take yi tana tunanin ta in da zata kalli Ramish, amma shiru babu shi babu labarinsa.
Yauma dai kamar kullum, ta gama aikin gyaran parlourn ita da su Fadila da suka tayata, tana shirye cikin arab jallabiya ash color, ta yi kyau matuƙa, yanzu ta kara gogewa ta yi wani fresh da ita, ta kuma ɗan yi kumatu, amma kullum tana cikin zulumi tare da fargabar ya zata kalli Ramish? And ya zata kaya da wannan aiki da yau tsawon wata guda kenan bata fara shi ba? Yaushe zata kammala wannan aiki har ta koma ga mahaifinta?. Kullum tana cikin yin wannan tunani.
"Leesharh ki je ki gyara room ɗin guyson and na Aunty Sharifat bari mu kuma mu fara shirya kayan abinci kamar yadda muka saba". Cewar Fadila.
Da okey ta amsa masu tare da nufar room ɗin nasa, shi kansa Omar ɗin yau tsawon wata kenan bata samu damar ganinsa ido da ido ba, sai dai a wannan hoton, kuma kullum ita take gyara mashi room ɗin nasa, amma suna samun saɓani sosai da shi, wani lokaci sai ya fita take shigowa ta gyara ɗakin, wani lokaci kuma tana gama gyara ɗakin ta fita shi kuma zai shigo, Sharifat ta so ta haɗata da shi dan ya ga kyakkyawa, amma ina ba dama, dan kuwa bai zauna ba, yana shirye shiryen komawa KINGDOM OF POWER, so dayawan lokuta yana gidan King Badeen, yanzu bai cika zama a gidan Abu Abdussalam ba, shiyasa basu haɗu ba.
Room ɗin nasa ta nufa, hannunta na rike da mooper da abin share share. Duk da ta san cewa ba lallai ta sami mutun a cikin room ɗin ba hakan bai hanata ta yi sallama cikin sanyin murya ba. Tana yin sallamar kuma ta afka cikin room ɗin. A tsakiyar ɗakin ta ajiye kayan share share da goge gogen nata. Kai tsaye ta nufi saman katafaren bed ɗinsa na alfarma mai matukar girman gaske, room ɗin nasa ya ji komai na more rayuwa, sai tashin kamshi yake yi, ko'ina tsab tsab, amma a haka sai ta sake gyarawa ta goge ko'ina.
Jibgegiyar duv ɗinsa dake a saman bed ɗin nasa ta sanya hannu tana ƙoƙarin janyewa, domin ta cire ta canza mashi wani, kullum sai ta sake wani bedsheet ɗin, bata da tabbacin ana kwanciya a gadon ne ko ba'a kwanciya, amma dai kullum sai ta canza.
Tana ganyo duv ɗin mutun ya bayyana kwance a saman gadon, da yake duv ɗin yana da girman da idan mutun ya kule a ciki ma ba lallai kasan yana a cikin ɗin ba, ba zaka yi zaton akwai shi a ciki ba, shiyasa ta zo ta janye kawai.
Tana janyewa kuma kamar wadda aka yi wa allura ya fara mutsu mutsu haɗe da murkusoso kamar wadda yake shirin mutuwa, tamkar ana zare mashi rai, juyi ya fara yi a saman bed ɗin, jikinsa na a sanye da farar jallabiya tas da shi, farar kyakkyawar fuskarsa ta yi kal kal da ita, ya yi wani fayau, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin mawuyacin hali, kyakkyawar arab hairnsa da ya zubo mashi har ta gaban goshinsa yasa ba'a ganin face ɗinsa da kyau, ga shi kwanciyar ruf da ciki ya yi, so ya bawa Leesharh ɗin baya, ko ba'a gaya mata wanene bane tasan shi ne guyson, saboda room ɗinsa ne, kuma tasan hotonsa, kullum idan ta shigo babbar parlourn da face ɗinsa take fara cin karo, yana sakin ƙayatatcen murmushi, so tasan shi ne.
Ganin shi cikin wannan mawuyacin hali ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, a razane ta zaro dara daran idanun nan nata tana kallon yadda take juyi kamar ba zai rayu ba, idanuwansa a rufe ruf, yama datse idanun nasa ne sosai tamkar zai fasasu, da alama yana jin tsananin azaba, kuma da alama ma baya a cikin hayyacinsa, sai wasu siraran hawaye da suke fita mashi daga idanuwansa suna bin gefe da gefen face ɗinsa, hakan zai kara tabbatar maku da yana cikin mawuyacin hali.
Sam Leesharh bata taɓa kallon irin hakan ba, hakan yasa hankalinta ya yi mummunar tashi, cike da ruɗu ta...........
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 26/8/2024.....✍️📚🌹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
*Assalamu alaikum everyone ina fatan kowa yana cikin ƙoshin lafiya?! Allah yasa! Ina yi wa kowa da kowa fatan alkhari tare da fatan kasancewa cikin ni'ima da kuma rahmar Ubangiji, a duk in da kuke Allah ya cigaba da dafa maku yana kara tsareku da tsarewarsa, Allah ya jiɓanci al'amuranmu bakiɗaya, ina matuƙar farinciki tare da godiya da irin tarin addu'oinku dana samu daga bakunanku masu albarka, na kuma ga tasirin addu'oinku wlh, Allah ya amsa jikina ya warware Alhdulillah, babu abin da zance maku face in ce Allah ya bar kauna ya kuma cikaku da farincikin da babu bakinciki a bayansa, arxikin da babu talauci a bayansa, daga karshe Allah ya bar kauna ina godiya 💘 taku PRINCESS TEEMA ta amana✍️💘*
E____________38🔥
Sam Leesharh bata taɓa kallon irin hakan ba, hakan yasa hankalinta ya yi mummunar tashi, cike da ruɗu ta kai hannunta ta mayar mashi da duv ɗin da nufin ta gudu ta fice daga room ɗin kada ace ita ta yi mashi wani abin, kunsan maras gaskiya da shegen tsarguwa, sai yaga kamar komai ƙanƙantar motsi idan ya yi asirinsa zai iya tonuwa.
Sannan kuma kunga tana janye mashi duv ɗin ne ya fara wannan murkusoson, so sai tana ganin kamar za'a ce ita ce sila.
Har ta juya zata fita ta tsinkayo zazzaƙar voice ɗinsa ya daki dodan kunnuwarta, idanunsa a datse gam yana ruwan hawaye, voice nasa ɗan siriri kamar na mata, ga shi cool voice gare shi sosai, akwai daɗin saurara, bare da ya haɗu da yana cikin ciwo, sai maganar tasa tana fita wani iri.
Cikin harshen larabci ya fara faɗin. "Shareee.... Shareee zo ki bani drugs ɗina, kada ki kira su Ummie kin ji?". Yana magana ne a tunaninsa Sharifat ce, da alama ya ji shigowarta kenan.
Kamar zata gudu, dan tana tsoron kada ace ita ta yi mashi wani abin, bare kuma yadda ta ji kowa a gidan yana yawan maganarsa tasan tabbas ɗan gata ne da ake ji da shi, to tana tsoron kada wani abin ya haɗasu tun bata fara aikinta ba ta shiga uku. Amma kuma tana da tausayi da raunin zuciyar da ba zata iya tafiya ta barshi a cikin wannan hali ba.
Juyowa ta yi a hankali tare da kai kallonta saman gadon, har lokacin yana murkusoson nan dai yana ambatar sunan Sharifat come and give me my drugs. Shiru ta ɗan yi tana tunanin Sharifat dai bata nan, tana school, koda kuma tana nan ita a ina tasan zata nemota a cikin wannan gida har ta kira mashi ita? Yau watan ta guda kenan a gidan idan ba time to time ba ko Ummie bata wani samun damar gani sosai a wannan hawa da suke, Sharifat ɗin ma ita take zuwa in da suke dan ta ce Leesharh na yi mata kyau, yarinyar tana da saukin kai, so ita take zuwa wajen Leesharh ɗin ta ce ta zo su ɗan yi hira, Leesharh ta bata labarin ƙasarsu, so dani da ku duk mun san a kan dokar da Leesharh ɗin take na ja mata kunnuwa da aka yi a kan kada ta yarda ta yi hira da kowa, hakan yasa bata taɓa yarda ta saki jiki da Sharifat ɗin bare ma har su yi hira, bata yarda da hakan, sai dai ta yi shiru.
Idan Sharifat ɗin ta ce mata to ki yi magana mana, sai ta ce ai bata san me zata ce ba, murmushi kawai Sharifat take yi ta ce na lura baki da yawan magana amma zan koya maki, iya murmushi kaɗan kawai take yi daga haka bata sake yin magana, to haka suke rayuwa a cikin gidan, Leesharh tana yawan janye jikinta ga mutane sosai, bata taɓa yarda ta buɗe baki ta yi magana, izuwa yanzu voice ɗinta ya koma yadda yake sosai da sosai, maganarta na fita da kyau da kyau, tana da daɗin murya sosai, ta gama shanye magungunan da Dr Suhail ya bata.
Sanin cewa ba zata sami Sharifat bane kuma tana da zuciyar tausayi sosai, ta ji ba zata iya guduwa ta bar shi a cikin wannan mawuyacin halin ba ne yasa ta juyo da sauri ta dawo wajen bed ɗin. Kaɗan ta sake janye duv ɗin kasa. Sosai da sosai yake kuka, har wa lokacin kuma idanuwansa a rufe ruf.
Matsowa kusa da shi kaɗan ta yi tare da duƙowa kansa, cikin kwararriyar laraɓcinta tare da yi mashi magana ƙasa ƙasa a tawajen kunnuwansa ta tambayi ina magungunan nasa suke?.
Duk da yana cikin raɗaɗin ciwo hakan bai hana ya gane cewa wannan ba voice ɗin Sharifat bane, hakan yasa ya ɗan yi jim kaɗan kafin kuma ya ce. "Who're you?".
Dum dum ta ji gabanta ya bada bugu, sai ta ji ta yi nadamar zuwanta wajen nasa ma, a cewarta da ta gudun kawai abinta, ta tsorata sosai saboda bata kullo gaskiya ba. Kai ya Allah kasa mu kasance masu gaskiya a duk in da muke, rashin gaskiya bai yi ba, domin kuwa idan baka da gaskiya ka rinƙa shiga fargaba da faɗuwar gaba koda sunanka kawai aka kira a waje, duk karasa sukuni ka takura kanka, ka rasa walwala ka kasa iya rayuwa kamar kowa, koda iya wannan kawai aka barka kana cikin masifa wlh, jama'a mu riki gaskiya da amana domin samun rabauta duniya da lahira!!.
Jin ta ɗan yi shiru ne yasa ya sake maimaita mata tambayar da ɗan kausasshiyar murya tare kuma da fara ƙoƙarin buɗe idanuwansa da suka yi mashi tsananin nauyi saboda ciwo, ga kuma kukan da ya sha, har wani sara mashi kansa yake yi.
Ƙoƙarin juyawa ta yi dan ta gudu, a shirmenta zata je ta tonawa kanta asiri, ko me abin guduwa a wajen oho, ta tsargu ne.
Bata bar wajen ba ya damko hannunta da ɗayar hannunsa tare kuma da ƙarisa waro waɗan nan manya manyan idanuwan nasa masu kama da na Auta Gimbiya Zunaira.
Idanun nasa sun yi jajir da su kamar wuta saboda kuka. Nutsuwa ta yi tsit tare da sunkuyar da kanta ƙasa, tsoro ne karara a saman face ɗinta, sai dai hakan bai hana ta rinƙa satar kallonsa ta ƙasan ido ba, kullum ma idan ta shigo babbar parlourn sai ta yi ta karewa hotonsa kallo, yana yi mata kyau sosai da sosai, bare ma iya ɗaukar wankarsa, guy ne sosai, in dai ɗaukar wanka ne to daga kansa an rufe kofa, gwani ne, kowani irin kaya ya saka zama mashi suke yi ɗas a jikinsa kamar dan shi aka yi su.
"Who're you?". Ya sake tambaya yana ciza laɓɓansa, alamar yana jin azaba. Ga hawayen kuma suna cigaba da wanke mashi fuskarsa.
Cikin in'ina ta gaya mashi wacece ita da kuma matsayinta a cikin wannan gida nasu. Sake mata hannunta ya yi tare da mayar da idanunsa ya datsesu gam. Shiru ya ɗan yi na ƴan sakani kafin ya ce ta buɗe drawers ɗinsa ta ɗauko mashi drugs ɗinsa and bottle water mai ɗumi ba mai sanyi ba.
A hanzarce ta amsa mashi da okey, har lokacin jikinta yana ɗan kerma ta fara bubbuɗe drawers ɗin, dan bai gaya mata a cikin wanne drawer magungunan suke ba, ya dai ce kawai ta buɗe drawers ta kawo mashi magungunan.
Tana buɗe drawers ɗinsa na wajen bed ɗin ta ci karo da uban tulin hotuna sosai, kala kala, wanda yake a saman kawai ta kurawa idanu ne, hotonsa ne shi da twins Obaid and Omaid ƴan albarka jikokin hajiya Akka tamu......😅
Da yake su twin's ɗin suna da tsawo sosai sai yasa da kaɗan Omar ɗin ya fisu tsawo a hoton, sun yi matuƙar kyau sosai da sosai, a gidan kakansu King Badeen suka ɗauki hoton, dukkansu suna cikin arab alkyabba bakake, while daga ta ciki suna sanye da farar arab jallabiya, sun naɗa rawani irin na sarauta fari tas, Omaid yana rike da sandar sarauta mai matuƙar kyau mai kuma tambarin kan zaki, Obaid da Omar fuskokinsu ɗauke da cool murmushi, shi kuwa Omaid fuska a ɗaure sosai, dama idan baku manta ba shi bai cika dariya ba sai sun shirya mugunta sosai. One thing about this twin's da baku sani ba shi ne, su fa ba normal makaranta suke yi ba, tun suna yara they're very very stubborn, hakan yasa Ramish ya sanya su special swat academy, a tunaninsa idan suka shiga nan zasu nutsu in sun ci kwakwa, bai san cewa kuskure ya tabka ba, domin kuwa ƙaro rashin ji over tare da taurin zuciya da rashin imani suka yi, sun zama basu da tausayi, ga ɗan banza rashin ji! Mugunta kuwa ba'a magana kuma shaida ne, kun ganewa idanunku, da alama duk wasu kayan muguntar da suke amfani da shi daga school suke tahowa da shi, domin dai in ba daga school ba babu in da zasu samo shi. (Yah Ramish ne ya kaisu special swat academy, wato makarantar koyar irin aikinsa kenan, ya kai su ne dan ya samu su nutsu, amma kun dai ji yanzu ga shi mahaifiyar Yah Ramish ɗin wato maman Gimbiya Aneesa ita suke shiryawa mugunta da zasu yi mata idan zasu dawo Dubai😅 hmmm ba zan yi magana ba, amma wlh idan Ramish ya kamasu ko King Zuhair sai ya yi da gaske zai iya gane su, saboda irin ragargazar da Ramish ɗin zai yi masu😅 Allah dai ya kwacesu, mu dai ana yi muna shan Maltina ko my people's?.🥱)
Kasancewar tasan halin da yake a ciki ne yasa bata tsaya gulmar ganin hotunan ba, amma dai ta so duba hotunan ko zata kalli hoton Ramish ko dai na wani daga cikin ƴan gidan, amma haka ta hakura ta rufe drawer ta miƙe.
Kusa da shi ta dawo, a nutsu ta ce. "Guyson ban ga drugs ɗin naka ba".
Ciza lips ɗinsa ya yi da karfi, alamar azaban zafi yake ji, juyi ya yi ya sake kifawa a kan cikin nasa, idanuwansa a lumshe ya sanya ɗayan hannunsa yana laluɓar saman bed ɗin kamar mai neman wani abin.
Cike da tsoro tab a ranta ta ce. "Wani abin kake nema ne?".
Ƙasa ƙasa ya amsa mata da. "My phone".
Ɗan juye juye ta fara yi tana neman mashi phone ɗin, hannu ta kai ta kara janye duv ɗin nasa ƙasa. Can wajen kyawawan fararen ƙafafunsa ta hango haɗaɗiyar wayar tasa. Cikin hanzari ta ɗauko mashi, hannunta sai kerma yake yi.
Miƙa mashi ta yi tare da ce mashi "This is the phone".
In a low voice sosai ya ce. "Check my contacts, ki duba Yah Ramish or Yah Raj ki kira mun ɗaya daga ciki".
Wani irin muguwar faɗuwar gaba ta ji jin sunan Ramish, har wani irin haɗiyar wahalallen yawu ta yi, a duk lokacin da kunnuwanta suka ji sautin sunan Ramish har cikin ranta take jin kanta a matsayin gawa, ji take yi kamar shi ne ajalinta, ita da bata ma san wanene bane, amma a yadda ta kalli yanayin gidan da kuma yanayin yadda take tsintar maganarsa time to time a bakin su Radia yana mugun sakawa ta ji cewa in dai asirinta ya tonu to tabbas Ramish shi ne ajalinta!.
Tana shiga contacts ɗinsa da sunan My baby (Gimbiya Zunaira) kenan ta fara cin karo, ƙasan numberta kuwa number Dr Raj ne da ya yi saving da Yah Raj. Dialling na number ta yi, gabanta sai dukan uku uku yake yi. Ringing wayar ta fara yi har ta kusa katsewa, sannan ne aka yi picking call ɗin.
A hanzarce ta miƙa mashi wayar. Sam ya kasa iya kai hannunsa ya karɓa. Ganin hakan yasa ta matso mashi da wayar a kusa da ɗan bakinsa tare da sanya wayar a speaker.
Daga ɗayan ɓangaren wani irin cool voice ya fara magana da. "Assalamu alaikum Guyson".
Sautin kukansa ya kara tare da cewa. "Yah Raj come and help me........ My". Sai kuma ya yi shiru yana goggoga kansa a jikin pillown da ya kwantar da kansa.
Sosai Leesharh ta tsorata lokacin da Dr Raj ya yi magana a karo na biyu. "Omar where are you?!".
Ya yi maganar ne cikin ɗaga murya, hakan ne ya tsoratata, tamkar bashi ne ya yi magana cikin sanyin murya da farko ba.
"Yah Raj am in my room". Da kyar ya furta hakan.
Diff aka kashe kiran ba tare da an sake yin magana ba. Ajiye mashi wayar tasa ta yi a kusa da shi, a hankali ta lallaɓa ta nufi kofar fita daga cikin room ɗin.
Tana sanya kai zata fita suka yi karo da mutu, baya baya ta yi ta faɗi ƙasa. Shi kuwa shigowa ciki ya yi bai bi ta kanta ba, da alama ma bai san ya buge mutun ba, dan hankalinsa kacukam yana a saman bed ɗin guyson, tun da ya shigo waɗan nan eyes ɗin nasa irin na King Zuhair suna a saman bed ɗin kawai, sanye yake da wando three cuter milk color, sai t-shirt sky blue mai haske sosai, ƴaƴa King sun gado tsawo kam, dogaye da su, so shi ma Dr Raj yana da tsawo sosai, ga cikar halittar sai ka rantse da Allah renon commander ZAFAR ne shi ɗin, tsayayye ne sosai mai ji da lafiya, kyakkyawar gaske ne sosai, duk dai Akka suka ɗauko. Da alama yau bai je hospital ba, domin kayan shan iska ce