta duka tamkar mai yin ruku'e daga zaune tana ƙoƙarin laluɓar sarkokinta da sauran abubuwanta a cikin ruwan, da alama abubuwan suna da matuƙar muhimmanci sosai kasancewarsu a tattare da ita, shiyasa take ta ƙoƙarin laluɓarsu a cikin ruwan.

Yana zuwa ya yi mata magana a kan ta kawo hannunta bari ya fito da ita, ya yi maganar ce da wata harshe na daban, hakan yana nufin yana da yare a bakinsa kenan.

Ɗagowa ta yi daga sunkuyen da take, sam bata san me ya faɗa ba, saboda bata jin yarensa, kura mashi idanu kawai ta yi tana kallonsa, sai da ta ga ya miƙo mata hannunsa ne yasa ta gane abin da yake nufi kenan.

Kin miƙa mashi hannunta ta yi, saboda wani dalili nata da bata bayyana ba. Sake yi mata magana ya yi a kan ta kawo hannunta ruwan nan yana karuwa ne. Nan ma bin shi da idanu kawai ta yi, dan bata gane ko kalma ɗaya da ya faɗa ba.

Da yaga hakan, sai ya miƙe ya nufi wajen manyan itatuwa dake wajen, zabgegiyar itaciya ɗanya shakaf ya karyo, sannan ya dawo bakin ramin.

Zura mata itaciyar ya yi a cikin ramin. Ba musu ta kama itaciyar shi kuma ya ja, da kyar ya iya fitar da ita, alamu sun nuna hannunta ne bata son ya taɓa, kome dalili? Mu je dai zuwa, koma menene zamu ji.

A bakin ramin ta zauna tare da dafe cikinta tana numfashi da kyar da kyar kamar zata mutu. Tsugunnawa a kusa da ita ta gabanta ya yi yana tambayarta meyake damunta?.

Sam bata jin yaren da yake yi mata, bata gane komai ba.

Ganin bata bashi amsa bane yasa ya fahimci bata jin yarensa ne, dan haka sai ya ce mata "Are you hearing English?". Ya yi maganar a hankali, yana da sayayyar murya sosai.

Da sauri ta gyaɗa mashi kai alamar tana ji, tana ciza laɓɓanta saboda azabar da take ji.

"Okey what i said here is what's wrong with you? Is there any problem?". Ya yi maganar cikin sanyin murya sosai, kuma daga yanayinsa ya nuna shi mutun ne da sam sam bai da yawan magana, so silent yake, face nasa ta nuna ba mutun ne mai son hayaniya ba.

Da hannu ta nuna mashi cikinta dake ta faman zubar da jini.

Kai kallonsa wajen da take nuna mashi ɗin ya yi. A dubu ya zaro waɗan nan dara daran fararen idanuwan nasa yana kallon yadda kifiyar ta soketa, sam bai lura ba time da ya jawota ta fito daga cikin ramin.

Hannu ya kai zai taɓa wajen, cikin sauri ta ɗan ja baya, hakan yasa ya ce mata to ta lallaɓa su je wajen da ya kwantar mata da yaranta, bari ya ciro ganye ya yi mata rumfa da shi, sannan sai ya kawo mata maganin kifiya.

Kasa tashi ta yi, duk wasu gaɓɓai a jikinta sunki bata haɗin kai wajen ta ɗan miƙe, duk sun galabaita, hakan yasa ta fara ja a kasan kawai. Da kyar da suɗin goshi suka isa wajen.

Tana zuwa wajen ta kwanta tare da sake dukkanin ilahirin jikinta ta bi lafiyar kasa tana mai da numfashi.

Kamar yanda ya faɗa, ganyayyaki dayawa haɗe da itacuwa ya karyo, ya zo ya yi masu rumfa kamar ɗakin bukka, da alama ya jima a wannan dajin, dan ga dukkan alamu yasan duk wasu dabaru na zaman daji ta yadda wata dabba bazata cutar da mazaunan wajen ba.

Yana ƙoƙarin yi mata magana kamar saukar aradu wata zazzaƙar murya mai sautin amo mai matuƙar daɗi ta karaɗe kewayen wajen da faɗin "KAMRAN! KAMRAN where are you". Muryar ta kasance muryar mace ce mai zaƙi.

Da sauri ya wuce yana mai buɗe muryarsa shi ma da karfi yana faɗin "Here I am, one minute am coming".

Daga haka ba'a sake yin magana ba, shi ma bai sake yin magana ba ya yi maza ya kutsa ta cikin wasu dogayen bishiyoyin ɓaure dake fuskantar gabas.

Ita kuwa wannan mata tun da ta kwanta ta lumshe idanu, bata sake motsawa ba, suma baby's ɗin nata basu sake motsawa ba, shi ma mai tsallara kuka ɗazun ya yi shiru, da alama ya yi barci ne, ko kuma dai wani abin, amma fa ɗayan babyn nan sam bai motsa ba, da alama dai babu rai ɗin ne da gaske a tattare da shi.

Haka har ruwan saman nan ya ɗauke, gari ta washe, ta yi shar shar, amma har yanzu daga baby's har maman baby's babu wanda ya sake motsawa a cikinsu, shi kuma wadda ya taimaka masu, wato wadda aka kira da KAMRAN, har yanzu bai sake dawowa wajen ba, tun da ya tafi shiru kake ji.

After some hours. A hankali maman baby's ɗin ta fara motsawa, gabaɗaya jikinta ya yi mata wani irin muguwar nauyi, da kyar ta iya waro idanuwanta da suke kunbure sun yi luhu luhu, saboda azaba da ta sha.

Tana waro idanuwanta kai tsaye sai a saman ganyayyakin da KAMRAN ya yi masu rumfa kamar bukka, a lokacin ruwan sama ta ɗauke cak, gari har ta ɗan fara yin haske.

A hankali tamkar mai jin tsoron wani abin ta kai hannunta ɗaya a saman cikinta in da kifiyar nan ta caketa, ga mamakinta sai ta ji wajen a ɗaure, tamkar an sanya abune an ɗaure mata, kara waro idanuwanta sosai waje ta yi, dan ta tabbatar wa da kanta ba mafarki take yi ba.

Tabbas ba mafarki bane, magani aka sanya mata a wajen, sannan aka ɗaure mata wajen da wata farar kyakkyawar kyalle mai matukar kyan gaske, shi ma kyallen ta sakar audiga ce, kuma sakar hannu ce, kamar dai kayan jikin KAMRAN. Da yake akwai sauran jini dake fitowa kaɗan kaɗan a wajen, sai ta ɓata wannan farar kyalle da aka sanya mata, kyallen ta yi ja ta ɓaci da jinin.

Yunƙurawa ta yi domin ta mike, sai dai ina, ko motsawa ba zata iya yi ba, gabaɗaya gaɓɓan jikinta sun yi la'asar over, sun yi laushi, ga wani irin azababben ciwo da take ji a ko'ina a jikinta, mararta ma ciwo yake yi mata.

Ganin ba zata iya miƙewa bane yasa ta hakura ta kwanta shiru tare da ɗan juyo da kanta gefen da yaranta suke kwance, dan ta kalli shin a ina suke ne?.

Sun kasance ne a cikin wani ɗaki kamar bukka wanda aka saƙa shi da ganye and itace, kamar dai bukkar rugar Fulani, sai dai wannan ya sha banban da bukkar ruga, domin sakar ma ba iri ɗaya bace, wannan daban take, kwararrun masu fikira ne suka saƙa shi.

Ga wasu kwarya masu kyau da ɗaukar hankali a kusa da ita, anyiwa kwaryar zanen kwalliya mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, baby's nata suna kudundune a cikin wani kyakkyawan towels farare kal kal da aka saƙa da audiga, ga kuma wani katon kasko irin na taɓo da ake yin nan, an cika kaskon da garwashin wuta a cikinsa, wutar ta yi jajir, hakan yasa gabaɗaya wajen ya ɗauki ɗimi, kamar ba yanzu aka gama sharara ruwan sama mai uban sanyi ba, da alama suma baby's ɗin wannan ɗimin yasa suka yi shiru suna barci, dama shi ɗayan baby already kunsan bai motsa ba tun da aka haifesu.

Daga gefen baby's ɗin kuma wasu kyawawan towels na sakar ce guda biyu da aka ajiye masu bacin wanda aka lulluɓesu da shi, sannan da alama an yi wa baby's ɗin wanka ko kuma dai an goge masu jiki, kuma an yanke masu cibiya.

To fa waye kuma ya yi masu dukka wannan hidimar?.

Da kyar ta iya motsa hannunta ta ɗan buɗe baby guda ɗaya. Kara waro idanuwanta waje sosai ta yi, mamaki ne ya lulluɓeta na ganin anyankewa babyn cibiya, ga jikinsu babu datti ko kaɗan, duk da cewa dama already ruwan sama ya taɓasu.

Zuba masu idanu ta yi da mamaki fal a cike a cikin ranta, da alama ba ita kaɗai aka yi wa magani ba, har da baby's ɗin aka yi wa magani, dan kuwa ga jikinsu nan duk an murje masu ganye, sun yi kore shar, ganyen magani kuma irin na cikin wannan kwarya da yake a kusa da ita ɗin ne.

Jin yanda wajen yake da ɗimi duk da ruwan saman da aka yi ne yasa ta fara jujjuya idanuwanta tana bin ko'ina da kallo daga kwance, ta yi mamakin jin wannan daddaɗar ɗimin a wajen, sai dai bata iya hango kaskon wutar, saboda yana ta wajajen kafafunta ta kofar bukkar ne, kallonta ba zai iya kaiwa can ba daga kwance, sai ta miƙe.

A hankali ta lumshe idanuwanta tana mai tsananta godiyarta ga Allah a cikin zuciyarta, yau Allah ya ceceta ita da baby's ɗinta, koma waye ya yi mata wannan hidima ta sanya wa ranta cewa bawan Allah ne from nowhere Allah ya aiko masu.

To bari mu kutsa cikin dajin, dan muga menene a cikinta, wata kila kafin mu dawo Maman ƴan biyu ta kara samun sauki.

Kamar dai yadda kuka sani ne, daji ne mai matuƙar girman gaske wanda kallon iyakarsa ma ba abu bane mai yiwu wa sam sam, sannan akwai haɗari sosai a cikinsa, sai dai haɗarin ta wasu ɓangarori daga cikin dajin ne yake, ba dukka ko'ina bane, muggan namun dawan ba'a ko'ina suke zama ba, suna da ɓangarorin da suke zama a cikin dajin, already kunsa kowani dabba da irin wajen da yake yin rayuwa, ko a daji ba'a ko'ina suke zama ba, sai wajen da ya yi dai'dai da rayuwarsu.

Saman wani katafaren tsauni, a hankali wani hayaki yake tashi daga wajen, da alama akwai mutane a wajen, saboda su dai namun dawa basu shiri da wuta bare hayaki, sam basu so, basu zama ma a wajen da aka kunna wuta, sai dai idan ɗauresu a wajen aka yi babu yadda zasu yi, amma basu son wuta ko ya take.

Sannu a hankali wannan yanaki yake fitowa, kuma bashi da yawa, sannan hayaki ne mai haske ba irin bakin hayakin nan ba, wannan tsauni yana nesa daga in da maman waɗan nan ƴan biyun take, sai dai idan ka tsaya a samanta ka yi magana da karfi, to duk wanda yake kewayen wannan yanki zai jika, saboda dajin tana amsakuwa.

Dai'dai tsakiyar saman wannan tsauni ta gabas ta sakiya, wani jibgegen dutse ne a wajen, yana da girma da kuma faɗi, sannan yana nan tamkar kogo, dan yana da zurfi da faɗi cikinsa, daga ta cikinsa wannan hayaki yake fitowa, kofar shiga cikinsa kuwa, ɗan ƙaramin ne wanda babban abu ba zai iya shiga ba, idan ɗan Adam ya cika ƙiba sosai, to ba zai iya wucewa ta kofar ba, dan bata da girma, sannan akwai wata ƙaramar dutse mai kauri da ake rufe ɗan bakin kogon da shi, alama dai ya nuna wannan ƙaramin dutsen shi ne kofar kogon.

Tamkar gida haka cikin wannan kogon yake, an yi ciki da parlour da wani ɗaki na daban, duk kuma jinin anyisu ne da taɓo, ma'ana an gine cikin kogon, kasancewar yana da girma sosai cikin kogon, sai ya bada abin da ake so, ginin nasu kuma ya fita sosai, duk da cewa da taɓo suka yi shi, ga kuma itatuwan bambu da suka yi amfani da su wajen kawata kujerun zama na saka, tamkar gado haka suka yi kujerun zamar, ma'ana babu Head na kujerun, iya wajen zama ne kawai, haka zalika beds dake a cikin bedrooms guda biyun, dukka da itacen bambu da kuma ganyen ciyawa mai kyau aka yi su, shi ainahin gadon anyi shi da itacen, katifa kuma da ciyawan harawa, sai dai ya saƙu da kyau da kyau ba karya, ya yi matuƙar kyau kuma, an shinfiɗe bed's ɗin da bedsheet na sakar audiga ta hannu, kunsan sakar hannu da masifar kyau, ga shi bedsheet ɗin an yi mai two color, sai abin ya kawata idanuwar mai kallo sosai, ga ɗaukar hankali, wasu kyawawan smalls pillows ne jere a saman beds ɗin dukka ɗakuna biyun, suma pillows ɗin suna sanye ne a cikin rigarsu irin kalar bedsheet ɗin, sun kara kawata beds ɗin sosai.

Komai da yake a cikin wannan kogo da itacen bambu da kuma taɓo aka kyara su, tukunyaye da kaskon wuta duk na taɓo ne, da alama makyarin waɗan nan abubuwa mutun ne mai kaifin basira da ƙwaƙwalwa sosai, dan harda kwanon cin abinci da aka yi da itace, ga su cups, tamkar kowani gida dai, haka suke, harda yi wa kwanikan nasu design kala kala da wani jar kala, sun kuma yi bala'in kyau ba kaɗan ba.

Ƙasar wannan kogon kuwa ya kasance itacen bambu ne suka yi shi kamar tiles, ya kawata wajen sosai, abin da zai kara burgeku da wannan gida nasu shi ne, yadda ya kasance kowane kofar ɗaki da labulen da aka saka da audiga, very talented people's ne suke zaune a wannan waje, dan komai dake wajen basira ce ziryan ta yi aiki a kansa ba kaɗan ba, da akwai ramuka da suka ɗan huhhuda, saboda samun haske da kuma iska a cikin ƙogan, ramukan suna da yawa, amma basu da girma, kanana aka hudasu, kuma haske da iska suna shiga sosai, dan kunsan shi iska baya rena hanyar wucewa, abin kara ɗaukar hankali ma cikin wannan gida shi ne, harda dining table suke da shi a parlourn nasu, dining ɗin shi ma da itacen bambu suka yi shi, ya saku sosai, ya yi matuƙar kawata wajen sosai da sosai.

Ko'ina tsab yake tamkar babu kowa da yake amfani da wajen, sai kamshin kayan itatuwa da yake tashi a wajen.

Kwance a saman ƴar kyakkyawar bed nasa KAMRAN yake, a nasa bedroom ɗin kenan, hannunsa na rike da wani littafi mai matuƙar kyau yana karantawa, da alama littafin tarihi ne, sam ba kayan ɗazun bane a jikinsa, ya canza izuwa wasu masu kyau, suma dukka na tsakar audigan ne, still da akwai hular sanyi a kansa, kyakyawar fuskar nan tasa sai glowing take yi, tamkar ya shafa baby oil, sai ya kara wani irin kyau abinsa.

A zahiri idan ka kalle shi karatun littafin yake yi, amma kuma baɗininsa ba ita yake yi ba, ya rike littafin ne kawai, hankalinsa yana can wani wajen.

"Kamran the food is ready, am waiting for you".
Wannan zazzaƙar murya ta ɗazun da ta kira shi ne time da yake wajen maman ƴan biyu, ita ce ta sake yin wannan magana a yanzu.

"Mamma am okey, I can't eat anything today". Ya faɗa yana ɗaure fuska, tamkar Mamman tasa tana a gabansa.

A hanzarce aka yaye labulen dake kofar bedroom ɗin nasa aka shigo. Kyakkyawar mace ce kyakkyawar gaske, doguwa sosai, gata ƴar caras cas, fara kal da ita kamar madara, launin fatarta ya banbanta da tasa sosai, saboda ta fishi haske nesa ba kusa ba, ga hanci har baka, da gani ba tambaya kasan mahaifiyarsa ce, saboda tsananin kamanceceniya da take a saman fuskokinsu, itama idanuwanta dara dara farare kal da su, sai dai ita kwayar idanuwanta ba baki irin nasa bane ba, ya ɗan yi brown mai haske, sai ya yi kamar foreign tiger eyes, tana da tsananin kyau da abin da ake cewa farin jini, da ganinta ba tambaya kasan jarumace sosai, dan kuwa waɗan nan idanuwan nata babu alamar tsoro ko miskala zarratin a tattare da ita, macece mai kamar maza, jarumar gaske, da alama a wajenta ya gaji jarumta.

Ita ma tana sanye da doguwar riga ta saka launin white color mai matuƙar kyau.

"Kamran what are you saying? You can't eat anything today? why?".

Ta faɗa a ruɗe, tana magana dimple nata suna lotsawa, ga dimple ɗin nata gwanin ban sha'awa, dan bai yi irin zurfin nan sosai ba, ɗan daidai mai ɗaukar hankali. Tana da sayayyar murya irin tasa, da ga ji maganarta kasan a wajenta ya gado cool voice.

"Mamma yes i can't eat anything today until you tell me the reason why you don't like people? Why you don't want me to go out? Everyday you're try to hidden our life, ni gaskiya am tied, kuma ni ina son in taimaki mutane, meyasa ke baki so? Haka last time wancan mutumin da Tiger can ta cinye, kika ki yarda mu taimaka mashi, muna ji muna gani wannan bakar damusa ta hallaka shi har lahira, why?".

Ya kai karshen maganar tare da miƙewa zaune yana mai rufe littafin da yake a hannunsa, ya ajiye a saman waɗan nan kananan pillows ɗin.

Ƙarisowa cikin ɗakin ta yi, jiki a sanyaye ta zauna a saman bed ɗin, hannu ta kai ta fara shafa lallausan kumatunsa da yake kamar ta jarirai saboda laushi.

A nutse ta fara magana. "Kamran you know that i can't do something to hot you or na takurawa rayuwarka ko? Duk abin da zan yi i can do it because of your happiness ne my son, mutane ba abin yarda bane, don't trust anyone in your life, just trust yourself only".

"Amma kuma Mamma wasu mutanen ai ba mugaye bane ba, wannan mata da na gaya maki fa wlh she's...........".

Katse mashi maganar tasa ta yi ta hanyar ɗaga mashi hannu.

"Kamran! Kowani mutun da kake gani a rayuwar nan to wlh ba abin yarda bane, suffar tausayi ita ce suffa mafi haɗari a duniya, wanda kuma ni ba zan taɓa yarda da ita ba, duk wanda zai zo mun da fuskar tausayi dan na tausaya mashi, ba zan taɓa yarda da hakan ba".

"Mamma koda kuwa da gaske yake yi yana da bukatar taimakon ki?".

Ɗaure fuska sosai ta yi kafin ta ce. "Yes Kamran, ina son ka sani shi fa mugu bashi
End Ads