Abdussalam muke son zama, dan haka ba laifin Momma bane, kuma..........."
Wani irin ɗan iskan kallo da Yah Jaish ya wurga mashi ne yasa ba shiri ya haɗiye sauran maganar nashi, dan sun san Jaish ba kanwar lasa bane, ba shi bashi da hakurin Yah Jawad, yanzun nan zai sa su ji kamshin ma'aika azarailu, dan haka sai ya yi shiru tsit kamar babu shi a parlourn.
Ita kuwa Mama kallon walaƙanci ta wurgawa Momma ɗin kafin ta ce.
"Kina iya yin fin hakan ma ai, kisa yaranki basu daraja kowa".
Shiru gabaɗaya parlourn ya yi, kallon Obaid ta ƙasan ido Omaid ɗin ya yi, burinsu kawai su bar parlourn nan su je su shiryawa Mama ɗin nan wani munafurcin da sai ta yi kuka, dan wlh idan ba haka suka yi mata ba ba zata rabu masu da Mommarsu ba, shi kuma Yah Jaish zai taka masu birki, wlh ka ana ha maza ha mata basu ga dalilin da zai sa su bar wata banza tana yi wa mahaifiyarsu kutse a cikin al'amura ba, a cewarsu sun lura Yah Jaish ɗin nan baya son Momma sam sam, tun da yana zaune Mama ta zageta bai iya cewa komai ba, to su dai ba za su ɗauki wannan iskanci ba, dole kowa ya san matsayinsa a gidan, kafin su koma Dubai sai sun yi maganinta....... Hmmmm lallai akwai kura!.
Shi kuma Jaish ya ja bakinsa ya yi shiru ne saboda King yana wajen, koma dai menene yasan da cewa King zan yanke hukuncin da ta dace, kuma dama a matsayinsa na babba mai ilimi da hankali me ruwansa da faɗan kishiyoyi fisabilillahi? Ai wanan ba layinsa bane, amma fa sosai abin ya sosa mashi zuciya, ji ya yi tamkar ya buge Mamar sai ta sume ko ta mutu a wajen, amma ya danne saboda kannensu dake a cikin parlourn ga kuma King and uncle Abbas sannan ga Akka a kwana!.
Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya bi ta kan kowa ba ya nufi hanyar fita, domin idan ya ce zai cigaba da zama a wannan tattaunawa ba makawa tsab zai yi wa Mamma one slap seven death, so gara mashi ya yi gaba tun bai hasala ba.
"Where are you going Jaish?".
Cewar uncle Abbas.
Duk yadda yake kaunar uncle Abbas ɗin ya kasa iya bashi amsa, dan zuciyarsa a kusa take, idan ya ce zai buɗe baki ya yi magana zai iya haɗiyar zuciya ya mutu, so sai ya yi kamar bai ji me uncle Abbas ɗin yake cewa ba, a hanzarce ya fice daga cikin parlourn dan ma kada King ya dakatar da shi. Already shi kuma King dama bai yi niyar dakatar da shi ɗin ba, saboda yasan halin ƴaƴan nasa da zuciyar bala'i, shi kansa ya ji zafin maganar Mamar bare kuma ƴaƴan Momma, ai dole abin ya sosa masu rai.
"Sarina, Fanan, auta, Jannat, Obaid and Omaid duk ku tashi ku tafi".
Cewar Aunty MieMie.
A hanzarce kusan a tare suka miƙe suka nufi waje.
Mummy kam tana zaune kamar mutun mutumi tana binsu da kallo, ita sam sam ma bata son hayaniya a rayuwarta, ba zaka taɓa jin maganarta a irin wannan abin ba, da girmar kujerarta hajiya uwargidan King Zuhair Abdul Malik ba.
King ya ɗauki a kallah 5 mins yana kallonsu tun bayan fitarsu Sarina, kafin ya ɗan nisa tare da fara yin magana cike da bada umarni da kuma izza.
"Kada wanda ya sake yin magana a kan hukuncin da Rahilarh ta yankewa ƴaƴanta na girmansu a hannun ƴan uwanta, kowacce a cikinku tana da damar da zata ce mun Zuhair a wajen kakaninsu nake son ƴaƴana su girma, iyayena da yayyuna haɗe da kannena sai kakanina ne fa a Dubai ɗin, me dan ƴaƴana sun girma a hannunsu? Ƴaƴana mata ne na ce bana buƙatar su matsa daga kusa da ni, amma maza ina iya turasu ko'ina su je su yi karatu, ita Zunaira da take mace ba ga shi tana gabana ba? To me wani sabon abu a ciki? Me abin ta da hankali? Bana son wannan hayaniya dukka, ba'a kan haka na taraku ba, abin da na tara ku a kai shi ne, kada ku kuskura ku gayyato mun wani cikin gidan nan da sunan yana son ƴaƴana, sannan Obaid and Omaid zasu koma Dubai gobe, Omar yana dawowa nan da kwana uku, Mummynsa zata shirya mashi walima, idan akwai wadda take buƙatar wani abin ta yi mun magana zan shiga ciki".
Ya kai karshen maganar tasa cikin nuna cewa tsantsar umarnin yake basu.
Mummy baiwar Allah, Omar dai ba ɗan ta bane, ɗan Momma ne yayan Zunaira, amma kun ji har walima ta nemi izinin shirya mashi dan zai dawo, ita dukka ƴaƴan nasu abu guda ta ɗaukesu saɓanin Mama.
"Zan iya tafiya?". Cewar Mama, da alama ranta bai so maganar da king ya yi ba sam.
Akka ce ta ce "Kowa ma zai iya tafiya a yanzu".
A hanzarce Mama ta miƙe ta yi waje, Momma ce ta biyu a fita ta rufa mata baya, sai Mummy ta uku, princess Aunty MieMie ta rufa masu baya. Parlourn ya rage daga Akka, uncle Abbas sai King. Uncle Abbas ma miƙewa ya yi tare da sanar da su zai je ya shirya dan zai koma baƙin aikinsa. Sallama suka yi ya wuce, ya rage saura Akka da King, su kuma suka cigaba da hira na tsakanin uwa da ɗa.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
Shiru Leesharh ta yi, gabaɗaya ta shiga ruɗani, kanta ya ɗaure, duk ta rasa me yake yi mata daɗi, yanzu ya zata yi?.
Dafa shoulder ɗinta da kyau Jasrah ta yi tare da fara magana cikin nutsuwa da ƙoƙarin nuna mata illar da abin da zata aikata zai haifar mata ita da danginta gabakiɗaya, dan wlh idan aka kamata ko mahaifinta da take burin take ikirarin ta koma gida ta je ta gani ba barinsa za'ayi ba, babu wanda zai iya tsira daga cikin familynta, babu wanda zai tsallakewa Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen, duk sai ya ragargazasu, to babban abin tambayar ma a nan shi ne wanenen shi wanna Ramish ɗin kam? Ya yake? Meyasa ake farautar rayuwarsa har haka da ake ƙoƙarin leƙar asirinsa? Kuma kun ji matar ta ce suna da ma'aikata a gidan, hakan na nufin ba ita Leesharh ɗin bace ta farko, kenan an jima ana sanya mashi idanun? Da alama har yanzu haƙarsu bai cinma ruwa bane yasa suka buƙaci Leesharh a wannan aiki, idan kuka yi duba da yadda matar ta ce ma'aikatan nasu a iya harabar gidan suke ba su sami damar shiga ciki ba, hakan yasa basu iya sanin me Ramish ɗin yake ciki, ita kuwa Leesharh karamar yarinya ce da ba za'a barta a harabar gida ta yi aiki ba, dole idan za'a ɗauketa aiki a can cikin gida zata yi aikin, kila ma a ta fannin kitchen ko kuma gyaran ɗaki or wani abu makamancin haka, babu wanda zai kawo wa ransa ita ɗin leƙar asiri ta zo yi, kunga zata sami damar sanin wanenen Ramish da kuma motsinsa a cikin gidan, ina ga tabbas kafin su tunkari Leesharh da wannan magana sai da suka yi gagarumin bincike a kanta, sai kuma da suka shirya sosai.
Amma kuma matsalar a nan shi ne, ita Leesharh idan ta amince ta karɓi wannan aiki da ankamata fa shikenan ita da danginta ne zasu girbi laifukan da basu suka shuka ba! Domin bata san wannan mata ba! Tab akwai cakwakiya na gasken gaske kuwa, yanzu nasu wasan kuma zai fara kenan, zamu ga wanene zai yi nasara a wannan game ɗin da za'a buga kuma!!!.
"Leesharh a wannan magana babu wani tunani da zaki yi, domin kuwa baki da wata mafitar da ya wuce ki ce mata ba zaki je ba, idan kuma kika ki, to wlh karnikan gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen ne zasu cinye gawarki a ɗanyarta, kuma ki sani sun cinyeki sun cinye banza, ke bama wannan ba, wlh duk danginki babu wanda zai iya tsallakewa, babu wanda zai sha a hannun Ramish idan asirinki ya tonu, kuma yadda suke da mahaukatan cameras a gidan kin san kuwa dole asirinki zai tunu, ke ta ina ma zaki fara yin wannan aikin fisabilillahi Leesharh? To ina mai tabbatar maki ganin waɗan nan mugayen fusatattun securitys ɗin da suke gadin kan titin da zata ratsa ta shigar dake unguwar da gidan yake ma ya isa ya sanya ki saki fitsari a wando, duk rashin tsoron nan naki da ƴan gidan nan suke faɗa wlh baki ga abin tsoro bane, bare ace ki ga securitys ɗin da suke gadin ainahin gidan, ina ga daga nan zaki sume, ke ni fa ban ma yarda matar nan zata iya shigar dake wannan gida ba, gidan ɗaya daga cikin ƴaƴan the most powerful King Badeen da duniya take magana a kansa, kowa idanunsa naa kansa, ga karfin iko kamar shi ya bawa kansa, kuma defence minister da duk wani mai kaki yake a ƙarƙashinsa, sai da izininsa kaki zata motsa, lallama kam, ni dai a matsayina na ƴar uwarki ban baki goyon baya ba, ko da bamu da alaƙa ta jini addinin Musulunci ya haɗa mu mun zama ƴan uwan, kuma ba zan zuba maki idanu ina ganin abin da zai cutar dake da familynki na yi shiru ba, dole na gaya maki gaskiya koda zaki gujeni".
Ta kai karshen maganar tana mai cigaba da kallon fuskar Leesharh da tsoro ya gama bayyana a samansa sosai. Bata taɓa shiga irin wannan yanayi ba, ko lokacin da aka kawota gidan da sunan ta kashe mahaifiyarta babu irin makamancin wannan tsoro a face ɗinta, bata taɓa tsorata a cikin wannan gida ba duk da ta san hukuncin kisa ne a kanta, tasan kasheta za'ayi, amma babu tsoron hakan a ranta, yau dai ta tsorata da jin wannan irin bala'i na aikin da zata je.
"Ke fa Jasrah baki da mutunci, yanzu saboda mugunta ne kike son hanata fita daga cikin wannan gida, kina ji Leesharh? Wlh duk abin da Jasrah take faɗa karya ne, kawai bata son ki kuɓuta daga hukuncin kisa da yake a kanki ne, bata son ke kifita ita a kasheta ne, shiyasa take ƙoƙarin sare maki gwiwa, dan haka kada ki yarda, ki je kawai Allah ya bada sa'a, zamu tayaki da addu'a". Cewar Sahra dake makale a saman gado kamar wata mage........ Mugunta dai babu kyau Sahra!!.
Taɓe baki Jasrah ta yi tana mamakin irin wannan kiyayya, kiyayya ido da ido suke nunawa Leesharh babu ko sakayawa! Sai ka ce ba musulmai ba, yaran nan sam sam basu da mutunci, sun tsani Leesharh over, duk wani munafurci ƙoƙari suke yi suga sun kullah mata, su basu ki ba ma a matso da hukuncin kisan da yake a kanta ya dawo yau yau a kasheta su huta, ko me ribarsu idan an kasheta?..............🤔
"Sahra laifin me kika yi ma aka kawo ki gidan nan?".
Cewar Leesharh, daga jin yadda ta yi magana ƙasan zuciyarta ta gama karaya, gwiwowinta duk sun sage, ta tsorata sosai da wanna al'amari, ita tunaninta ma ɗaya shi ne ya zata yi ta cewa wannan mata ba zata yi wannan aiki ba ta, fasa?.
"Dole ki tambaya mana wani irin laifi ta yi aka kawota gidan yarin nan, dan na lura babu Allah a ranta". Cewar Jasrah.
Wani irin matsiyacin kallo Sahra ɗin ta watsa masu kafin ta ce. "Baku kai na baku amsa ba, bani ma da lokacinku ƴan wahala kawai".
Sahra kenan wadda ta turo yaron mai aikin gidansu daga saman bene ya faɗo ƙasa ya mutu, kuma cameras na harabar gidan nasu da wanda yake a balcony duk sun ɗauketa time da take tura yaron ƙasa, yaro ɗan ƙarami wanda bai wuci 5 years ba a duniya, abinku da yarinta, kawai dan ya ɗauki Teddynta yana wasa da shi a wajen balcony shikenan ta wurgoshi ƙasa babu imani bare tausayi, ko da yake ina zata ga imani yarinya mara kunya har haka? Shi ne laifin da ta aikata, gata da uban rashin kunya kamar wadda shaiɗan yake yi wa busar sarewa a kunne, ga shegen rai'na na gaba da ita, iyayi da manyance, ga kauɗi da rawan kai, bata ganin kowa da gashi, bata jima da shigowa cikin gidan ba, yanzu haka iyayenta suna can suna ta faman ta yadda za'ayi su fito da ita, sai faman rokar ƴan aikin suke yi da ta yafewa ƴarsu, dan ita kaɗai suka haifa, suna can suna wahala suna kashe kansu a kanta, ita kuwa tana nan tana tsula tsiyarta son ranta, da yake iyayen nata sun gaya mata ai ba za'a kasheta ba, sun kusa yin nasarar fitar da ita, shi ne nan rashin kunya ya karu sanka sanka, ta zagi uban kowa a cikin gidan babu mai tanka mata, saboda suna tsoron ruwan bala'inta, bata da mutunci, kwata kwata 15 to 16 years ke gareta.
Kawar da kai Jasrah ta yi daga kan Sahrar tare da dawo da kallonta a kan Leesharh da nufin su cigaba da maganarsu dan ganin sun samowa kansu mafitar yadda zasu yi da wannan bala'i da yake shirin tunkarosu. Bata kai ga buɗe baki ta yi maganar ba sai ga wata ganduroba tana ƙoƙarin buɗe kofar ɗakin nasu zata shigo.
Jan baki Jasrah ta yi ta yi shiru tare da bin gandurobar da kallon mamaki tare da kara tsorata sosai, saboda bata san me ya kawo matar ba, abin da ta sani dai shi ne a duk lokacin da kaga wata ganduroba to ba alkhari bane ya kawota, ammafa a nasu ganin kenan.
"Leesharh let's go".
Shi ne abin da gandurobar ta faɗa bayan ta gama buɗe kofar, ta yi maganar kuma tana wurgawa Jasrah wani irin kallo mai wuyar fassaruwa, kamar dai ba kallon lafiya ba.
Miƙewa Leesharh ta yi jiki ba kwari, ga shi babu halin ta tambaya ina zata je kuma? A tsorace take kada ace matar ce ta dawo ɗaukarta ko kuma makamancin hakan.
Ita ma Jasrah tsoro sosai ya kara bayyana a saman face ɗinta, fargabarta ɗaya shi ne kada ace matar ce ta zo ɗaukar Leesharh ɗin, sai addu'a take yi Allah yasa Leesharh ta gayawa matar ba zata je ba idan ma ita ɗin ce ta dawo, Allah kuma yasa idan ta gaya mata ba zata je ba ta hakura ta kyaleta, gara masu su kare rayuwarsu a nan har izuwa lokacin da wa'adin hukuncinsu zai cika a kashesu kawai, a kan wannan aikin, dan yafi mutuwa haɗari, fargaba da tsorata tare da faɗuwar gaba ne ma kawai zai Kasheka a gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen.
Salun alum Leesharh ta wuce gaba, jikinta sai kerma yake yi, saboda tsoro, ta yi gaba matar ta rufa mata baya.
Dai'dai Leesharh zata wuce office na ɗazun in da suka yi magana da matar can, wannan gandurobar ta dakatar da ita ta hanyar cewa. "Ba nan zaki shiga ba ai".
Da mamaki sosai tare da tsoro Leesharh ta juyo da kallonta a kan gandurobar.
Ɗaure fuska matar ta yi tare da nuna mata wani hanya da yake a tsakanin wasu ɗakuna na wasu yaran dake dakon lokacin hukuncinsu ya cika su girbi abin da suka shuka.
Bata da zaɓin da ya wuce dole ta bi wannan hanya, domin ko damar yin magana ma ba'a bata ba. Wucewa kawai ta yi gaba matar ta rufa mata baya, suna tafiya matar tana waige waige kamar wata maras gaskiya, da alama dai ba gaskiyar bane aka kullah. To koma dai menene mu kam namu ido, zamu so ganin wannan cakwakiya, dan da alama zai ƙayatar ya kuma rikitar tare kuma da tarwatsa ƙwaƙwalwale, ya hargitsa tunani gami da ruɗar wa!!.
Sun yi tafiya mai nisa kafin su isko wani ɗan siririn hanya da yake a daf karshen wannan hanya, zuciyar Leesharh sai harbawa da karfi karfi yake yi, ji take yi kamar ta ce zata koma wajen Jasrah, amma ina babu bakin yin magana, tana tsoron gandurobobin sosai, saboda basu da sakin fuska ko kaɗan, kullum rai a haɗe kamar waɗan da aka yi wa wahayin mutuwa tare da lokacin da zasu mutu ɗin.
Wannan kwana suka bi, suka sake tafiya mai ɗan dogon zango kaɗan kafin su isko wani kofa a ƙarshen hanyar. Wasu irin makullai matar ta ciro daga aljihunta, makullai ne masu tarin yawa sosai da a kallah sun fi guda 70, ga su kala kala.
Wanda ya fi ƙanƙanta a cikin makullan ta sanya a kofar ta buɗeta, nan take haske ya bayyana a wajen. Da mamaki Leesharh take ganin wajen.
Da akwai dogayen bishiyoyi masu tarin yawa a wajen, kowa dai yasan yadda bayan dayawan prisons suke, kamar daji daji wajen haka yake.
Da hannu matar ta nunawa Leesharh hanya a kan ta fita. Kamar zata musa taki fita, sai kuma bata ga fuskar yin hakan a tattare da matar ba, dan haka salun alum ta lallaɓa ta kama kanta ta rufawa kanta asiri ta nufi waje.
Tana fita matar ta mayar da kofar ta rufe tare da murje key ɗin, sannan ta juya ta koma cikin prison ɗin ta baro Leesharh a waje. To fa babbar magana!!.
Wani irin bugu da kirjinta ya yi ne yasa Leesharh bata san lokacin da ta sanya hannu ta dafe kirjin nata ba, ji take yi kamar zuciyarta zai