damuwa sosai na ganin baban nata yaki ya ci abinci, bata ɓoyewa Sadiq komai ba ta gaya mashi tas, sannan ta kara da cewa abin ya hanata yin barci ne yasa ta fito.
Zama ya yi a bakin dakalin da aka kewaye fampon da shi, sannan ya ce ita ma ta zauna. Ba musu ta zauna a gefensa, hakika ya shiga damuwa sosai, irin wannan matsala yake gujewa maman Zainab tun tuniya yasa yake ta ƙoƙarin ganin bata sauka daga kan hanya ba, amma ta yi busur da zancensa ta yi son ranta, ga shi yanzu wankin hula yana neman kaita dare, tura ta kai bango baban Zainab ya fara juya mata baya, yanzu wa gari ya wayanwa?.
Rarrashin Khadija ɗin ya fara yi tare da bata hakurin, sannan ya sanar da ita dama a tsakanin mata da miji ana iya samun wannan matsala, aure ya gaji hakan, babanta mutumin kirki sosai da yake ɓuye masu ire iren wannan faɗa na mata da miji yasa basu san da hakan na faruwa ba, dan haka kada ta sanya damuwar kowa a ranta, ta yi hakuri zuwa da safe In Sha Allah babanta zuciyarsa zata sauko, dan shi mutun ne mai hakuri, ta yi hakuri komai ya yi zafi maganinsa Allah, ta koma cikin room ɗinsu ta ɗauro alwala ta gabatar da nafila raka'a biyu tare da rokan Ubangiji da ya kawo mata mafita, In Sha Allah zata samu dama ta yi barci, komai kuma zai wuce.
Haka dai ya cigaba da rarrashinta yana bata kwarin gwiwa har ta ji sanyi a ranta. Sai da ya tabbatar ta ji daɗi damuwarta ya gudu, sannan ya ce ta tashi ta shiga ciki. Duk da rashin yawan magana irin tata sai da ta ce. "Kawu Sadiq ka bari mu ɗan yi hira kaɗan, zan kara samun nutsuwa na sani".
Bai musa mata ba ya jata da hira har wuraren karfe 10, sannan ne ya ce ta tashi ta shiga ciki. Ba musu ta miƙe ranta a sake, fuska ba yabo ba fallasa ta wuce ciki tana yi mashi zai da safe. Shi ma sai da safe ya yi mata kafin ya miƙe ya koma cikin room ɗinsu a in da ya sami Haidar yana riƙe da wayarsa yana kallo, ko shakka bayayi fina finan batsa yake kallo duba da yadda ya takure jikinsa waje guda, kuma yasha kamasa yana kallon fina finan batsa dama, sau da dama yasha yi mashi nasiha a kan hakan babu kyau ya daina, amma ina ya yi nisa baya jin kira, hasalima idan bai kalli batsan ya samarwa da kansa nutsuwar hankalinsa da ya ɗaga ba baya iya yin barci, hakan yana ɗaya daga cikin abin da yasa yake son taɓa jikin Khadija sosai, shi bai kima ta dawo kwana a ɗakinsu ba, ɗan iska saboda yana kalle kalle batsa kullum yana cikin ɗagawa kansa hankali, dole ya yi ta ƙoƙarin latsa ƴar mutane. A kullum idan Sadiq ya fara yi mashi nasiha a kan ya dai'na kallon film irin haka, to wlh faɗa ne yake biyowa baya, basu wanyewa lafiya, hakan yasa Sadiq ɗin yanzu bai ci bi ta kansa ba, ya sharesa kawai tun da baya ji kuma ai ba yaro bane shi, ya fi Sadiq ɗin shekaru da shekaru biyu, kamata ya yi ace shi yake yi wa su Sadiq ɗin faɗa da nasiha, amma ina, ina ma yaga hankali ne wannan kam, sai dai Allah ya kyauta.
Yanzu ma girgiza kai kawai Sadiq ɗin ya yi tare da nufar nasa gadon, already da alwalar barcinsa a tattare da shi, dan har ma ya kwanta mamarsa ta kirasa ya tashi ya fita, so yanzu yana dawowa addu'ar barci kawai ya yi tare da kashe wayarsa ya kwanta, ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.
A ɓangaren Khadija ita ma bayan ta yi sallar nafila raka'a biyu kamar yadda kawun nata ya ce, sannan ta rufe da shafai da witiri, hankalinta ya kara kwanciya sosai, ta ƙara samun nutsuwa sosai da sosai in da ta zo ta haye gadon ta kwanta, cikin ƙanƙanin lokaci barci ya ɗauketa, dama ita Zee already ta yi barci abinta.
Mamarsu kuwa, cikin kuka ta sanar da Aunty Hauwa halin da ake ciki. Hakuri Aunty Hauwar ta bata tare kuma da ce mata ta kwantar da hankalinta gobe da safe zata zo gidan, kada ta ji ta wani damu zasu yi maganin baban Zainab. Da haka dai ta rinƙa rarrashinta har ta hakura a nan barci ya yi awon gaba da ita, in takaice maku labari dai bata yi sallar mangariba bare isha, a haka barci ya saceta saboda kukan da ta sha.
(A gaskiya ina jin labarin gidansu Khadija tamkar true life story, wato tamkar gaskiya, wlh duk idan na zo rubuta part ɗin ji nake yi kamar gaske, saboda abu ne da yake faruwa yau da gobe a zahiriya sosai da sosai, Allah dai ka ƙara tsaremana imaninmu ka rabamu da ƙawaye jahilai.)
Washegari da safe kamar yadda suka saba haka Maman Zainab ta tashi tare da biyan bashin sallolin da suke a kanta na tun jiya, sannan ta nufi kitchen da nufin ta yi masu girki, kasancewar farar shinkafa da miya ta dafa masu daren jiya wadda basu ci ba, sai ta ɗauko shi ta sake ɗumama masu, saboda bai yi komai ba, kuma yana da yawan da bai kamata su zubar ba, so sai ta sake mayar da shi wuta ta ɗumama, shi ta sanyawa su Khadija a kulolin makarantarsu.
Suma su Khadijah suka yi wanka suka shirya kamar yadda suka saba, baban su ne kawai yaki fitowa, da yake dama sai maman Zainab ta haɗa mashi ruwan wanka sannan take tashinsa daga barci, to jiya dai ya rufe room door ɗinsa da key, koda ta kammala shirya masu komai kamar yadda ta saba ta nufi room ɗin nasa dan ta tashesa, sai ta ji kofar a rufe da key.
Kamar zata yi knocking, sai kuma ta hakura ganin cewa su Khadija suna nan, kuma tasan halinsa tun suna saurayi da budurwa, damone sarkin hakuri over, amma kuma idan ya zuciya wlh abin da zai sanya shi ya sauko ba karamar abu bace, kuma duk yadda yakai ga kawar da kai ga abu idan fa ya zuciya tura ta kai bango to fa mantawa yake yi da wata kawaici ko makamancin haka, yanzu haka a yadda yake cikin fushi sosai ɗin nan yana iya yi mata faɗa tatas sosai koda a gaban su Khadijah ɗin ne, zai manta da wani tarbiya.
Tuna hakan yasa ta fasa yin knocking na kofar ta juya izuwa nata room ɗin, bata sake bi ta kan su Khadijah ɗin bama ita ma. Bayin Allah da suka ga lokaci na ƙurewa zasu yi latti ga Khadijah suna dab da fara rubuta Exams, sai suka fito suka nufi wajen kawunsu Sadiq, dan ya kai su school kamar yadda ya saba, yau dai sun hakura da yin sallama da baban nasu tun da bai fito ba.
Knocking suka yi masu Sadiq a kofar ɗakin, ba'afi second ashirin ba sai ga Sadiq ɗin nan ya buɗe kofar ya fito. Shirye yake cikin dakakkiyar shaddar mai shegiyar kyau, da alama yau ma yana da class.
Har suna haɗa baki wajen cewa Uncle Sadiq ina kwana. Murmushi ya yi yana kallon Zainab sarkin tsiwa kafin ya amsa masu gaisuwar, yarinyar nan Zainab ba dai iyayi ba, haka take zama ta karewa maman Haidar da kakansu zagi fes kamar an aikota, bata da sauki, Khadija kam daga e sai a'a, sai kuma gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa.
"Dama na shirya ku nake jira, ina da class karfe 7:30 dai'dai mu je ko?". Sadiq ya faɗa yana kai hannunsa ya ɗan bugi bakin Zee da take aikin turo shi kamar wadda aka zaga.
"Kai kawu Sadiq menayi maka to?". Ta faɗa tana ɗaure fuska.
Khadijah ce ta amsa mata da. "Kwaɗayin duka yake ji yasa ya dake ki, ko dai bai kai bane?".
Wani irin harara ta bi Khadija da shi. Shi dai Sadiq wucewa ya yi izuwa wajen mashin ɗin baban nasu, da yake key na a hannunsa, fito da mashin ɗin ya yi kamar yadda suka saba, ba ɓata lokaci ya ce su yi sauri su hau su tafi lokaci yana ƙurewa. Da sauri suka hau Zainab sai raki take yi. Da haka suka bar gida, shi kuwa Haidar yana can yana barcin asara, wani lokaci ma sai 10 yake tashi ya tafi kasuwa ko kuma wajen mamarsa or kakarsa, kullum aiki ɗaya, ya kusa yin aurema bai canza hali ba, ko waye zai ciyar mashi da matar idan ya yi auren? Shi da kasuwar ma sai yaga dama yake zuwa. Akwai matsala sosai, akwai case ba kaɗan ba.
Misalin karfe 9 dai'dai sai ga Aunty Hauwa ta nufo gidan kamar yadda ta faɗawa maman Zainab zata zo jiya. A lokacin baban Zainab bai fita ba, yana ciki, da alama yau ba zai je kasuwa da wuri ba, ita ma maman Zainab tana cikin ɗakinta ta yi zaman ƴan bori a saman tsakiyar gado, ta haɗa hannayenta ta buga uwar tagumi kamar wadda aka aikowa da wahayin yinsa, ta luluƙa duniyar tunanin ya zata yi da rayuwarta, har yanzu ta kasa iya gane cewa damar da Allah ya bata a baya ne take wasa da shi son ranta, tana yi kuma ba tare da godiya ga Allah ba, to yanzu damar tana neman kubce mata, ta kasa iya gane hakan ma bare ta yi ƙoƙarin dawo da damar izuwa gareta..... Tirƙashi, akwai matsala fa my people's, mu je dai zuwa.
A parlourn Aunty Hauwa ta zauna, ta tsantsara kwalliyarta cikin wata shegiyar lace mai kyan gaske, da alama ma case ɗin maman Zainab ɗin bai wani dameta ba, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya a kanta irin yau ba mutuncin nan, sai wani kwaɓe fuska take yi kamar wadda taga kashi.
Fitowa maman Zainab ta yi daga room ɗinta cike da damuwar halin da take a ciki, tsawon shekarun nan da suka yi aure baban Zainab bai taɓa yi mata makamancin haka ba, har ya share tun jiya bai yi mata magana ba har yau, abin dole ya jefata cikin damuwa sosai, a maimakon ta kira mahaifiyarta ta sanar da ita abin da yake faruwa, sai ta sake kirawo Aunty Hauwa kuma.
"Hauwa ki zo mu shiga cikin bedroom, baban Zainab yana nan fa". Maman Zainab ta faɗa murya ƙasa ƙasa.
Okey Aunty Hauwa ta amsa tare da ɗaukar wata ƴar figaggiyar jakarta irin na dillalai, ga gyalenta dama a kafaɗa ta yafo shi kamar ba matar aure ba, burinta kawai su shiga ciki ta tambayi maman Zainab ɗin baban Zainab ya sha maganin? A ƙage take da ta ji ya sha ɗin ko bai sha ba?.
A haka ta miƙe da nufin su shiga cikin bedroom ɗin dan rashin hankali irin na maman Zainab da kuma damuwa da ya rufe mata idanu.
Tana miƙewa tsaye sai ga baban Zainab ya fito cikin shirinsa na shadda mai shegen kyau launin sky blue, ɗinkin manyan kaya ne, so ya ɗaura babbar rigar ma a sama, a takaice dai makurar shigar mutunci ya yi, da alama yau ma ba zai ci abincin maman Zainab ba, kamar dai daren jiya, dan dai ga shi ya kammala shirin fita abinsa.
"Sannu da fitowa, ina kwana?". Aunty Hauwa ta faɗa cikin sanyin murya.
Turus ya ja birki ya tsaya tare da juyo da kallonsa a kanta, wani irin faɗuwar gaba ya ji a lokacin da ya sauke idanunsa a kanta. Da ni da ku duka mun san cewa baban Zainab in ya shigo ya sami maman Zainab da bakuwa wlh ko kallon in da suke baya yi, baƙin suna gaishesa ma baya tsayawa, wani lokaci kafin ya amsa masu gaisuwar nasu ma ya kai bakin kofar ɗakinsa, amma yau sai ya tsaya tare da juyowa yana kallon Aunty Hauwa.
Maman Zainab ta ɗan yi mamaki, amma sai ta ce kila zai tambayi Aunty Hauwa ɗin ina ta je jiya ne, dan haka sai bata wani damu ba.
"Sannunki da zuwa Hauwa ya gida ya yara?". Ya faɗa yana bata full attention ɗinsa.
Murmushi ta sakar mashi kafin ta amsa mashi da komai lafiya lou.
Shiru ya ɗan tsaya tare da zuba mata idanu yana ta kallonta. Maman Zainab kuwa sai ta taɓe baki tana ganin abin kamar a Tv a gabanta, ita kuma Aunty Hauwa sai wani irin murmushi take yi mashi.
"Yanzu zaki tafi ne na kai ki gida?". Baban Zainab ya tambaya.
Wani irin zaro idanu maman Zainab ta yi, abin da bata taɓa ji ba, ba kuma ta taɓa gani a tattare da shi ba, kai ina bata yarda ba, a mafarki ta ɗauki abin, dan haka sai ta kai hannunta saman face ɗinta ta ɗan mari kumatunta wai idan mafarki take yi ma ta farka.
Amma ina sai ma ji da ta yi Aunty Hauwa tana cewa. "E zamu iya tafiya a tare duk da ba yanzu naso tafiya ba, amma tun da zaka mayar dani ai komawa ta kamani".
"To muje ko?". Ya faɗa yana mai cigaba da kallon face ɗinta sosai, sai wani uban murmushi take yi.
Maman Zainab bata ankara ba tana can tana tunanin mafarki take yi ne ko ba mafarki ba kawai sai ganin Aunty Hauwa ta yi sun jera da baban Zainab sun nufi wajen parlourn.
Ai bata san lokacin da ta bi bayansu ba, a harabar gidan ta ce. "Hauwa menene haka kuma?".
Dakatawa daga tafiyar da suke yi Aunty Hauwa ta yi tare da juyowa ga maman Zainab ɗin, ɗaure fuska ta yi sosai kafin ta ce. "Wacece kuma Hauwa? Ni kike kira ko dai wata?". Tashin hankali da ba'a sanya mashi date kenan!!.
Wani irin zaro idanu waje maman Zainab ta yi, tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa, cikin tashin hankali ta ce. "Hauwa ban gane me kike faɗa ba? Ban gane me kike nufi ba? Ko dai kunnuwana sun dai'na ji ne? Ko dai har yanzu a cikin mafarki nake ne?".
Kallon baban Zainab Aunty Hauwar ta yi tare da cewa. "Abu Zee mu je ko? Bani da lokacin A'isha ni kam".
Da okey kawai ya amsa mata ba tare da ya kalli in da maman Zainab ɗin take tsaye ba, kamar bai taɓa saninta ba a duniya.... Tashin sense kenan yau ake yinta a wannan gidan.
Gaba Aunty Hauwa ta yi tana wani rangwaɗa tare da kara gaya mashi su je ita fa bata da lokacin maman Zainab a yanzu. Rufa mata baya ya yi da nufin su tafi ɗin.
Ai tsabar kishi da bakin ciki yasa Maman Zainab bata san lokacin da ta yi kukan kura ta damko wuyar Aunty Hauwar ba, idanunta sun rufe, wani irin bakin cikin take ji kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, wani irin cin amana ne wannan mai azaban raɗaɗin zafi haka?.
Cikin sauri baban Zainab ya fara ƙoƙarin kwatar Aunty Hauwar daga shaƙar da maman Zainab ta yi mata, da alama mafa baban Zainab ya manta wacece maman Zainab. Tirƙashi.
Maman Zainab kuwa ta shaƙeta da iya karfinta na karshe tana faɗin wlh sai ta kasheta, azzaluma maciyi amana, su taso a tare su yi karatu a tare, komai a tare suke yi ne zata nemi ta ci amanarta haka? To wlh ba zata barta ba, kasheta zata yi sai dai duk abin da zai faru ya faru.
Wani irin mari da baban Zainab ya sakar mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wuyar Aunty Hauwar ba tana zunduma ihu kamar zararriya. Wani irin kukan kura ta sake yi ta................
Tashin hankali, akwai babbar cakwakiya na kin ƙarawa a wannan gidan, kenan Aunty Hauwa amanar maman Zainab ta ci? Ta kaita wajen malami da sunan samun mafita kenan kanta ta shiryawa hanya mai kyau ba maman Zainab ɗin ba?🤔 Ita kuma maman Zainab cikin rashin sani ta bashi maganin kaunar Aunty Hauwar da hannunta ya sha?🤔 Ga shi har da ƴaƴanta su Khadijah ta bawa suka sha dan rashin hankali da rashin tunani? To kenan ya makomarsu take su kuma? Suma zasu bi ayarin Aunty Hauwa kamar babansu kenan? Bala'in nan, wannan shi ne bala'i, akwai yaki gagarumi a cikin wannan gida, ya makomar maman Zainab? Farkoma ya makomar auren Aunty Hauwar? Da ni da ku dai duk mun san tana da aure? Alamu kuma sun nuna baban Zainab dai ya kamu da sonta, kuma ga dukkan alamu ita ma hakan take so, to ya kenan batun nata mijin?🤔 Ina su maman Haidar? Zasu yarda da hakan kuwa? Kada ku manta sun yi mashi mata fa a cikin family, lallai akwai rikici da rikita rikita, yau akan Aunty Hauwa baban Zainab ya mari Maman Zainab, tab duniya kenan, amana ta yi ƙaranci, ni dai PRINCESS TEEMA na haɗa kayana sai mun haɗe daku gobe dan jin yadda wannan bala'in yakin da ta tinkaromu zata kaya!! RAWANIN ZALINCI ya fara ɗaukar tafasa ma ba zafi ba, Zalunci ta ko'ina😥💔
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
Wani irin mari da baban Zainab ya sakar mata ne yasa bata san lokacin da ta saki wuyar Aunty Hauwar ba tana zunduma ihu kamar zararriya. Wani irin kukan kura ta sake yi ta damko wuyar Aunty Hauwar, idanunta sun rufe, ita dai ta kashe Aunty Hauwa kawai hankalinta ya kwanta.
A karo na biyu baban Zainab ya kara mata wani zazzafar mari, sai dai a wannan