ɓacewa ganinsu, hakan yasa shi ma ya sake juyowa a karo na biyu domin ya yi masu kallon bye bye.
Ganin ya juyo yasa ta kawar da kallonta daga kansa, ta sunkuyar da kai ƙasa tana wasa da ƴan ƴatsun hannunta. Ita dai Sweetie da yake bata iya ganin komai, sai ta yi shiru abinta babu ruwanta.
Ya ɗauki a kallah two mins yana kallonta kafin ya sa kai ya wuce. Kafin ta ɗago kai ta yi mashi kallon karshe har ya wuce ya bar wajen.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta dawo da kallonta a kan Sweetie dake fuskantar hanyar shigowa, sai dai baiwar Allah bata iya ganin komai, abin gwanin ban tausayi.
"Sweetie ki koma ki yi kwanciyarki, mutumin ya tafi ai, ni kuma bari na yayyaka mana irin gayyakin da mum take yanka mana ɗin nan".
Ta yi maganar tana mai taimaka wa ƴar uwar tata dan ta kwanta. Duk wani abin da yake cikin ɗakin nan nasu daga cikin gari aka kawo masu shi, waɗan nan masu taimaka masun ne suka kawo komai, amma sun kasa iya ɗaukarsu su fitar da su daga cikin wannan dokar dajin, sai dai su kawo masu taimako a cikinta su kuma tafi su barsu a cikinta, abin da abin mamaki da kuma ɗaure kai!.
Kamran kuwa, yana fitowa Rocky ya yi maza ya miƙe yana shinshinarsa, wucewa gaba ya yi ba tare da ya bi ta kan Rockyn ba, dan yanzu baya a cikin natsuwarsa sosai, ƙwaƙwalwarsa cike take tab da tarin tambayoyi game da tunani, ya saka wancan ya kwance wancan, ya rasa amsar da zata gamsar da shi, ya rasa amsar da zata sanya mashi nutsuwa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga ruɗani sosai a kan al'amarin twins ɗin nan da mum ɗinsu.
Da kyar ya iya farautowa Mamma namar da ta aike shi, jikinsa duk babu kwari, a mace yake.
Yau nama ɗaya ma ya kama, kuma akuyar daji ce ya kama, a saman bayan Rocky ya ɗaurata, dan shi yau baya da kuzarin iya ɗaukar abu mai nauyi.
A haka suka isa wajen tsauninsu, Rocky ne ya fara hayewa dan ya je ya sauke wannan akuyar dajin dake a saman bayarsa. Shi kuma Kamran ɗin yana ƙoƙarin hawa ya ji alamar motsi ta bayan tsaunin nasu.
Shiru ya kasa kunne yana son ya ji motsin menene?. Tabbas akwai motsin dake fita da sauti kaɗan kaɗan, sai dai bai iya tantace motsin menene bane, hakan yasa ya fasa hawrawa saman tsaunin, sai ya nufi wajen da yake ɗan jiyo motsin dan ya duba.
Kai tsaye ya nufi wajen, bai yi tunanin komai ba, dan a cewarsa ai motsin babu sauti sosai, dan haka koma menene a wajen ƙaramin alhaki ne.
Sai dai kash ya yi tunani mara kyau a wanna gaɓar, dan kuma yana dimfarar wajen wasu jiga jigan zataran warriors ne guda huɗu a wajen, suna tsastsaye kamar wasu zakuna, duk sun sauƙa daga saman dawakansu, ɗaya daga cikinsu yana gyara wukar takobin dake a ƙugunsa, ɗaya daga cikinsu kuma yana ɗaure takalmar dake a kafafunsa da kyau da kyau, biyun kuma suna tsaye suna bin dajin da kallo, sun rike linzaman dawakan nasu.
Ba halin Kamran ya koma da baya, dan ya riga da ya dimfarosu gadan gadan, bai yi tunanin mutane bane a wajen, sun kuma rigada sun gan shi, ba halin ja da baya. Hakan yasa ya tsaya cak a in da yake ɗin yana binsu da kallo.
Cikin zafin nama biyu daga cikin warriors ɗin suka nufesa tare da zare takubansu, kamar waɗan da suke jiran shi dama, yadda kuka san dama suna jiran kiris ne su farwa duk wanda suka samu.
Shi kuwa Kamran ko alamar tsoronsu babu a idanuwansa, ganin kananan kwari ma yake yi masu, kada ku manta renon Mamma ne shi ɗin.
Suna zuwa basu yi wata wata ba suka yi yunkurin sare mashi wuya dan zalunci, sai kace ya yi masu wani laifi.
Ai kuwa shi ma bai yi kasa a gwiwa ba wajen ƙoƙarin kare kansa, nan take faɗa ya kaure a tsakaninsu mai munin gaske, dan ƙoƙarin kashe shi suka so yi, shi ma ya fito da nasa wukar dake a ƙugunsa ya fara ƙoƙarin kare kansa da ita.
Da yake shi ma ya san dabarun faɗa, yasan cewa faɗa ba karfi ake sakawa ba a cinma nasara, dabara ce kawai da zaka yi wajen ganin ka kai abokin faɗan naka ƙasa, sai Allah ya taimakesa ya kashe ɗaya daga cikinsu da wannan ƴar karamar wuƙa da take a kugun nasa, saboda shi ma yasan dabarun yaki ba kaɗan ba. Amma fa duk da haka yasha wahala kafin ya kashe ɗayan nasu, domin kuwa suma ba ƙananan kwari kamar yadda yake tunani bane, suna da karfi, kuma a matsayinsu na warriors kuma kunsan ai dole su san dabarun yaki, dan tsayayyen namiji ne shi ɗin yasa ma ya iya samun damar kashe ɗayansu, bugu da kari kuma bai tsokane su ba, bai shiga hanyarsu ba, kawai su suka kawo mashi farmaki, shiyasa Allah ya taimakesa a faɗar.
Kashe ɗayansu da ya yi ne ya kara harzuwaƙasu, gadan gadan suka nufe shi gabaɗayansu, bawan Allah bai yi masu komai ba saboda shegen zalunci sun farmakesa, a wajen kare kansa ya kashe ɗaya kuma sun sake harzuƙa sun yi kansa da nufin kashesa, a cewarsu wannan ƙaramin kwaron har ya isa ya yi wani yunkuri a gabansu, basu san cewa giwa yake mai tafiyar ƙasaita ba, basu san cewa shi ne king of this Forest ba, basu san cewa shi ɗin gayyace mai zaman kansa ba, guru ne renon zakanya Mammarsa!!.
Faɗa suka fara yi cikin tsantsar kwarewa da nuna fifiko a tsakaninsu, su uku bawan Allah shi kaɗai.
Cikin ikon Allah, Allah ya bashi iko ya sake kashe mutun ɗaya daga cikinsu, hakan yasa suka fusata sosai, a harzuƙe suka yi kansa a in da suka damƙe shi, ɗaya daga cikinsu ne ya damƙe shi tare da yin baya da hannayensa, suka murɗe mashi hannayensa dukka biyu baya, hakan yasa dole ya nutsu, amma sai tafasa zuciyarsa take yi mashi, kunsan dama Kamran ba dai zuciya ba, akwai ta kam na kin karawa.
Ɗayan ne ya matso kusa da su tare da ɗaga takobinsa zai cirewa Kamran ɗin wuya, shi kuma ɗayan yana rike da shi gam ya murɗe mashi hannu ta baya, sai haki suke ta yi tamkar waɗan da suka sha gudu suka ƙoshi, ba karamar wahala suka sha ba wajen samun damar kama shi, dan Kamran fa ba baya ba wajen faɗa, idan ka taɓo shi tab kafin a iya kwantar da tarzomar faɗarsa sai an shirya.
Wani irin haniniya da dawakansu suka fara yi suna ƙoƙarin guduwa ne yasa warrior da ya ɗaga wuƙa zai cirewa Kamran ɗin wuya ya dakata, a dubu suka juyo da kallonsu izuwa kan dawakan nasu, domin suga menene yasasu irin wannan haniniya suna ƙoƙarin watsewa su bar wajen?.
Wayam basu ga komai ba, sai dai basu ankaraba kuma suka ga gabaɗaya dawakan su watse da gudu kowanne ya yi ta kansa.
A zabure warriors ɗin suka fara waige waige suna neman menene dawakan nasu suka gani da yasa su suka yi irin wannan watsewa haka? Ko dai maciji suka gani ne? Kunsan doki bata shiri da maciji ko kaɗan, basu haɗa hanya.
Suna tsaka da wannan waige waige nasu basu ankara ba kamar daga sama Rocky ya faɗo gabansu yana wani irin numfashi mai rikitarwa. Ai wannan warrior da ya rike Kamran ɗin bai san lokacin da ya sake shi a dubu ɗari ba, shi ma wanda ya zaro takobi zai cire mashi wuya bai san lokacin da ya yi wata uwar ja da baya ba. Damuwa akwai kwarjinin bala'i, komai jarumtarka idan ka ganta sai ka ji fitsari na ƙoƙarin zubo maka, yo ka yi haɗuwar mutunci da damusa ma ya ka kare da bugawar zuciya da sauri da sauri, bare kuma ace ka yi haɗuwar rashin mutunci da ita? Ai shikenan faɗuwar gaba da bugawar zuciya ce ma kawai zata kasheka har lahira, kun san Damusa ta fi Zaki faɗa sosai, shi Zaki yana da hakuri, ba kasafai ya cika faɗa ba, sai zuciyar bala'i ke gare shi, amma ita Damusa, habawa ai koba tsokaneta ba wlh ta ganka sai ta farma, zaka iya tsokanar Zaki ya hakura kamar bai ganka ba, amma Damusa tab hmmmm ba'a magana.
Wani irin tsalle Rocky ya daka kan kace me ya kafawa ɗaya daga cikin mayakan waɗan nan garma garman hakwaran nasa a wuya, sai jini, tuni ya tsinke agarar wuyar. Ai a dubu ɗari ɗayan ya fasa cikin dajin da masifar gudu yana kurma ihu.
Gudu biyu Rocky ya yi ya capkosa, dama ina za'a haɗa gudun mai kafa biyu da kuma mai kafa huɗu? Ai ba zasu haɗu ba sam.
Nan take Rocky ya kashesu dukkansu biyu, ya samu nama, ya maye gurbin namar Pretty da Kamran ya hana shi ci.
Duk wannan faɗar da suke yi fa Mamma tana tsaye a sama nauninsu tana kallonsu, sam abin bai yi mata daɗi ba, bata so Rockyn ya kwaci Kamran ɗin daga hannunsu ba, tafi son Kamran ɗin ya kwaci kansa gabaɗaya, dan a tunaninta irin horon da ta bashi ya ci ace zai iya kashe warriors ire iren waɗan nan har guda 20 ba tare da ya gaji ko ya nuna sarewa ba, a tunaninta a irin horon da ta bashi waɗan nan mayaƙa kananan kwari ne a gabansa, sai kuma ta ga kash da sauran aiki a gabanta, ba yadda take tunani bane, dole sai ta sake ɗaura ɗamara sosai in har tana son Kamran ya kai matsayin da take kai shi ɗin nan. MAMMA LAMARINKI BABU SAUKI🤦 LAMARINKI ABIN DUBAWA NE, YANZU INA LAIFI A NAN? AI YA KWACI KAN NASA KO? YA KASHE ZARATAR MAYAƘA DA AKA SHA DAMAWA DA SU A FAGEN YAKI YA KASHE HAR MUTUN BIYU AMMA A HAKA KICE BAI YI ƘOƘARI BA?🤔 YA MAMMA TAKE SON KAMRAN YA KASANCE KENAN?🤔
Nufar saman tsaunin Kamran ɗin ya yi yana mayar da numfashi, ya baro Rocky yana cin nama, yau dai sallar Rocky, namomi baja baja abinsa, yo me yafi ransa? Ai yau shar zuciyarsa, Rockyn mu na amana.........😅
Dawakan warriors ɗin kuma sun watse sun bazama cikin daji, sun yi ta kansu kenan.
Ganin Mammarsa tana tsaye tana kallonsu ne yasa ya bita da kallon mamaki.
"Mamma what are you doing here?".
Ya faɗa yana mai cigaba da mayar da numfashi.
"Yanzu Kamran waɗan nan ƙananan kwarin ne ba zaka iya kashesu ba har sai da Rocky ya taimaka maka?". Yadda ta yi maganar zaka fahimci tabbas ranta ya sosu sosai da rashin kashesu gabaɗaya da Kamran ɗin ya yi.
"Mamma me zai hanani iya kashesu? Ai goma irinsu ma zan iya faɗa da su, kina tunanin zan bari su kashe ni ne? Ai ba zan tsaya ba, kawai dai shi Rocky shi ya yi shigar faɗar shigar sauri, kuma kinsan ba wanda ya isa ya hana shi shigar mun faɗa ko? Ba dan haka ba da kai'na zan gama da su".
Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi wajen da Rockyn ya yardar mashi da akuyar dajin da ya kamo.
Juyawa Mamma ta yi ta nufi cikin ƙogon nasu, tabbas ta yarda da zancen ɗan nata da yake cewa zai iya kashesu, dan ita tasan ba horon wasa ta bashi ba, tun yana ɗan shekara uku a duniya ta fara koya mashi faɗa, tana da burin taga ya zama shahararren guru, bujumin Zaki, Barde tsayayyen jan wuya wanda jarumtarsa zata gigita duk wani halitta mai rai, wannan dalili yasa ta tsaya tsayin daga a kansa babu wasa.
Aikin gyarawa Mammar tasa namar ya fara yi, yana feɗe fatar akuyar kamar yadda ya saba yi mata idan ya kawo namar, shi yake gyarawa ya yanka gunduwa gunduwa, sannan ya kai mata wajen madafanta ta ƙarisa sauran aikin.
Sai dai yana yin aiki zuciyarsa gabaɗaya yana wajen tunanin su pretty, burinsa kawai yanzu ya gama taya Mamma iya abubuwan da zai tayata, ya yi wanka ya je wajensu, shi ko tunanin cin abinci ma bayayi, so bai sanya abinci a lissafinsa ba, shi dai ya gamawa Mamma aiki ya yi wanka ya nufi wajensu kawai. Bawan Allah ba, baruwansa da rigingimun duniya, kamar wani Musulmin kwarai.
Ni kuma kafin nan bari na leƙa gidansu Khadija, kafin mu dawo kila Kamran ya gama gyaran nama ya yi wanka, sai mu bishi wajensu pretty a karo na biyu mu ga me ake ciki.🤨🧐
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
🔥GIDANSU KHADIJAH💔🥲
Misalin karfe biyuna rana dai'dai baban Zainab ya dawo gidan, kamar yadda ya yi mata alkawarin kawo mata wasu kayan haka ya dawo mata da su, sai dai kuma da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan cewa yana cikin tsananin damuwa da tashin hankali, da alama haɗuwarsa da mahaifiyar tasa sam bata yi mashi daɗi ba.
Ganinsa a haka yasa Maman Zainab tasha jinin jikinta, dan bata taɓa ganinsa a irin wannan yanayi ba.........
🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
Ganinsa a haka yasa Maman Zainab tasha jinin jikinta, dan bata taɓa ganinsa a irin wannan yanayi ba.
Kamar ko yaushe sannu da dawowa ta yi mashi kafin ta karɓi kayan hannunsa, bata jima da kammala girki ba, fitowarta daga wanka kenan, ko kaya bata sanya ba, towel ne a jikinta sai ta sanya hijabi jin cewa ana buga kofar gida, sai ta je ta buɗe kofar.
A parlourn ya zauna yana mayar da numfashi, kamar wanda ya yi gudu, duk ransa a matuƙar jagule yake.
"Ina Haidar yake maman Zainab?".
Shi ne tambayar da ya fara jefa mata.
Shiru ta ɗan yi tana mamaki, domin ita ko in da Haidar ɗin yake ma bata sani ba, time da ya bar gidan tana barci, a tunaninta ai baya zuwa ko'ina sai kasuwa ko wajen mamansa, bata san Haidar kam kasuwar ma sai ya yi ra'ayi yake zuwa ba.
"Haidar ya fita, kuma ina barci time da ya fita, so na ɗauka ai yana kasuwa".
Shiru ya ɗan yi mata na a kallah tsawon good 5 mins, sannan ya nisa kafin ya ce. "Jeki gama shirinki kizo mu yi magana kafin su Khadija su dawo daga school, dan naga lokacin dawowarsu ya kusa, yanzu ba jimawa Sadiq zai je ɗauko su".
Cikin nutsuwa ta amsa mashi da to, sannan ta miƙe ta nufi cikin bedroom tare da kayan da ya shigo da su, shi kuma ya kishingiɗa a saman sofa tare da miƙe ƙafafunsa ya ɗaura hannu guda a saman idanuwansa kafin ya lumshesu.
Cikin ƙanƙanin lokaci Maman Zainab ta kammala shirinta, yau ko make up bata tsaya yi ba, saboda saurin da take yi ta ƙariso wajensa, dan ya ce magana zasu yi, so bata wani ɓata lokaci ba ta shirya ta fito.
A saman kujerar dake kusa da wanda yake kwance ta zauna, cikin nutsuwa dai ta ce mashi gata nan ta fito.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya miƙe zaune daga kishingiɗar da ya yi tare da gyara zamansa da kyau da kyau ta yadda yana fuskantarta.
"Fitana daga gidan nan da safe wajen Mama naje kafin na wuce kasuwa kamar yadda ta buƙata kafin ta bar gidan nan da safen".
Kara nutsuwa Maman Zainab ɗin ta yi tare da tattara mashi dukkannin hankalinta a waje guda, dan ta saurare shi da kyau ta kuma fahimce shi.
Cigaba da yin maganarsa ya yi shima cikin nutsuwa tare da tattara mata hankalinsa a waje guda.
"Na je mun yi magana da ita ko kuma nace maki tayi maganarta bisa bani umarni da zaɓi guda biyu, a ciki dole na zaɓi guda ɗaya...."
Cikin zaƙuwa ta katse shi da tambayar wacce irin zaɓi ne ta bashi umarni a kai haka?.
Ɗan nisawa ya yi kafin ya ce. "Na farko ta ce mun ko na sake ki na auro wadda take kaunarsu, ko waye ya ce masu ke baki kaunarsu? Na yi ƙoƙarin gaya mata duk wadda zan auro ba zata taɓa kaunarsu kamar yadda ke kike kaunarsu ba, amma bata saurareni ba, kuma kema kin san dama ba zata saurareni ba, and zaɓi na biyu kuma shi ne, idan bana son rabuwa dake ba zata takura mana ba, amma nan da one month na zaɓi yarinya a cikin family na aura, a tunanin mama aure a cikin family shi ne zai sa na auri mai kaunarsu kamar yadda suke faɗa ɗin, na yi ƙoƙarin gaya mata ni bana da buƙatar mata biyu, dan ina da abin da nake son ginawa familyna wanda ko yau na mutu ba zasu wahala ba kuma ba zasu walaƙanta ba, amma ta zage sam sai na kara auren ko naki ko na so, and lastly ta ce a tare za mu koma sabon gidanmu da ita, sannan da amarya!". Babbar magana!!.
Ya kai karshen maganar yana kawar da kallonsa daga saman fuskarta, saboda baya ma son yaga halin da zata shiga, ya sani idan akwai abin da maman Zainab ta yi wa muguwar tsana a duniya to bai kai tsanar kishi da ta yi ba, sam bata son jin batun kishiya, saboda gani take yi kamar kishiyar zata rabata da mijinta da ƴaƴansu, hakan yasa ta tsani jin koda sunanta.
A ɓangaren shi kuma baban Zainab saboda kyautatawa da take yi mashi yasa ya sanya a ransa ba zai taɓa yi mata kishi ba, saboda ita ɗin macece mai kirki da shi da kansa yana jin kunyar ya yi mata abin da bata so, idan