Ɗan sunkuyawa ya yi ya ɗauko wayarta da ta yasar a kasar, pause ɗin video da take ɗauka ya yi, sannan ya yi saving video, yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi mata magana ta raɓa gefensa da gudu da nufin ta yi waje.
Cikin sauri ya riƙo hannunta tare da ɗaure fuska sosai. "Where are you going?". Ya faɗa cikin sanyin murya.
Bai san cewa uncle Abbas ta gani a bayansa yasa zata gudu ta je wajensa ba, yanzu ya shigo room ɗin, sallama ya zo yi da Akka zai wuce, shi ne da ta ga ya tsaya a bakin kofa yana kallonsu zata gudu ta je wajensa, hankalinta ya ɗan kwanta uncle nata ya zo shikenan ta tsira, shi kuwa Yah Jawad bai san da uncle Abbas ɗin ya shigo ba.
Janyota ya yi ta dawo ta gabansa, kara ɗaure fuska sosai ya yi irin ba wasan nan. Gabaɗaya hankalinta na'a kan uncle Abbas ɗin, shi ma ya harɗe hannu a saman kirjinsa yana kallonsu. Ganin hankalinta na'a kansa yasa ya yi mata alama da ta yi shiru bari ya ga gudun ruwan Jawad ɗin.
Ganin uncle Abbas ɗin ya yi mata alamar ta nutsu ne yasa ta nutsu tare da yin ƙasa da kanta.
"Am i not talking to you?". Yah Jawad ya yi maganar yana sakin hannun nata da ya riƙe.
"Am so sorry babu in da zanje". Ta bashi amsa tana ɗan satar kallon uncle Abbas.
"Wai Jannat anya babu wata matsala a tattare da ke kuwa? Ban hanaki ɗaukar hoto ba?".
"Mantawa na yi, amma ka yi hakuri ba zan sake ba".
Nisawa ya ɗan yi kamar wani wadda ya yi wani aikin ya gaji. "Yanzu wani hukunci kike son na yi maki?".
Sai a lokacin ta ɗan ɗago da kanta, a hankali ta kai kallonta izuwa saman face ɗinsa, while shi ma face ɗin tata yake kallo, hakan yasa suka kalli juna a cikin idanu. "Dan Allah Yah Jawad kada ka yi mun komai, Allah ba zan sake ba, na tuba, wlh bana son kneel down ɗin nan, please Yah Jawad, gwara mun ka kwace wayata na har abada akan ka ka bani punishment ka ji?". Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar, a shagwaɓe kuma ta yi maganar, ga ragowar guntun hawayen ɗazun a saman fuskarta.
Lumshe idanunsa ya yi, har cikin ransa ya ji voice ɗin nan nata. "Last time bana ce ki sameni a part ɗina ba? Meyasa baki zo ba? Kin rai'na ni ko?".
A hanzarce ta girgiza mashi kai alamar a'a tana mai cigaba da maimaita mashi kalmar sorryn nan dai da ta saba faɗa kullum.
"Ina Akka?". A hanzarce ta amsa mashi da. "Bata nan ta fita, ina ga ko tana wajen daddy ko kuma wajensu mummy".
"Meyasa kika ce mata ni na hanaki zuwa Dubai?".
Zaro idanu waje ta yi, ita kwata kwata ma ta mance da cewa ta kai karansa wajen Akka ɗin, wannan shi ne laifi a kan laifi, dan kuwa Akka ta je har part ɗinsa wai sai ya gaya mata dalilin da yasa ya hana Chuchu zuwa Dubai?. Da kyar ya shawo kanta ta rabu da shi, wannan dalilin yasa ya biyo Chuchun, yasan confirm zai sameta a nan ɗin, shi ne ya zo.
"Ba zaki bani amsa ba kenan ko? Wai ni Jannat yaushe na zama abokin wasanki ne?".
Cigaba da girgiza mashi kai ta yi, nan take idanunta suka sake ciko da kwallah, kan kace me sun fara bin kumatunta.
"Another case kenan, bana hanaki kuka ba?".
Da sauri ta sanya hannu ta fara goge hawayen nata.
"Okey jeki part ɗina ki yi kneel down ina zuwa".
Okey ta amsa mashi da shi tare da raɓawa jefensa ta wucewa da sauri. Tana wucewa ya juyo da kallonsa a kanta domin ya kara tsareta da idanu. Mugun jin daɗin kallonta yake yi ɗan rainin wayo, amma tsabar walaƙanci da mugunta sai ya rinƙa baƙanta mata rai, ya yi ta takura mata yana sakata kuka.
Yana juyowa suka yi ido huɗu da uncle Abbas da ya saki baki yana ganin ikon Allah, shi dai yasan babu wanda ya taɓa yi wa su Jawad ɗin makamancin haka, amma su sun zo suna cin zalin kannesu.
Ɗan zaro idanu ya yi yana kallon daddyn nasa, yana son ya san yaushe uncle Abbas ɗin ya shigo room ɗin, adduarsa ɗaya Allah yasa bai ji abin da ya ce da Chuchu ba, dan yasan halin uncle Abbas sarai, idan kana son kaga ɓacin ransa to ka taɓa mashi ƴan matan nan nasa, sam baya son yaga an taɓasu, ƴan lelene, shagwaɓasu yake yi over, shiyasa suma suke matuƙar kaunarsa sosai, ba dan ba dan bama sai mu ce sun fi kaunarsa sama da daddynsu King Zuhair.
"Welcome daddy yaushe ka shigo?". Ya faɗa yana satar kallon Chuchu da ta fita a yanzu, yana magana yana fargabar kada ace daddyn nasa ya ji maganganunsu da ita.
Shiru uncle Abbas ɗin ya yi har sai da Chuchu ta yi nisa da room ɗin, sannan ya ce. "Tun lokacin da kake sanya mun ƴata kuka na shigo".
Ɗan shafa arab hairnsa ya yi tare da ɗan sunkuyar da kai ƙasa. "Kai daddy ni yaushe na sakata kuka? Kawai sune sun cika yin kuka banza banza, kuma duk kai ka shagwaɓasu ai, ni iya faɗa kawai nake yi mata".
"Jawad wlh ina jiye maka tsoron kar ka tabka kuskure". Uncle Abbas ya faɗa tare da ƙarisowa cikin room ɗin. A saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna tare da ɓalle botir na suit ɗin jikinsa.
"Daddy kuskuren me kuma?". Ya faɗa da iya gaskiyarsa, dan shi bai san wani kuskure daddyn nasa yake hango mashi ba.
"Zaka ce mun baka san abin da nake jiye maka tsoro bane?". Ya yi maganar yana wurga mashi wani irin kallo da waɗan nan idanun nasa irin na Akka.
"Kai daddy wannan kallon fa?". Ya kai karshen maganar tare da dawowa kusa da daddyn nasa ya zauna a saman sofar.
"Ai dole na kalleka da kyau tukun nan, na tabbatar lafiya kake da zaka ce mun baka san tsoron da nake jiye maka ba".
Ɗaura wayar Chuchu a saman hannun sofar ya yi tare da cewa. "Daddy da gaske ban san wani irin kuskure kake ji mun tsoron na tabka ba".
"Jawad kenan, to ina jiye maka tsoron ranar da zaka bayyanawa Jannat gaskiya ita kuma ta ce bata so bazata yarda ba saboda kana mata mutunta, a ranar ne zaka gane ka yi kuskure".
Ɗan zaro idanu ya yi, ƴar mamaki ce ta bayyana a saman face ɗinsa. "Daddy wace gaskiya kuma zan bayyanawa Jannat har da zata ce bata so?".
Hararar wasa uncle Abbas ɗin ya wurga mashi kafin ya ce. "Yanzu zaka ce mun ba son Jannat kake yi bane?".
"So kuma daddy? Ni ɗin?". Ya faɗa cike da mamaki sosai.
"A'a ba kai ba ni, wai Jawad lafiyarka ma kuwa?".
Shiru ya ɗan yi yana tunani, sake furta cewa son Jannat ni kuma, ya yi tare da nuna kansa, mamaki abin ya bashi ne.
"Baka yardanwa kanka kana sonta ba ko? To bari na baka wani Assignment ka je ka aiwatar da shi yanzu, idan ka kammala sai ka kirani a waya ka sanar da ni amsa".
Dawo da kallonsa a kan daddyn nasa da kyau ya yi kafin ya ce. "Okey daddy ina jinka wani Assignment?".
Kallon shi da kyau uncle Abbas ɗin ya yi kafin ya ce. "Ba ka ce ta je ta yi kneel down a part ɗinka yanzu ba?"
Gyaɗa mashi kai ya yi almar e ya ce.
"Okey in ka je part ɗin naka yanzu ka barta ta yi one hour tana kneel down, kuma kada ka hanata yin kuka, ka barta ta yi kukanta, sannan idan ta cika one hour ɗin ka ce ta tafi room ɗinta da kafafunta, idan ta kasa ka ce dole ta tafi, ko kukan jini zata yi kada ka kulata ta taka da kafafunta dole, idan ka iya aikata hakan ka kirani ka gaya mun.....". Ya kai karshen maganar yana kallon ɗan nasa har cikin ido, dan shi dai yasan tun Chuchu bata kai haka ba yasan da cewa Jawad ɗin yana sonta, shi ne dai bai gane hakan ba, amma yanzu zai gane ne dolensa, uncle Abbas yasan ko dede da minti ɗaya Jawad ba zai iya jure kukanta ba, amma dai koma me yanzu zai gane ai.
"Daddy wai yau da kanka kake cewa na bawa ƴan gatanka punishment? Kuma kace ko ta yi kuka na barta ta yi ta yi? Anya daddy kai ne kuwa?".
Ɗan murmushi ya yi tare da faɗin. "Ni ɗin ne dai, Abbas ɗin da kasani ne, ni nace ka je ka yi ai, kawai ka je ka aikata, idan ka iya sai ka kirani ka sanar da ni, dan ni daga nan wucewa zan yi......".
Girgiza kai ya fara yi yana faɗin. "No daddy banda kuka kam, ni bana son ganin kukanta, amma zan iya sanyata kneel down sosai, har ma fin one hour, amma ba zan iya jure ganin kukan nata ba".
Harararsa uncle Abbas ya yi kafin ya ce. "Okey tom shikenan na janye wannan Assignment ɗin bari na baka wani, idan ka koma part ɗin naka yanzu, ka kalleta ido cikin ido na a kallah one mint, duk tunanin da ya zo zuciyarka a wannan lokacin ka kirani ka gaya mun, dan shi ne gaskiyar abin da yake a tsakaninku".
"Daddyyyyyy kai ni wlh wahalar dani kawai kake son yi, Jannat is my sister that's all, bayan haka ni babu wani abin, to daddy Jannat ma nawa take? Yaushe ta girma ma? Me zan yi da ita? Ai ta yi mun ƙanƙanta, ni bani ma da lokacin mata a yanzu".
Ya kai karshen maganar yana turɓune fuska, shi sam bai ma san cewa ya saki layi a maganar tasa ba, ko da yake shi dama bai kai Jaish kunya ba.
"Babu abin da zaka yi da ita, kuma bata girma ba amma a haka kullum kake tsare mun ita da ido, idan kana kallonta ma har mantawa kake da in da kake, jiya ma fa a parlourn Yah Zuhair ina ganinka sai kalle mun ita kake yi kamar ka samu Tv, gaskiya zan gayawa yaya ma duk ku bar family part ɗin nan ku koma gidajenku, saboda kun sakawa ƴaƴana ido, ku barmun su su sakata su wala".
Da yake gidajen nasu dukka a cikin kingdom ɗin yake, sai dai yana da ɗan nisa da family part gaskiya.
"Kai daddy wai ni yaushe na kalleta ne? Kai da uncle Taheer da dad kun saka mun ido fa, shi ma dad daren jiya har da ce mun wai yanzu aure zai yi mun ni da Jaish ya huta, to mu laifin me muka yi yanzu fisabilillahi da kuke neman ɗaura mana wahala?.".
Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ɗauki wayar Chuchu ɗin da ya ajiye, sannan ya nufi waje. "Allah ya kiyaye hanya daddy".
"Zaka ga mun saka maka idanu ne, sai na yi mata miji cikin ɗaya daga cikin ƴaƴan abokaina ba tare da saninka ba za'a ɗaura auren, a nan ne zaka san mun saka maka ido, ka jira ka gani".
Shiru ya yi, dan har ya ji ransa ya ɗan ɓaci da last zancen daddyn nasa, da sauri ya wuce ya fita dan kada ma daddyn ya ƙara yi mashi magana mara daɗi irin haka.
Da kallo uncle Abbas ya bishi, sai da ya fice ne ya ce yaro yaro ne, zaka yi bayani ne, ai ita so ba'ayi mata wargi.
Part ɗinsa kai tsaye ya nufa, sai saƙa kalaman daddyn nasa yake yi a cikin ransa. Ƙasa ƙasa ya yi sallama kamar mai ciwon baki. Babu kowa a parlourn nasa, sai tashin kamashi da ko'ina yake yi, kai tsaye cikin room ɗinsa ya nufa.
A nan ya isko Gimbiya Chuchu ta yi kneel down sai aikin sharar kwallah take yi, har idanunta sun yi jajir saboda kuka.
A kusa da ita saman katafaren bed ɗinsa ya zo ya zauna tare da ajiye wayoyinsa haɗe da nata a gefensa. Zancen daddy nasa ne kawai yake yi mashi yawo a cikin kansa. Ji kawai ya yi zuciyarsa ta aminta da ya yi abin da daddyn nasa ya faɗa.
Slowly ya kai hannunsa ya ɗago haɓarta daga yadda ta sunkuyar da kai ƙasa tana ruwan hawaye. Datse idanunta gam ta yi saboda tsoron su haɗa idanu da shi.
Sai da ya ji tsikar jikinsa ya wani irin tashi na ganin face nata kawai da ya yi, a haka ma ba cikin kwayar idanun nata ya gani ba, ga shi face ɗin nata ma ya yi jaga jaga da hawaye, duk ya ɓata mata kwalliyarta.
In a low voice sosai ya furta. "Open your eyes".
Bata da zaɓin da ya wuce ta buɗe idanun nata, slowly ta warosu waje, sai dai taki yarda su kalli juna ido cikin ido, sai ta kawar da kallonta gefe guda tana mai cigaba da ruwan hawayenta suna bin gefe da gefen face ɗinta kasancewar ya ɗaga mata kanta sama.
Wani irin shock ya ji tun daga tsakiyar kansa har izuwa tafin kafafunsa, yana kallon face nata sosai a duk time ɗin da suka haɗu, amma bai taɓa jin yanayi irin na yau ba, anya ba baki uncle Abbas ya yi mashi ba kuwa? Ya tambayi kansa da kansa. Luluƙawa duniyar tunani kawai ya yi, ji yake yi har cikin ransa yana sha'awar ya yi ta kallon face nata ba gajiyawa.
Kyawawan laɓɓanta ne suka fara kerma saboda yadda ya ɗaga mata wuya sama ya fara yi mata zafi, hakan yasa ta tsananta kukan nata da take yi, shi ne dalilin ja mata kermar laɓɓan nata.
Slowly ya mayar da kallonsa a saman lips ɗin nata, yadda suke kerman nan ba ƙaramin kyau suka yi mashi ba dan mugunta, har shaiɗan yana ƙoƙarin raya mashi wani abin na daban a cikin zuciyarsa. Ganin ya fara tunanin ya yi kissing na lips ɗin tata ne yasa ya yi saurin sakar haɓar tata tare da dafe kansa da hannu ɗaya.
"Tashi ki tafi Jannat". Ya faɗa cikin wata iriyar murya mai kama dana mai jin barci.
Da sauri ta miƙe, ba tare da ta kalli in da yake ba ta yi saurin nufar waje. Da idanu ya bita da kallo har ta fice. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya kwanta a saman bed ɗin, tunanuka kala kala ne a cikin ransa wanda bai bama kowa damar sani ba.
A haka barci ta yi awon gaba da shi, ba shi ya farka ba sai da ringing ɗin wayarsa ta tashesa, cikin barci ya ji wayar tana ƙara, da kyar ya iya buɗe idanuwansa da suka yi mashi bala'in nauyi, jikinsa duk a mace, wannan barci da ya yi tun daga farkonta har izuwa ya tashi mafarkin Gimbiya Chuchu kawai ya rinƙa yi, ta tsaya mashi a rai kamar uncle Abbas ya yi mashi baki.
Da kyar ya iya laluɓar wayar tasa, ɗaukota ya yi tare da bin saman screen ɗin da kallo. Ɗan zaro idanuwansa waje ya yi lokacin da idanunsa suka sauƙa a kan time. Karfe 8:30 pm, ko sallar mangariba bai yi ba ga issha ta wuce. Shafa arab hairnsa ya yi tare da yunƙurawa zai miƙe.
Ina kasa miƙewar ya yi, duk jikinsa a mace, ga barcin yamma ga kuma mafarkin Chuchu, abin ya haɗu ya yi mashi yawa, dama kuma da tunaninta ya yi barci.
Call na biyu ne ya sake shigowa wayar tasa, dan wancan ta katse kafin ya ɗauki wayar. Ganin sunan my daddy ne yake yawo a saman screen ɗin yasa ya yi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnensa.
"Hello daddy". Ya faɗa cikin murya ƙasa ƙasa, dan bai wastsake ba.
Daga ɗayan ɓangaren uncle Abbas ya ce. "Barci kake yi ko my son?".
"Wlh daddy barci ne ya ɗaukeni sai yanzu na farka".
"Oh ka ci abinci dai ko?". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya amsa da no bai ci ba.
"To ka tashi ka ci abinci, amma kafin nan bani amsata na Assignment dana baka a kan Jannat".
Miƙewa zaune daga kwanciyar da yake ya yi. "Daddy i didn't feel anything ni kam, na kalli cikin idanunta ban ji komai ba". Ya faɗa yana kwaɓe fuska.
Sarai uncle Abbas yasan ba gaskiya ya gaya mashi ba, dan shi yasan wlh tun Chuchu tana ƴar shekara 5 yake daƙon sonta, idan anyi magana sai ya ce kawai sistersa ce, bayan haka babu komai, wannan soyayya ba ta yau bace, ta jima, tsohuwar zuma ce.
"Okey tashi ka ci abincin zan zo next month ai". Uncle Abbas ya faɗa, shi kwata kwata ma bai san cewa ko sallah ɗan nasa bai yi ba, yana can duniyar mafarkin babynsa, ya tashi kuma tsabar bushewar ido wai shi bai ji komai ba, bayan kuma har da mafarki, kai maza duniya.........🤔
"Okey dad take care". Ya faɗa tare da katse kiran, a hankali ya zuro kafafunsa kasan bed ɗin tare da miƙewa tsaye ya nufi toilet dan ya yi wanka tare da ɗauro alwala.
Da alama uncle Abbas yana son haɗa Gimbiya Chuchu da Yah Jawad aure, ga shi Mammie kuma kun ji ta dakawa Yah Jawad ɗin warning a kan Chuchun, ta ce bata sonta, to ko ya zasu kare? Akwai cakwakiya babba kuwa, dan kuwa Mammie idan bata son abu babu abin da ba zata iya aikawa dan ta rabu da wannan abin ba...... Hmmm akwai rikici nan gaba ba kaɗan ba.
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🕊️🌼🕊️🌼🕊️🕊️
UAE💔😥
DUBAI HILLS ESTATES💔😥
Kai tsaye cikin wani haɗaɗɗen bedroom wannan matashiyar matar ta kai Leesharh. Tun da suka sanya kafafunsu cikin room ɗin Leesharh ta saki baki tana kallon irin dukiyar da aka narkawa wannan room ɗin, kamar room na hajiyar gidan gabaɗaya, amma a haka ace ɗakin ƴar aiki? Wai me mutanen nan suke so ne a rayuwarsu? Irin wannan uban tarin dukiya dukka kuma suke neman leƙar asirin wani, wannan ya tabbatar ba kuɗin suke yi wa ba, sai dai idan wutar ɗaukar fansa ce take ruruwa a cikin zuƙatansu, kuma da alama ba waɗan nan mata ne kawai suke shirya wannan abin ba, da alama akwai shegun manyan kai daga sama, idan kuka yi duba da yadda hajiya two seater ta kawo Leesharh kuma