da sauri ta mayar da rigarta tana turo baki, danasanin meyasa ta nunawa Chuchun ma ta fara yi, har da wani cewa da tasan haka ne ai ba zata gayawa kowa ba, da farko ma Yah Jaish ta so fara zuwa ta gayawa kafin ta gayawa Chuchun sai ta gayawa Mommarta, ashe Allah ya taimaketa ma da bata je ta gayawa Yah Jaish ta kuma nuna mashi ba.
Nima na ce amma da ta je ta gaya mashi zan yi mata dariya kam, yanzu ma n yi mata, Chuchu ta kalle mata tula tulanta da suka fara fitowa😅😅😅😅😅 bye my people's sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu.....
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 5/9/2024.....✍️📚🌹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
"Meyafaru our Auta?". Ta tambayeta tana ɗan murmushin.
"Babu komai Aunty Chuchu". Ta yi maganar kamar zata fasa kuka, ta kuma yi maganar tana sanya hannu ta goge kwallar da yake a saman face ɗinta.
Ɗan rungumota kaɗan Chuchun ta yi tare da ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi tana ɗan tsokanar.
"Sai ki sanar da Yah Omar ko?". Cikin zolaya ta yi maganar.
"Allah Aunty Chuchu ki bari mana bana so". Ta yi maganar kumatu a kumbure kuma cikin shagwaɓa.
"To na bari, amma kin manta ke da Yah Omar akwai amana ne? Bafa ki ɓoye mashi komai shi ma kamar yadda baki ɓoye mun, wannan ne yanzu ba zaki iya gaya mashi ba? Lallai Auta kenan yanzu babu amana da nuna kauna? Kin manta yawan gaya mashi da kike yi cewa shi ne pleasurenki? Tun ba'a je ko'ina ba an fara ɓoyewa pleasure abubuwa". Still cikin zolaya ta yi maganar.
"E ɗin Aunty Chuchu na ɓoye mashi ɗin, kuma kema Allah da ban nuna maki abuna ba".
Wani irin dariyar iyashege ta tuntsure da shi, cikin dariyar take faɗin. "Kai menene kuma abunki ɗin to? Bashi da suna ne".
A ƙule Autar ta raba jikinta dana chuchun tare da ɗaukar wata jibgegiyar pillow da ta sha rigar bedsheet mai matuƙar tsada da nufin ta fara dukan Chuchun da shi.
Ai da gudu Gimbiya Chuchu ta sauka daga gadon tana faɗin. "Bari ma na je na gayawa su Aunty Sarina har da Aunty MieMie cewa Auta ta fara kirgan dangi, ta girma".
Da gudu Autar ta biyota tana faɗin. "Allah Aunty Chuchu ba zan barki ba kuma mun ɓata, kada ki sake yi mum magana, babu ruwana dake daga yau". Tana magana tana binta da gudu.
Kai tsaye part ɗin King Chuchu ta nufa sai dariya take yi kamar wata zararriya, yau Auta na neman kasheta da dariya.
Tana gudu tana waigo Autar taga ko ta kusa isota har ta shiga parlourn King, sai waigowa take yi bata ankaraba ta ji fa bugi faffaɗar kirjin mutun. Baya baya ta yi tana ƙoƙarin faɗuwa tare da ƙoƙarin dakatar da dariyarta da yake shirin zama kuka duba da yadda ta yamutsu fuskarta, da alama ta bugu sosai saboda gudu take yi.
Wuyar doguwar rigar jikin nata ya riƙo tare da janyota gaba ya tsayar da ita a kan kafafunta bai bari ta faɗi ƙasa ba.
Auta ko a jikinta da gudu ta ƙariso wajen ta fara sauke mata wannan pillown a gadon bayanta tana faɗin. "Kuma ko na dakeki ba zan huce ba, mun ɓata kenan, tabbas mun ɓata da gaske!".
A hanzarce Jawad ɗin ya sanya hannunsa ya tare dukar da Autar take kawo mata ba kakkautawa. Saura kaɗan Chuchun ta kifa a kan kirjinsa saboda dukan da Autar ta yi mata ta baya da pillown na ƙarshe yasa ta yi gaba kamar zata kifa, shi kuma a lokacin yana sanya hannunsa zai tari pillown kenan, hakan yasa ta kusa kifawa a kirjin nasa.
"Sorry our Auta tuba muke yi". Yah Jawad ya faɗa yana riƙo pillown da hannunsa ɗaya.
"Allah ya Jawad ni na zan yi sorry ba, yau mun ɓata da Aunty Chuchu baram baram!". Tana magana tana kwaɓe fuska tare da turo baki.
Cike da iya shege da tsokana tana murje gaban goshinta ta ce. "Yah Jawad to ka tambayeta me nayi mata da zata kama dukana haka?". Tana kai karshen maganar wani dariyar ne ya so kubce mata duk da turɓune fuska da ta yi lokacin da ta buge da kirjinsa, maganar a tambayi Autar yasa ta ji dariya ya zo ya kori kukan da take ƙoƙarin yi wa yayan nata.
Kuka Autar ta sanya masu tare da juyawa zata bar wajen dan ta ji cewa Yah Jawad ya tambayi me Gimbiya Chuchu ta yi mata. A hanzarce ya riƙo hannunta bai bari ta bar wajen ba. Cikin sanyin murya ya ce. "Zo Autarmu, zo ki gaya mun me ta yi maki in rama maki yanzun nan".
Habawa me Chuchu zata yi face dariya, shi Yah Jawad fa bai san tambayar me Chuchun ta yi mata bane yasa zata gudu ya zo yana wani tambaya shi ala dole zai rarrasheta kuma ya rama mata.
Hawayen gaske ta fara yi mashi bata ce komai ba, sai wani irin harara da take wurgawa Chuchun da waɗan nan dara daran idanuwan nata. Shi dai Jawad ya rasa gane me matsalar, sun saka shi a duhu.
"Ki faɗi me na yi maki Yah Jawad ya rama maki ya ce". Chuchu ta faɗa ita ma tana jefa mata hararar.
Bakinciki kamar Auta ta sanya hannu a kai ta kurma ihu. Faɗawa jikin Yah Jawad ɗin ta yi tana ɓoye fuska tare da fara yin hawayen gaske, dan ranta ya ɓaci sosai, Chuchu ta kureta.
Wani irin kallo mai wuyar fassaruwa Yah Jawad ɗin ya jefawa Chuchun kafin ya sassauta muryarsa kasa sosai. "Me kika yi mata Jannat?".
Da sauri Autar ta ce. "Babu abin da ta yi mun Yah Jawad". Tana magana tana goga kanta a kirjinsa.
Izuwa yanzu ya fahimci abin sirri ne a tsakaninsu Chuchu take yi mata wasa da hankali take kuma sanyata kuka a banza. Dan haka sai ya ce. "Shikenan our Auta, jeki abinki yanzu zan bata punishment ba tare da na ji ma me ta yi maki ba". Ya yi maganar yana shafa kyakkyawa arab hairnta da ko ɗankwali bata ɗaura ba ta shigo room ɗin na Chuchun a ruɗe, dan a tunanin wani abin ne ya sameta.
Da sauri ta raba jikinta da na shi tare da nufar hanyar komawa room ɗin na Chuchun rike da pillown tana faɗin. "Allah Aunty Chuchu ba zan yafe ba idan kika gayawa wani".
Juyawa da gudu ita ma Chuchun ta yi da nufin ta bi bayanta dan ta ji Yah Jawad ɗin ya ce zai bata punishment, ba zata iya ɗaukar punishment ɗinsa ba.
Aikuwa bai bari ta bar wajen ba ya yi saurin riƙo hannunta tare da janyota ta dawo in da take tsaye ta tsaya. Ƙasa da murya sosai ya yi kamar wani na yi mashi laɓe, kamar kuma maras gaskiya ya fara magana, ita kuma Auta ta yi tafiyarta sai kumbure kumbure take yi.
"Me kika yi mata? Meyasa zaki saka mana ita kuka?". Yana magana yana kallon cikin kwayar idanunta, while ita kuma tana ɗan satar kallonsa ta wani yi ƙasa da kai kamar wata mai ɗaukar darasin hadisi a islamiya!.
"Babu fa komai Yah Jawad". Ta faɗa a sanyayye.
Shiru bai sake yin magana ba, domin ya shagaltu da kallonta, gaskiyar uncle Abbas da King da suke cewa in dai zai haɗu da chuchu sai ya karewa ƴarsu kallo tsab sannan yake kama kansa, ashe dai sun san komai.
Jin ya yi shiru bai sake yin magana bane yasa ta ɗago ido dan ta ɗan saci kallonsa. Ai kuwa tana ɗagowa suka yi four eyes.
"Yah Jawad in tafi?". Ta faɗa ba tare da ta kawar da kallonta daga saman fuskarsa ba, sai dai ba kallon cikin kwayar idanunsa take yi ba.
"Ban gama kallonki ba ai my Jannat". Ya faɗa ba tare da yasan lokacin da hakan ya fito daga bakinsa ba, sai da ya ji ta ce. "Kallona kuma Yah Jawad? Na yi kyau ne?".
Nisawa ya yi, kamar mai jin barci ya furta. "Over ma kuwa kika yi kyau".
"To Yah Jawad ka mun hoto". Cike da zumuɗi ta yi maganar.
Wani irin cool ajiyar zuciya ya sauke tare da ciro wayarsa ɗayar. "Where's my other phone da na baki jiya?".
Sai a lokacin ta tuna da wayar. "The phone is in my room, in je in kawo shi yanzu?". Murya a warware ta yi maganar.
Girgiza mata kai kawai ya iya yi alamar a'a, bai iya sake furta komai ba sai matsowa da ya yi kusa da ita tare da shiga camerar wayarsa, sannan ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman shoulder ɗinta. Zafafan hotuna ya fara ɗaukarsu, ita da ta ce ya ɗauketa ita kaɗai ya ɓige da ɗaukarsu a tare.
Sai canza style suke yi sun manta da cewa a parlourn King fa suke, ga shi yau King yana da baki sosai saboda zuwan su Ramish da za su yi gobe, jama'a suna ta kai koma a part ɗin, already kun san dama akwai part na saukar muhimman bakinsa na kusa sosai a cikin part ɗin nasa, so su Jawad suna tsaye ne a tsakanin wannan ɓangare na saukar bakin da kuma hanyar nufa master room na King.
Canza style ya yi daɗi harda kwanciya a saman kirjinsa ta yi, yau abin nema ya samu, Chuchu mayyar ɗaukar hoto, to ga dama ya samu, mai hanata ɗaukar hoton ya takura mata yau da kansa yake ɗaukarta, ai style kuwa sai abin da kuka gani.
Suna tsaka da kashe hotunansu basu ankareba kawai sai tsinkayo muryar Akka suka yi a cikin kunnuwansu tana sababi, ta nufo parlourn ɗin ne tana ta surfa sababi da masifa, da alama wani ya taɓota. Tun daga nesa take faɗin. "Ai Zuhair shi ne ya mori aure, ku cigaba da yi, har ku kwanta a gadon ajalima kada ku dai'na, yo ni idan baku yi haka ba ai sai nace sam sam Zuhair ba mata ya aura ba, kuma idan baku yin haka ai sai na sa a bincika mun ku ko da wata munafurcin a ƙasa, dan cikakkun mata kam dole sai sun ɗana wannan kishi, shi kuma Abbas ba yadda ban yi da shi ba dan ya ƙara aure ya ji daɗin aure amma yaki, shi sam ba aure ya yi ba, dan idan baka haɗa mata biyu a gida suna nuna kishi karara kamar dai matan Zuhair suna faɗa a kanka ba to ba aure ka yi ba, ku ta yi abinku shi ne dai'dai, wadda ta fi sanin kan duniya ta kwace Zuhair ɗin ya tattare a wajenta". Sai sababi take yi.
(Jama'a kun ji mun wannan tsohuwa da bala'i 🤔 ita fa har dattijon arzikinta wato mijinta King Abdul Malik ya kwanta dama ita kaɗai ce matarsa, bata da kishiya, amma take cewa uncle Abbas ya karo aure, Akka sam bata son zama lafiya, ga rikicin tsufa, mata suna faɗa tana kara hura wuta 😅)
Jin motsinta tana surfa wannan uban sababin yasa Jawad yaja hannun Chuchun da sauri suka haura izuwa master room na King, domin idan ya bari Akka ta kama shi da Chuchu a ɗan wannan lungu to fa ya shiga uku, ai ta rinƙa takurawa rayuwarsa kenan, idan ma bata ce zai lalata mata jika ba, dama kun san ba shiri suke yi ba, kullum cikin faɗa da samun saɓani suke, kuma idan baku manta ba Akkar ta sha shiga tsakaninsa da Chuchun tana rabasu faɗa, so tasan basa shiri sam sam, yanzu kwatsam ta gansu a tare a wannan ɗan hanya na zuwa master room ai shikenan ya shiga uku a cikin wanna kingdom ɗin, ba zata barshi ya zauna lafiya ba, kuma abin da yake gudu na kada Jaish ya san halin da ake ciki na tsakaninsa da Chuchun fa to sai ya sani idan Akka ta gansu, bugu da kari Mammiensa ma sai ta sani, kuma ɓoye mata yake yi dan yasan bata son alƙarsa da ƴaƴan King Zuhair, shi kuma a part ɗin ya taso ya girma, ya fi sabawa da su fiye da ƴan uwansa su Sarina ɗin ma, amma bai san dalilin Mammaien ɗin tasa na bata son taga yana alaƙa da ƴan uwan nasa ba, jini ɗaya suke amma tana son raba jini da karfi da yaji.
Kai tsaye room na King suka nufa da gudu, wajen hawa ƴan ƙananan stage da suke a bakin kofar room ɗin na King Chuchu ta yi tuntuɓe ta faɗi, gudun da suke yi ne yasa bata lura da sun iso wajen ba.
Cak Yah Jawad ya ɗauketa suka ƙarisa shiga room ɗin. A lokacin da suka shigo kuma King yana wanka, bai jima da dawowa daga masallacin jumma'ar ba, so shi dama kayansa na zuwa masallaci daban suke da sauran kayansa, saboda daraja da girma da yake bawa ranar, a ranar kwalliya na musamman yake yi, saboda jumma'a babbar rana ce, kayan zuwa masallacin nasa ma na musamman ɗin na musamman ne, idan ya dawo daga masallacin kuma yana yin wanka ya canzasu izuwa wasu na musamman ɗin dan komawa fada ya zauna zuwa yamma irin karfe 5 ɗin nan bayan sallar la'asar kenan, sai a fita yin wannan gasa tasu da suke yi.
Coz yau ba zuwa fada zai yi ba, saboda abin da yake faruwa da Mama, yanzu haka idan ya yi wanka ya shirya wajen Mamar zai wuce, domin idan bai yi haka ba sai ta ce bai yi mata adalci ba, idan Momma bata da lafiya ko Dubai ta koma can yake tarewa, kunga kuwa idan yana son zaman lafiya dole ya zauna kusa da Mamar ma, idan ba haka ba a tashi gidan gabaɗaya da ruwan bala'i......... 😅
Akka dai ta ce idan basu yi haka ba to ba mata Zuhair ya aura ba, da alama fa Akka tana jin daɗin wannan diramar tasu, suna ɗebe mata kewa.
Ganin cewa King na cikin toilet yana wanka, ga kuma Akka a bayansu tana zuwa yasa Yah Jawad ɗin ya sauketa a tsakiyar room ɗin saman shinfiɗar tsakiyar ɗakin, sannan ya riƙo hannunta da sauri suka faɗa cikin dressing room na King. A bayan wajen glass na jera watch ɗinsa suka tsaya suna mayar da numfashi.........
Akka kuwa cikin room ɗin ta shigo tare da zama saman shinfiɗar King ɗin in da yake zama ya huta. A nan ta zauna tana jiran ɗan nata ya fito daga wanka, da alama su Momma sun bakanta mata rai ne yasa ta nufo wajen King dan su yi magana, har ta zauna saman wannan sofa da aka kawata da shinfiɗu na alfarma na gashin jimina bata dai'na zance su Momma ba, sai sababi take yi, aikuwa Allah ya rufawa Yah Jawad asiri, dan a yadda take kan tsini tana surfa sababin nan ta gansu shi da Chuchun a yadda suke ɗin nan ai shikenan rayuwarsa tana kwale kwale, dan ya shiga talatin ma ba uku ba.
Ni kam na ce to su yanzu da suka shigarwa King cikin dressing room ɗinsa ku gaya mun idan ya fito daga wanka zai sanya kaya ya kenan?.🤔 Ya zasu yi idan zai shigo sanya kayansa?🤔 Ga dai Akka a cikin ɗakin, King kuma zai shigo nan, my people's kuna ganin a gudun nan da suka yi sun tsira kuwa?🤔 To ni dai bari na leƙa Daular Abu Abdussalam wato Dubai in dawo, sai naga zasu tsira ne ko asirinsu zai tonu.
Abu Abdussalam empire🤍🔥
LEESHARH....✍️💘
A hankali ta ɗan waro idanun nata waje, from down ta fara kallonsa, a maimakon ta ɗaga idanu ta kalli face ɗinsa, sai ta fara kallon kafafunsa da suke sanye cikin cover shoe masu kyau da tsada launin baki. In a slow ta fara ɗaga idanunta tana binsa da kallon from down ɗin har up.
A tsananin razane ta miƙe tsaye tana zaro idanu waje kamar za su faɗi ƙasa. Domin kuwa a karya na idanunta face ɗin Ramish yake nuna mata, shi ya yi mata gizo a kan fuskar guy ɗin, wannan guy ɗin daban, amma da yake tunanin Ramish ne a ranta sai take ganin kamar shi ne.
Cikin harshen larabci wannan guy ɗin ya ce mata lafiya ta yi irin wannan miƙewa haka? Meyasa kuma ta tsorata da ganinsa? Ko dai ta san shi ne?. Bai san cewa face ɗin Ramish ta gani a tattare da shi ba. Wannan magana da ya yi ne yasa ta dawo cikin hankalinta, nan take idanunta suka kallan mata ainahin kamannin guy ɗin wannan da yake cikakken arab men, fari tas da shi kuma kyakkyawa.
Miƙa mata handkerchief ɗin ya yi yana mai sake ce mata lafiya take kuwa?.
Bata karɓi handkerchief ɗin ba sai dai ta raɓa ta gefensa da sauri domin ta wuce. A dai'dai lokacin kuma Guyson ya iso waje, zai je duba Yah Ramish da ya ki halartar taron ne, zai wuce sai ya hangota tana kuka, shi ne ya ce bari ya ƙariso ya ji me ya sameta ko dan Sharifat sai ya kulata.
Ganin Guyson a gabanta yasa ta ja birki tare da sanya hannu ta hau goge hawayen face ɗin nata da sauri sauri.
Wani irin kallo Guyson ɗin ya bi matashin da ya miƙa mata handkerchief ɗin nan da shi kafin ya ce da shi. "Meka yi mata?". Cikin harshen larabci ya yi maganar. Yadda ya yi maganar kuma sai ka rantse da Allah Bilal ko Ramish ne suka yi maganar, ya yi maganar a dake irin babu wasa a tattare da shi ɗin