da sosai kamar wasu yara, tun kafin su yi aure haka suke, har izuwa yanzu kuma basu canza ba, abin gwanin birgewa, ban sha'awa da kuma ɗaukar hankali tare da ɗaukar darasi.
Ya ɗauki a kallah good 10 mins yana zubawa sanyin idaniyar tasa addu'oi kafin ya shafa mata, sannan ya janyo duv ya lulluɓeta bayan ya manna mata kiss a saman 4 ahead ɗinta, yana ji da ita sosai, ya ce ita ce ke kama da shi a dukka cikin ƴaƴansa, King akwai neman magana, kawai dan yasa Momma yin magana ne yasa yake cewa Zunaira ce mai kama da shi, dan yasan sai ta yi magana, saboda da ita Zunaira take kama ba shi ba, duk da cewa ita da shi ɗin ma suna kama kamar ba mata da miji ba, idan ka gansu sai ka zaci wa da kanwa ne, saboda jini guda ne dama.
Bayan ya kammala tofa mata addu'a saukowa ƙasa ya yi tare da nufar door ɗin fita, dama abin da ya kawosa kenan, kuma ya gama, Momma zata same shi a part ɗinsa, dan yau dama kwananta ne.
A ɓangaren Gimbiya Chuchu kuwa, barci ne mai nauyi ya ɗauketa tun bayan cin abinci da suka yi, ko wankan dare bata samu ta yi ba, da yamma ma da kyar ta iya yin wanka, sai da Gimbiya Fanan ta taimaka mata, tana sanye da doguwar riga mai ɗan nauyi a jikinta da haka barcin ya kwasheta, ita kaɗai ce a bedroom ɗin, idan baku manta ba na gaya maku Akka tana part ɗin uncle Abbas.
Ƙasa ƙasa Yah Jawad ya yi sallama ya shigo cikin bedroom ɗin, hannunsa na rike da waɗan can kwalaben magunguna daya karɓo daga hannun waɗan can nurses ɗin.
Tun ɗazun yake ta jiranta ta zo ya bata ta shafa a kafafun nata amma shiru bata zo ba, shi ne ya biyo sahu, dama idan baku manta ba ya ce ta same shi a part ɗinsa, baiwar Allah barci ɓarawo yasa ta manta gabaɗaya.
A saman bedside drawer ta kusa da ita ya zauna tare da ɗaura wayarsa a saman gefen bed ɗin ta kusa da ita, da waya guda ɗaya ya fito, ya baro ɗayar ta jama'a a ɗaki, dama ya fi yawan fita da ta family, dan kada ya yi missing call ɗin kowa daga cikin ƴan uwansa.
Hannu ya sanya ya yaye duv da take lulluɓe da shi, sai sharara barci take yi kamar babu gobe, ta ɗan ƙudundune hannayenta a saman kirjinta. Face ɗinta ya ɗan ƙurawa idanu na ƴan sakani kamar mai nazarin wani abin. Can kuma sai ya gangarar da hannunsa ƙasa ya ɗan ɗage mata dogowar rigar jikin nata izuwa santala santalan cinyoyinta.
Sai da gabansa ya yi wani irin mummunar faɗuwa, na ganin kyakkyawar farar fatan tsala tsalan cinyoyin nata da suke luwai luwai suna sheki, sai ji ya yi kamar Akka zata zo ta same shi, idan kuma ta same shi a haka to ya shiga talatin, sai ta addaba mashi da surutun ko dai yana son Chuchu ne? Ba zata barshi ya zauna lafiya ba, wannan tsohuwa akwai baki, so shi surutun ne baya da buƙata, dan haka sai jikinsa ya fara ɗari ɗari, ya ji kamar kada ya shafa mata ganin ya barshi kawai.
Amma kuma ina ba zai iya ba, ba zai iya barinshi ɗin ba, saboda abin da ya fito da shi kenan, ya kasa iya rintsawa ne, har ya yi shirin kwanciya ya kwanta, sai kuma ya kasa iya rintsawa, saboda yana tunanin in dai bai kula da ita ta samu lafiya ba to bai kyauta ba gaskiya, dan koma me shi ne silar jin wannan ciwo tata, so yana da kyau ya kula da ita ta samu lafiya, hakan yasa ya kasa rintsawa har sai da ya fito.
Mayukan ya buɗe tare da fara ɗebowa da nufin ya fara shafa mata, abin mamaki hannayen nasa ne suka fara kerma, ji yake yi kamar ba zai iya shafa mata ɗin ba, da mamaki yake kallon hannun nasa yadda yake kerma kamar wadda akacewa ya taɓa wuta.
Ajiye kwalbar maganin da yake a ɗayan hannunsa ya yi, ya kai hannun ya ɗan shafa lallausan arab hairnsa tare da furta why? A hankali. Nisawa ya ɗan yi kafin ya yi ta maza ya ƙarisa kai hannunsa ya shafa mata. A hanzarce kamar mara gaskiya ya yi sauri ya shasshafa mata sama sama, duk gudun kada Akka ta zo ta kama shi ta janyo mashi jangwangwan ga kuma tsikar jikinsa dake ta faman tashi na taɓata da yake yi.
Ganin Chuchun ta fara ɗan motsawa kamar tana son farkawa ne yasa ya yi saurin miƙewa ya ɗauki wayarsa tare da nufar door ɗin fita ba tare da ya ɗauki ragowar magungunar ba. Har ya kai tsakiyar ɗakin kuma ko me ya tuna ya yi saurin juyowa ya dawo, a hanzarce hannunsa na kerma ya sauke mata rigarta ya mayar mata da shi dai'dai tare da janyo duv ɗin ya rufeta, da sauri ya nufi door ya fice, sai motsawa Chuchun take yi tana son farkawa daga barci.
🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️
UAE💘
AAJ PRISON💔😥
After two dys. Zaune yau ma Leesharh take a saman bakin bed ɗinta, ta buga uban tagumi kamar dai ranar, ta yi shiru, da alama bata a tare da mutane, ta luluƙa duniyar tunani, kamar ko da yaushe suna cikin uniform na AAJ ɗin, kala biyu ne uniform ɗin nasu, akwai fari kuma akwai blue, yau su canza wannan gobe su canza wannan.
Jasrah ce ta shigo ɗakin cikin shigar fararen uniform ɗinta ta sameta. A kusa da ita ta zo ta zauna tana mai faɗin. "Queen of thinking, yau kuma waye kika tuna a cikin familyn naku?".
Sam sam babu alamar murmushi ko mai ƙanƙantarsa a saman fuskar Leesharh, da alama yarinya ce da since before bata dariya, saboda bata ma yi kama da wadda take ko yaƙe bane, duk abin da za'ayi na dari wlh bata taɓa yi, Jasrah ta taɓa ɗaukar 30 mins tana surutan banza duk dan ta sanyata ko da murmushi ne, amma ina ko yaƙe ta kasa sakata, a tsawon shekara ɗaya na zaman da ta yi a gidan AAJ wlh sai dai suga hakwaranta idan tana magana ko tana yin brush, amma ba dai dariya ba, sam walwala da farinciki baya a saman fuskar yarinyar na, kullum cikin kuncin zuciya take, daga tagumi sai kwanciyar rigingine, abinci ma wani lokaci sau ɗaya take ci a rana, na safe kawai, bata wani damuwa da cin abinci, sai yawan tunani kamar me.
Ita kuwa Jasrah ta ce tun da nan da shekara guda za'a kasheta kamar yadda doka ta yanke mata, gara mata ta ci abincinta ta yi duk abinda tasan zata yi, dan tasan dokar nan ba zai kau daga kanta ba, sai dai wani ikon Allah, amma babu wanda ya isa ya sanya a fasa kasheta, kisa ba fashi, so dan haka gara mata ma ta saki ranta ta samu ta yi bankwana da duniya da kyau da kyau.
Ita kam Leesharh saura mata shekaru uku ta kai munzalin ɗaukar hukuncin da aka yanke mata........ Hmmmmm ni ko na ce hmmmmm.
"Ni kam a duniya waye nake da shi da zan yi tunaninsa da ya wuce mamata?". Leesharh ta bata amsa tana mai dawo da kallonta a kanta su fuskanci juna kenan.
"To amma Leesharh where's your father? And you Said you're from Africa, so what brought you here Dubai?". Jasrah ta jefa mata tambaya.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin yin magana Aaradiya dake kwance a saman bed ɗinta ta rigata da cewa. "Shima baban naki kashe shi kika yi ko? Dan naga ke horuwa ce, tun da kika zo gidan nan ko hakwaranki ba'a gani a waje, ke anya ma ba mayya ba ce Leesharh? Dan naga duk gidan kin fi kowa manya manyan idanu kamar ball".
Cike da shakiyanci da isgilanci sosai Aaradiya ta yi maganar.
Ɗayar yarinyar da take kasan bed ɗin Aaradiyar ce mai suna Sarah ta ce. "Kuma fa Aaradiya kina da gaskiya, kila mayya ce, ta kashe babanta, yanzu kuma ta kashe mamanta, muma fa kada ta kashe mu".
Ta kai karshen maganar tana zaro idanu.
A ɗan fusace Jasrah ta ce. "Ko ta kashe ku ko bata kashe ku ba nan da lokaci ƙalilan kasheku za'ayi, kuma idan ma ta kashe ku a yanzu ai saukaka maku zata yi".
Jasrah damo sarkin hakuri, bata magana a kan kome za'ayi mata, amma bata son taga irin cin fuskar da suke yi wa Leesharh a gidan, dan ita ce kawai aka kawo wadda ta kashe mahaifiyarta da hannunta, hakan yasa yaran da kansu suke tsangwamanta, yara ma kenan sun san daɗin uwa bare kuma manya, shiyasa sam sam Leesharh bata fita waje, dan idan ta fita kowace yarinya da kalar zagin da take yi mata, ƴan manyan cikinsu ma sai ku ji suna cewa Allah ya tsine maki la'ananniya, la'ananniya ce kawai zata kashe uwar da ta yi silar zuwanta duniya.
Wannan dalilin yasa bata fita, ta gwammaci ta yi ta ƙunsuwa a cikin ɗaki kamar daddawa, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa kullum take cikin ƙuncin zuciya da ɓacin rai tare da tunani. Ga shi kuma taki buɗe baki ta gayawa kowa ya aka yi ta kashe mahaifiyarta da kanta, ko da jami'ai suka tambayeta ma iya e kawai ta amsa masu da shi, anyi anyi ta yi magana ta bada labarin yadda aka yi, amma ina taki yarda ta buɗe baki.
"Ai munsan zaku iya kashe mu ba sai kin gaya mana ba, ke da kika kashe Ameer bai yi maki komai ba".
Cewar Sarah kenan.
Shiru Jasrah ta yi bata sake bi ta kansu ba, dan in ta biye masu faɗa zasu yi sosai, kuma dukkansu zata girme masu da shekara guda, amma saboda su basu da kirki sun rainata, sun mayar da ita kamar wata kanwarsu suna yi mata cin kashi.
"Leesharh amsa me where's your dad?". Cewar Jasrah.
Nisawa Leesharh ta yi tare da ƙoƙarin fara yin magana kenan wata ganduroba mace ta shigo cikin ɗakin nasu bakinta a ɗauke da siririn sallama, tana sanye cikin uniform ɗinsu na aiki.
"Who's Leesharh?".
Shi ne abin da ta faɗa tana mai binsu da kallo.
Miƙewa tsaye Leesharh ɗin ta yi tana faɗin gata nan.
Wucewa matar ta yi ta fita tare da cewa. "Follow me".
Da sauri Jasrah ta miƙe tana faɗin. "Ina zaku kaita?".
Abin da kun rigada kun sani ne ba amsa mata zasu yi ba, dan ba sha'aninta bane su ɗin, dan haka sai ta yi wucewarta ba tare da ta sake juyowa ta kallesu bama. Leesharh kuwa bata da zaɓin da ya wuce ta bi bayan matar.
Komawa Jasrah ta yi ta zauna tare da buga uban tagumi tana tunanin to me zasu yi wa Leesharh da suka wani zo suka kirata? Ko dai wani nata ne ya kawo mata ziraya? Ko kuma wani aikin zasu sakata? Ka dai za'a canza mata ɗaki a rabasu ne?. Tunani dai kala kala take ta yi a wajen.
Da kallon banza Sahra and Aaradiya suka bita da shi tare da binsu da addu'ar Allah yasa a kashe Leesharh ɗin ma a yau kowa ya huta, yadda kuka san a kansu Leesharh ɗin nan take zaune, sam basu kaunarta.
Kai tsaye office na shugaban gandurobobi wannan mata ta wuce da Leesharh dake ta faman jan kafa kamar zata faɗi a ƙasa, sam babu kuzari a jikinta, da alama bata ci abincin rana ba yau ma, dik a galabaice take baiwar Allah. Da alama a baya Leesharh tana da ɗan ƙiba kaɗan, saboda yanayin shape ɗin jikinta ya nuna rama ta yi, da ta fi hakan cikar bom bom and hips.
Shugaban gandurobobin tana a zaune a saman kujararta, ta yi crossing na leg's ɗinta, sanyin Ac na dukanta, office ɗin nata ya kawatu iya ƙawatuwa, tana sanye cikin haɗaɗen jallabiyarta launin sky blue a jikinta, yau bata sanya uniform ba, ta sanya wani ɗan ƙaramin please call me hijab da bai wuce kirjinta ba, ƴar siririya da ita, bata da ƙiba ko kaɗan, amma akwai kyau sosai da sosai, balarabiya ce ta usli, ga manya manyan idanu farare tas. Sai uban tulin takardu a gabanta kamar wata mai MD na Company, idanunta sanye suke da wani haɗaɗɗen farin glass mai ɗan girma, sai kamshi take zubawa ita kanta, ga kuma kamshin da office ɗin yake zubawa shi ma.
Wata macece zaune a zaman kujerar zaman baki idan suka zo a cikin office ɗin, daga sama har ƙasa idan ka cire nikaf da yake a fuskarta sanye wannan mata take da fararen kaya, nikaf ɗinta ne kawai baki, amma komai da ta sanya a jikinta fari ne tas, harta luxury hand fashion bag ɗinta ma fari ne, ta yi rolling na veil a kanta, ƴar dai'dai da ita, ba zaka kirata da mai ƙiba ba, haka zalika ba zaka kirata da siririya ba, ta dai ci ta ƙoshi, babu yunwa a tattare da ita, da alama kuma daloli bama nerori ba daloli sun yi mata mugun jiƙo, dan babu alamar gurbin talauci a tattare da ita, diamond ring da yake ɗan ƙaramin yatsan hannunta ma kawai ya haura 10 million, idanunta suna a sanye da black glass kamar wata mara gaskiya, ga nikaf ga kuma glass.
A ƙasa saman carpet Leesharh ta zo ta zauna a gaban ogar tasu, ita kuma wancan gandurobar da ta je ta zo da ita juyawa ta yi ta fita bayan ta isar da saƙon ga Leesharh nan ta kawota.
Cikin girmamawa da muryarta da sam kwata kwata bata fita sosai kamar wata mai koyon magana Leesharh ta ce. "Ganin nan".
Cikin harshen larabci ta yi maganar.
Kallon wannan mata dake zaune a saman kujara ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya shugaban gandurobobin ta yi, da hannu ta nunawa Leesharh wannan mata tana faɗin. "Bani ne nake kiranki ba, ga mai buƙatarki nan".
A hanzarce Leesharh ta juyo da waɗan nan dara daran idanun nata a kan matar, tun shigowarta bata kalli matar ba sai yanzu da aka nuna mata ita, hankalinta na'a kan shugaban gandurobobin ne kawai baiwar Allah.
Cikin girmamawa ta sake ce da wannan mata gani nan Aunty.
Kallon shugaban gandurobobin wannan matar ta yi, ɗan guntun numfashi ta ja tare da saukewa a hankali kafin ta ɗan ja ƴan mintoci da a kallah zasu kai biyu ba tare da ta ce komai ba, sannan calmly ta fara magana cikin kwararriyar laraɓcinta da zazzaƙar muryarta mai daɗin sauraro.
"Bismillah Abida kina iya bamu waje a yanzu".
Ta faɗa cikin sanyin murya, sai dai da alama akwai isa sosai da ji da kai a tattare da muryar tata.
Miƙewa shugaban gandurobobin ta yi ba tare da ta sake cewa komai ba, ta nufi out door, sai dai da alama ranta bai so fitar ba, kawai an fi karfin ta ne.
Bayan fitarta da kamar minti biyar haka, suna zaune shiru, wannan mata sai karewa Leesharh kallo take yi ta cikin black glass ɗinta, ita kuma Leesharh ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da hannunta. Tana son ta ɗago kai ta saci kallon wannan mata, amma kuma tana tsoron su haɗa ido ko kuma ta ganta, hakan yasa ta sunkuyar da kan nata shiru kawai.
"Shin kina son fita daga cikin wannan bakin gida da zuwansa ba alkhari bane Leesharh?".
Ta tambayeta cike da fargabar amsar da zata bata, tana tsoron Leesharh ɗin ta ce bata sha'awar fita daga gidan, hakan zai sa buƙatarta ba zai biya ba......... Ko wani buƙata take da shi a kan Leesharh? Muje dai zuwa.🤔😥
Tamkar saukar aradu haka Leesharh ta ji sautin zazzaƙar voice ɗin wannan mata ya daki dodon kunnuwanta.
A wani irin hanzarce ta fara gyaɗa mata kai in doubling. Baiwar Allah da alama bata da wani burin da ya wuce ta fita daga cikin wannan gida na AAJ........ Ba dolema ta so fita ba ko dan yadda sauran yaran suke tsangwamanta suka takura mata.
Wani irin cool ajiyar zuciya wannan mata ta sauke, ta cikin nikaf ɗinta ta saki wani irin shu'umin murmushi wadda fassara shi zai yi matukar wahala, da alama haƙarta zai cinma ruwa.
"Very good Leesharh, na ji matuƙar daɗi da ya kasance kina son fita daga cikin wannan gida".
Ta faɗa muryarta cike da tsantsar farinciki saɓanin ɗazun da magana kawai take yi babu walwala a tattare da ita.
"Aunty ina son na fita daga nan sosai, ko dan saboda tsangwamanta da suke yi suna kyarata, ga zagina da suke yi, kuma bana son a kasheni a nan, ina son na koma kasarmu, ina son na je wajen kabarin mamata na ganta".
Ta yi maganar idanunta suna cikowa tab da kwallah, muryar Leesharh sam baya fita sosai idan zata yi magana, yadda kuka san harshenta a naɗe yake, kamar mai koyan magana, gata kyakkyawa ajin farko, amma sam bata iya yin magana ya fita, a wani daddame maganar tata yake fita, idan ba ka nutsar da hankalinka sosai ba ba zaka taɓa iya gane me take son cewa ba ko me ta ce ba.
Shiru wannan mata ta ɗan yi tana ƙoƙarin iya fahimtar me Leesharh ta faɗa, dan bata wani gane me ta ce ba bayan cewa da ta yi mamanta, iya kalmar maman kawai ta iya ji a cikin maganar nata. Da kyar ta iya fahimtar wasu daga cikin abin da Leesharh ɗin ta ce, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce.
"Idan kina so yau ba sai gobe ba zan fitar dake daga cikin wannan gidan, kuma zan kai ki asibiti a gyara maki voice ɗinki, zan ƴantaki ki zama mai gata, zaki zama ƴa kamar kowa, zaki samu farinciki da jin daɗi fiye da ƴaƴan shugaban ƙasa, zaki samu rayuwa mai cike da jin daɗi, zaki ci abinci mai rai da lafiya a kullum da ko yaushe kike da buƙata, zaki kwanta a ɗaki mai Ac, zaki kwanta a katafaren bed ɗin da nasan da idanunki ma baki taɓa ganin gado irinsa ba, zaki saka suturuna na alfarma wadda ƴaƴan manya suke sakawa, ke har da gida da mota zan iya saya maki mai kyau da tsada, idan kina son yin karatu ma zaki yi, kome kike so zan yi maki amma da sharaɗi, kin amince?".