x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 69 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 204001 words
  • 207000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 393

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
dare? Kawai fa shan iska muke fitowa yi, sai mu ɗan lelleƙa mu gani ko akwai wanda bai yi barci ba a gidan, kaga tsaron kannanmu muke yi".

"E haka ne babu shakka, to zo ka wuce na ji bayananka, ka jira nawa kuma, yanzu zaku yi tsaro da tushe". King ya faɗa tare da wucewa zai shiga room ɗin Chuchu.

"Daddy to wani mataki zaka ɗauka ne wai?". Ya tambayesa a ƙage, dan yasan halin King ƙaramin aikinsa ne da safe suji wata zancen da basu yi tsammani ba.

"Good night son ka yi addu'a kafin ka kwanta, babu ruwan ka da matakin da zan ɗauka". Yana kai karshen maganar ya shige cikin room ɗin.

"Kai daddy Allah ka iya jefa mutun cikin tunani, to yanzu wai wani mataki zaka ɗauka a kan mu kuma?". Ya tambayi kansa tare da sa kai ya wuce izuwa nasa part ɗin. Yana shiga ya haye saman bed ɗinsa tare da jawo bargo mai laushi ya shige ciki, sannan ya kashe wutar ɗakin ta hanyar amfani da remote, ya ɗaura hannayensa ɗaya a saman cikinsa, ɗayan kuma a saman fuskarsa, nan take tunanin Gimbiya Chuchu ya faɗo mashi cikin ransa, yadda take kwance take sharara barcin nan kawai yake hangowa, da alama dai yanzu ma sai ya yi mafarkinta, dama yaya lafiyar kura bare ace ta yi zawo?.


🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

Idan kuma koma ɓangaren su Kamran kuwa wato Forest.

🏞️FOREST🏞️

"Kamran me nake ganin a kan nan naka haka?". Mamma ta faɗa tana ɗaure fuska sosai, domin bata taɓa zaton ganin kitso a kansa ba.

Shiru ya ɗan yi yana tunanin me zai ce mata ya tsira? Yau dai bashi da mafita gaskiya.

"Kamran am i not talking to you? What's this I said?".

Kame kame ya fara yi, tsabar ruɗewa ma har in'ina ya fara yi a magana. "Mamma i don't know, kuma ni ban san ta ya aka yi ya zo kai'na ba, and Mamma please don't ash me any questions again now, am feeling to much of hungry, and my Head is penning me". Yadda yake maganar rashin gaskiya ce ƙarara ta bayyana a tattare da shi, ya yi wani tsuru tsuru da shi.

"Kamran am i your mate?".

Girgiza mata kai ya yi alamar a'a yana faɗin. "Sorry Mamma".

"Na yi maka kalar wadda zaka yi wasa da hankalinta?".

Nan ma girgiza mata kai ya yi alamar a'a.

"Okey now tell me who did this thing to you? Dan nasan dai kai kam baka iya ba".

Wani irin tsoro ne ya kamashi, yasan da cewa tabbas idan tasan da su Pretty sai ta rabasu babu makawa, shi kuma har ga Allah ba zai iya rabuwa da su ba, gara ta kashe shi kawai ta huta da ta rabasu, sun zamar mashi wani ɓari na rayuwarsa.

Har wani zufar tsoro ce take tsastsafo mashi, duk ya ruɗe ya rasa abin faɗa. Voice ɗinta ne ya katse shi da cewa. "I'm waiting for your amsa ne fa Kamran".

Ɗago da idanuwansa izuwa kanta ya yi, sannan ya koma bakin bed ɗin ya zauna, ko zai mutu ba zai gaya mata ga wadda ta yi mashi wannan kitso ba, sai dai yau duk abin da zai faru ya faru. Dan haka shiru ya yi mata bai iya sake cewa ko uppan ba, yana jinta sai tambayarsa take yi, da yaga zata matsa mashi sosai ma sai ya miƙe da sauri ya nufi waje da nufin ya barmata kogon ma mai gabaɗaya.

"Where are you going?". Ta jefa mashi tambaya.

Ina ai bai tsaya ba, da sauri ya nufi waje irin shi ya yi fushin nan. Da sauri ita ma ta rufa mashi baya. Kusan a tare suka fito wajen kogon.

Damko gashin kan nasa da karfi ta yi har sai da ya furta wash. Ai kuwa yana furta wash ɗin nan Rocky da yake kwance ya yi tsalle da nufin ya haye kanta. A hanzarce ta kauce mashi, kamar dama tasan zai aikata hakan, ko da yake tasan cewa ko ita ta taɓa Kamran Rocky baya barinta, dan yafi sabawa da Kamran ɗin sama da ita, so in dai zata taɓa shi sai ya yakusheta da waɗan nan shegun faratunan hannun nasa dake fasa fatar mutun.

Ko da ta kauce mashi kuma bata saki gashin Kamran ɗin ba, kaucewar da ta yi kuma yasa ta ja mashi gashin da karfi ta yadda ya sake furta wash da karfi, hakan yasa Rockyn ya sake daka tsalle ya yi kanta da karfi a karo na biyu.

A wannan karon kam dan dole ta saki Kamran ɗin tare da yin baya baya. Tana sakinsa kuma bai bi ta kanta ita da Rocky ɗin ba yasa kai ya sauka ƙasa daga saman dutsen.

Sunansa ta fara kira da karfi karfi, amma ina Kamran yaki ko juyowa ya kalleta, yasan idan ba haka ya yi mata ba ba zai rabu da ita lafiya a kan su Pretty ba, yasan yanzu idan ya nuna mata ya yi fushi ya tafi wuni zunbur bai dawo ba, to da kanta zata fita nemansa, idan kuma ta nemosa lallaɓasa zata fara yi tana rarrashinsa, daga haka zata mance da zancen kitso......... (Ashe dai Kamran ma ya iya tsiya😅)

To bari dai mu leƙa gidansu Khadija mu je mu dawo.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥


Lokacin shan Maltina ta yi🥱



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍


🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)






🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 19/8/2024.....✍️📚🌹




For information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








E____________37🔥




🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

Duk yadda Maman Zainab ta yi tsammani abin ya wuci nan, the thing is getting out of hand, ya sha gaban tunaninta, wasa wasa dai da gaske baban Zainab ya juya mata baya, komai ya lalace mata, ga Zainab bata jin maganarta, saboda maganin Aunty Hauwa ya taɓa Zainab ɗin, amma bai taɓa Khadija ba, saboda da ni da duk mun san Khadija da Zainab akwai banbanci sosai a tsakaninsu, Zee yarinya ce, and kuma bata wani riƙo da addini kamar Khadija, bata kai Khadija ilimi ba, so ita abin ya ɗan taɓata duk da ba sosai ba, bata dai'na son mamar tata ba, amma kuma bata jin magana, ko kina yi mata magana sai ta ga damar amsawa, idan mamanta zata yi mata magana sau dubu sai lokacin da ta ga damar amsawa take amsawa, wani lokaci maman tana magana ma tana mayar mata da martani..... Abin akwai tsananin ciwo sosai.

Da farko har Sadiq ya so dukanta sosai a kan hakan, sai maman ta hana shi, dan tasan ba laifin Zee ɗin bane, bama ta san tana yi ba. Duk abin da ya faru from A to Z maman Zainab ta kwashe ta gayawa Sadiq ɗin, shi kansa sai da ya ji kansa ta yi wani irin sara mashi, ya jima yana guje mata irin wannan matsala, amma sam taki yarda, duk wani abin da zai gaya mata sai ta saka kafa ta shure, yanzu yadda komai ya lalace ɗin nan ta ina zasu fara neman mafita ma tukun nan?.

"Ki kira mama ki gaya mata batu a kan Zainab, watakila akwai abin da zata taimaka maki da shi". Cewar Sadiq da yake tsaye a bakin kofar parlournta, ya dawo daga school ne, ya shigo kenan ya samu tana kuka, shi ne ya je jin ba'asi, a nan ne take sanar da shi ai ga abin da ya faru duka.

Haƙiƙa ya yi matuƙar tausaya mata sosai da sosai, sai dai kuma bashi da wani abin yi a yanzu face ya taya da addu'ar samun mafita.

Duk ta wani uban rame kamar ba ita ba, bata cin abinci, sai idan ta ji yunwa sosai ne zaka ganta tana shan ruwan tea, ba yadda Khadija bata yi ba wajen rarrashinta, amma ina taki ta hakura, a yanzu fa shi baban Zainab yana yin kwana uku ma bai leƙo gidan ba, to a ina yake kwana kenan? Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana.

Kasuwar ma baya wani zuwanta, ko maman Zainab ta tambayi Sadiq baban Zee ya je kasuwa, sai dai ya ce mata a'a, Sadiq ne mai kula da komai yanzu, shi kuma baban Zee sai a hankali, ƴan kwana biyun nan ma kamar baya garin ne gabaɗaya, domin kuwa idan da yana garin baya kwana uku huɗu haka yana zuwa ya ɗauki abin da ba'a rasa ba a room ɗinsa.

Sai dai ko ya zo gidan yadda kuka san bai taɓa sanin yana da wata mata da ƴaƴa a duniya ba, ko kallon in da suke bayayi, ko maman Zainab ta yi mashi magana tamkar da mutun mutumin da aka sassaƙa take yi ba shi ba, kamar yadda bango baya magana haka shi ma baya kulata, wannan abin shi ya fi komai ɗaga mata hankali. A kowani lokaci ta kira mamarta a waya ta sanar da ita, amsa ɗaya take bata shi ne ta cigaba da yin istigifari tana tuba har izuwa lokacin da Allah zai karɓi tubanta ya dubeta da idon rahama, kuskure dai ta rigada ta tapka shi, shirka haɗa Allah dawani ai dole taga sakayya, dan haka ta yi hakuri ta cigaba da tuba tana gayawa Allah kukanta one day one time komai zai wuce In Sha Allah.

Haƙiƙa maman Zee ta shiga tashin hankali na kin karawa, bare ma kuma idan ta tuna harda ƴarta Zainab abin ya shafa, wannan abin yana kara ɗaga mata hankali ta yadda take jin har wani juya mata duniya take yi, sannan ga batun aure Khadija da Haidar da yake ta kara matsowa, kun dai san ba fashi wannan aure, koda baban Zainab baya nan kuma baya a cikin hayyacinsa dole za'a ɗaura auren in ji hajiyarsa, saboda already anrigada an bawa Haidar ita, maman Zee dai a yanzu ita kam jira kawai take yi taga ranar da zuciyarta zai fashe ta mutu kowa ya huta, abin gwanin ban tausayi.

Ta ce da mamarta zata dawo gida da zama, maman ta ce mata a'a kamar yadda ta zauna a ɗakin mijin nata ta ruguje komai ta lalata farincikinta dana ƴaƴanta, hakan zata zauna a yanzu ma a buga da ita ta gyara komai kamar yadda ta lalata. Wannan dalilin yasa ta hakura ta cigaba da zama.

Tun daga ranar da abin ya faru bata sake saka Hauwa a idanunta ba, ta aika Sadiq gidan ya fi sau a kirga, amma ko ya je kullum gidan a rufe da kwaɗo, abin ya yi mugun ɗaure mata kai, to ina Hauwa ta tafi? Tana son samun amsa, ga shi mamarta ta ce bata yafe mata ba idan har ta sake saka kafafunta ta fita waje ba tare da izinin baban Zee ba, kuma bata yafe mata ba idan ta kuskura zata fita ta yi mashi karyar ga in da zata je ta je wani wajen na daban, domin kuwa duk shi ne ya jefata cikin wannan bala'i, fita bada izininsa ba, da ya sani ai baya bari ta je ba, yanzu ga shi tana kuka tare da danasani maras amfani.

"To shikenan Sadiq, bari na kirata na gaya mata halin da ake ciki a kan Zainab ɗin". Ta bashi amsa kamar zata fasa ihu, duk ta yi wani futu futu da ita yadda kuka san ba maman Zee ƴar kwalliyar nan ba, duk ta fice daga hayyacinta.

Khadijah na zaune a saman sofa a gefenta, ita kuma Zainab tana cikin dakin, ba kasafai ta cika fitowa ba a yanzu, duk kuma saboda wannan magani ne.

Nasiha sosai Sadiq ɗin ya kara yi mata tare da haɗawa da Khadija da take a zaune, daga karshe ya rufe masu da cewa. "Maman Zainab dama akwai maganar da nake son mu yi dake, shi ne ma ya dawo dani ta nan, ba dan haka ba kasuwa na so wucewa tun da kinga yanzu komai ya dawo kai'na, baban Zainab baya zuwa kasuwar".

Da kyar ta iya amsa mashi da. "Ina jinka Sadiq, faɗi duk abin da kake so".

Nisawa ya ɗan yi tare da gyara tsayuwarsa kafin ya ce. "Maman Zainab sanin kanki ne bani da wani iko a kan su Khadija, babansu yana raye kuma danginsa ma suna raye, ni kaninki ne kawai, a halin yanzu sai dai na basu shawara a matsayina na kawunsu, ba wata magana zan gaya maki ba face na tuna maki da abin da kika manta, ki sani ke kika haifi yaran nan, duk in da za'a je a dawo kina da iko da kayanki, babu wata daga cikin ƴan uwan babansu da zata nuna maki iko a kansu, addini bai ce hakan ba, kina da damar buɗe murya ki yi magana a kansu! Ba wai zan haɗaki faɗa da ƴan uwan baban Zainab bane, amma ki sani shirunki zai iya ja maki danasani mafi girma a kan yaran nan, su suka haifa maki su ne da zasu rinƙa tsara maki ga yadda suke son rayuwar yaran ta kasan ce? Dukkansu ba mata bane? Ba suna da yara ba? Akwai wanda ya isa ya ce ga abin da zasu yi wa ƴaƴansu ne? To meyasa sai ke kawai suke tsarawa naki yaran abin da suke so? Ke kuma kin zuba masu ido kina ganinsu, ko kin manta da cewa ƴaƴa amana ce da Allah ya bawa iyaye? Ko kina tunanin idan Allah ya tambayeki meyasa kika tauyewa ƴaƴan nan naki hakkinsu idan kika ce mashi maman su Haidar ne sila shikenan sai Ubangiji ya yafe maki? To idan ma haka kike tunani kin yi kuskure, ba Maman Haidar Allah ya bawa amanar su Zainab ba, ita Maman Haidar tana da nata amanar da zata amsa tambayoyi a kansu ranar gobe ƙiyama, babu wanda zai amsa na wani, kowa nasa zai amsa, dan haka yana da kyau ki buɗe baki ki kuma tsaya komai zai faru ya faru amma ki tabbatar baki jefa rayuwar yaranki cikin kunci ba". Ɗan dagatawa ya yi da maganar yana mai da numfashi kafin kuma ya cigaba da cewa.

"Khadijah bata ɓoye mun komai ba, ta gaya mun duk wani abin da Haidar yake yi mata, to ina son ki sani ni daga nawa ɓangaren na hanata tsayawa hira da Haidar, na gaya mata ko ya tsayar da ita kada ta sake kula shi dan bashi da hankali ko kaɗan, sannan na gaya mata in dai ya sake ɗaura hannunsa a jikinta to kada ta yi tunanin komai ta koya mashi hankali, na bata goyan baya da ta zabga mashi mari, nasan zai iya cewa zai daketa dan ba hankali ne da shi ba, dan haka na ce mata ko kusa ko alama kada ta tsaya ya daketa, sannan kuma kada ta sake nuna cewa tana jin tsoro ko shakkarsa, ina son ki buɗe kunnuwanki kema ki saurateni, ko a cikin parlourn nan Haidar ya zo yin hira da Khadija kada ki sake bari, kada ki yarda, ki ce mashi kin hana hirar daga yau, ya bari sai anyi auren, sannan shiru da kike yi kina zuba wa Haidar ɗin da uwarsa ido ya isa haka, ba wai na ce ki yi wa yar mijin rashin kunya bane, a'a, kada ki manta yarsa ba uwarsa bace ba, dan haka ba kowani irin takaki zata yi ki yi shiru ba, lokacin da ya dace ki yi fito na fito da su ya yi, yanzu ne yakamata ki gyara masu zama su san da cewa kema ƴa ce, kuma dan zaman aure ya kawo ki cikin familynsu ba hakan yana nufin kema naki familyn basa sonki ba, ƴa ce kamar kowa, kuma kamar yadda kowasu iyaye suke son ƴaƴansu haka kema ake sonki, dan haka yana da kyau ki mayar da hankali, a yanzu baban Zainab hankalinsa baya a kanku gabaɗaya, yanzu ne lokacin da ya dace ki taka masu birki dukkasu, ki zana masu jan layi, su shiga taitayinsu da kyau......". Sake dakatawa ya yi yana sauke ajiyar zuciya, yau ya samu ya fitar da abin da ya jima yana cinsa a cikin zuciyarsa, ya jima yana son gayawa yayar tasa da wannan shirun nata a kan ya yi yawa, amma taki bashi dama ta saurare shi, ta biyewa Hauwa a tunaninta hakan ce mafita, to Alhdulillah a yanzu dai ya samu ya fitar da abin da yake cikin cikinsa, ya huta.

Bai ɓoye mata komai ba, duk abin da Haidar yake yi wa Khadijah ya sanar da ita tas, sannan ya ɗora da cewa. "Ga Khadija ɗin a zaune a gabanki, ki binciketa da kyau a iya haka abin ya tsaya ko kuma ya wuci hakan, kin tsaya biyewa Hauwa har ya zama ƴarki bata samun damar da zata iya gaya maki halin da take ciki sai dai ta zo ta sameni ta sanar da ni, kinyi kuskure babba, kuma yanzu lokacin ɗaukar mataki ne.......".

Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon knocking na kofar gida da suka ji ana yi.

"Khadijah je ki duba wanenen mai buga kofar nan". Cewar Maman nasu.

"No ta barshi bara na dubi". Sadiq ya faɗa tare da sa kai ya nufi wajen.

Shiru maman Zainab ta yi tana tunanin maganganun ɗan uwan nata, duk abin da ya faɗa zancensa haka ne, yana a kan gaskiya, tun farko ma ita ta yi masu sake, yanzu ga shi wankin hula ya kaita dare.

Wani irin mamaki ne ya kama Sadiq a lokacin da ya buɗe kofar gidan, ba kowa bane yake knocking face baban
End Ads