x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 59 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 174001 words
  • 177000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 400

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
da kuma sautin zubar ruwan koramu, gari babu hadari.

Rocky yana kwance a kasar wata jibgegiyar bishiyar ɗorawa da take a kusa da ƙoramar wajen su Pretty, da alama ma barci yake yi. Sweetie tana zaune a kusa da shi, kasancewar bata gani baiwar Allah bata san a kusa da ita Rocky yake kwance ba, kayan marmari ne a gabanta take sha cikin nutsuwa.

Su kuma sarakan suna saman dutse, Kamran yana zaune ya miƙe kafafu ruwan koramar tana sauƙa a saman kafafun nasa, ita kuma Pretty tana zaune a ta gabansa, sai dai ta bashi baya ta ɗan kwanto a jikinsa, ita ma ta miƙe waƴan nan ƴan guntayen kafafun nata, ko wajen ƙoramar kafafun basu iya kaiwa ba saɓanin nasa da yake cikin ruwa tsulumdum, sai takura mashi take yi a kan su matso baki bakin dutsen dan ita ma kafarta ya shiga cikin ruwan. Shi kuwa ya ce ai ita gajera ce ko sun matso kafafun nata ba zasu iya taɓa ruwan ba, ta bari sai ta zama babba kamar shi.

Mai hali dai baya fasawa shi ne ta sa mashi kuka tare da miƙewa tsaye wai zata faɗa cikin ruwan mai gabaɗaya.

Jawota ya yi ta zauna, dukkansu biyu hannunsu na rike da abin busar suna busawa ne dama, sun yi harbi da kifiya har sun gaji ne suka koma yin busa.

"Kai our Pretty kin iya rigima fa". Ya faɗa yana jan hancinta.

"Ba wani rigima, ni ka matso nima kafata ta rinƙa taɓa ruwa".

"Sai ki yi mun busar da ta fi ta jiya daɗi zan matso". Ya yi maganar yana tattare mata gashin kanta da iska ke kaɗata tana rufe mashi fuska.

"Idan na yi maka zaka goyani mu hau kan Giwa?".

Ƙulle mata gashin nata ya yi yana faɗin. "E amma ai ba yau bako? Dan yau ba zamu je wajen giwayen can ba, kinga lokacin komawata gida ta kusa".

Turo baki ta yi kafin ta ce. "To ba kai ne ka je ka jima wajen cirowa Sweetie fruit ba? Ni Allah ba zan yarda ba sai mun sake zuwa wajen, akwai daɗi hawa bayan giwa......"

Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Akwai daɗi kuma kike yi mana ihu? Jiya duk kin yagushe mun wuya da waɗan nan faratunan hannun naki, duk saboda tsoron giwa, kin wani ƙanƙameni kamar idan zasu cinyeki ba zasu haɗa da ni ɗin dukka su cinye ba, kin sa na koma mamma tana tambayata me ya jimun ciwo, sai da na ce mata mage ne ta yakusheni". Ƙasa ƙasa sosai ya yi maganar kamar mai raɗa.

Sweetie dake shan fruits ɗinta ne ta amsa zancen da cewa. "Ai ba zaka kara kaita ba Kamran, jiya da daddare muna barci sai ta yi ta kurma ihu cikin tsakiyar dare wai ga giwa ya buɗe baki zai cinyeta na ceceta, sai da na rinƙa tofa mata addu'oi sosai kafin na samu ta yi barci".

A hanzarce Prettyn ta ce. "To waye ya ce ki gaya mashi? Ya tambayeki ne? Ni ba wani ihun da na yi, sharri ne kawai dan baki son a kaini, kuma sai ya kaini ɗin".

Shi dai dariya suke bashi idan suka fara wannan diramar tasu, ita Pretty bata son ace ta gaza a kan wani abin, ta fi son ace ta iya komai, ita kuma Sweetie sai iya faɗar gaskiya bata rufawa Prettyn asiri......... 😅

"Nikam Kamran ka kammala karanta littafin da mum ta baka ɗin ne?". Sweetie ta tambaya, dan a cewarta ba zata biyewa Pretty ba, haka dama take yi kullum, bata biyewa Prettyn.

"No na dai fara karantawa, amma ban samun ishasshen lokaci sosai ba, ni kai'na ina son na kammala karantawa, a ƙage nake da na karanta, dan naga duk wani abin da ta bar mun a cikin saƙo kama daga waɗan nan ring ɗin da komai da komai akwai labarinsu a cikin littafin, shiyasa nake son karantawa na ji me zan yi mata da su, amma da na fara marantawa ne sai Mammata ta zo, bana son kuma taga littafin da kuma kayan, shiyasa sai na ɓoye, bana samun lokaci a gida na karanta, a waje kuma ina tare da ku, da daddare kuma ban isa in kunna wuta a ɗaki na ce zan yi karatu ba, mamma zata ce me nake yi ban yi barci ba, amma soon zan karanta". Yana magana yana ta murɗawa Pretty kyakkyawar dark black curly hairnta. Ita kuma ta wani kwanta mashi a jiki sarkin son jiki.

Sweetie tana ƙoƙarin yin magana Prettyn ta rigata da cewa. "Ni Kamran ka matso bakin dutsen nan please, ina son kafata ta taɓa ruwa, kuma gobe zaka kaini wajen Giwa, Allah Sweetie babu ruwanki, tun da ke kin ce ba zaki je ba ai sai ki barni ya yi ta kaini yawo nikam".

Dogon hancinta ya ɗan ja tare da faɗin. "Ki yi ta wahalar da ni ina goyaki ko? Saboda tsoro sai ki ce ba zaki tafi da kafafunki ba, kisa na goyaki duk na gaji".

Sweetie ce ta ce. "Katuwa da ita zata yi ta karya maka baya ko ta saka ka ciwon kwankwaso ba?".

"Allah Sweetie bana so, babu ruwanki da ni, ni ƴar karama da ni ɗin ne zaki ce zan karya mashi baya? To ni yaushe ma nake da ƙiba? Baki fini girma bane? Kin fini ai, kuma a haka shekaran jiya ya goyaki muka tsallake duwatsun can, ke baki ɓalla mashi baya ba sai ni? Kamran kada ka kulata sharri take yi mun ko? Ina bani da nauyi?".

Yadda ta yi maganar gwanin ban dariya, irin ita ma wai zata yi mashi wayon nan ta saka mashi magana a baki.

Shiru ya yi bai amsa masu ba, dan yanzu idan ya amsa da cewa tana da nauyi Sweetie zata ji daɗi, ita kuma Pretty ba sai na faɗa ba kunsan kuka zata yi mashi ance tana da nauyi, idan kuma ya amsa bata da nauyi, to Prettyn zata yi dariya har ma ta yi wa Sweetie gwalo, ita kuma Sweetie bara ta ji daɗi ba ga watsa mata ƙasa a ido, dan haka sai ya yi shiru ya kyalesu, haka suke yi mashi wani lokaci, sai su saka shi a tsakiya ya rasa bayan waye zai bi bawan Allah. Idan ya bi bayan wannan, sai wannan ta yi fushi, idan ya bi na wannan, wannan ta yi kuka, shirun dai shi ne mafita a gare shi!.

Rayuwarsu gwanin birgewa sosai da sosai, sai sun baka sha'awa idan ka gansu, sun ɗauki Kamran tamkar ɗan uwansu na jini, shi ma duk da yana jin son Pretty a ransa sosai da sosai baya taɓa yarda ya nuna masu banbanci, ya fi nunawa Sweetie ma kulawa, saboda akwai ranar da ta ce mashi Kamran saboda bani da ido bana gani ne yasa baka hira da ni sai Pretty kawai ko? Wannan maganar tata ta taɓa mashi zuciya sosai da sosai, hakan yasa ya ɗaura ɗamarar koyan zama dasu su dukka ba tare da nuna masu wani babanci ba, sai ma ya fi bawa Sweetie kulawa dan kada ta ji babu daɗi ta ji kamar cewa ita ba mutun bace dan bata da ido, yana janta a jiki sosai yanzu.

Ita kuwa Pretty ta daban ce a cikin zuciyarsa, yana bala'in kaunarta, kome ta yi kyau take yi mashi, amma kuma abin da bai sani ba shi ne Sweetie ce take son shi ba Pretty ba, ita Pretty da kauɗi ya yi mata yawa a kai ina ma take wani bi ta kansa sosai, ta dai shaƙu da shi fiye da Sweetien, tana kuma kaunarsa a matsayin ɗan uwa da suka ɗaukesa, bayan haka babu wani abin, amma watakila a gaba zata iya fahimtar tana son shi. Akwai cakwakiya sosai kam, domin ita Sweetie da iya gaskiyarta take son shi, bata san ya kamaninsa yake ba, amma zuciyarta ta kamu da kaunarsa, wannan ita ce ma kauna ta gaskiya duk da ita ma bata san me kaunar ba a yanzu, saboda ƙananun shekarunsu.

Hmmm akwai case ba kaɗan ba, mum ɗinsu ma auren Pretty ta bashi bana Sweetie ba, Allah sarki baiwar Allah ga cutar makanta gana soyayya, to Allah ya baki ikon cin jarabawarki. Bari mu leƙa DUBAI mu dawo.

🌼DUBAI🌼


🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍



🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)






🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 9/8/2024.....✍️📚🌹




For information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








E____________32🔥





🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️


🌼DUBAI🌼

After some days.🕊️


LEESHARH🌼

Kwance take a saman bed ɗin nata, idan ka kalleta zaka yi zaton ba ita bace, ta goge ta yi wani kyau da ita, dattin gidan AAJ duk ya fita, ta ɗan yi dumurmur da ita, alamar ta samu huta da kula, ba karya suna kula da ita sosai, dan a halin yanzu ita ce kawai hope ɗinsu, ita ce zata biya masu buƙatarsu da suke ƴinwace wajen nema, kula da ita sosai suke yi tamkar kwai a saman bajajjen plate.

Mayuka da sabulan gyaran jiki kala kala masu kyau da tsada suka saya mata take amfani da su, wannan mata dai ta zage sai koya mata aikin take yi kamar yadda suka gaya mata.

Sai dai kuma har yau bata iya samun damar ganin ko face ɗin mutun ɗaya daga cikin gidan ba, ta yi iya ka baƙin ƙoƙarinta wajen ta samu ta ga face ɗinsu, amma abin ya ci tura. Daga harshe dai sai ta hakura ta fawwalawa Allah komai... Hmmm ga shi ita da kanta bata san a wani location wannan gida yake ba, an dai keto da ita cikin unguwa, ga gidajen da yake a unguwar duk ginin iri guda ne, in fact bama ta san wace unguwar bace ba, bata san komai dan gane da su ba.

Duk nacinta da yadda ta so ta iya sanin wani abin a dangane da su to fa hakura ta yi, domin ance duk wanda ya rigaka kwana to zai rigaka tashi, wannan haka yake, sun ko fita wayo, idan juranta sammako to su a tafe suka kwana, sun ki yarda su bata wani dama, a shirye suka tsab kafin su fara duk abin da za su yi.

Ta kwanta shiru tana tunanin duniya, mahaifinta ne kawai a cikin ranta, ta ƙurawa sama idanu kamar wata mai kallon wani abin, dama kun san akwai ta da ido kam, tafi kowa manyan idanu a gidan AAJ.

Wani irin jiniya ne ya karaɗe gabaɗaya unguwar ta su, jiga jigan motoci ne suka saki jiniya tun daga nesa da wannan gida, ya karaɗe ko'ina, tun da Leesharh ta zo wannan gida bata taɓa jin jiniya makamancin hakan ba, wani lokaci jefi jefi tana jin karar jiniyar motar ƴan'sanda ya wuce, da yake unguwa ce ta manya, akwai irinsu ƴan majalisu, ciyamomi da sauransu, hakan yasa wani lokaci motocin ƴan'sanda da sojoji suke giftawa tare da motar wani ɗan majalisa, to amma na yau jiniyar ta daban ce, domin ta karaɗe ko'ina a faɗin unguwar, daga ji kasan wasu manyan shegu ne suka dimfari arear.

Kamar wadda aka tsira ta miƙe zaune a tsakiyar bed ɗin, tunani ta fara yi akan wannan jiniya kuma na menene? Waye ne kuma ya zo?.

Bata ankara ba sai jin jiniyar ta yi har tsakar kanta kamar zasu tashi gidan nasu, alama ce ta motocin cikin wanna gida suka shigo.

Ai a dubu ɗari ta diro kasa daga saman bed ɗin, da gudu ta nufi wajen window dan taga wanene? Sai addu'a take yi Ubangiji Allah yasa su basu rufe face ɗinsu ba, ta samu dai taga koda mutun ɗaya ne, dan tasan ya kamanin ƴan gidan yake.

Jikinta na kerma ta ɓalle labulen window, har tana ƙoƙarin faɗuwa saboda sauri. Kurawa parking space ɗin gidan idanu ta yi kamar idanun nata zasu faɗi ƙasa. Danƙara danƙarar motoci masu numfashi har guda goma ne suka keto cikin wannan gida, kai daga ganin motocin kasan na manyan shaggu ne, sun haɗu iya haɗuwa, ga motar polices biyu a baya ɗaya a gaban jerin gwanon motocin nasu.

Gabaɗaya bodyguards ne a cikin motocin da suka kasance launinsu bakake, mota ɗaya ce ta kasance launinta fari a cikinsu, mamallakin wannan mota kuma bai fito ba, bodyguards ne kawai suka firfito tare da tsaitsayawa a gefe da gefen motocin, ƴan'sanda kuma suka diro ƙasa daga saman bayan motocinsu hannayensu a riƙe da wasu shegun bindigu waɗan da basa saɓa saiti.

Daga bodyguards ɗin har ƴan'sanda dukka akwai face mask a face ɗinsu, su bodyguards ɗin ma sun kara da black glass a idanunsu, jiga jigai ne bodyguards ɗin, suna ji da ƙoshi da lafiya.

Ƙara kura masu idanu sosai Leesharh ta yi tana jiran taga wanenen mamallakin wannan luxurious white car ɗin, ga shi bodyguards sun buɗe mashi kofar motar amma shiru bai fito ba, yana zaune a ciki.

Ji Leesharh take yi tamkar ta fita ta je ta janyoshi ya fito daga cikin motar koma wanene ta gansa. Amma ina ba hali, dole ta yi jira sai lokacin da aka ga damar fitowa.

An ɗauki a kallah tsawon good 10 mins kafin nan ya sako kyawawan kafafunsa waje, wadda yake sanye cikin wani haɗaɗɗen black booth mai matuƙar kyau da tsada, kai daga ganin wannan shoe ɗin kasan bana ƙananan kai bane.

Ko da ya sanya kafafun nasa waje ma sai da ya ɗan ɗauki 2 mins kafin ya fito waje mai gabaɗaya, nan take bodyguards ɗin suka fara sara mashi.

Matashei ne mai ji da lafiya, cikakken namiji ne wanda a kallah zai iya kai 27 years a duniya, sanye yake da ƙananan kaya, wandon jeans dark ash and white polo shirts, arab hairnsa yana kwance har wajajen bayan wuyansa, ya gyara gashin nasa sosai da sosai, farin balarabe ne tas da shi, kyakkyawa ne ajin farko, duk da kansa a sunkuye yana kallon ƙasa hakan ba zai iya hana ka gane kyakkyawan gaske bane.

Hannunsa ɗaya na ɗaure da wani dankareran diamond watch, ɗayan hannunsa kuma babu komai yana riƙe da wayarsa, arab skin ɗinsa sai sheki yake yi, ya ji hutu har ya gaji. Daga yanayinsa zaka fahimci jininsa a tafashe yake.

Cikin tafasar jini ya taku ya nufi cikin gidan kai tsaye, Leesharh bata samu damar ganin face ɗinsa da kyau sosai ba, amma dai tabbas ta gansa, saboda bai rufe face ɗinsa da komai ba, da alama ba ɗan gidan bane, duba da rashin amfani da face mask da ya yi kamar yadda su suke yi.

Wani irin ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙara mannewa da jikin windown tana tunanin to wanenen kuma wannan haɗaɗɗen guy ɗin?

Kamar saukar aradu daga bayanta ta ji an ce. "What are you doing there?".

A razane ta juyo da kallonta kirjinta na dukan uku uku. Wannan mata ce mai koya mata aiki, ita ce ta jefo mata wannan tambaya.

Ƴan kame kame ta fara yi na rashin gaskiya tana zaro waɗan nan idanun nata kamar ball ɗin mota, cikin rawar murya ta amsa da nothing tare da sakin labulen window ta bar wajen. Da kallo ta cikin nikaf matar ta bita da shi har ta isa saman bed ɗinta, sumui sumui kamar munafuka da asirinta ya tonu aka kamata tana munafurci haka ta haye saman bed ɗinta ta takure waje guda.

Wucewa wannan matar ta yi ta nufi cikin toilet ba tare da ta sake yi mata magana ba. Shiru Leesharh ta yi tana binta da kallo, ita ta kasa iya gane halin wannan mata, yau ka ganta kamar mutuniyar kirki, gobe kuma sai kaga wlh ta ma fi shaiɗan iya shaiɗanci, ga bakin hali, mugunta da rashin son magana, idan ka yi mata magana ko ka tambayeta wani abin, sai dai ta nuna maka da hannu ko ta ɗaga maka kai, amma ba zaka ji tana magana ba, sai ayi magana goma bata amsa ɗaya da muryarta ba, sai dai da hannu ko kai kamar ƙadangaruwa, yadda kuka san mai ciwon baki.

Jim kaɗan ta fito daga cikin toilet ɗin ta nufi kofar fita. Ko sanu bata sake cewa Leesharh ba, dama ita kuma Leesharh ba magana take yi mata ba, a haka suke rayuwa a cikin wannan ɗaki, sai dai fa ba'a nan matar take kwana ba, da dare ya yi zata bar ɗakin, ba zaka sake ganinta ba sai gobe da safe, tun abin yana bawa Leesharh mamaki har ya dai'na, yanzu ita ta riga ta saba da ahalin wannan gida.

Matar na fita ba'afi da minti biyu ba sai ga wannan matashiyar matar ta shigo cikin room ɗin bakinta a ɗauke da sallama. Amsa mata sallamar Leesharh ta yi tare da ɗan sakin fuskarta kaɗan, domin sun saba da wannan mata, ita kaɗai ce Leesharh take ganin ta Allah a gidan, ita kaɗai ce mai yi mata magana mai daɗi, ƙananun shekarunta yasa ta kasa iya banbanci kalaman soyayya da kuma kalman yaudara, ita dai a ganinta wannan matashiyar matar tana sonta tsakani da Allah..... Hmm yaro yaro ne bai san wuta ba sai ya taka. Wannan hali na matar shi ake kira da makirci kuma kisan karkashin ƙasa or mummuƙe! Leesharh dai bata gane ba, bata san suwa ye ake cewa makiran mutane ba.

A bakin bed ɗin wannan mata ta zauna, cikin nutsuwa ta ce. "Leesharh gobe za'a kaiki gidan Abu Abdussalam bin Badeen, ki tsaya sosai ki jajirce ki yi aikinki, ki mai da hankali ki yi abu da wuri
End Ads