x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 17 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 48001 words
  • 51000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 356

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
cewa sautin zubar ruwan korama ne yasa Kamran ɗin nufar wajen cikin takun jarumta tare da isa da ƙasaita, akwai dogayen ciyayi a gabansu waɗanda suka kare masu hangen ƙoramar daga nesa, kai tsaye ya nufi wajen ciyayin. Shi kuma Rocky wata hanya daban ya bi, dan yana jin wata iriyar kamshi a wajen wadda sam bai yarda da ita ba, kunsan su dabbobi da kamshi ko wari suke iya tantance abu yana waje ko akasin haka, musamman ma ɗan adam, da kamshin mutun suke iya fahimtar lallai akwai ɗan adam a wannan waje, so shi Rocky ya ji kamshi ne ya tafi duba menene?

ROCKY BA DAI GULMA BA, WAI YA JE DUBA MENENE KAI JAMA'A 😅

Shi kuwa Kamran yana zuwa ya sa hannu ya ya ye waɗan nan dogayen ciyayi dake a wajen, nan take katafaren ƙoramar ta bayyana a idanuwnsa.

Zaro dara daran idanuwan nan nasa ya yi yana mai kallon ƙoramar, katuwa ce sosai, ruwan da yake taruwa a ƙasarta ma teku ne guda, ruwan yana ganganrawa ne har izuwa cikin tapkeken tekun dake gaba da ƙoramar, sam Kamran duk yawonsa a cikin wannan daji bai taɓa sanin cewa akwai wannan tapkeken tekun ba, haka zalika bai taɓa sanin da akwai wannan tapkeken ƙoramar ba.

A zahirin gaskiya kowa ya kalli Kamran a wannan hali da yake ciki da kuma irin wannan tsayuwa da ya yi zai ce wannan ƙoramar yake kallah, amma kuma sam ba ita yake kallah ba, shi kwata kwata idanuwansa ma basu sauka a kan ƙoramar ba, yana yaye ciyayyin idanuwansa suka yi wani irin kyakkyawar gani wanda bai taɓa yin irinsa ba, hakan tasa bai ma bi ta kan ƙoramar ba, kawai ya tsaya cak yana ta kare mata kallo.

Macece ƴar yarinyar da bata wuce shekaru goma ba a duniya, kyakkyawar gaske ce sosai, a kallon farko ma idan ka kalleta sai ka rantse da Allah aljanace ta rikiɗe izuwa siffa mafi kyau a duniya, sanye take da kaya masu bala'in kyau sosai, ba irin kayan dajin bane, hakan yasa ta sake yin kama da aljana, domin kuwa kayan jikin nata ba kaya ne kamar sauran kayayyakin da kuka saba gani yau da kullum ba.

Wata iriyar skit ce wadda daga kugunta zuwa mazaunanta ya yi mata daidai cif cif, daga dai'dai matsayar hips nata zuwa ƙasa ya yi wani irin bala'in buɗewa sosai, sai ƴar farar vest ta sama wadda ta tsaya mata a iya cibiyarta, launin skit ɗin pink color ne, yana da kyalliya sosai a jikinsa wanda kwalliyar ta mamaye ko'ina a jikin kayan, baka iya tantance ainahin yadin da aka yi amfani da shi wajen yin wannan sket ɗin, saboda yawan kwalliyar jikinta, ga kuma duwatsu masu haske da aka kawata ta da shi.

Zaune take a saman wani dutse mai ɗan girma da yake a kusa da ƙoramar, ta zura kyawawan fararen kafafunta a cikin ruwan dake a gaban ƙaramar, ruwan da yake gudu izuwa cikin tekun nan kenan, ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana da wani irin bakin gashi, ya yi baki sosai har ya yi kamar dark navy blue, sai wani irin sheki yake yi, an ɗaure mata gashin kan nata ɗauri biyu, gefe da gefe, jelar gashin nata ya sauko mata har bayanta, kasancewar kanta na sunkuye sai jekar gashin ya sauko mata ta gabanta har izuwa saman kirjinta, hannunta na rike da wani sanda ɗan ƙarami tana kaɗawa, ta yi shiru kamar mai tunanin wani abin, duk da bata ɗago kanta ba, a iya fatar jikinta zaka tabbatar da kyakkyawar gaske ce, fara tas da ita, ga jikin nata mai bala'in kyau, da alama girman kayan marmari ce, kun san kayan fruits da balai'n gyarawa ɗan adam fatar jikinsa yake, daga gaban koshinta wasu kyawawan sidif ɗin kashi ne dake kwance a wajen, tana da gashi ɗan dai'dai a gefe da gefen fuskarta, gashin yana kwance luf, farar fata ga bakin gashi kwance a wajen, ya kuke ganin kyan zai kasance? Abin ba'a magana. Ga ta ƴar caras cas, babu ƙiba, jikinta mai kyau ne sosai, ƴar ɓul ɓul da ita, alamar ta ci ta ƙoshi dai amma ba ƙiba.

Kamran dai ya zaro idanu yana kallon wannan kyakkyawar halittar, ya ƙasa motsawa daga in da yake, da alama ya afka wata duniyar ne, bai taɓa kallon kyakkyawar halitta irin wannan ba, Mammansa kyakkyawar mace ce sosai, amma gaskiya bata kai rabin wannan yarinyar a kyau ba, shi kansa Kamran ɗin kyakkyawa ne sosai, amma ina, wannan yarinyar kyanta na daban ne, hasken fatarta har ma ta fi Mamman Kamran ɗin haske, kun san dama Mamma ta fi Kamran haske sosai, to wannan yarinyar dai ta fi Mamman ma haske, in dai mutun ba jarumi ba, kai ko jarumi ne idan ba ya dake sosai ba idan ya yi ido biyu da wannan kyakkyawar halitta a kallon farko sai ya tsorata, bare ma ace yasan babu mutane a dajin, wlh tsab kyanta zai tsorata shi ya ce aljana ce.

Amma shi Kamran ya dake sosai, dan shi fa tun da ya taso bai san menene ma tsoro ba a rayuwarsa, kuma kunsan mutun ya girma a irin wannan dajin ai dole ba zai san menene tsoro ba, this Forest no be small thing ooooo.

Ya yi nisa a kallonta da yake yi bai ankara ba sai ganin Rocky ya yi a bayanta, dama idan baku manta ba shi Rocky ya yi wata hanya daban, dan ya ji kamshi ɗan adam a wajen, shi ne ya je dubawa, to yanzu ya ganta.

Da gudu ya hauro saman dutsen, kuma ya hauro ne da nufin ya far mata, saboda shi Rocky idan ba Mamma da Kamran ba to baya ragawa kowa, wlh ko maharbi ya gani idan yana jin yunwa cinyewa yake yi fes abinsa, kuma dai kunsan damusa ki sabo ce, da alama zamansa da su Mamma ma ba haka kawai bane ba, amma koma dai me lokaci ne zai nuna mana.

Jin diran abu a kusa da ita yasa ta ɗago kai a tsananin raza ne, ɗago kai da zata yi kuma kai tsaye kallonta sai cikin idanuwan Kamran da yake tsaye ya tsareta da idanu, dan suna saiti da juna ne.

Wannan ɗagowa da ta yi yasa ta kara jefa mana Kamran namu cikin wata iriyar ruɗu tare da afkawa wani irin kogon yanayin da baki ba zai iya fassarawa ba, dan yadda kasan ita ta halicci kanta, face nata ɗan dai'dai, hancinta dai'dai da face nata, bai yi irin mummunar tsawon nan ba, ɗan dai'dai, sai olive dara daran eyes nata, farin idanun nata kuwa, fari ne tas, sai ka rantse da Allah tasa kwalli a ido, saboda yadda idanun nata suka kara fitowa sosai kamar tasa kwalli, olive green eyes ɗin nata ya fito sosai da sosai, lips nata jajir da shi, ga bakin nata ɗan karami da shi, kumatunta ɓul ɓul.

Har cikin ido take kallon Kamran, ta kasa iya juyawa ta kalli damusar dake kusa da ita, da alama mayyar tsoro ce sosai yarinyar, dan daga jin numfashi Rocky dake futa da wani irin gurnani yasa har jikinta ya fara kerma sosai, nan take wani irin tsoro na wuce misali ya bayyana a saman wannan kyakkyawar fuskar tata, tsuke ɗan bakin nan nata ta yi tana mai cigaba da kallon Kamran ɗin, sai dai da alama kallon Mamaki take yi wa Kamran ɗin, da alama bata taɓa yin tunanin zata yi tozali da wata halitta ta ɗan adam irin tata a cikin wannan dajin ba, shiyasa take yi mashi kallon mamaki har haka.

Wani irin numfashi mai karfi da Rocky ya saki ne yasa bata san lokacin da ta kara tsuke fuska ba, balai'n tsoron juyawa take yi su yi ido biyu da Damusa.

(Amma na ce ba My people's idan kune a cikin irin wannan hali anya zaku iya juyawa ku yi ido huɗu da Rocky kuwa?😅 Ni dai zan iya amma idan na furta kalmar shahada na gama😅 dan ko ya haɗiyeni ma burina ya cika na karisawa da kalmar shahada 😅)

Shi kuwa Kamran ya zubawa waɗan nan olive eyes ɗin nata idanu kawai yana ta kallo, da yake shi ya saba da Rocky, sai sam abin bai dame shi ba, a tunaninsa Rockyn ba zai yi mata komai ba, shiyasa ya kyaleta da shi, shi kuwa Rocky har ga Allah cinyeta ya yi niyar yi, dan dama yana ɗan jin yunwa.

Kafin Damusa ta ci mutun, kai ba ma mutun ba, Damusa tana da wata dabi'a guda ɗaya, kafin ta ci abu sai ta waje baki tare da ɗaga kai sama, wani lokaci idan suka daga kan nasu suna yin wani irin kuka, wani lokaci kuma basu yi, amma confirm ainahin Damusa baya cin abu sai ya yi wannan abin, ɗabi'ar su ce, so shi ma Rocky hakan ya yi, ya wani wage bakin nasa gari guda, dai'dai lokacin kuma yarinyar ta yi namijin ƙoƙari wajen iya juyowa a hankali hakwaranta na garuwa da juna, saboda tsananin tsoro.

Tana juyowa kuma ta yi ido biyu da garma garman hakwaran Rocky da ya buɗe baki, ga hakwaran waɗan nan biyu na sama da biyu na kasan kamar wasu kifiyoyi, suna da tsini sosai, su Damusa take kafawa a jikin wuyar dabba ko mutun, idan ta cakasu suka shi cikin namar mutun, sai su tsinka mashi jijiyar wuya da ita, haka ma idan dabba zasu kashe, shiyasa idan suna farauta zaku gansu wuya kawai suke kamawa, saboda su tsinka agarar wuyar, kunga kuwa suna tsinke agarar wuyar shikenan abu ya zama gawa.

Wani irin ihu ta saki mai razana ƙwaƙwalwa, kan kace me tuni ta yanke jiki ta faɗa cikin wannan uban ruwan.

Shi kuma Kamran ganin Rockyn ya buɗe bakin yasa bai san lokacin da ya nufesu da sauri yana ƙoƙarin yiwa Rockyn magana ba, sai dai bai kai ga yin magana bane yarinyar ta juya taga hakwaran Damusan, daga haka kuma sai suma.

Kunsan ita fa Damusa wlh ko bata buɗe baki ba ka ganta sai zuciyarka ta tsinke, idan kana da zuciya a kusa ma sai suma ko mutuwa, saboda tsananin kwarjininsu, dole ake jin tsoronsu ko ba'a so.

And one thing about Damusa, basu shiga cikin ruwa, akwai waɗan da suke shiga cikin ruwan, sai dai masu shiga cikin ruwan basu da yawa, normal Tiger daji kamar sauran dajuka basu shiga cikin ruwa, bawai ba zasu iya shiga bane, no zasu iya, kawai basu shiga ne, dan idan ruwa ta yi yawa tana tafiya dasu.

A dubu ɗari Kamran ya ƙariso wajen, da gudu Rocky ya nufesa, wani irin harara ya wurgawa Rockyn kafin ya yi tsalle ya faɗa cikin ruwan shima, Rocky ya bashi haushi ba kaɗan ba.

Tsayuwa a wajen Rockyn ya yi yana wani girgiza, shi a dole ransa ya ɓaci bai ci nama ba, sam bai damu da harararsa da Kamran ɗin ya yi ba, shi dai nama kawai yake tunani........😅

Da kyar da suɗin goshi Kamran ya iya ceto yarinyar nan daga cikin ruwan, amma ta sha ruwa sosai kam, Allah ma yasa bata ƙarisa faɗawa cikin ainahin tekun ba ya kamata, da ta faɗa sai wani labarin ba dai nata ba, kasancewar ruwar tana ganganrawa ne yasa Kamran ya sha bakar wahala wajen iya fitowa daga wajen, da ace ruwan yana tsaye ne to da sauki, amma tana gudu kuma ganganra, kuma kunsan ba dan ya saba da shiga cikin ruwa ya kuma iya ruwa sosai ba, ai da daga shi har ita sai sun faɗa cikin tekun nan, kuma suna faɗawa shikenan, sai dai Mamma ta rungumi sorry ta kurɓi ruwan ganye shayi, dan Kamran kam da ya tafi kenan, dan ma Allah yasa duwatsu ne a wajen sosai, ya yi ƙoƙari wajen kakkamasu har ya samu ya hauro sama daga gangarar ruwan, kuma ya yi sa'a yarinyar karama ce, bata da wani nauyi, hakan tasa ya ɗauketa a saman shoulder ɗinsa kamar ƴar baby.

A bakin ƙoramar ya kwantar da ita, da gudu Rocky ya ƙariso wajen yana wani numfashi mara daɗin ji, alamar huci yake fitarwa na ransa ya ɓaci.

Shinshinar yarinyar ya fara yi kamar wani tsohon maye, cikin wannan yaren nasu Kamran ɗin ya ce mashi. "Rocky ka kyaleta mana, ka sa ta faɗa cikin ruwa ma bai isheka ba sai ka zo kana wani shinshinata ko? To cinyeta zaka yi ne?".

Yana magana yana ƙoƙarin haɗa hannayensa dukka biyu waje guda, dan ya danna mata cikinta ta amayar da ruwan da ta sha.

Cigaba da shinshinata Rocky ɗin ya yi, ya yi kamar bai ji me Kamran ɗin ya ce ba, kunsan dama dabbobi irin wannan haka suke yi wa mutun, sai su yi ta wani shinshinasa kamar wasu mayu. Sai da Kamran ɗin ya sake yi mashi magana ne, sannan ya koma gefe guda ya kwanta yana wani zuro harshe waje yana lashe bakinsa.

(Tab da Kamran bayana nan fa da yanzu Rocky ya cinye mana wannan kyakkyawar halitta...💔😭 Amma da mun yi asara😅)

Daddana mata cikinta a hankali hankali ya fara yi, nan take ta fara amayar da ruwan da ta sha.

Cigaba da danna mata ya yi har sai da ya tabbatar ta amayar da ruwan da ta sha tas, sannan ya zame hannunsa daga saman lallausan fatar cikin nata yana mai cigaba da kallon face nata.

Shiru shiru bata farka ba, ga dai ruwan ta amayar da shi, amma bata farfaɗo ba.

Ganin hakan yasa ya matso kusa da ita sosai tare da matso da kansa izuwa saitin kirjinta, kunnuwansa ya kai saitin kirjin nata, dan ya ji shin kirjinta yana harbawa ne ko dai ta mutu?.

Ba shakka kirjinta yana harbawa fat, fat, fat, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ji daɗi sosai da ya ji tana raye.

Zuba mata idanu kawai ya yi yana ta kallonta, ta jima sosai a haka kafin ta fara motsawa, duk kuma wannan jimawa da ta yi Kamran na tsare da kallonta, kamar zai cinyeta da ido.

Kyawawan fararen kafafunta ta fara motsawa, kun san dama idan mutun ya tsorata ta dalilin haka har ya suma, to farfaɗowarsa akwai wuya, bare kuma ita da ta faɗa cikin ruwa, tana faɗawa kuma ta farfaɗo saboda ruwan da ya taɓata, ta sha ruwa ta sake suma, ai tama yi ƙoƙari da ta iya farfaɗowa a yanzu.

A wani irin razane tana kurma ihu ta farfaɗo, a zabure ta miƙe zaune tana ƙoƙarin tashi ta gudu, da alama ba'a cikin hayyacinta ta farfaɗo ba, ta tsorata ne ainun.

Da sauri Kamran ɗin ya rikota, dan idan ya barta zata je ta afka wani wajen ta cutu ba tare da ta sani ba, dan bata a cikin hayyacinta.

Ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi, idanuwanta a rufe ruf, burinta kawai ta gudu, a tunaninta ma damusar ce ta riketa, hakan yasa ta sake zunduma ihu mai sauti, sai ƙoƙarin fusgewa take yi.

Da hannu ɗaya Kamran ɗin ya riketa, amma ta kasa iya kwace kanta, ga shi taki buɗe idanun taga a hannun waye take.

Cikin yaren nan nasa dai ya yi mata magana a kan ta nutsu. Sai dai ina, sam bata ji me ya ce ba, sai cigaba ma da ƙoƙarin kwatar kanta da ta yi dan ta gudu.

Ganin haka yasa tunanin Mum twins ya faɗo mashi a cikin ransa, ya tuna ranar da ya fara yi wa mum twins magana da yarensa, sam bata ji, sai turanci kawai take ji, hakan yasa sai ya yi wa yarinyar ma magana da turanci a kan ta yi shiru ba Tiger bane, shi ne nan ya riketa.

Jin sautin muryarsa yasa ta ɗan nutsu, sai dai ta kasa iya buɗe idanuwanta, dan tana ganin kamar idan ta buɗe idanu fa waɗan nan garma garman hakwaran Rockyn zata sake gani, hakan yasa taki yarda ta buɗe idanuwanta.

Shiru Kamran ɗin ya zuba mata idanu yana ta kallonta, shi dai a duniya bai taɓa ganin kyakkyawa haka ba, bare ma fatar jikinta, a hankali ya mayar da kallonsa izuwa saman wuyarta, tana da abin da ake cewa gurun wuya, ga shi gurun wuyar tata mai balai'n kyau, bai yi irin cika sosai ɗin nan ba, ya yi dai'dai da jikinta, namar wajen ya ciko dai'dai, hakan ba kamamin kyau ya yi mata ba.

Jin shirun ya yi yawa ne yasa ta fara motsa idanuwanta a hankali tana son buɗesu.

Sai dai kash, tana buɗe idanun nata ta yi rashin sa'a a in da ta sake yin ido biyu da Rocky da ya iso wajen yanzu, dan ya kalli Kamran ɗin ya sankare waje guda yana ta kallon face nata ne yasa Rockyn ya kariso wajen shi ma yaga me yake kallo haka.

Wani irin mahaukacin ihu ta sake zundumawa tare da fara ƙoƙarin kwace kanta daga hannunsa ta gudu.

Ganin hakan yasa ya yi saurin juyar da kansa dan ya ga me ta gani daga buɗe idanuwanta ta sake ruɗe mashi haka.

Gamin Rocky ne yasa ya yi ƙoƙarin gaya mata cewa ta nutsu Rocky babu abin da zai yi mata, idan ta gudu ne ma zai bita, dan zai yi tunanin ta yi wa Kamran ɗin wani abin ne ta gudu, so zai bita ya kamata ya dawo da ita wajen Kamran ɗin, rufin asirinta kawai ta nutsu.

Amma ina ita ai ta kasa yarda ta nutsu, gani take tsab Rocky zai cinyeta idan ta tsaya. Da iya karfinta take ƙoƙarin kwace kanta.

Ganin da gaske take yi zata kwace kanta ta gudu ne yasa Kamran ɗin ya jawota jikinsa sosai, ya riketa da kyau yana mai cigaba da ce mata ta nutsu babu abin da Rocky zai yi mata.

Kankame shi ta yi tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tun da take bata taɓa kallo Tiger a wajen ba, da alama babu Damusa ko kaɗan a yankin nan nasu, kuma da alama basu shigowa wajen, dalili kuwa shi ne yashi (kasa) ta yi yawa sosai a wajen, sannan kuma akwai teku a wajen, Damusa kuma bata son waje irin haka sam, shiyasa ma basu leƙowa arear wajen, dan tekun da yake wajen ma ba irin kogin da namun dawa suke zuwa shan ruwa bane, babban teku ne wanda suke tsoron zuwa wajen, dan kar ruwa ya tafi da su.

Wani irin kuka take yi wadda duk wanda ya ji sautin sai ya ji ta
End Ads