x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 77 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 228001 words
  • 231000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 420

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
dan kuwa wlh idanunsu iri ɗaya sak, kamar Akka ta samu sabo ta basu tsoho..........😅

Murmushi ta sakar mashi tana ƙoƙarin yin magana auta ta rigata da cewa. "Ni gaskiya Yah Rizwan ban yarda ba, nifa nagama shirina tafiya kawai zamu yi kace zaku yi hira? Wlh idan ba so kuke na fara kuka na kai karanku wajen daddy ba Allah ku bar hiran sai mun dawo".

"Wai ina zaku je nema?". Rizwan ya tambaya.

Chuchu ce ta bashi amsa da. "Nima dai ban sani ba, kawai Yah Jawad ya ce mu shirya mu same shi a part ɗin Aunty MieMie....."

Katseta auta ta yi da cewa. "Wai dama Yah Jawad ya ce mu same shi a wajen Aunty MieMie ne kika zauna a nan ban sani ba, baki gaya mun ba, to ni dai na tafi". Tana kai karshen maganar ta miƙe da sauri ta nufi hanyar fita daga room ɗin mayafin kayan na jan ƙasa, ta tattaro ƙasan sket ɗin da hannunta ɗaya kamar dole.

Da sauri ita ma Chuchun ta miƙe tana faɗin. "Yah Rizwan in tafi ko?".

Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya dai tsareta da ido yana ta kallonta. Katse kiran ta yi ba tare da ta sake yi mashi magana ba. A hanzarce ta rufawa auta baya tana murmushi.

Kai tsaye ƙasa suka yi tare da nufar part ɗin Aunty MieMie, suna tafiya suna hira, kamar wasu taurari. A kan hanyarsu na tafiya ta wajen tsakanin part ɗin uncle Abbas da part ɗinsu suka ci karo da commander ZAFAR tare da Sadauki Hoorain da kuma wani jarumin mayaki ɗaya suna tsaye suna tattaunawa, da alama magana mai mahimmanci suke yi.

Cikin girmamawa Sadauki Hoorain da wannan mayaki suka ɗan dukar da kansu ƙasa tare da yi masu sannu, shi kuma commander Zafar bai duka masu ba, amma cikin mutunci ya yi masu sannu tare da tambayar ina zasu je?.

Chuchu ce ta basu amsa da cewa part ɗin Aunty MieMie zasu je, ita kuwa Auta tuni hankalinta ya koma kan mutuminta wato Sadauki Hoorain, ta tsaya ne ma tana tambayarsa wai ina yake shiga ne kwana biyun nan bata ganinsa sosai?.

Cikin girmamawa ya yi ƙasa da kai, da wannan sanyayyar muryar tasa ya amsa mata da cewa. "Kece kika dai'na fitowa lambu ranki shidaɗe, shiyasa baki ganina, amma ina nan".

Kallon commander Zafar ta yi kafin ta ce. "Abbu kai ma fa na dai'na ganinka sosai".

Duk cikin masarautar kowa da commander Zafar yake kiransa, ɗansa Hoorain ne kawai yake kiransa da Abbu, sai kuma auta da take bin bakin Hoorain ɗin, ita kaɗai take bashi wannan darajar, shiyasa yake kaunar yarinyar, shiyasa shi ma Hoorain yake kula da ita sosai, tana da girmama manya.

"Gimbiya ina nan, kamar yadda Hoorain ya gaya maki ne, muna nan kece baki fitowa yasa baki ganinmu".

Hannunta Chuchu ta ja tana faɗin. "Ke idan mutun ya biye maki sai ki kwana a nan, wuce mu tafi, ke kowa kika gani sai kin tsaya tambayarsa ina ya shiga kwana biyu? Bayan kina kule a cikin room ta ina zaki gansu dama?".

Da kallo kawai su commander suka bisu da shi, auta tana son tsayawa ta ɗan yi magana da Hoorain and commander, amma Chuchu ta hanata, haka ta hakura ta bi bayan Chuchun suka nufi ɓangaren Aunty MieMie da mijinta kenan.

A babban parlourn kasa suka isko Aunty MieMie zaune a tare da Jawad suna tattaunawa. Aunty MieMie tana shirye cikin kayan sarauta kusan kamar kullum, ga alkyabbarta dake jan ƙasa a jikinta.

Suna shigowa suka haye jikin Aunty MieMie, har suna rige rigen kwanciya a kafarta.

"Ni ku tashi kada ku karyani, yanzu kun zama ƴan'mata har ma kun kusa zama matan wasu". Cewar Aunty MieMie. Ta yi maganar tana kallon Jawad, da alama akwai abin da ya gaya mata dangane da chuchun, shiyasa da ta yi maganar sun kusa zama matar wasu sai ta ɗago tana kallonsa.

Kawar da kansa ya yi kamar bai ganta ba.

"Ku tashi mu fita ta part ɗin Aunty MieMie nan, bani key ɗin motarki Aunty Babba". Cewar Yah Jawad ɗin, ya yi maganar kuma yana miƙewa tsaye.

"Ni dai ba zan bada key ɗin motata ko guda ɗaya ba, haka kawai za'a fitarwa da daddyna ƴan'matansa waje bada saninsa ba, to sai dai a bani cin hanci ko kuma na tona asiri". Cewar Aunty MieMie.

Auta ce ta ce. "Aunty MieMie ni zan baki cin hancin kin ji? Please ki bamu kin motar mana, amma fa idan daddy ya kamaki kina karɓar cin hanci babu ruwana".

"Sarkin son yawo ba, da anyi hutun school ki ce Dubai, yanzu kuma a nan ma zaki fara ko? Bari daddy ya kamaku zaku yi bayani". Aunty MieMie ta faɗa tana kallon auta.

Dariya kawai suka yi ita da Chuchu, shi kuwa Jawad ya tsaya yana ta satar kallon Chuchun, a ƙagare yake Aunty MieMie ta basu key su tafi, dan ya fitar da su ya je ya yi ta kallonta a wajen, amma Aunty MieMie kuma ta tsaya tana ta wani ja mashi rai, ya sani da gangan take yi mashi hakan.

Sai da ta ja masu rai sosai sannan ta ɗauko mashi keys dayawa ya zaɓi guda ɗaya. A hanzarce ya wuce gaba yana cewa su zo su tafi.

Da sauri suka miƙe suka bi bayansa suna dariya, sai addu'ar Allah ya dawo da su lafiya Aunty MieMie take yi masu suna amsawa da Amin. Bayan sun shiga cikin motar ne ya tambayesu meyasa suka jima kafin su zo?.

Auta ce ta bashi amsa da cewa. "To ba Aunty Chuchu bace ta tsaya biyewa Yah Rizwan suna ta hira...."

Da sauri Chuchu ta tari numfashinta da cewa. "Waye ya fara yin hira da shi? Ba kece kika shigo mun room da wayar kuna yin video call ba? Ai kece nan kika zauna tun a room ɗinki kika rinƙa hira da shi, ni babu ruwana kada ki yi mun sharri, ina gaisawa kawai muka yi, kuma bai wuci 5 mins ba muka gama......".

Auta ta buɗe baki zata yi magana. Katsesu ya yi da cewa. "To dai shikenan ya isa haka, yanzu dai kusa seat belt ɗinku zamu tafi".

Dukkansu gidan gaba suka shiga, da kansa zai ja su kenan. Ba ɓata lokaci ya tada motar bayan sun sanya seat belt ɗin, kai tsaye ya nufi tampatsetsan gate da zai fitar da shi daga ɓangaren Aunty MieMie, suka ratsa ta bangaren uncle Abbas sannan suka nufi katafaren gate one na kingdom ɗin.

Sai daɗi su auta suke ji kamar me, ya ji daɗi sosai shi ma na ganin suna a cikin farinciki har haka.

Suna fita daga masarautar Jaish ya kira shi a wayarsa dake hannun Chuchun. Miƙa mashi ta yi, kamar ba zai ɗauki kiran ba, sai kuma dai ya ɗauka. Daga ɗayan ɓangaren Jaish ɗin ya ce mashi ina yake ne?.

Shiru ya ɗan yi kafin ya bashi amsa da baya nan kuma ya ɗan yi nisa, uncle Abbas ne ya aikesa, amma ba zai jima sosai ba zai dawo.

Sosai Jaish ya yi mamakin jin hakan, domin ya gano karya yau Jawad ya yi mashi, daga yanayin maganarsa ya fahimci ba gaskiya ya faɗa ba, yasan halinsa sarai, tare suka taso.

"Jawad me kake ɓoye mun?". Cewar Jaish.

"Mekuma zan ɓoyemaka Jaish? Babu komai, amma meyasa ka ce na ɓoye maka wani abin".

Shiru Jaish ɗin ya yi na ƴan sakani kafin ya ce. "Saboda ba gaskiya ka gaya mun ba shiyasa na ce me kake ɓoye mun? Kai kanka kasan ba gaskiya ka faɗa ba, kawai ka gaya mun ina kake?".

"Kai my blood kana saurin gane abubuwa, na ɗan je wani waje ne to, but idan na dawo zamu yi magana".

Hmmmm kawai Jaish ya ce mashi. A hanzarce ya katse kiran, a cewarsa ko hauka yake yi ba zai bari Jaish ya gano cewa yana son chuchu ba, dan ba zasu wanye lafiya ba, Jaish ɗin zai ce shikenan ya gama ja masu raini a idanun kannensu, ya gama zubar masu da mutunci, ya gama da su, ba karamar dirama zasu yi ba, dan wlh Jaish ba zai yarda ba, bare ma shi da ba sanin darajar soyayyar ya yi ba, ba yinta yake yi ba, bai taɓa yi ba bare yasan zafinta ko sanyinta, ai kunga ba zai ɗauketa da mahimmanci ba, zai ce Jawad ya haukace, ina ai bama zai yarda ba, Jawad ɗin yasan da hakan shiyasa yake ɓoye mashi, kuma shi ma Jawad ɗin a rashin sa'arsa da ya tashi ɓoye abin sai ya ɓoyewa har da ita Chuchun, a cewarsa yanzu ta yi karama, idan ya gaya mata cewa yana sonta na farko zata rai'na shi, na biyu kuma a gaskiya ta yi ƙanƙanta da batun soyayya, karatu yake son ta yi, shiyasa ya barta a duhu bai sanar da ita ba, ya dai ce zai koyawa kansa shakuwa da ita, zai na sakar mata fuska su saba, amma banda zancen soyayya, dan a ganinsa tana jin cewa yana sonta shikenan ta rai'na shi. Tashin sense!. Akwai cakwakiya ba kaɗan ba, da alama Rizwan zai riga shi bayyana mata soyayyarsa, ita kuma dai kunga bata taɓa yin soyayya ba bare ta ce akwai son wani a ranta, so a yadda take a yanzu duk wanda ya ce yana sonta daga cikin ƴan uwanta zata iya amince mashi, bare kuma a yadda suke son juna dukkansu, babu nuna banbanci a tsakani.

(Yah Jawad yana ruwa kusa da.....🥱🤔 Akka😅🤭)

Tuki yake yi yana kallonta ta wutsiyar idanunsa, wannan kwalliya tata ta tafi da imaninsa sosai da sosai. Ita kuma sai kallon hanya suke yi ita da auta, suna farinciki yau dai ga su a wajen Kingdom, kamar bakinsu ba zai rufu ba.

Kai tsaye wani haɗaɗɗen wajen da suke yawan zuwa shi da Jaish su zauna su huta idan pressure ya yi masu yawa a kai ya nufa da su, idan sun tarawa kansu aiki ko kuma Jaish yana son su tattauna ba'a office ɗinsu ba kuma ba'a gida ba, sai su zo wannan wajen hutawar mai cike da kayan alatu su zauna su yi duk tattaunawar da za su yi cikin sirri. Jaish ɗan jarida ne babba, so ba kamar Jawad yake ba, kwakwalwarsa kullum tana cikin aikin ƙaƙale ƙaƙale, shiyasa yake son keɓewa shi kaɗai dan ya rinƙa zurfafa tunaninsa tare da faɗaɗata. Shi kuwa Jawad ai kunga har lokacin soyayya yake da shi abinsa.

"Yah Jawad ka kaimu zoo mu kalli namun dawa, daga nan ka kaimu wajajen wasanni mu ɗan yi wasa". Cewar Chuchu.

Ɗaga mata gera guda ya yi kafin ya ce. "Jannat har yanzu baki yi girma da zuwa wajen wasanni ba ko?". Ya yi maganar yana zama a ɗaya daga cikin tsala tsalar sofas dake part na musamman a wajen, part ne na musamman wanda sai wane da wane suke zuwa wajen, babu hayaniya sam sam a wajen.

"Kai Yah Jawad to duka duka shekaruna nawa? Ko sha shidda fa ban kai ba". Ta faɗa tana turo baki.

Auta ce ta ce. "Yah Jawad tun da yau mun fito ka kaimu har da gidan kallo mu kalli Film".

Girgiza kai ya yi, kwata kwata su auta basu da wata matsala a rayuwarsu, wai gidan kallo, su dai tun da yau sun fito shikenan kuma, sai abin da Allah ya yi, akuyar ɗaure an samu sake.

"Zaku ci abinci a waje yau?". Ya tambayesu yana kallon face ɗin chuchu.

Har suna haɗa baki wajen amsawa da e zasu ci, basu taɓa cin abincin waje ba.

Bai sake yi masu magana ba ya buga masu oder kawai, a kawo masu kayan cima da abinci mafi tsada a wajen. Ba'a ɓata lokaci ba aka kawo masu.

"Bismillah ku ci abincin waje yau ku ji ya take". Ya faɗa yana ciro wayarsa, sai kuma ya kawar da kallonsa daga kansu, dan ba zai so ganin yadda za su yi da fuska ba, sai ɗauki su kuma suke yi yau dai za'a ci abincin waje.

Chuchu ce ta fara ɗaukar spoon ta ɗebo madbe dake a saman plate na gabanta. Madbe ba sabon abinci bane a wajensu, amma yau ji suke yi kamar sabon abu aka kawo masu, saboda na waje ne ba su kuyanga Zubaida ne suka haɗa ba.

Fuska a ɗauke da murmushi ta kai shi bakinta, ta zuba ta fara tauna. Nan take ta kwaɓe fuska kamar wadda ta tauna wani abin mai ɗaci.

A hanzarce ta tufo shi waje tana kara kwaɓe fuska. Dariya ne ya so kubce wa Yah Jawad ɗin, dama yasan za'ayi hakan shiyasa ma ya kawar da kansa, ba zai so ganin sauyawar fuskar masoyiyarsa daga murmushi zuwa ƙunci ba.

"Aunty Chuchu what happened naga kin fito da abincin?". Cewar auta.

"Isn't sweet at all auta, like coffee and salt".

Ai kuwa Jawad bai san lokacin da dariyar da yake ɓoyewa ta kubce mashi ba, bama abin da ya bashi dariya kamar yadda ta ce wai kamar coffee da gishiri, innalillahi Chuchu anji ɗanɗano kam tab.

Ganin yana yi masu dariya ne yasa Chuchu ta gane da gangan ya yi masu hakan, kenan yasan ɗanɗanon babu daɗi ya barsu suka ci? Har da wani ɗaukinsu zasu ci wani abinci na daban bana kingdom ba. Hakan yasa Chuchun ta fashe da kuka mai sauti, ta ji haushin dariyar da yake yi masu.

Ita kam auta mamakin ganinsa yana dariya ya sa ta ƙasa iya yin magana, ta dai san yana ɗan yin murmushi time to time, amma dariya mai sauti haka bata taɓa ganinsa yana yi ba sai yau.

Ita kuwa Chuchu zagewa ta yi da gaske tana kuka har da hawaye. Ganin hakan yasa ya dakatar da yin dariyar tasa, sannan ya fara ƙoƙarin rarrashinta.

Ƙin yin shiru ta yi, ta cigaba da yin kukanta. Da yaga da gaske fa take kukan sai ya miƙe ya dawo saman nasu sofan, dama su sun zauna ne a mai zaman mutun uku, shi kuma ya zauna a mai zaman mutun biyu, so sai ya miƙe ya dawo kusa da ita.

Ɗan rungumota ya yi yana faɗin. "Sorry my sister, tuba nake yi, kuma ai dama ba laifina bane, da nace maku babu daɗi kada ku ci ai da zaku ce na hanaku, kuma nasan halinku sarai zaku yi ta jin haushi na, amma kuma dana barku kuka ɗanɗana ai kunji da kanku ko?".

Cikin kuka ta ce. "To Yah Jawad meyasa zaka yi mun dariya?".

"To na tuba, ba zan sake ba". Yana magana yana ƙoƙarin goge mata hawaye, ita dai auta da Allah ya rufa mata asiri bata ɗanɗana ba lafiya lou ɗanɗanon bakinta yake.

"Yanzu ga shi ɗanɗanon bakina ya ɓaci". Ta faɗa tana fito da harshe domun ta goge harshen nata.

Sake guntse dariyar ya yi. (Ni ina tantanma ma, anya da ya tashi buga oder nan bai ce a ɓata abincin Chuchu ba kuwa?🤔 Dan wannan dariyar dai na mugunta yake yi, da biyu gaskiya, da gangan ya yi mata hakan.)

Hannu ya kai yana tayata goge ɗan harshen nata yana faɗin. "Bari ma na tayaki gogewa". Yana magana yana guntse dariya.

Kome auta ta tuna sai ita ma ta kwashe da dariya kamar wadda aka tsikara.

"Me kike dariya ke kuma?". Chuchu ta tambayeta.

Cike da zolaya ta ce. "Aunty Chuchu ɗanɗana nawa madbe ɗin ki ji kamar ya fi naki daɗi....."

Ƙasa ƙarisa maganar ta yi sakamakon harara da Yah Jawad ɗin ya wurga mata, da alama dai ya tabbata da gaske da gangan yasa aka ɓata na Chuchu dan ya tsokaneta.

"Ba zata sake ɗanɗana komai ba, salon ɗanɗanon bakinta ya kara canzawa ko?" Ya tari numfashin auta da sauri, dan ma kada Chuchun ta ce zata ɗanɗana ta ji akwai banbanci da nata, idan ta ji hakan kuwa kuka zata sanya masu ta ce sai ta ji dalilin da yasa nata ɗanɗanonsa daban.

Ganin irin hararar da ya yi mata ne yasa autar ta gane shi ya shirya komai, dan haka sai ta ja bakinta ta yi shiru, amma fa a cikin zuciyarta ta ƙuduri niyar sai ta gayawa Chuchun gaskiya idan suka je gida.

Cigaba da rarrashinta ya yi, ya kuma goge mata ɗan harshen nata tas, sannan ya ɗauko mata ruwan da ta zuba a cup da nufin ta sha idan ta gama cin abinci, yana ɗan rungume da shoulder ɗinta ya kawo mata cup ɗin saitin bakinta. Da sauri ta fara girgiza mashi kai tare da ce mashi ita ba zata sha ruwansu ba, kila ruwan ma sun zuba gishiri.

Dariya ne cike fal ransa, amma ya danne ya ce auta ta ɗauko mashi ruwa a mota bari ya bata ta kuskure baki. Ita dai auta ƴar ba ruwana, koma me za'ayi sai ayi ta yi babu ruwanta.

Auta na fita ya ce. "To juyo naga harshen naki ko ya fita?"

Ba musu ta juyo suna fuskantar juna, sakin shoulder ɗin nata ya yi tare da ƙurawa face ɗinta idanu.

"Yah Jawad har sai da harshena ya yi ja fa nasani". Ta faɗa tana mayar da harshen nata.

Jin ya yi shiru bai amsa mata bane yasa ta ɗago dan ta kalli meyasa ya yi shirun. Tana ɗagowa suka haɗa ido. Dariya ne ya so kubce mashi, domin da suka haɗa idon sai ya tuna da lokacin da ta ɗanɗana madbe ɗin ta kwaɓe fuska.

Yankar salar lemu ya ɗauko daga cikin kayan ciman da aka kawo masu ya sanya mata a ɗan bakin nata yana faɗin. "Ɗan kuskure baki da wannan tukun nan".

A hanzarce ta fara ƙoƙarin turo shi waje, dan a tunaninta duk kayan wajen akwai gishiri a cikinsu. Ɗan riƙo shoulder ɗin nata ya yi yana faɗin. "Kisha babu komai".

Make mashi kafaɗa ta yi tare da faɗin. "A'a Yah Jawad babu daɗi kayan waje, gaskiya ni na ƙoshi".

Yana ɗan murmushi kaɗan kaɗan ya yi ƙasa da murya. "Sorry ki sha kaɗan ki ji". Ya yi maganar tare da ɗauko mata wani lemun, dan ta tufar da wancan da ya bata da farko. A bakin ya sake saka mata, bata yi musu ba ta karɓa.

Yana rumgume da shoulder ɗinta auta ta dawo wajen ta same su.

"Yah Jawad babu ruwa fa a cikin mota". Ta faɗa tana komawa mazauninta ta zauna.

Dama yasan babu ruwa a motar, kawai ya aikata ne. Dan haka sai ya karɓi key ɗin motar kawai ya cigaba
End Ads