ratsa mashi zuciya sosai. Haka shi ma Kamran ya ji sautin wannan kukan nata tana ratsa mashi zuciya, hakan yasa ya kara rungume sosai yana mai cigaba da gaya mata ta yi shiru babu abin da Rocky zai yi mata, har da gaya mata ya yi cewa Rocky fa abokinsa ne, dan haka ta kwantar da hankalinta.
Ina ta jima tana wannan kukan zuci a kusan kafin Kamran ya samu ta yi shirun da kyar, sai sauke ajiyar zuciya take yi.
Sun ɗan jima a haka kafin ta ɗan ɗago kanta daga saman kirjin nasa, cikin tsananin tsoro ta ɗan ɗago idanunta tana leƙo da kai tana leƙen Rockyn, shi dai yana tsaye yana ta kallon ikon Allah.
Ganin sai kallonsu Rockyn yake yi ne yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai yanzu ta yarda da zancen Kamran ɗin na cewa babu abin da Rocky zai yi mata, yanzu kam ta yarda, tun da ga shi yana tsaye shiru yana kallonsu bai cinye su ba, hakan yasa ta yi ƙoƙarin barin jikin Kamran ɗin, tana cigaba da sauke nannauyar ajiyar zuciya.
Bai hanata barin jikin nasa ba, sai ma binta da kallo da ya yi, sai a yanzu da ta nutsu sosai ne kamanninta ya kara bayyana, kuma a yanzu kusa da kusa yake ganinta.
Ɗan kara zaro idanuwan nasa ya yi yana kallonta sosai, ko mutuwa ya yi ya dawo ba zai taɓa mantawa da kamanin mum twins ba, domin lokaci guda matar ta yi wani irin shiga mashi cikin ransa sosai, bayan Mammarsa da kuma Rocky bai taɓa kaunar wani abin a duniya ba kamar yadda ya kaunaci mum twins da twins nata, kullum suna cikin tunaninsa.
Ganin ya kara zaro mata waɗan nan fararen idanuwan nasa yana kallonta ne yasa ta ɗan tsorata, nan take tsoro ya bayyana a saman fuskarta, hakan kuma sai ya kara bayyanar mashi da kamanninta da mum twins, dan rana ta farko da ya fara kallon mum twins fuskarta a cike yake tab da tsoro, duk a firgice take, so ba zai taɓa mantawa da wannan yanayi da ya fara ganinta a ciki ba.
Da sauri ta raba jikinta da nasa, a tsorace ta fara yunƙurin barin wajen.
A hanzarce ya riko hannunta, da harshen turanci ya tambayeta ina mamanta da ƴar uwarta?.
Ɗan zaro idanunwanta ita ma ta yi tana tunanin a ina ya san tana da mama da ƴar uwa? Waye shi ma tukun nan.
Bata bashi amsa ba, sai ta yi ƙoƙarin gudu ta bar wajen, sake ta ya yi tare da miƙewa tsaye, nan take yanayin face nasa ta sauya, kome yasa hakan oho?
Yana saketa ta miƙe da gudu ta nufi ta gefen ƙoramar. Da gudu Rocky ya yi yunƙurin bin bayanta, da sauri Kamran ɗin ya dakatar da shi, dama yasan in dai ta gudu Rocky zai bi bayanta ya kamota ya dawo da ita.
A hanzarce Kamran ɗin ya rufa mata baya, dan yaga ina ta nufa, ita kuwa tana barin wajen nasu sai ta daina guduwar, ta fara tafiya da sauri sauri, dan kafarta babu takalma, idan ta ce zata yi gudu to tana iya taka wani abin ya ji mata ciwo, so dole ta kula sosai, ta tafi cikin nutsuwa, ta kuma lura da in da zata taka.
Bata san Kamran ɗin ya biyo bayanta ba, dan a sese ya biyo ta, baya son ta gansa, yana so ne kawai yaga shin suna a tare da mamarsu ce ko dai bata a tare da su.
Meyasa yake tunanin bata tare da su kuma? Hakan na nufi akwai wata a kasa kenan? Ko kuma akwai wani abin da ya sani? To mu dai namu ido kawai.
Ta yi tafiya mai ɗan nisa kafin ta isa wani wajen da gabaɗaya farin yashi ne a wajen, babu ciyayi, sai bishiyoyi dake ɗan gefe gefe. Cigaba da tafiya a cikin yashin ta yi har sai da ta isa karshen yashin, ta fara shiga cikin ciyayi, sannan ta tsugunna a wajen tare da sa hannunta a cikin ciyayin ta buɗe wani waje kamar kofa da aka yi da itace, tana buɗewa ta shiga cikin wajen tare da zuro hannunta ta ja marfin ta rufe, wajen ya koma kamar ba'a taɓa buɗe shi ba.
Mamaki kaɗan ne ya ɗan kama Kamran ɗin, a jikinsa yana jin duk yadda aka yi wannan ƴar mum twins ce, koma yaya ita ce ɗaya daga cikin twins, dan ga kamannin mamarsu a saman fuskarta, duk da ba wani kama sosai suke yi ba, amma tabbas wannan ƴaƴanta ne, dan jini ba wasa ba. Nan take kuma fuskarsa ta sake sauyawa, alamar damuwa da ɓacin rai ta bayyana a saman fuskar nasa, a take jikinsa kuma ta saki kamar wadda aka zarewa laka, tunanin mum twins yana jefa shi cikin mawuyacin hali, ko me dalili oho?.
Ya jima a tsaye a wajen kamar wadda aka zarewa laka, jikinsa duk ya yi la'asar, da kyar ya iya motsawa daga in da yake tsaye ya nufi wajen da ta shiga ɗin, dan ya duba ita da waye a cikin?.
kafin ya ƙarisa wajen bari mu leƙa KINGDOM OF POWER mu dawo.
🔥✨KINGDOM OF POWER💪👊
Zaune Gimbiya Zunaira take a saman wani haɗaɗen shinfiɗi na alfarma, tana zaune ne a wani irin waje da aka kawata shi da..........
Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.
🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI.
Zaune Gimbiya Zunaira take a saman wani haɗaɗen shinfiɗi na alfarma, tana zaune ne a wani irin waje da aka kawata shi da kyawawan kwalliya na gidan sarauta, da alama wajen hutawa ne, wajen hutawar ma da alama na wani babba daga cikin ƴan gidan ne, babba kuma wanda ake ji da shi, domin yanayin wajen sam bai yi kama da na ƙananan kwari ba, na manyan kai ne.
Tulin tuffa ne a cike a cikin gwando a gabanta, kuyanga ce ta kawo mata tuffar, yau dai Hoorain baya a tare da ita, da alama yana ta wani wajen, tana nan dai cikin wannan shiga tasu ta ƴaƴan manyan sarakuna da ake ji da su, shigar yana yi mata mugun kyau sosai, kowa dai yasan kayan yara ya fi na manya kyau, to haka idan ta sa kaya sai ya fi kyau a jikinta sama da su Gimbiya Chuchu.
Har wa yau dai bata sanya hular alkyabbar a kanta ba, sai dai a yau ta sanya wani kyakkyawar hula mai matukar kyan gaske a kan nata, ta rufe gashinta, ba kasafai ta cika yawan sanya ɗankwali ba, dayawan lokuta zaka ganta babu ɗankwali a kai, ta fi son shan iska ta ko'ina.
A nutse ta kai hannu ta ɗauki apple guda ɗaya daga cikin kwandon Apple dake a gabanta, ta kai saitin ɗan bakinta zata gutsira. Bata ji motsin mutun ba, bata ji komai ba sai gani ta yi an kwace apple ɗin daga hannunta, bata ƙarisa kai shi bakin taba.
Cikin sauri ta ɗago kanta tare da ɗago da idanunwanta sama, dan taga wanene da wannan ɗanyen aikin?.
Tsaye yake a gabanta, cikin kayansu na jarumai kuma jajirtattun mayaka, kamar kullum wannan hula tasu mai kan zaki tana a kansa, tsayuwar jaruman mazan nan nasa masu jini a jikan nan dai ita yake yi a kullum, kai daga ganinsa ma bakaga wajen wasa ba, baya ɗaukar wargi.
Zuba mashi ido ta yi bata ce da shi ko uppan ba, yau karo na farko da ta ji tana son kallon fuskar wannan dakaren nata.
Ɗan dukar da kansa ƙasa ya yi, cikin girmamawa ya ce.
"Afuwa ranki shi daɗe, ina neman izinin yin magana".
Yau ya yi maganar da ɗan sauti, sau da dama idan ya yi magana na kusa da shi ma basu jin me ya faɗa, saboda a hankali yake magana, baya fitar da sauti, baya ɗaga murya.
Gera ɗaya ta ɗaga mashi alamar go ahead ya yi maganarsa ba tare da ta yi magana ba.
Sake ɗan risinar da kansa ƙasa ya yi alamar ya karɓi umarnin kuma ya gode. Cikin natsuwa ya fara magana words ɗinsa na fita ɗaya bayan ɗaya babu hayaniya.
"Afuwa ranki shi daɗe, ban binciki tuffar bace shiyasa ban bari kin kaita bakin ki ba, Gimbiya Sarina ce ta aike ni, shiyasa ban samu damar bincikar tuffa ɗin ba har aka kawo maki".
Tun da ya fara magana ta zuba mashi wayan nan dara daran idanun nata, ta kasa koda kyaftawa, yau shine rana ta farko da ta fara jin muryarsa da sauti, idan yana magana kasa kasa sosai yake yi, kullum tana tare da shi, amma bata taɓa ganin ya yi magana da kowa ba, sannan bata taɓa ganin fuskarsa ba, sakamakon wannan hular tasu ta mayaka dake rufe musu ko'ina a fuskarsu, baka ganin komai sai ido da tsagen ɗan baki, sai kofofin hanci, suma kaɗan kaɗan ne, bayan haka baka samun damar ganin komai na fuskarsu, ga kayan yakin nasu kuma da karfe aka yi shi, kunsan dai yadda kayan shahrarrun mayaka suke ai?, Amma duk cikin dakarun dake Masarautar ya fi su natsuwa, yana da hankali sosai, yana bata kulawa, gabaɗaya masu kula da su shi yafi bata kariya yadda ya dace, ko motsi ta yi sai ya matso kusa da ita dan ya ga menene, tana da tabbacin ko barci dare baya samun dama ya yi sosai, saboda ita, baya taɓa rabuwa da bakin kofar shiga arear part na King Zuhair.
Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce mashi. "Ai babu komai a cikin Apple ɗin, daga ɓangaren Momma aka ɗauko mun fa, kuma Aunty Chuchu da kanta ita ta haɗa mun su a kwando, amma nagode da kulawarka a gareni".
Ita ma cikin nutsuwa take magana, da alama yarinya ce mai hankalin manya.
Jinjina mata kai ya yi tare da risinar da kai ya sake ɗagowa, sannan ya tsugunna a gaban kwandon Apple ɗin, dan ya duba ya tabbatar da ingancinsu, saboda ya tabbatar da aikinsa, ya tabbatar ya bata tsaro yadda ya dace.
Da ido kawai ta bishi da kallo, bata ce da shi komai ba, shi ma bai sake yin magana ba har ya kammala bincikensa a kansu, sannan ya miƙe tsaye tare da komawa ɗan gefenta kaɗan ya tsaya. Ƙasa ƙasa kamar dai kullum ya ce mata zata iya cin Apple ɗin yanzu, babu wata matsala.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da dawo da kallonta a kan gwadon Apple ɗin, a kullum idan zata ci abu in dai a waje ne ba'a cikin ɗakinsu ba, to sai Hoorain ya binciki wannan abin tsab, sai ya tabbatar da ingancin wannan abin, sannan yake barinta ta ci, hakan yasa take jin daɗin kasancewa a tare da shi, yana da kula sosai, ga shi babu ruwansa da kowa da komai, in da ya sa kansa kawai yake kallah, baya ɗaga kai ya kalli wasu ma abinsa, ga namijin jarumta da kuma nutsuwa.......... Ɗa ɗaya tilo ga commander ZAFAR kenan.💪
Baki a ɗauke da sallama wata kuyanga ta shigo cikin wajen, hannunta na rike da wani kyakkyawar kuma tsadadden Apple laptop, sabuwa gal da ita.
A gaban Gimbiya Zunaira ta zo ta tsugunna, cikin girmamawa ta nemi izinin yin magana.
Yadda kuka san mutun mutumi haka Hoorain yake tsaye, ko kallon in da suke bai yi ba, yana tsaye kamar saƙago yana fuskantar kofar shigowa abinsa.
"Mama Haulat menene yake tafe dake?". Cewar Gimbiya Zunaira ɗin.
Kuyangar ta kasance babbar macece, dan zata iya kai 35 to 40 years a duniya, hakan yasa Gimbiya Zunaira take girmamata take ce mata Mama, duk cikin ƴaƴan KING ZUHAIR babu wanda yake girmamata yake ce mata mama sai Zunaira, dama na gaya maku ita tana da saukin kai da kuma girmama na gaba da ita, sam bata ɗauki duniya da zafi ba, kuma ita wannan Mama Haulat ɗin ita ce kuyanga mafi matsayi a cikin kuyangun dake yi wa Momma wato mahaifiyar Zunaira ɗin hidima, so a part ɗin su Zunaira ɗin take.
"Dama ranki ya daɗe Gimbiya Momma ce ta ce na kawo maki wannan abin Yah Omar yana son ya yi magana dake".
Ta kai karshen maganar tana miƙo mata laptop ɗin.
Kyawawan hannayenta dukka biyu tasa ta karɓi laptop ɗin, sannan ta juyo da screen ɗinta a dai'dai saitin fuskarta.
Wani kyakkyawan matashi ne yake a zaune a saman ɗaya daga cikin wasu shegun luntsuma luntsumar sofas masu bala'in kyau, zaune yake a cikin wata katafaren parlourn mafi haɗuwa da ƙawatuwa, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, kyawawan fararen halayensa ɗaya na rike da cup mai bala'in kyau, ɗayan hannun kuma yana rike da pen, sai tiriri ne yake tashi daga cikin cup ɗin, da alama abu mai zafi yake sha.
Kyakkyawa ne sosai, da ka gansa babu tambaya kasan yayan Zunairar ce, dan suna kama duk da ba sosai can can ba, fari tas da shi shi ma, gashin kansa baki siɗif, ga gashin nasa ya sauko mashi har gaban goshi, da alama kuma shi yake yanke baki bakin gashin yana dai'dai tasu, shiyasa suka yi mashi kamar wadda ya kifa hula a kan nasa, yana da dara daran idanuwa kamar na King Zuhair, farin idanun nasa ya yi tas da shi, kwayar idanun nasa kuma bai yi baki sosai ba, idan ka gansa ma zata zaci brown ne ba baki ba. A shekaru ba zai wuce 15 to 16 years ba, sanye yake da puma rigar da wandon dukka farare tas, bai sanya hular kayar a kansa ba.
"Yah Omar me kake yi ne?".
Ta faɗa tana kallon pen ɗin hannunsa, ta yi maganar kuma cikin Dubai Arabic nata.
"Koyar da gaisuwa nake yi".
Ya baya amsa calmly, kamar mai ciwon baki, voice nasa yana kama da nata, ance blood is thicker than water!.
"Kash na manta ne ina wuni tom?".
Ta yi maganar a shagwaɓe.
Cup dake hannunsa ya kai saitin bakinsa ya ɗan kurɓi abin da yake ciki kafin ya amsa mata gaisuwar tata, sannan ya ce mata. "Ina Akka?".
"Tana part nata".
Ta bashi amsa tana mai cigaba da kallonsa.
"Ai na ɗauka kina wajenta ne".
"A'a tun ɗazun na baro wajenta, amma zan je anjuma kaɗan, yawwa Yah Omar kada ka dawo fa ka jirani sai na zo mu taho a tare".
Shiru ya ɗan yi mata kafin ya ce. "Kin gayawa daddy aikar da na yi maki ne?".
"Laaaa wlh na manta, amma zan je na gaya mashi".
Guntun hararar wasa ya wurga mata kafin ya ce.
"Tun jiya fa na aikeki, Ina Omaid da Obaid?".
Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Kila suna part ɗin Mommy, kasan yanzu basu cika zuwa part ɗin Mama ba ai".
Kasancewar yasan matsalar gidan nasu sai bai tambayeta dalilin da yasa su Obaid basu zuwa part na Mama ba, sai ma ya kawar da zancen da cewa.
"Yah Jawad ya tafi office ne?".
"Ni ban sani ba, rabona da shi tun da safe".
"Tom ki je ki gayawa daddy saƙona kin ji ko?".
"To amma Yah Omar gaskiya sai anjuma zan je, yanzu fada tana da baki sosai, dan na kalli motocin dayawa sun zo".
Ta yi maganar tana ɗago da kallonta izuwa kan Hoorain dake tsaye tamkar saƙago.
"Ba wasu baki, uncle Abbas ne ya zo wajen daddy, ai Momma ta gaya mun, dan haka ki je ki gayawa daddy abin da na ce".
Miƙewa ta yi tsaye, cikin murna tare da bayyanar ƙayatattcen murmushi a saman fuskarta ta ce.
"Yah Omar da gaske uncle Abbas ne ya zo?".
Jinjina mata kai ya yi alamar e.
"Wayyo daɗi, yau su Aunty Sarina zasu ga daddynsu, ni ma bari na je na gansa".
"Bafa ganinsa na ce ki je ki yi ba, ki je kawai ki gayawa daddy saƙona, idan kin faɗa in ya so sai ki tsaya a wajen uncle Abbas ɗin".
Da okey ta amsa mashi tare da miƙewa wannan kuyangar wato mama Haulat laptop ɗin, cikin hanzari ta nufi hanyar fita daga wajen.
Cikin zafin nama da taku irin na jaruman maza Hoorain ya rufa mata baya, sai murna take yi a kan zata je ta ga uncle Abbas wanda ya kasance kani ne ga mahaifinta, shi ne yake bin King Zuhair a wajen haihuwa, cikakken ɗan siyasa ne mai faɗa aji a faɗin ƙasar, yana da aure, matarsa ɗaya da ƴaƴansa huɗu, maza biyu mata biyu, familynsa suna cikin KINGDOM ɗin, shi ne dai ba mazauni ba, time to time yake zuwa, mutun ne mai kirki da son ƴan uwansa, yana matuƙar kaunar King Zuhair da ƴaƴansa, sai dai ita kuma matarsa tana so ne yazama shi ne sarki ba King Zuhair ba, shi kuma sarauta ba ita ce a gabansa ba, siyasa yake da ra'ayi, ita kuma a haukarta cewa take yi kujerar siyasa ba'a gadarta, idan ya gama wa'adin mulkinsa sauka zai yi wani ya hau, amma ta sarauta kuma fa? Ba zai sauka ba sai lokacin da ya tsufa, sannan kuma ɗansa ne zai gaji kujerar idan ya sauƙa, wannan shi ne dalilin dayasa tafi son ya mulki KINGDOM OF POWER ba wai siyasa ba. Akwai case fa my people.
A can cikin gida kuwa, labari ya gama shiga ko'ina cewa uncle Abbas ya zo, sai murna kowa yake yi, dan har ga Allah gabaɗaya ƴaƴan KING ZUHAIR suna matuƙar kaunar uncle ɗin nasu, kun san kowace zuciya tana son mai kyautata mata, to shi gaskiya mutun ne mai faram faram ga jan ƴaƴan nasa a jiki, hakan yasa idan ya kawo masu