Aikuwa tana yin ido biyu da wannan parrot ɗin ta fara yunƙurin miƙewa a guje dan ta bar wajen, dama Kamran yasan za'ayi hakan, shiyasa ya shammaceta ya kama parrot ɗin, yasan idan ta ji saukar shi a kusa da ita haukace mashi zata yi, kaɗan daga aikinta kenan sarkin tsoro.
A hanzarce ya riƙota yana faɗin. "Zauna ki ji".
Bata ankaraba sai ji suka yi parrot ɗin ya maimaita abin da Kamran ɗin ya faɗa na zauna ki ji, sai dai maganar akun bata fita sosai. Hakan na nufin akun mai magana ce, kun san akwai waɗan da basa magana, to shi wannan yana yi, sai dai maganar bata fita.
Wani irin zaro idanu waje Pretty ta yi na jin yadda wannan Parrot ɗin ya maimaita maganar Kamran, waɗan nan olive eyes ɗin nata kamar zasu faɗo kasa saboda zarosu da ta yi, cike tab da mamaki ta ce. "Kamran magana fa na ji ya yi......"
Ai bata kammala rufe ɗan bakin nan nata ba Parrot ɗin ya maimaita abin da ta faɗa na cewa Kamran magana fa na ji ya yi, still dai maganar bata fita sosai, amma ana iya gane me ya ce.
"Na shiga ukuna, Kamran dama tsuntsaye suna magana ne?......" Parrot ɗin ya maimaita abin da ta faɗa.
Ina ai a dubu ɗari ta yunƙura zata tashi, dan ita bata taɓa ji ko gani ba, ta dai san dabbobi basa magana. Kamran dai sai kallonta yake yi, dama da gangan ya kama parrot ɗin, dan kawai ta sanya shi yin nishaɗi, yana jin matuƙar nishaɗi idan yana kallon wannan kyakkyawar face ɗin tata cikin tsoro, idan ta tsorata ba ƙaramin kyau take karawa ba, sai ma ta zaro idanun nan nata, sai ka ji kamar ka yi ta kallonta kada ka gaji, hakan yasa wani lokaci har Allah Allah yake yi ta tsorata ya kalleta da kyau yana nishaɗi.
Kara janyota jikinsa ya yi tare da matso mata da parrot ɗin kusa da ita, ƙasa ƙasa ya fara yi mata magana bayan ya ɗan sunkuyo da kansa a dab da kyakkyawan razanannen face ɗin tata.
"Tsuntsaye basa magana Pretty, amma shi parrot yana magana sosai ma, kada ki ji tsoro babu abin da zai yi maki". Yana maganar yana kallon face ɗinta.
Ai kuwa yana rufe ɗan bakinsa Parrot ɗin ya maimaita abin da ya faɗa mata shi ma.
Sanya idanunta cikin nasa ta yi da kyau. Calmly ta ce. "Kenan ba aljani bane?". Yadda ta yi maganar a kusa da shi sosai hakan yasa sai da ya ji wani iri, ga shi kuma ta yi maganar tana zaro mashi waɗan nan dara daran idanun nata masu rikitar da shi, sannan tana magana kyakkyawan lips ɗinta yana ɗan kerma, dan already ta rigada ta razana tun farko.
Kafeta da idanu ya yi ya kasa iya bata amsa, shi kaɗan yasan a wani hali yake shiga a duk lokacin da zata yi magana kusa da kusa da shi har haka, bare ace maganar ta haɗu da tana cikin firgici ta yi sa tana zaro idanun nan, ai abin ba'a magana.
"Kuma ba zai cinyeni ba Kamran?". Ta sake jefa mashi tambaya tana mai cigaba da zaro idanun nata alamar mamaki abin ya bata.
Sam bai san lokacin da ya saki parrot ɗin nan ya tashi sama abinsa ba, ya luluƙa duniyar sama jannati na kallon ƴar diramarsa.
Ganin ya saki tsuntsun ne yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da ƙara shigewa jikinsa tana hamdala ga Allah daya sanya Parrot ɗin bai cinyeta ba. Sam bata lura da duniyar tunani da kuma kallonta da Kamran ɗin ya afka ba. Ita dai da ta ga ya saki parrot ɗin ya tashi sama sai ta juya ta cigaba da busar da take yi. Wannan shi ne yana yi bata san yana yi ba, ita dai babu ruwanta da wani abu wai soyayya, yo Allah na tuba dama nawa take? Ga rashin nutsuwa a tattare da ita, ita kanta Sweetie nutsatsiyar ma yaushe ta san menene soyayya bare wata Pretty, ai ita Pretty bata da wata damuwa a rayuwarta da ya wuce ta ci abinci, ta yi wanka ta kuma yi sallah, dan suna yin sallah a kan lokaci kam, kuma da rana suke auna lokaci, wani lokaci kuma da yanayin garin suke auna lokaci kamar yadda mum ɗinsu ta koya masu, bayan sallah kuma shikenan sai Kamran ya kaita yawo, iya abin da ta sani a duniyarta kenan ƴar albarka.
Sweetie ita ce mai zama ta yi tunani a kan gobensu da kuma makomarsu, wani lokaci har tana gayawa Kamran cewa tana ji a jikinta tabbas wannan dajin ba iya shi kaɗai bane a duniya, akwai wani waje, sannan shi ma wajen tana ganin kamar mutane suna rayuwa a ciki. Tun Kamran baya wani ɗaukar maganganunta da mahimmanci har abin ta fara shiga zuciyarsa shi ma, hakan yasa shi ma ya fara tunanin ƙure wannan dajin a wajen tafiya ko zai iya ganin makamancin abin da Sweetien take hangowa na wasu mutane da suke rayuwa a duniya........ Tirƙashi, lallai Sweetie tana son ɓallowa Mamma ruwa, dan kuwa idan ya fita wannan dajin dai kunsan zai haɗu da mutane, idan kuma ya haɗu da mutane ku da kanku readers kun san labarin dole ya canza salo, dan kuwa ba karamar dirama zasu buga shi da Mamma ba, idan ma ya dawo a kan lokaci kenan, akwai fa cakwakiya idan har Kamran ya yarda da wannan hasashe na Sweetie, zai iya cewa ma Mamma munafurtarsa take yi ta ki gaya mashi bayan wannan dajin akwai wata rayuwa ta daban, kuma ina da tabbacin zai ce ba zai cigaba da zama a wannan daji ba, dan kowa dai baya son wahala sai dole, bare shi da yake bai yi kalar ƴan kauye masu duhun kai ba, da wayonsa da kuma iliminsa dai'dai gwargwado, kunga kuwa ai dole zai so canjin rayuwa, akwai cakwakiya, Sweetie ta zo da wata al'amari mai girman gaske wanda zai iya tarwatsa zuciyar Mamma, domin kuwa da ni da ku dukka mun san Mamma bata da kowa a duniya sama da Kamran, tana kaunarsa fiye da yadda take son kanta, kuna dai ganin yadda take kula da shi, ko nan da can bata son taga ya matsa, ace rana tsaka ya fita cikin wannan dajin, sannan ya dawo ya ce mata shi ba zai sake zama a nan ba wajen mutane zai tafi ya yi rayuwa? Kuna tunanin zuciyarta ba zai tarwatse ba? Hmmmm akwai case!.
"Pretty". Ya ambaci sunanta a hankali, ƙasa ƙasa kuma a ta cikin kunnuwanta.
Dakatawa da yin busar ta yi tare da juyowa gare shi. "Kamran lafiya ka kirani?". Ta yi tambayar tana riƙo hannayensa dukka biyu. Abin busar ta sanya mashi a hannunsa ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ta ɗaura shi a saman a shoulder ɗinta ta ɗan kwanto a saman kirjinsa.
"Pretty kin san menene soyayya?".
Tana daga kwance a jikinsa ta ce. "A'a ban sani ba, shima wani kalar abincin na Mammarka ko kuma fruits ne?". Ta yi maganar ba tare da ta ɗago ta kalle shi ba, tana kwance tana ganin zubar ruwar ƙorama abinta.
Ajiyar zuciya ya sauke, jiya wuni zunbur ya yi yana bincike cikin littatafan Mammarsa ba tare da sanin Mammar ba, a nan ne ya ci karo da wata littafi mai suna true love never end, da yake litattafin bata da yawa sosai, short story ne da bata wuci pepar ashirin ba, sai ya nutsu ya karanta, a nan ne ya samu abubuwa da dama har amsarsa na dan gane da aure, kasancewar a littafin ya karanta duk wahalar da jaruma da jarumin suka sha daga karshe sun yi aure sun mallaki juna, kuma sun haifi ƴaƴa, a nan ne ya fara tunanin kenan shi ma dai yana da baba? Ba iya mama bace kawai?. Ya dai samu abubuwa da dama a ciki littafin, ya kuma yi masu kyakkyawar fahimta, ya kuma tarawa kansa uban tarin tambayoyin da ƙwaƙwalwarsa take ƙoƙarin kasa ɗauka, ya kasa iya tambayar Mammarsa ina babansa? Ya kasa iya gaya mata labarin su Pretty, ya kuma rasa ta ina zai iya sanar da ita cewa an bashi auren Pretty, kuma da ya karanta wannan littafin ya fahimci yana son yarinyar nan Pretty, kuma zai aureta ɗin kamar yadda mum ɗinta ta bashi aurenta, duk ya kasa samun kwarin gwiwar iya sanar da mamma komai, ya shiga damuwa na wuce misali, sai saƙa da warwara yake yi na yadda zai ɓullowa da Mamma ta bashi amsoshinsa a kan waɗan nan al'amura.
Lallai akwai cakwakiya, finally ga shi dai Kamran yasan menene aure da ma ita kanta soyayyar, sannan kuma yasan cewa yanzu mace bata haihuwa ita kaɗai, har ya fara tunanin to shi ina nasa uban? Ga wani sabon cakwakiya kuma da Sweetie ta matsa mashi a kan su kurewa dajin nan tafiya ko akwai wasu mutane a wajen dajin, dan ita bata yarda da cewa suma warriors ɗin nan a cikin dajin nan suke ba. To Kamran fans ya kuke tunanin makomar Mamma idan har Kamran ya fita daga cikin wannan dajin yaga akwai mutane a wajen? Anya zai sake yarda ya zauna a dajin kuwa? Anya zai iya yin hakuri ya danne ba tare da ya buƙaci sanin ina mahaifinsa yake ba kuwa? One day one time da wuya idan bai tambayi Mamma da ta fito mashi da babansa ba, duk da yanzu yana tsoron tambayarta, amma dakamar wuya ya iya hakuri da babansa... Tashin hankali kenan, babbar magana!!. Forest ma ya kusa kamawa da wuta da alama!.
"Pretty soyayya ba abinci bane sarkin son cin abinci, kuma soyayya ba kayan fruits bane, wani abin ne na daban". Ya bata amsa ta hanyar raɗa mata a kunne.
Jin cewa ba abinci bane kuma ba kayan fruits bane soyayya yasa ta yi saurin ɗago da kanta daga saman kirjin nasa ta juyo garesa. "To menene kenan?".
Yadda ta ɗago da kan nata sai ya zama suna fuskantar juna. Tsura mata ido ya yi yana kallonta, tun da ya fahimci sonta yake yi sai ya dai'na jin wani irin yanayi tare da fargabar kallon cikin idonta, sai ya zamana ma idan bai kalli cikin idanun nata ba sam baya jin daɗi.
"Ya kake ta kallona haka Kamran? Na ce maka menene soyayyar baka bani amsa ba? Wajen yawo ne to? Ko dai wasu dabbobin ne?".
A hankali ya motsa kyawawan lips ɗinsa ya furta. "Kece soyayyar mana".
Kyafta idanunta sau biyu ta yi tare da sakar mashi wani irin cool murmushi mai kara mata matuƙar kyau, har dimples ɗinta suka lotsa. "Kai kam Kamran wani lokaci ka iya maganar banza, ni ce soyayya kuma? To ni dai sunana Pretty ba soyayya ba".
Tun daga yanayin maganar Pretty zaka fahimci duk wanda zai auri wannan yarinya yana ruwa kusa da kada, sai ya shirya shanye duk wani shirmenta har Allah ya gyara mashi ita, ko da yake yarinta ne sosai a kanta, ƴar shekara goma zuwa shaɗaya nawa take dama? Ai yarinya ce sosai.
Da yake shi Kamran ya saba da halin kayarsa, sai ya ɗan matso da face nasa dab da tata, ƙasa ƙasa kamar mai tsoron wani kada ya jisu ya ce. "Ai ban ce maki sunanki ne soyayya ba bare ki ce mun sunanki Pretty, duba idonta a wajen kamar na raƙumin dawa".
Da yake ba'a yi mata ta kyale sai da ɓallah mashi harara tare da faɗin. "Ai garani ma idon Raƙumin dawa ce da ni, kai kuma idonka kamar na wannan Rocky ɗin naka". Ta kai karshen maganar tana kara ɓallah mashi harara.
Murmushi kaɗan ya ɗan sakar mata kafin ya ce. "Na ji to, yanzu dai koma menene ki sani dai ina sonki".
Shiru ta ɗan yi, sai yanzu kalmar ina sonki ya fara dawo mata a cikin ƙwaƙwalwata, mum ɗinsu tana yawan gaya masu cewa ina sonku ƴaƴana, kune duniyata kuma kune komai nawa, ina alfarhari daku kuma ina son yin rayuwa da ku, na kasance da ku na kuma kula da ku, na baku tarbiya irin ta addinin Musulunci na kuma baku ilimin addini dana zamani, ina kaunarku fiye da yadda nake son kai'na.
Sosai maganganun mum ɗinta suka rinƙa yi mata zarya a cikin kunnuwanta zuwa ƙwaƙwalwarta, kenan yanzu shi ma Kamran irin son da yake yi mata kenan? Irin son da mum ɗinsu take yi mata?
Ganin ta luluƙa duniyar tunani ne yasa ya kai hannunsa ya ɗan shafi lallausan kumatunta haɗe da dogon kyakkyawar hancinta da ya zauna ɗas a face ɗinta.
"Kema kina sona ko?". Ya faɗa a hankali.
Kara kallon cikin kwayar idanunsa da kyau ta yi kafin ta ce. "Ni ban san menene ma'anar kalmar ina sonki ba, mum ɗinmu tana faɗa mana shi, so ni ban san me take nufi ba".
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fara yi mata bayanin menene soyayya kamar yadda ya karanta a wancan littafin, sai dai ya ɓoye mata menene aure da kuma ganowa da ya yi cewa suna da iyaye maza, dukka ya ɓoye mata wannan, saboda a ƙananun shekarun nan nata ba fahimtar komai zata yi ba, sai dai ta kara tabka mashi shirme, dan haka sai ya yi mata bayanin abin da zata gane kawai cikin sauki.
Ɗan taɓe baki ta yi a lokacin da ya gama yi mata bayanin menene soyayyar. "Dama wannan ce soyayya? To ai ina sonka nima". Ta bashi amsa tana kallon cikin idonsa.
Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗi da sakar mata cool murmushi mai matukar kyau, ya ji daɗi sosai. Tabbas kamar yadda ta faɗa tana son shi haka ne, tana son shi amma ba kamar yadda shi yake sonta ba, kunsan kowace zuciya tana son mai kyautata mata, to hakance, dole zasu so Kamran sosai, dan a yanzu shi ne komai nasu.
Cigaba da hirarsu mai shegen daɗi a tsakaninsu suka yi, yana kara fahimtar da ita yadda soyayya take, ta wani kasa kunne tana ɗaukan bayanai, ita kuwa Sweetie tana can tana barci abinta, ba ruwanta da hayaniya.
Sun jima a haka kafin nan ya ce mata zai koma gida ta tashi ya rakata wajen maɓoyarsu da yamma zai dawo su sha hira da soyayyarsu. Sam bata so tafiyarsa ba, kawai dan ba yadda zata yi ne, tana matuƙar jin daɗin kasancewa da shi, idan ya ce zai koma har ji take yi kamar ta yi kuka ko kuma ta bi bayansa su tafi a tare, amma ba hali. Haka ta miƙe tana turo baki, sai hakuri yake bata, har da goyata a bayansa ya yi izuwa wajen bakin ramin nasu, duk dan baya son ganin fushinta, duk dan ya lallaɓata ta yi farinciki kafin su rabu.
Da kyar ya iya sakata dariya kafin su rabu, sai da ta yi dariya mai sauti ma tukun nan, sannan ya ce ta shiga ciki kuma kada ta yarda ta tashi Sweetie daga barci, sannan kada ta sake fitowa waje sai ya dawo da yamma. Da okey kawai ta amsa mashi kafin ta sa kai ta wuce ciki. Shi kuma bayan ya tabbatar da ya rufesu da kyau sai ya nufi gida.
A bakin kofar shiga ƙogonsu ya ci karo da Rocky dake ta faman barci, da alama ya ci ya ƙoshi ne, wucewa ciki ya yi izuwa cikin ɗakinsa. Ga mamakinsa sai ya isko Mammarsa a cikin ɗakin nasa tana yi mashi bincike.
Bai nuna mata ya yi mamakin hakan ba, ya wuce kawai ya haye saman gadonsa yana faɗin. "Mamma sannu da hutawa ina abincina?".
Zuba mashi idanu sosai ta yi na ƴan sakanni kafin ta ce. "Kamran cire hular kankan nan bari na gani".
Da yake ya manta shap da zancen cewa Pretty ta yi mashi kitso, sai bai wani damu ba, yana kallon face ɗin mammar tasa ya cire hular.
Kun san fa idan mutun ya yi kitso koma ya take sai face ɗinsa ta ɗan canza, shi ne yasa Mamma ta iya ganewa, kuma da yake taga wannan uban tulin gashin nasa da idan ya sanya hula take cika hular duk ta ɓace, hakan yasa ta fahimci an taɓa mashi gashin, shi yasa ta ce ya cire hular ta gani, sam bata kawowa ranta cewa kitso ma aka yi mashi ba, ta dai fi tunanin cewa shi ne ya datse gashin nasa ya zubar.
Zaro idanu waje ta yi sosai tana kallon kitso guda biyun, tun da take da shi ko da sunan wasa bata taɓa yi mashi kitso ba, bata taɓa kwatanta yin kitso bama, dan ita gashin kanta baya kitsuwa saboda tsantsi, to a ina kuma ya samo kitso? Tasan dai ba shi ya yi wa kansa ba, dan bai iya ba.
Shi kuwa ganin yadda ta zaro idanun nan nata tana kallon kan nasa ne yasa ya yi saurin kai hannunsa saman gashin nasa dan ya ji menene ya sanyata zaro idanu haka?.
Ai bai san lokacin da ya miƙe tsaye a dubu ba time da ya ji kumbusa kumbusar kitson da rigimammiyarsa Pretty ta yi mashi. Yau ya shiga uku! Wani amsa zai bawa Mamma kenan? Me zai ce yau kuma? Ya mance da kitson ne da tun a hanya zai warwareta........
(Kamran fans yau ba zata yi maku ta daɗi ba😅 baku da amsar da zaku bawa Mamma, kuna tsaka mai wuya, Pretty ta kai ku ta baroku 😅 ku daɗi soyayya ba? To yau zaku ga soyayya kuwa😅)
Readers me kuke tunanin Mamma zata ce mashi? Wani action zata ɗauka? Shi ma wani action zai ɗauka dan kare kansa kada a raba shi da Pretty? Ga shi ya bayyanawa Pretty ɗin soyayyarsa, ya kenan zata kaya?. To ni dai bari na leƙa KINGDOM OF POWER na dawo, wata kila kafin nan Kamran ya samowa kansa mafita.
𝗞𝗜𝗡𝗚𝗗𝗢𝗠 𝗢𝗙 𝗣𝗢𝗪𝗘𝗥💪🔥
Haɗe gabakiɗaya family suke a saman dining table dake dining room ɗinsu na part ɗin King. Kuyanga Zubaida ta yi serving ɗinsu, cikin nutsuwa suke cin abincin nasu. Kowa yana saman table ɗin amma banda Yah Jawad, Yah Jaish and Gimbiya Chuchu dake cikin part ɗin Akka, taki fitowa, Akka ta fito daning room ta barta kwance a saman gado, wai sai anjuma kaɗan zata sha complex or coffee ko dai wani abin mara nauyi, dan bata jin yunwa a yanzu.