x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 82 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 243001 words
  • 246000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 401

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
da kunya ko kaɗan, kuma idan baku manta ba tun suna yara Zainab ɗin tafi kowa tsanar Hauwar, bata son ganinta ko su haɗa hanya, bare kuma yanzu da ta ji abubuwan da suka faru, mamansu ta gaya masu komai bata ɓoye masu ba, dan gudun kada su aikata irin kuskuren da ita ma ta aikata, hakan yasa ta sanar da su, so sun san komai, shiyasa Zainab ta kara tsanar Hauwar over ta kuma ɗaura ɗamarar yi mata rashin mutunci idan ta shiga gonarta. Kawai cakwakiya kam.

Girgiza kai Hauwar ta yi ba tare da ta sake yin magana ba, da alama akwai abin da zata ƙullawa Zainab ɗin kenan.

In short haka Maman Zainab ba musu ta ɗauko mayafinta tare da sanya su Khadija suka ɗauko nasu mayafan domin su tafi, abin da yasa zata je sabon gidan kuma domin su gwabza ne, a cewarta yanzu ta dai'na yin shiru, duk uban da ya ce mata kule sai ta ce mashi cas, sannan kuma tasan tun da Hauwar ta zo ta ce su tafi to fa ko ta ce ba zata je ba baban Zainab zai ce lallai dole ta shirya su tafi, ga shi mamanta ta hanata sake yi mashi musu a kan abu, so gara kawai kada ta yi wani ja in ja ta kara zubar da mutuncinta a gaban Hauwar, dan tasan a yanzu idan ta yi ja in ja da baban Zainab ma yana iya saka mata hannu ya kai mata duka, kunga kuma ai mutuncinta ya kara zubewa a idon Hauwar, dan haka gara mata kawai ta bisu, ta nunawa Hauwar ita ma a shirye take da su je sabon gidan ai. E lallai yanzu kam maman Zainab ta shirya gwabza faɗar domin kwatar ƴancinta.

Suna fita daga gidan ba jimawa sai ga su maman Haidar sun zo, dan sun sami labarin yau ya zo gida. Sai dai ko da suka zo kofar gidan a rufe, already su baban Zainab ɗin sun tafi, baban Zainab ya sayi sabuwar mota ba tare da sanin ƴan uwansa ba, Hauwa ce nan ta sanya shi ya sayi motar wai dan ya koya mata, idan ta iya sai ya bar mata kyauta, aikuwa ya saya kuma yana ɗan koya mata a hankali hankali, so a yanzu da motar suka zo suka ɗauki su maman Zainab, Hauwa an dake a kujerar gaba, sam maman Zainab bata nuna kamar ta wani damu ba, ta shiga gidan baya a tare da Zainab da Khadija.

Su maman Haidar kuwa ganin gidan a rufe yasa suka juya suka nufi kasuwa ita da maman Hanif, a tunaninsu zasu same shi a kasuwa, ba a tare da hajiyarsu suke ba yau, Hajiyar tasu ta ce idan sun gan shi su ce yazo tana son ganinsa, shi ne ma yasa suka zo nemansa.

To bari mu leƙa kasar TUNISIA, wato KINGDOM OF POWER muga me ake ciki.

KINGDOM OF POWER. 💪🔥❤️

Yau ta kasance ranar jumma'a, kuma a yau su Obaid jirginsu ya ɗaga zuwa Dubai kamar yadda King ya bada umurnin komar tasu, sai dai fa jirgin nasu bai ɗaga da wuri ba, jirgin karfe 6 na safe zasu bi, amma saboda abin da ya faru a cikin kingdom ɗin yasa suka bi jirgin 11 na rana, shi ma dai da kyar suka tafi ɗin, sai da Jaish ya kaisu airport da kansa, domin yau kingdom babu lafiya, ɗaya daga cikin matan king bata da lafiya, hankalin kowa a tashe ban da Jaish da shi ko a jikinsa, ba abin da ya damesa tun da ba mommarsa bace abin ya shafa, shiyasa ma ya iya raka su Obaid airport hankalinsa a kwance, shi ma Yah Jawad bai wani damu sosai ba, ya dai ji babu daɗi, ita kuma Mammaien Yah Jawad ɗin har wani farinciki da rashin lafiyar na mama ta yi............. To me ya sami mama kuma?🤔

King kuwa yana.............


🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)






🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 3/9/2024.....✍️📚🌹




For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️






E____________44🔥




KINGDOM OF POWER. 💪🔥❤️


King kuwa yana room ɗin na mamar, saboda ya duba jikin nata, hankalin kowa a cikin kingdom ɗin nan a tashe, kowa sai tunani yake yi a kan me ya sami ɗaya daga cikin matan King ɗin, bayani kuma bai fita a kan me ya sameta ɗin ba, an dai sanar da cewa bata da lafiya. Abin da yasa aka sanar da cewa bata da lafiyar ma shi ne, kingdom of power tana da wata gasa da take gabatarwa na dawakai a kowani jumma'a, kowacce sati suna gabatar da wannan gasa na tseren dawakai wanda jaruman mayaka zasu fito a gabza gasar, wanda ya yi nasar zuwa na ɗaya yana da gagarumin kyauta daga hannun King, daga ɗaya zuwa na goma ake bawa kyauta, ana gabatar da gasar ne domin nishaɗi. A gabaɗaya tarihin kingdom of power ba'a taɓa yin jarumin mayaki biyun HOORAIN ba, shi ne a kullum yake zuwa na ɗaya, kuma kowani sati sai ya shiga wannan gasa, na gaya maku shi ɗin abin alfaharin KINGDOM OF POWER ne, suna ji da shi, haka zali babu yakin da za'a tafi ba tare da shi da commander ne suka ja ragamar rundunar mayakan ba, kuma ko ciwo Hoorain bai taɓa ji a wani yaki da suke zuwa ba, gara commander ya taɓa jin ciwon da sai da ya kwanta jinya, saboda jikin tsufa ya sha wahala sosai, shi kuwa Hoorain sabon jini ne, jininsa a tafashe yake, lafiya lou yake jan ragamar rundunar sadaukan yaki sama da dubu biyar ya jagorancesu su je yaki su dawo, basu taɓa fita yaki basu yi nasara ba, duk girman daula in dai Hoorain da Commander suka jagoranci rundunar mayakan to fa sai sun jijjige wannan daula sun jefar da ita, basu gudu kuma basu ja da baya a fagen yaki komai tsanani kuwa.

Idan ka kalli Hoorain ta wata fuska zaka gansa so silent haka, baya da magana kuma baya son hayaniya, amma fa da zaka same shi cikin abokansa mayaƙa ƴan uwansa, yana hira da su sosai, idan ka kalle shi ta fuskar assistant commander kuwa ba zaka so ka sake yin ido huɗu da shi ba, domin kuwa ganinsa a wannan siffar fa bata da kyau, wasu suka ce tamkar ganin mutuwa ne ganin Hoorain a siffar assistant commander, gara ku haɗu da shi a Hoorain ɗinsa a kan ku haɗu da shi a assistant commander.

So a kullum a tseren gasar dawakai ma shi yake zuwa na ɗaya, kunsan ita fa doki tana gudu ne kusan dai'dai da bugawar zuciyar wanda yake a kanta, iya karfin da ka sanya mata iya gudun da zata yi kenan, iya yadda zuciyarka take harbawa domin muradin cin nasara, iya power da zata baka kenan, so shi Hoorain yana da zafin zuciya sosai, bugu da kari akwai karfin dantse kamar dokin, idan ya hau kanta yana bata wuta sosai da sosai ta yadda idan ya zo na ɗaya ma ratar dake tsakaninsa da wanda zai zo na biyu ba ƙaramar rata bace, yana kere masu sosai, ko kamshinsa basa jiyowa a gasar. Shi fa har wani wasa yake yi da dokinsa a hanya ma idan ya kusa iso wa, har wani irin karkatawa yake yi kamar zai faɗo kasa, amma har ya dawo cikin kingdom ɗin babu mai iya cin masa bare ma ya wucesa.

Sosai Gimbiya Zunaira da kuma Gimbiya Chuchu suke jin daɗin kallon wannan gasa, saboda Zunaira ma yasa King ya kara karfafa wannan gasa ta zama kamar al'ada a masarautar, wajen da ake yin wannan gasa a cikin masarautar take, amma ba ta bangaren fada ba, ta baya ne, an ƙawata wajen sosai, babban fili ne sosai da sosai, tsawon wajen gasar har ta fita daga cikin kingdom ɗin, basa iya ganin karshen filin daga in da suke, kafin a fara gasar dama already za'a ɗaurewa wata lafiyayyar bujumar doki wani jan kyalle mai ɗauke da tambarin kingdom of power wadda kowa yasan tambarinsu shi ne kan zaki, so za'a ɗaurawa wannan lafiyayyar dokin wannan kyalle, sannan a saketa kamar da minti 20 haka, sannan su Hoorain su bi bayanta da nasu dawakan, wanda ya riga kama wannan dokin ya ciro wannan jan kyalle ya kuma ɗaure dokin dan kada ta yi wani wajen, sannan ya dawo da kyallen wajen King shi ne ya yi nasara, abin fa ba sauki ne da shi ba, ba ƙaramin abu bane, har faɗa mayaƙan suke yi a tsakaninsu, su jiwa juna ciwo, amma a haka kullum sati Hoorain ne yake yin nasarar zuwa na ɗaya, duk masu yin wannan gasa fa matasan sadaukan mayaƙa ne masu jini a jika, dukkansu basu wuce sha'anin Hoorain ɗin ba a shekaru, amma shi ya kerewa tsara, renon Commander Zafar ai dama ba za'a haɗa shi da kowa ba, ɗan commander da kansa ai dole dama ya kerewa tsara, horon da ya samu na musamman ne, tun yana ɗan ƙaramin yaro Commander yake koyar da shi dabarun yaki da sauransu.

So a takaice dai saboda wannan gasa yasa labarin rashin lafiyar mama ya fita, King ya tsoke yin wannan gasa a wannan sati saboda rashin lafiyar tata, hakance yasa kowa ya sami labarin bata da lafiya, amma babu wanda ya san me ya sameta sai ƴan cikin gida.

Nasan kuma kuna son jin me ya sami mama, to ku saurara, daren jiya ne aka samu wasu mayun kwari da babu wanda yasan daga ina suka fito, suka rinƙa ɗana mata harbi kamar zasu kasheta, kafin ta yi ihu a samu a kawo mata agaji duk sun yi mata ruɗu ruɗu da jiki, duk in da suka ɗana mata harbi sai wani kuraje ya bayyana a wajen tulele da shi jajir, abin ku da farar fata, duk jikinta ya yi ruɗu ruɗu, hakan ya saukar mata da mummunar kuma zazzafar zazzaɓi sosai, ga kurajen sai yi mata zogi da raɗaɗi suke yi, ga azaban kaikayi, babu kuma halin ta sosasu, idan ta ce zata sosa sai raɗaɗin azaba ya kasheta, wannan shi ne halin da take a ciki, harta face ɗinta waɗan nan shegun kuraje basu bari ba, har face kwarin suka cijeta, fuskarta ya kunbura kamar cincin puk puk.

Tun a wannan dare da abin ya faru, family gabaɗaya suka taru a room ɗinta lokacin da take ihun neman taimako, ba wasu masu yawa bane fa kwarin, basu fi su goma ba amma suka yi mata wannan aika aikan, kuma baa iya gane menene ya cijeta ɗin ba, domin kuwa kwarin basu da yawa, gasu ƙanana ido baya ganinsu. Sai dai tun a daren Momman Zunaira ta fahimci tabbas wannan cizon na waɗan nan kwarin na su Obaid ne, sai dai bata nuna kamar ta gane nasu ɗin bane, domin kuwa tasan idan kowa yasan nasu ne ba ƙaramin rikici abin zai zamar masu ba, mama tana da yara ita ma, so suma za su ce ba zasu bari ba sai sun ɗauki fansa, saboda dai suma jinin Modarawa na gudu a jikinsu, akwai jinin Akka, ba sai na sake faɗa ba kun san dai Modarawa basu barin bashi, ko ya ka taɓosu sai sun rama, babu yafiya, idan baka taɓosu ba kusan za'a ce sun fi kowa iya zaman amana da adalci ga mutane, amma ka kuskura ka taɓosu fa sai sun rama, ba ɗaga kafa, idan kowa ya ce zai ramawa mamarsa to fa daga nan gida kuma ya dai'na zaman lafiya, duk da cewa dama yanzu ma ba wani zaman lafiya iyayen suke yi ba, ɗan garama yaran nasu da yake basu ne masu yin kishinba, su kansu a haɗe yake, amma iyayen dai sai a hankali, kun san da hakan.

Wannan dalilin yasa momma ta ɓoye cewa kwarin nan nasu twin's ne suka ciji Mama, amma dai ta ƙuduri niyar sai ta yi masu faɗa sosai, zata tsawatar masu ta yadda ko da sunan wasa ba zasu sake yi wa wani makamancin irin hakan ba, domin wannan irin cizon kwarin ba ƙaramin azaba ne da shi ba.

Amma kash bata samu damar ganawa da su ba har suka wuce Dubai, hakan kuma ya samo asali ne saboda suna a tare da mamar ita da Mummyn Gimbiya Chuchu da Mammiensu Yah Jawad, sai kuyangun da suke yi wa mamar aiki, su ne a tare da ita.

Kwararrun likitoci kala kala har kala wajen biyar ne suke a kan mamar suna kula da lafiyarta, ba'a kaita hospital ba duk da a cikin kingdom ɗin asibitin yake, King ya ce likitoci su zo har cikin room ɗinta su yi treating ɗinta.

Hakan kuwa aka yi, suka zo suna kula da ita, so su Momma suna a tare da ita. King ma yau bai fita fada ba, yana a tare da ita, bata iya gane wanda yake kanta ma saboda zafin zazzaɓi, tasha bakar azaba, har da suma ta yi kafin likitocin su zo, a sume suka zo suka sameta. Da kyar da taimako Allah suka bata taimakon gaggawa ta farfaɗo.

King bai bar wajenta ba sai da lokacin tafiyarsa masallacinsa na jumma'a ya kusa, sannan ya nufi part ɗinsa domin ya je ya shirya.

Akka ma tana cikin room ɗin, ita ma Akka ta so ta gane cewa waɗan na kwari na su twin's ne suka ciji mama, saboda ita ma Akkar ƴan biyu ce, daga wajenta aka gado twin's ɗin nan, sai dai ita ɗan uwanta namiji ne, amma kuma sai zuciyarta ya raya mata a kan me su twin's zasu yi wa mama wannan aika aikan? Ganin babu wani dalili ne yasa ta kawar da tunanin su suka yi wannan aikin. King bawan Allah yana can yana tunanin ta ina aka samu irin waɗan nan shegun kwarin masu cizon har cikin room ɗinta saman gado? Dan ya gano waɗan nan kuraje da suka feso mata a jiki cizon wasu halittune daga cikin halittun Ubangiji, sai dai bai san ya aka yi aka sami kwarin ba, bai kuma ga kwarin da idanunsa ba, yasa an cire komai na gadonta an kakkaɓe, amma basu ga komai ba! Ya ɗaura tuhumarsa a kan kuyangun da suke gyara mata ɗaki, bai san shakiyan ƴaƴansa suka yi aika aikan ba, sun koma Dubai sun barsu da jidali. Wannan rashin lafiya ta mama ai jidali ne suka ɗaurawa family, dan kowa sai jikinsa ya gaya mashi, zasu sha wahala kafin mamar ta sami lafiya.

Sosai King ya yi shirinsa kamar yadda ya saba zuwa masallacin, ya haɗe a cikin farar alkyabbar wadda kwalliyar jikinta ma duwatsun gold ne, sai kyalli suke yi, haka zali takalmar sarautar da suke a kafafunsa kwalliyar jikinsu da zallar madarar gold aka yi su, ya sha naɗin na wani haɗaɗɗen farar rawanin, ya yi masifar kyau sosai, haka ya fito domin zuwa masallacin. Already an ƙawata mashi dokin da zai hau, ta sha kwalliya da kayan ado na dawakai masu bala'in kyau da tsada, kuɗin kayan kwalliyar dokinsa kawai ya isa ya sayawa mutun katafaren gida a babban birnin tarayya Abuja Nigeria.

Tun ba'a buɗe kofar fada ba kilishi da sallama suka fara zuba kirarin sarki zai fito, masu busa suka hau yin busa, tun kafin a buɗe kofar fada da take fuskantar harabar kingdom ɗin mai sanarwa ya sanar da fitowar sarki ta hanyar amfani da amsakuwa. Hakan yasa kowani bawa mai rai da yake cikin masarautar sai da ya nutsu jin sarki zai fito.

Nan take masu busar dake a wajen fadar suna dakon fitowarsa suka fara buga busar tasu, masu kirari ma suka fara rera kirarinsu, abin gwanin ban sha'awa, komai cikin tsari da bin ka'ida tare da ƙayatarwa, mayaka duk sun nutsu, ga wasu jiga jigan mayaƙa da a kallah zasu kai su 100 da suka jeru tun daga farkon kofar fadar har izuwa karshen stage na haurawa wajen kofar katafaren fadar, duk waɗan nan mayaka suna a ƙarƙashin kulawar Hoorain ne tare da bin umarninsa, already dama sun saba yin hakan, suna tsayawa a wajen ne domin tabbatar da sun bawa King tsaro har ya hau saman dokinsa zuwa masallaci.

Commander kuwa dama shi a cikin Fada yake zama kun sani, da shi ake tattauna duk wata zance da ta shafi fada dama kingdom ɗin gabakiɗaya. Bawan Allah tsufa ta ɗan fara kama shi, yana da ƙoƙari da jajircewa ne sosai, assistant commander yana kula da mayakan sosai, shi kuma yana cikin fada, idan ma zasu je yaki to yana ciki zasu tattauna, idan King ya tsayar da zance sai ya kira Hoorain ya gaya mashi, shi kuma ya hau shirya sadaukai kawai, so haka tsarin yake.

Sai da komai ta kankama sannan aka buɗe katafaren kofar fadar, su Galadima ne a gaba shi da malam liman, sannan su makama suka biyo baya, King yana a tsakiya an rufe shi, wasu jiga jigan mayaƙa biyu suna take mashi baya, Hoorain and commander kuma suna ta gabansa, su ne masu bashi tsaro ta gaba.

A haka suka fito suka nufi wajen dokin da aka shirya mashi dan zuwa katafaren masallacinsa da yake a cikin kingdom ɗin, sai dai masallacin yana da nisa da family part.

A haka King ya nufi masallacinsa masu busa suna ta aikin busa tare da zazzaga mashi kirari kala kala. Dakarun kwararrun mayaka ne suka yi gaba domin sharar hanya kada ko tsinke ya taɓa mai girma King.

Ni kuwa na haɗa kayana zuwa DUBAI dan kwaso maku
End Ads