x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 40 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 117001 words
  • 120000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 385

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
wasu munafukai suka kwashe da dariya a tare, har da rike ciki suna rungumar juna da hannu ɗaya, ai idan baka san halinsu ba wlh sai su haukataka, yanzu zasu canza fuska kamar masu tausayi da imani, cikin second ɗaya kuma zasu iya sake komawa tantiransu, yanzu dai kunga Obaid wai ya tausayawa Yusuf, amma a take kuma sun sake kwashewa da dariya har da cewa ba zasu fasa abin da suka yi niyya ba, kai Allah ya shirya mana su, goyon kaka ne, kada ku ga laifinsu!.

A ɓangaren Gimbiya Sarina kuwa, suna tsaka da cin wannan abincin Yusuf ya matso kusa da ita kamar wanda zai yi mata raɗa a kunne. A hanzarce ta ja baya kaɗan, dan idan baku manta ba na gaya maku ita bata haɗa hanya da maza, bata bin maza, so ko kusa da ita bata yarda namiji ya zo.

Kara matsowa kusa da ita Yusuf ɗin ya yi, da mamaki ɗauke a saman fuskarta ta ɗago ta kalle shi.

Ta ɗan tsorata da ganin yanayinsa, idanunsa sun sauya sun yi jajir da su, amma bata nuna alamar ta tsorata ba, sai ma ta dake ta ce mashi lafiya kuwa yake matsota haka?.

Shi ma abokinsa da mamaki yake binsu da kallo, dan yasan Yusuf dai ba zai matsa kusa da ita haka kawai ba, ba halinsa bane kusantar mata har haka, tare suka yi karatu suka yi komai, tun da yake bai taɓa ganin Yusuf kusa da mace har haka ba, amma da yake ita Sarina ya mace a kanta sosai, kuma abokin nasa ya sani, dan tun kan su zo ya bi ya cika masu kunnuwa da zancenta tare da yabon kyanta, hakan yasa abokin nasa ya yi tunanin ko dukka shaukin soyayya ne take ɗebarsa yasa ya matsa kusa da ita har haka.

Kuyangunta da suke tsaitsaye a ɗan gefe ta bayansu ma baki suka saki suna ganin wannan ikon Allah.

Ita ma Gimbiya Sarina shiru ta yi tare da zuba mashi idanu tana jiran taga gudun ruwansa, sam bata san komai da yake faruwa ba.

Shi kuwa sai kara gaba yake yi, daga matsowa kusa da ita yanzu ya kai ya sa hannu ya rungumota jikinsa. A zabure ta ɗago da kanta daga jikin nasa tare da fara ƙoƙarin ture shi, saboda ita tun ainahi ma ta rai'na class ɗinsa, taɓa ta da ya yin nan sai take ganin ya cuceta ya zubar mata da class, ta fi karfin ya taɓa koda dan yatsarta.

Shi kuwa abokinsa bai san time ɗin da ya miƙe tsaye yana kallonsu ba, sunansa ya fara ambata Yusuf, Yusuf ba tare da yasan yana ambatar sunan ba, kawai ruɗewa ce tasa yake kiran sunan.

Ina ai Yusuf baya ji baya gani, kara ƙanƙameta sosai ya yi a jikinsa ya fara ƙoƙarin ta yadda zai yi ya rabata da kayan jikinta. Tashin hankali.

Zaro idanu kuyangun nata suka yi suna kallon ikon Allah, ga shi su ba halin su yi magana.

Abokinsa ma izuwa yanzu ya gama tsorata, bai san lokacin da ya yi kansu yana ƙoƙarin janye Yusuf ɗin ba, ita ma Sarina ƙoƙarin kwace kanta take yi daga gare shi, shi kuwa ƙoƙarin rabata da kayan jikinta kawai yake yi, idanunsa sun rufe baya ji kuma baya gani.

Ko da abokin nasa ya zo kama shi ma ina ya kasa, domin Yusuf ɗin yaki bashi wani dama, sai ma hankaɗesa gefe guda da ya yi ya fara ƙoƙarin yin rapen ɗinta da iya karfinsa.

Sosai abokinsa ya ruɗe tare da tsorata, ganin abin yake yi tamkar a mafarki, sam bai yarda cewa Yusuf ne yake aikata hakan ba.

Da dai gimbiya Sarina taga da gaske yake yi zai yi mata fyaɗe ya keta mata mutunci, sai ta fara ihun neman taimako, ga shi kuma da iya karfinsa ya riketa babu halin ta kwaci kanta, duk ya sauya lokaci guda kamar ba shi ba, sai haɗa uban gumi yake yi, ya zama kamar wani mayunwacin zaki, ga wasu zafafan gumi da suke tsastsafo mashi daga gefe da gefen face ɗinsa, jikinsa har wani tsuma yake yi, burinsa kawai ya rabata da kayan jikinta.

Ihu sosai take kurmawa tana neman taimako, kuma da iya gaskiyarta take yin wannan ihun, har ga Allah bata yi excepting haka daga gare shi ba, ganin ya yi shigar mutunci yasa ta yi tunanin yana da mutum koma yaya take, ashe ba haka bane.

Abokinsa ya kasa iya kwatarta daga hannunsa, domin kuwa Yusuf ɗin ya saka dukka karfinsa ne a kanta. Ganin hakan yasa kuyangunta suka yi waje da gudu dan su je su sanar da family ga abin da yake faruwa.

A hanya suka ci karo da commander ZAFAR da ya fito daga fada zai je wajen mayaƙa ƴan uwansa, kamar kullum yana shirye cikin kayan yakinsa. Ganin yadda suke a birkice suna gudu yasa ya tambayesu menene yake faruwa?. Ba dan shi ɗin bane da ba zasu saurari kowa ba sai fadan King zasu kai rahoto, amma da yake sun san wanenen Zafar, sai suka dakata daga gudun da suke yi, suna ta aikin mayar da numfashi, da kyar suka iya gaya mashi cewa bakon Gimbiya Sarina ce zai yi mata fyaɗe a cikin parlourn baki.

Ai tun basu gama magana ba Zafar ya nufi wajen da sauri, su kuwa suka nufi fada da gudu dan su kai rahoto, duk suna ruɗe, sun ga abin da basu taɓa tunani ba, bako ya zo har cikin gida zai yi wa ƴar gida fyaɗe kuma a cikin parlourn iyayenta? Wannan wani irin abu ne? Lallai akwai kura ba kaɗan ba, za'ayi karamar yaki kuwa yau, King Zuhair da yake sanyawa a dandake gaban masu yi wa mata fyaɗe ne yau za'a zo har cikin gida za'ayi wa ƴar ɗan uwansa fyaɗe? Tab akwai rikici kuwa.

Ko da Zafar dattijon arziki ya shigo cikin parlourn ya tararda Yusuf ɗin ya rabata da alkyabbar jikinta yana ƙoƙarin cire mata doguwar rigar tata, sai ihun neman taimako take yi, ga abokinsa ma a kansu yana ƙoƙarin janye Yusuf ɗin daga gareta, sai abin ya yi kama da shi ma abokin yana son ya yi mata fyaɗen ne, dan a yadda yake duke a kansu sai Zafar yaga kamar tare suke ƙoƙarin yi mata fyaɗe shi da Yusuf ɗin, duk sun wargaje kayan abincin da yake waje, sun watsa komai a ƙoƙarin kiciniyar faɗa a tsakanin su ukkun, parlourn ya yi kaca kaca.

Cikin tafasar jini Commander Zafar ya ƙariso cikin parlourn, ransa idan ya yi dubu to ya ɓaci, nan take idanunsa suka kaɗa suka yi jajir, wannan ai rai'nin hankali ne ma, ace a samu wasu su iya keta duk wasu zaratar warriors da suke cikin KINGDOM OF POWER su sami damar shigowa wajen ƴar gida kuma har su yi ƙoƙarin yi mata fyaɗe? Lallai ma waɗan nan hukuncin da za'ayi masu karema ba zai shinshina ba, a gaskiya ran commander ya yi muguwar ɓaci, dan ganin rai'nin wayo ma ya yi wa abin.

Yana isowa kansu da hannu ɗaya ya sa ya damko wuyar abokin Yusuf da yake ƙoƙarin janye Yusuf ɗin daga kanta. Cikin ɓacin rai Commander ya sanya kafa ɗaya ya take wuyar Yusuf ɗin, sai ga shi ya zube ƙasa wanwar, jinin Commander sai kara tafasa take yi, jikinsa har wani tsuma yake yi, kafarsa dake sanye da waɗan nan shegun takalmar yakin nasu masu kama da takalmar karfe yasa ya take wuyar Yusuf ɗin a kasan, shi kuma abokin nasa ya shakesa da hannu ɗaya. Maza kake ji, ai ba sai an gaya maku waye commander ba, dattijon kirki mai zafin nama haɗe da tafasashiyar jini da ya shafe sama da shekaru 20 yana bawa zaratan mayaƙa daban daban horo, namijin gaske jarumin jarumai kuke ji!.

A guje Gimbiya Sarina ta samu ta miƙe tsaye zata nufi waje, ƴar kaniya idanu sun rena fata, ta yi wani narai narai, duk ta yi laushi.

Bata kai ga fita cikin parlourn ba zaratan horarrun mayaka masu jini a jika da lafiya har guda goma ne suka shigo cikin parlourn, kowannensu ka gansa sai hantar cikinka ta kaɗa, a haka ma fa fuskokinsu na'a cikin hular kayan yakinsu, ba'a ganin ainahin fusatatciyar face ɗinsu, amma yadda kasan wasu mutuwa idan sun doso waje haka ake tsoronsu, saboda cikar halittarsu ga kwarjinin masifa mai razanarwa, sun sha horo wajen commander ai, dole su zama kamar wasu bujuman zakuna.

Daga King har uncle Abbas sai da suka baro fada domin su zo su ga abin da yake faruwa, a tare suka zo da waɗan nan jiga jigan zataran warriors ɗin, hakan yasa Sarina tana ganinsu ta tafi wajensu da gudun gaske tana kuka hawaye bibbiyu.

Daga King har uncle Abbas rige rigen tarbanta suka yi. Jikin King ta faɗa tare da kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, daga jin yadda take wannan kuka zaka fahimci da iya gaskiyar take kukan, ba wai na munafurci bane, ba'a taɓa yin yunƙurin yi mata fyaɗe ba a rayuwarta sai yau, abin ya yi mugun tsoratata ba kaɗan ba, haƙiƙa kuma ita bata san me su twin's suka shirya ba, dama ba gaya mata suke yi ba, shirya shirinsu kawai suke yi, sai dai ta gani a aikace, sau da dama idan zasu kori samarinta bata sanin plan ɗinsu, idan ta gaya masu bata son saurayin shikenan sai ta rabu da su su yi nasu shirin, hakan yasa bata yi excepting Yusuf zai yi ƙoƙarin yi mata fyaɗe ba, ƴar kaniya yau idanu sun rena fata, taga mutuwa kusa, ai badan kuyangun nan nata da take renawa ba da ta yabawa aya zaƙinta.

Kafin su King su yi wa Zafar magana ma har Yusuf da abokinsa sun sume a hannunsa, shakar da ya yi wa abokin Yusuf ɗin ne yasa ya sume, shi kuma Yusuf taka mashi wuya da ya yi ne yasa shi ma ya sume, dan basu samu numfashin da zasu shaƙa ba, dole su suna, Allah Sarki abokin Yusuf da shi kwatarta ma ya je yi, wannan shi ne ya taka sahun ɓarawo, a wannan hali da ake ciki kuwa mai kwatarsu sai Allah, ko ubansu ne shugaban kasa yadda aka kamasu da hujjarnan wlh basu isa a barsu haka kawai ba, tab King Zuhair fa, lallai za'ayi yaki kuwa ba kaɗan ba, su Yusuf sai dai mu ce Allah ya kwaceku, dan sai dai ayi yakin duniya amma King ba zai barsu ba, koma ƴan uban waye!.

Uncle Abbas ne ya ce da Commander Zafar ya barsu haka nan, a kwashesu a zubasu a prison na masarautar zuwa anjuma idan komai ya lafa sai asan abin yi.

Cikin ɓacin rai King ya ce ina babu wannan magana ta a kai su prison, yanzu zasu karɓi hukunci, kun san halin King bashi barin ko ta kwana, jinin Modarawa ai basu da hakuri malam, su sha yanzu magani yanzu ne, ba ɗaga kafa, dama ga King da tafasasshen jini ai su Yusuf sai ta Allah kawai.

"Yaya please ka bari tukun nan zuwa anjuma mu nutsu sai a yanke masu hukuncin da ta dace da su".
Cewar uncle Abbas.

Cikin nuna isa da izza rai a matuƙar ɓace King ya ce. "Malam liman ka karanto masu doka irinta addinin musulunci a kan wanda ya yi yunƙurin yi wa yarinya fyaɗe a cikin gidan iyayenta, Commander ka zartar masu da wannan hukunci ba tare da ɓata lokaci ba, Abbas na gama magana bana son sake jin wani abin kuma!".
Yana kai karshen maganar ya juya rungume da Sarina dake ta faman kuka a jikinsa, ta tsorata sosai, kuka take yi ba kakkautawa, yadda take kukan nan sai ta baka tausayi ƴar kaniya.

Kai tsaye part ɗinsa King ya wuce da ita dan ya rarrasheta.

Tashin hankali, ga shi dai su Yusuf sun suma bare a iya fahimtar ko wani abin Yusuf ɗin ya sha, kuma kunsan idan ya farfaɗo a yanzu dai koma me ya sha zata sake shi, da bai suma bane to ko King zai iya fahimtar ba lafiya yake ba, amma yanzu babu wanda zai fahimci hakan, bugu da ƙari ga abokinsa da ake ganin cewa a tare suka yi ƙoƙarin yi mata fyaɗen, kunga kuwa hakan ma hujja ce da zata kara sanyawa ayi masu hukunci ba tare da anyi tunanin ko dai ba lafiya yake ba, a gaskiya dai Yusuf bashi da hanyar da zai wanke kansa a cikin wannan al'amari, sannan bugu da kari duk abin da ya ci a wannan waje tare da Sarina da abokin nasa suka ci, to shi ta yaya wannan abin ya faru da shi shi kaɗai? Da alama kuma dole wani abin aka bashi ya ci or ya sha, dan farkon shigowarsa ai ba haka yake ba, to idan wani abin aka bashi ta yaya aka yi hakan kenan? Ko dai dama ya zo da ɓoyayyar manufa ce? Anya kuwa hakan zata faru? KINGDOM OF POWER fa, masarautar da jin sunanta ma kawai yake sanya hantar manya ta kaɗa bare kananan kwarin irin su Yusuf ne zasu yi tunanin shiga har su yi ƙoƙarin yiwa ɗaya daga cikin gimbiyoyi masarautar fyaɗe? Masarautar da mayakanta suke tamkar ajali. Akwai cakwakiya gaskiya, ni dai bari na koma gidansu Khadija mu ga wani hali ake ciki, wata kila kafin mu dawo wasu abubuwa zasu ɗan yi sauki ta nan, amma dai a gaskiya twin's shegun kaya ne na bugawa a jarida, dan ni su nake zargi, suna shirya plan ne ta yadda duk bala'in nacinka ba zaka taɓa gane cewa su suka shirya shi ba, they're very very smart, suna da shape barin. Amma kuma anya zasu iya shirya wannan babban al'amari har haka kuwa?

(Allah yasa akwai Camera a cikin parlourn 😅 dan a wanke abokin Yusuf 😌 amma ko akwai Camera shi dai Yusuf ba zai wanku ba gaskiya, dan ya riga da ya zurma, su twin's ma ko akwai camera ba zasu kamu ba, dan ai basu a waje kuma basu leƙo ba, ita ma Sarina ba zata kamu ba, dan ta nunawa Yusuf so da kulawa, babu wanda zai yi tunanin bata son shi dan haka zata iya yi mashi sharri, ta nuna so a fili, dan haka ta wanke kanta, gaskiya idan ka shiga hannun Team ɗinsu twins kagama yawo wlh💔)

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

GIDANSU KHADIJAH💔😥

Izuwa yanzu komai ya kara lalacewa maman Zainab, karin auren baban Zainab babu fashi, haka zalika auren Haidar da Khadija babu fashi, damuwa sun taru sun yi mata yawa, tsananin damuwa yasa ta manta da Allah take tunanin bata da mafita da ya wuce ta bi shawarar Aunty Hauwa, a haukarta gani take yi shi ne kawai the only way da ya rage mata domin tsira, ga shi kuma kamar daɗa hura wutar gaba a tsakaninta da sirikan nata ake yi, duniya ta yi mata zafi, ta manta da cewa duk wani mumuni baya rabuwa da jarabawa ta Ubangiji, idan kaga Allah bai jarrabeka da wata musifa bama to wlh ka binciki imaninka akwai tankarɗa, duk wanda Allah yake so da rahma to yakan zarabce shi, dan haka kada kuga kun shiga wata jarabawa ku yi tunanin ko Allah baya son ku ne, ko kuma ma ku manta da Allah ku fara tunanin wani kato, Allah yana jarraba bayinsa ne domin yaga shin a kowani hali suna tare da shi ne ko kuma dai yaya? To dan haka shawara shi ne kuyi kokari ko a wani hali kuka tsinci kanku ku kasance a tare da Ubangiji, kada ku taɓa yarda ku yi tunanin wasu.

Ba tare da ta yi tunanin me zai je ya zo ba, bata yi tunanin ta gayawa mahaifiyarta halin da ake ciki ba, kawai ta kira Aunty Hauwa a waya a kan ta zo su je wajen malamin nan, dan gaskiya ta rasa mafita, zuciyarta na gab da tarwatsewa, gidan farinciki yanzu yana shirin zama gidan ƙunci koma ace ya zama.

Baban Zainab yana ta ƙoƙarin yaga ya lallaɓa mamarsa ta janye daga maganar karin aurensa, amma ta tirje a kan lallai sai ya kara, ya ce mata in dai matsalar rashin haihuwar Maman Zainab ne damuwarsu da har yasa suka ce ya kara aure, to su yi hakuri In Sha Allah nan bada jimawa ba zata samu ciki ta haihu komai ya wuce a dawo kamar da. Ina ai wannan tsohuwa taki yarda, ta ce ita yanzu bata damu ba ko maman Zainab zata haifo yara ɗari ne wlh sai ya kara aure gara ma ya ji da kyau, ta faɗa da babban murya kuma umarnin take bashi ba shawara ba.

Bashi da zaɓin da ya wuce ya amsa da to, amma yana cikin wani hali, duk ta in da ya juya babu daɗi, ga maman Zainab ta rike mashi wuta a gida, bata kula shi, za dai ta yi mashi duk abin da ya dace ta yi mashi, zata sauke nauyin da yake a kanta, amma ko sannu bata ce mashi idan ya dawo, bata yi mashi magana, wasan ɓuya ma take yi da shi, idan ta ji ya dawo zata shiga ɗaki ta rufe kofarta, ba zata fito ba kuma har sai ta ji ya fita, ya yi magiyar duniyar nan taki sauraronsa, yadda kuka san shi ya yi mata laifi, bawan Allah bata san shi ma yana tsaka mai wuya ba.

A ɓangaren Haidar kuwa, sai shirye shiryen biki yake yi abinsa, duk ya sanar da mahaukan abokansa irinsa marasa kan gado, tsabar mugunta irin na Mammarsa ma har da wani cewa ai ba sai ya yi wa Khadijah ɗin kayan lefe ba, ai kanwarsa ce, kuma koba komai ya bautawa babanta a kasuwa, dan haka babanta ne ma yakamata ya yi komai na bikin, domin tun Haidar yana ƙarami yana wahala a shagonsa, dan haka lokacin da yakamata abiyasa ya yi, tsabar rashin imani irin na maman Haidar ɗin, yadda kuka san ba uwa ɗaya take da baban Zainab ɗin ba, yanzu so take baban Zainab ɗin ya yi wa Khadijah kayan ɗaki kuma ya dawo ya haɗawa Haidar lefen da zai kawowa Khadija, sannan ga nashi karin aure, bugu da kari ga shi hajiyarsa ta ce a sabon gidansu za'a kai amarya, dan haka dole ya ƙarisa gininsa cikin sauri, Allah ma yasa abu kaɗan
End Ads