ta ƙuduri niyar sai ta yi maganinsa, zata gyara mashi zama, shi da yana can bai ma sani ba tana nan tana haukarta, har da wani ɗaukarwa kanta alkawarin ko yana so ko baya so sai ya auri Fanan, bata fa da tabbacin cewa ita Fanan ɗin tana son Jaish ɗin, ita dai tsarinta kawai take tsarawa kamar yadda take ƙoƙarin ruguje soyayyar Jawad ta gina na Rizwan, abin nata dai sai ita ta san me take nufi da bayin Allahn nan, duk so take taga kowa a cikin ƙunci ne ko yaya ne oho mata dai, lokaci ne zai nuna mana ainahin me take da buƙatar cinmawa a ranta.
A bangaren su Jawad kuwa, kamar yadda ya sakata kuka ta hanyar sanyawa a ɓata mata abinci, haka ya sake sakata dariya ta hanyar kaita yawo duk in da take so, sai dai duk in da suka je sai ya tsokaneta ta ɗan yi kuka hankalinsa yake kwanciya, ita dai auta ta tara abubuwan da zata gayawa Chuchun wanda Yah Jawad ya yi mata da gangan idan suka koma gida.
Ko da suka je gidan zoo ma sai da ya tsokaneta, sun je wajen wasu irin macizan mesa masu haɗiye mutane, macizan suna cikin wani irin glass mai kyau aka sanyasu, sai yawaro wasu daga cikinsu suke yi, wasu kuma sun haɗiyi saniya suna ƙawance bata gama narkewa a ciki cikinsu ba, so sun zo wajen suna kallo, sai ɗaukarsu a video suke yi, auta ta tsaya sai magana take yi wa macizan wai su nannaɗu kamar taya yadda take gani a film bari ta gani a zahiri, sai ka ce an ce mata macizan dama magana ake yi masu sai su nannaɗu ɗin, ita kuma Chuchu ta tsaresu da ido tana kallon ikon Allah, idanunsu kawai take kallo, sai dai ta takure jikinta waje guda, da alama tsoro take ji, kawai ta dake ne ta cije ta tsaya a wajen.
Cikin zolaya ya ce mata. "Jannat menen a wajen kafafunki kamar kamar snaka? Kamar fa ɗan snake ɗin dake cikin glass ɗin ne ya fito......."
Bai iya kai karshen maganar ba ya dakata saboda wani irin ihu da ta zunduma, a guje ta bar wajen tana ƙoƙarin cire alkyabbar jikinta kamar ance mata a jikin alkyabbar macijin yake, kunsan irin wannan abin sai ka ji kamar da gaske yana taɓa maka jiki, musamman ma idan tun farko kaga macijan da idon ka, to wlh ko baa tsoratar da kai ba sai ka rinƙa jin kamar suna taɓaka, to ita ma haka ta ji, sai ta ji kamar da gaske yaron macijin ne yake taɓa mata kafa, ai kuwa ta rinƙa tsalle tana kakkaɓe kayan jikinta tana ƙoƙarin cire kayan ma gabaɗaya, sai ihu take yi.
Cikin sauri ya bi bayanta, da gudu ita ma auta ta bar wajen, dan ma kada su kamata.
Yana zuwa in da take ya riko wuyar alkyabbar tata dan ya hanata cirewa. Ƙanƙame shi ta yi tana faɗin. "Na shiga uku, Yah Jawad dan Allah ka cire mun shi, wlh na ji yana taɓa mun kafa".
Dariya kamar zata kashe shi, yau ba karya ya yi nishaɗi over to over, bare ma idan ta zaro ido tana faɗin. Ya yi sauri ya cire mata ta ji yana haura mata saman kafafu wajen cinyarta, innalillahi Jawad kamar zai mutu da dariya, bayan rike wuyar alkyabbarta da ya yi dan kada ta cire, ya kasa iya aikata komai, saboda dariyar da yake dannewa ta hana shi ko da ɗaga hannunsa bare ya yi rarrashi.
Ma'aikatan da suke wajen ne suka yi saurin ƙarisowa in da suke domin su ji ko lafiya. Hannu kawai ya ɗaga masu alamar su tafi babu komai. Cikin kuka ta ce. "Kada ku tafi, ku zo ku cire mun macijin nan kada ya kasheni, Wayyo mummyna, Yah Jawad ka mayar dani gida, ni ba zan sake fitowa ba, na shiga uku daddy yau zan mutu, idan ya cije ni shikenan na mutu".
Ai a wannan gaɓar dariyar ba zata dannu ba, ta ci karfinsa a in da ya fara tikar dariya kamar wani zararre. Ita kam auta ta rigada ta gane ba wani maciji da gangan ya yi wa Aunty Chuchunta haka, dan haka sai ta sanya hakan ma a cikin lissafin abin da zata gayawa Chuchu idan suka koma gida, zata gaya mata cewa da gangan ya yi mata hakan.
Ganin yana tikar dariya har da tsugunnawa a ƙasa yasa ita ma Chuchun ta ɗan tsagaita kukanta tana binsa da kallon mamaki.
Da kyar ya iya tsayar da videon da yake ɗaukarsu tun farko, har murɗa mashi cikinsa ta yi saboda dariya.
Jin ta ɗan tsagaita kukan ne yasa shi ma ya yi ƙoƙarin ya danne dariyar tare da miƙewa tsaye. Ɗan rungumota ya yi yana faɗin. "Ai tun ɗazun snake ɗin ya sauka daga kafafunki, ya koma wajen ƴan uwansa, kece baki gani ba". Yana magana yana guntse dariya.
Duba kafafunta ta fara yi da sauri tana mai cigaba da kuka. Rarrashinta ya hauyi yana yi mata sorry. Ita dai auta ta harɗe hannaye a kirji tana ganin ikon god.
"Sorry my sister, yanzu mu je muga su zaki dasu zamisa sai mu koma gida ko?".
Ai a ɗari ta ce mashi. "Ni Yah Jawad ka mayar da mu gida kawai babu in da zan sake zuwa".
Ɗan kara rungumeta ya yi yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi. Sai a lokacin kuma ya haɗa ido da auta da ta harɗe hannaye a kirji tana ganinsu. Ido ɗaya ya kashe mata tare da ɗaga gera guda, irin alamar Malama ya ne?.
Dariya ta ɗan yi mara sauti kafin kuma ta ɗan kawar da kanta tana faɗin. "Yah Jawad gida zaka mayar damu daga nan, mun yafe sauran wajen yawon".
Alama ya yi mata da hannu a kan ta zo. Ba mutu ta ƙariso wajen nasa da sari, haɗata ya yi da chuchun dukka ya rungume yana kara rarrashin chuchu, sai ajiyar zuciya take saukewa, ta sha zunduma ihu kam.
Sun dan ɗauki a kallah minti goma a haka kafin ya rabasu da jikinsa ya ce su wuce gidan tun da sun ce yawon ya ishesu.
Chuchu ce a gaba, ta yi sauri ta wuce zuwa wajen motarsu, taki ɗagowa ta sake kallon komai a wajen, wai dan ma kada wani abin ya sake bata tsoro. Sai murmushi kaɗan kaɗan yake yi ya riƙo hannun auta suka rufa mata baya.
Har suka shiga cikin mota bata dai'na sauke ajiyar zuciya ba, a haka ya tada motar suka nufi gida, sai janta da hira auta take yi, amma bata wani kulata ba, saboda hankalinta ya yi gida, so take ta koma ta cire kayan jikin nan nata, ta yi alkawarin ba zata sake saka kayan ba, zata bawa kuyangarta dake gyara mata ɗaki kyauta, dan ita tun da maciji ya taɓa kayan bata so kuma.
Suna isa gida ba ɓata lokaci ta fice daga cikin motar, Jawad ya yi mamakin ganin irin saurin da take yi, ko sallama basu yi ba, bai san tana son zuwa ta cire kayan jikin nata bane. A hanzarce auta ta rufa mata baya bayan ta yi mashi sallama, har lokacin wayar momma yana hannun autar, ta haɗa kuma da wayar da Yah Jawad ya bawa Chuchun ɗazun, domin Chuchun ta bata ajiyar wayar tun da suka fita, so sai ta haɗa da wayar ta nufi cikin gida, shi kuma bai lura da ta tafin mashi da waya ba, kawai ya fito ya nufi nasa part ɗin yana ɗan murmushi.
Ita kuwa auta sai sauri take yi dan ta je ta gayawa Chuchun cewa da gangan yah Jawad ya yi mata duk abin da ya yi mata ɗin nan.
A ɓangaren su Kamran kuwa, wato Forest.
Washegari da safe kamar yadda ya saba zuwa wajensu haka ya nufo in da suke bayan ya kammala yi wa mama dik abin da ya saba yi mata. Yana tafiya yana tunanin yadda zai yi ya fita wajen dajin nan da kuma yadda zai yi da mama ta barsa ya fita ɗin, ba zai iya tafiya bai tambayeta ba, domin yasan zata shiga tashin hankali na wuce misali, yana kaunarta over, amma kuma ya kasa iya gaya mata, domin yana tsoron kada hakan ya ja mashi rabuwa da su Pretty, ta hana shi zuwa in da suke ma kwata kwata, ƙaramin aikinta ne ta hana shi fita ma kwata kwata idan ta ji yana da burin barin wannan dajin.
A kan hanyarsa na zuwa wajensu ya cikaro da Rocky, bai wani kula shi ba ya cigaba da tafiyarsa kawai, rufa mashi baya Rockyn ya yi suka jera kamar yadda suka saba, sai wani miƙa yake yi da alama ya ci nama ya ƙoshi ne ya yi barci ya tashi.
Dajin gabaɗaya akwai danshi danshin ruwa, saboda ruwan saman da aka yi jiya, da wasu ganyayyakin itace suna zubar da ruwa, wasu ramukan sun cika da ruwa, idan suka zo wucewa sai Rockyn ga tsallaka Kamran yake bin bayansa, haka suka cigaba da tafiya har izuwa wajensu Pretty.
A waje Rocky ya kwanta, already kunsan baya iya shiga ciki, kofar ta yi mashi ƙarami. Ciki shi kuma Kamran ya shige, ga mamakinsa sai ya tarar basu a ciki dukkansu. Zaro idanu sosai waje ya yi yana tunanin to ina kuma suka tafi? Yasan dai Sweetie ita bata fita, koda Pretty ta ce tazo suje waje, in dai ba da shi bane bata yarda ta je, kullum tana cikin abinta, to ina suka je yau kuma?. Ya jefawa kansa tambaya.
Ganin babu mai bashi amsa ne yasa ya yi saurin juyawa cikin zafin nama ya nufi wajen. Rocky na kwance kamar yadda ya barshi. Bai bi ta kansa ba ya nufi wajen ƙoramar nan, dan ya duba su. Da sauri Rocky ya miƙe ya rufa mashi baya.
Tun daga nesa yake baza idanu ko zai gansu, amma kuma bai ga alamar su a kusa ba, hakan yasa ya yi saurin ƙarisawa wajen, dayawan lokuta tun daga nesa yake hango Pretty a saman durse tana wasa da ruwa, to yau dai bai ganta a wajen ruwan ba.
Har yana haɗawa da gudu ya ƙarisa wajen. Zaune suke a ƙarƙashin bishiya, Sweetie tana magana ita kuma Pretty ta buga uban tagumi tana kallon ruwan dake gudu a ƙasar ƙoramar.
A hankali Kamran ɗin ya lallaɓo kamar wani ɓarawo, ya ce da Rocky ya tsaya yana zuwa, da yake sun saba sai Rockyn ya tsaya, sanɗo ya fara yi kamar mai son yin wani abin, da yake Pretty ta bawa hanyar da yake zuwa baya sai bata gansa ba, ita kuma Sweetie dake fuskantar hanyar bata gani, so basu san da zuwansa ba.
Sanɗo ya cigaba da yi har ya iso kusa da Pretty, dama tana zaune ne a saman jijiyar bishiyar, irin bishiyoyin nan ne masu jijiya manya manya kamar jikin wani bishiyar, to a saman jijiyoyin suka zauna daga ita har Sweetien.
Yana ƙarisowa wajen cikin dabara ya sanya hannunsa ya capke kan black snake dake ƙarƙashin jijiyar bishiyar ta bayan Pretty ta kuma gaban Sweetie kenan, yanayin yadda suka zauna kamar suna fuskantar juna ne, Pretty tana fuskantar ruwa, ita kuma Sweetie tana fuskantar hanyar dake bayan Prettyn, so Pretty ta bawa macijin baya shiyasa bata gansa ba, ita kuma Sweetie bata gani ma bare ta ganshi, ga shi kuma a gabanta, sai dai bai yi yunƙurin cizonsu ba, yana kwance ne shiru shi ma macijin, da alama ma kamar bai ji motsinsu ba, kuma dai hira suke yi a kan mum ɗinsu, suna tattaunawa a kan ina take? Ina ta shiga? Ina ta tafi ta barsu? Ta mutu ne ko tana raye? Suna kewarta.
Yana damke kan maciji, macijin ya harɗe mashi hannunsa da bindinsa, matse kan ya yi da karfi dan ma kada ya fito da waɗan nan shegun harshen nasa mai baki biyun ya caka mashi dafi.
Kusa da Prettyn ya zauna tare da ɓoye hannunsa da ya riƙe macijin ta bayansa dan kada ta gani. Jin an zauna a kusa da ita yasa ta juyo da sauri.
"Lah Kamran kai ne?". Ta faɗa cikin tsantsar farinciki tana sakin murmushi.
Sweetie ma cewa ta yi. "Malam Kamran ya aka yi kasan muna nan? Sannunka da zuwa".
"Ai nasan ba zaku wuce nan ɗin ba shiyasa da naje can baku nan na zo nan, ya karfin jikinki?". Ya yi maganar kamar wanda shock na wutar lantarki ta kama, ba komai yasa hakan ba kuma face wannan maciji dake ta faman harɗe mashi hannu da bindinsa.
"I really missed you Kamran, yanzu ma am thinking of you, na ce baka zo ba har yanzu, ashe kana hanya". Cewar Pretty.
Sweetie ce ta amsa da cewa. "Kamran yesterday bamu yi sallama ba, you just go without telling me, pretty kawai ka gayawa".
Juyowa ga Sweetien ya yi da nufin ya bata hakuri. Ihun da Pretty ta zunduma ne yasa ya dakata da yin maganar, ya manta ya juya ta kalli macijin da yake ta faman harɗe mashi singalalin hannunsa izuwa sama, dan macijin yana da tsawo sosai, ga jikinsa sai kyalli yake yi, bakin kirin da shi, mugun maciji kenan, kumurci da idan ya cijeka minti biyar ta yi maka yawa a duniya idan ba'a kawo agajin gaggawa ba.
Ihun da ta zunduma yasa Rocky ya ƙariso wajen da gudu. Ita kuwa ta miƙe da gudu zata bar wajen, ta ruɗar da Sweetie da ba gani take yi ba, sai faman tambayarta take yi Pretty lafiya kike ihu, amma ina ita ƙoƙarin guduwa ta bar wajen ma take yi.
Cikin hanzari ya riƙota da hannunsa ɗaya yana ƙoƙarin ya yi mata magana, ai ina wani irin ihun da ta saki sai da dajin ya amsa, kan kace me kuma ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutar nema, akwai ta da shegen tsoro, kuma shi fa maciji kwarjini ne da shi, ba kowa yake iya kallonsa kuma ya wuni cikin walwala ba, bare kuma ace mutun yana da tsoro dama, idan ka kalle shi sau ɗaya a wuni sai ka rinƙa jin kamar fa yana nan tare da kai, koda kuwa an kashe shi a gabanka, duk sai ka ji kana takure.
Ai kuwa sume mashi a jiki ta yi. Yana ƙoƙarin sauketa ƙasa ya miƙe dan yasan ya zai yi da macijin, sai ga Rocky ya ƙariso wajen. Gabansa ya zo ya fara buɗe mashi baki a kan ya bashi kan macijin ya rike mashi sai ya zame hannunsa daga harɗe shi da macijin ya yi, da alama sun saba yin hakan. Ba musu Kamran ɗin cikin dabara ya bashi, ko tsoro bai ji ba ya warware hannunsa daga naɗin da macijin ya yi masa. Da gudu Rockyn ya bar wajen da macijin sai wintsila bindi yake yi.
Shi kuma ya kwantar da Prettyn a kasa a wajen ya miƙe tsaye ya riƙo Sweetie dake ƙoƙarin miƙewa tana ta ambatar sunan Pretty lafiya kuwa, duk ta ruɗe.
Riƙota ya yi yana faɗin ta yi shiru babu abin da ya sami ƴar uwarta, kawai ta ga maciji ne ta tsorata. Aikuwa ita ma Sweetien tana jin sunan macijin ta kara rikice mashi tana tambayarsa ina macijin yake? Ya cizan mata ƴat uwa ko? Nan take ta fara yi mashi ruwan hawaye.
Rarrashinta ya fara yi babu kakkautawa tare da gaya mata babu abin da macijin ya yi masu, sumewa kawai Prettyn ta yi. Subhanallah ai kuwa sake rikice mashi ta yi tana faɗin. "Na shiga uku sumewa kuma? Suma fa kanin mutuwa kenan, dan Allah Kamran ka tasan mun ƴar uwata kada ta mutu".
Dafe kansa ya yi yana danasanin gaya mata cewa suma ta yi, shi wlh idan abu ya rikice tsakaninsa da twin's ɗin nan suna rikita shi sosai, kusan buɗa mashi ƙwaƙwalwarsa suke yi, ba Sweetien ba ba Prettyn ba dukkansu idan abu ya rikice halinsu iri ɗaya ne.
Da kyar ya samu ta yi shiru, sannan ya zaunar da ita ya koma wajen Pretty, ɗaukarta cancak ya yi ya ƙarisa bakin ƙoramar da ita, a saman wani dutse mai ɗan faɗi ya kwantar da ita tare da sanya hannunsa ya ɗebo ruwa mai haske daga cikin ruwan dake gudu. A fuska ya shafa mata ruwan.
A haukace ta........
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2/9/2024.....✍️📚🌹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
A haukace ta farfaɗo tana ihun kada Kamran ya bari macijin ya kamata.
Da kyar ya samu ta nutsu ya iya gaya mata ai macijin baya nan ya tafi.
Kin yarda ta yi, ta ce ita lallai su bar wajen, ba zata sake zama a wannan wajen ba. Shiru ya ɗan yi yana tunanin da bai zo ba fa idan macijin ya farga da suna wajen zai iya yi masu illah, kuma ita Pretty ita zai fara yi wa illar, dan ta fi kusa da shi, tab ai kuwa da yau dajin nan babu zaman lafiya, da kowani namun dawa sai ya san da zamansu a cikin wannan daji, dan wannan ɗan bakin nata idan ta fara kurma ihu ina ga har Mamma yau sai ta jiyosu.
Ganin ya yi shiru ya afka duniyar tunani ne yasa ta miƙe da sauri tana faɗin. "Bari na je na kama hannun Sweetie mu koma, ba zamu sake zuwa wajen nan ba".
A hanzarce ya miƙe ya rufa mata baya, bai ce da ita komai ba, dan yasan ko ya ce zai yi magana ma ba zata saurare shi ba, ta rigada ta yanke hukuncin, kuma a yadda take