x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 95 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 282001 words
  • 285000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 399

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ciwon idanu, zubawa maganin ido ta yi tana kallonsa, tana son sanin maganain menene? Sai dai ba dama, dan basu gaya mata ba, ita kuma bata isa ta ce zata nunawa Sharifat ta ce zata tanbayeta ko ta san na menene bane, kada ta zo ta ɓata aikinta, amma tabbas tana son sanin maganin menene kafin ta zubawa bawan Allah.

Zuciyarta na ta ayyana mata maganin nan cutar da shi zai yi, zantukan babanta take yawan tunawa a kullum in da yake yawan gaya mata kada ta kuskura ta cutar da wani a duniyar nan, da ta cuci wani gara a cuceta, wannan dalilin yasa duk wani aiki da zasu sakata take yawan shiga zulumin a kan kada ta je ta cutar da wani.

Ta jima sosai a wajen tana tsugunne tana kallon kwalbar maganin kafin daga bisani ta miƙe da maganin riƙe a hannunta, sannan ta rufe akwatin nata, shi kuma maganin ta tura a cikin aljihun wandon jikinta.

Waje ta sake nufa domin kudurinta na neman mai kaiwa Ramish abinci, tana da jajircewa da kuma kafiya a kan abin da ta sanya a gaba, kuma bata taɓa sanyawa ranta sarewa ko karaya.

Sai dai a wannan karon tana yi tana fargaba tare da tsoron kada ta cutar da bayin Allahn da basu ji ba basu gani ba, mutanen da suka karɓeta hannu bibbiyu, suka yi mata gatan da bata taɓa samun makamancinsa ba a rayuwarta, bata taɓa yin tunanin zata taɓa samun irin wannan gata ba, sun bata bedroom haɗaɗɗe, ga cima mai kyau, ga sabulai masu zafi na gyaran jiki, ga haɗaɗɗun kayan sakawa duk bayan wata guda ana sayo masu dayawa, gasu da halacci da kirki sosai. Amma idan ta tuna mata mai nikaf ɗin can ta ce mata ba cutar da shi zasu yi ba, taimakonsa zasu yi, sai ta ji sanyi a ranta, sai ta ji zata iya aikata komai dan ita ma ta taimaka da nata gudunmawar. Amma wani ɓangare na zuciyarta ya ki yarda a kan taimakonsa suke son yi. Tana da ƙwaƙwalwar da basira sosai, amma akwai yarinta sosai a tattare da ita. Masu nikaf kuma da wannan yarinta tata suke amfani dan cika burinsu!!!.


🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)






🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 13/9/2024.....✍️📚🌹




For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️






E____________51🔥





🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼

KINGDOM OF POWER 💪🔥💘

"Jannat lafiyarki kuwa?". Akka ta sake faɗa cike da damuwar son sanin me ya sami jikar tata ta zunduma ihu haka.

Dawo da kallonta a kan Akkar ta yi, a hankali ta sake satar kallon dressing room ɗin, da farko kamar zata gaya mata gaskiya, amma sai wani tunani ya faɗo mata a rai, tunawa ta yi cewa to idan har Yah Jawad zai gudu ya ɓuyan wa Akka bai kamata ta gaya mata cewa yana nan ba, yin hakan zai sanya ya ji babu daɗi. Wannan tunani yasa ta dawo da kallonta kachokam kan Akkar.

"Akka babu fa abin da ya sameni, ji nayi ne kamar wani abin ya shiga mun cikin rigata yana tafiya, shiyasa na yi ihu"

Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke daga in da yake tsaye, sanyi sosai ya ji tana ratsa zuciyarsa, ba ƙaramin daɗi ya ji da bata faɗi gaskiya ba, sai albarka yake saka mata a cikin zuciyarsa.

Matsowa kusa da ita a hanzarce Akkar ta yi, riƙota ta yi tana faɗin bari ta duba cikin rigar tata ta gani kada ya zamana akwai wani abin a ciki ya ji mata ciwo, ko ya cutar da ita.

Ƙanƙame rigarta ta yi bata son Akka ta kalle mata tula tulanta, mamaki ne ya kama ƴar tsohuwan. "Jannat lafiya? Ki bari na duba mu gani".

Girgiza kai ta fara yi. "Akka ni ba sai kin duba ba, koma menene ya tafi, kuma ma babu komai a ciki ni ce na ji kamar da akwai wani abin". Ta faɗa tana turo baki.

Haba da yake Akka sarauniya ce wajen iya magana, tuni ta fara sababi. "Ah ah ah lallai Jannat, ƴan nonuwar naki ne baki son in gani ko menene?" Nan fa ta fara jero mata kan cewa ai ba ita ba su Aunty MieMie duk taga nasu bare ita, dan haka sai ta duba..........😅

Dariya ne ya so kubcewa Jawad dake laɓe cikin room, yana jiyo duk abin da suke faɗa, yau yaga ikon Allah, yarinya da kayanta Akka ta ce sai ta duba, duk sai ya ji haushi za'a kalle mashi abin da shi ma bai taɓa kalla ba, wai shi ya zai yi da Akkar nan ne? Mata idan ka nuna baka son abu sai ta ce sai ta yi shi, ita fa idan taga kana kin abu ka ce baka so, sai ta ce rashin gaskiya ka kullah a wajen, dan haka sai ta ce sai ta gani!!.

Jawad dai bai ji daɗin hakan ba, dan yasan ran Chuchunsa zai ɓaci sosai, babu wata budurwa da take tasowa wadda zata so a kalle mata abinta, bare ma idan tana da kunya, wannan dabi'a ce ta mata, a jininmu yake.

Ita kam Akka ta kafe sai ta duba cikin rigar, ita kuma Chuchu taki yarda har da kukanta, ran Jawad ya ɓaci sosai, kamar ya kifawa Akkar nan mari yake ji, sai dai ba hali, ya suka iya da ita? Ai dole sai hakuri.

Da Akkar ta ga da gaske kuka Chuchun take yi da hawayenta, sai ta kyaleta ta koma cikin toilet dan dama wanka zata yi, tana shirin farawa kenan ta jiyo ihunta, so sai ta koma kawai tana yi mata sannu haɗe da surutun Chuchu na ɓoye mata ƴan nonuwa.

Tana shiga cikin toilet ɗin ya fito da sauri, ransa a ɓace saboda sanya mashi beb ɗinsa kuka da tsuhuwar nan tasu ta yi. Ya ɗaure fuska kamar hadari.

Yana zuwa in da take ya riƙo hannunta tare da ɗauka mata school back ɗinta dake saman gadon Akkar wadda ta ajiye da kanta. Ya riƙo hannunta tare da nufar kofar fita. Har lokacin ƴan siraran hawaye suna bin saman ƙuncinta.

Kai tsaye part ɗinsa ya wuce da ita ba tare da ya ce mata ko uppan ba, ya kuma yi sa'a bai ci karo da kowa a hanya ba har ya isa part ɗin nasa, kasancewar da safe ne kowa yana can yana ta faman aikin shiryawa, masu zuwa school suna nasu shirin, masu zuwa office suna nasu, masu yin breakfast suna fama, kowa dai yana room nasa yana abin da yake yi.

A bakin bed ɗinsa ya zaunar da ita tare da ciro handkerchief mai kyau daga aljihunsa, ya zauna saman bedside drawer, a gefenta ya ajiye mata jakarta kafin ya kai hannu a hankali ya fara goge mata hawayen nata.

"Am so so sorry my sister, duk ni na ja maki yin kuka da sassafen nan, kyale Akka hai ki dai'na kuka ba zata gani ɗin ba". Ya faɗa ƙasa ƙasa.

Ƙasa ta yi da kanta, kunyarsa take ji sosai saboda ya ji yadda suka yi da Akka, ga Akka bakinta babu full stop ta rinƙa kiran sunan tula tulan a tsiraransu, abin ku da tsoffi sam bata wani sakaya sunan ba, ta rinƙa ambatarsa ba kakkautawa, wannan dalilin yasa Chuchun ta ji tana bala'in kunyar yayan nata, dan ya ji komai.

Shi ma ya fahimci kunyarsa take ji, sai ya kawar da zancen da cewa. "Yau na kai ki school da kai na ko?". Ya yi maganar yana ƙurawa jikinta ido, gani yake kamar gizo idanunsa suke yi mashi, kamar kuma da gaske ne bata sanya vest a ciki ba, kuma bata sanya bra ita.

Yana son ya tambayeta kuma yana jin fargabar yadda zata ɗauki abin, tsoro yake ji kada ta kalli hakan da wata manufa ko kuma ta fara gudunsa ko dai ta fara jin kunyarsa sosai. Idan ɗaya daga ciki ya faru ba zai ji daɗi ba!.

Wani tunani ne ya faɗo mashi cikin ransa, idan ya tashi daga office ya je ya yi masu shopping na vest dayawa ita da Auta, sai ya bawa Autar ya gaya mata kada su sake saka kaya ba tare da sun saka vest a ciki ba, wannan ce tunanin da ya yi, yanzu haka sam ransa bai so ta tafi school a haka ba, amma ba yadda zai yi, idan ya ce zai yi mata magana a yanzu to tabbas zata haɗa maganar da abin da Akka ta yi mata ta kwaɓesu, daga haka zata fara ja baya da shi.

Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e ya kaita school da kansa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Kin yi breakfast ne?".

Kai ta girgiza mashi alamar a'a. Waya ya ɗauko ya kira kuyanga Zubaida a kan ta kawo mashi kayan breakfast yanzu. Yana ajiye wayar ya hau janta da hira dan ta saki jiki ta mance da abin da Akka ta yi mata ta koma walwalarta.

Ba'afi minti biyu da kiran da ya yi wa kuyanga Zubaida sai gata ta iso baki ɗauke da sallama. Izinin shigowa ya bata ba tare da ya kawar da kallonsa daga kan Chuchu dake ta faman murmushi ba, har ya mantar da ita kuncin da take ciki, ya sanyata farinciki.

Saman carpet ya yi mata umarnin ta ajiye mashi abincin, a hanzarce ta karɓi umarninsa tare da aiwatarwa.

Bayan ta fita ne ya ce da Chuchun ta zo su je su yi breakfast a tare. To ta amsa mashi da shi, hannunta ya riƙo suka nufi wajen kayan abincin.

Zama ya yi tare da zaunar da ita a kusa da shi. Cup mai shake da coffee mai zafi ya ɗauko ya kai mata bakinta. Ba musu ta buɗe baki ta fara karɓa. Wayarsa ce ta fara kara daga cikin aljihun coat ɗin jikinsa. Hannu yasa ya ciro wayar tasa.

Yah Rizwan, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Cigaba da bata coffee ɗin ya yi yana haɗa mata da pepper soup na kaza mai bala'in daɗi. Cike da kaunar yayan nasa ya ɗauki wayar yana kuma mamakin kiran da yayan nasa ya yi mashi da sassafe haka.

"Assalamu alaikum Yah Rizwan barka da safiya". Ya faɗa cikin nutsuwa, yana magana yana yanko tsokar kazar yana cusa mata a baki. Ta saki jiki sai ci take yi abinta.

"Jawad ka tashi lafiya?". Rizwan ya tambaya, daga jin muryarsa kasa yana kaunar ɗan uwan nan nasa sosai, sannan muryarsa da alama damuwa matuƙa a tattare da ita.

Da lafiya lou Alhdulillah ya amsa mashi da shi, sannan ya ɗaura da cewa. "Yaya ya naga ka kirani da sassafe haka? Ko dai akwai wata matsala ne?".
Sai a lokacin Chuchu ta ɗago idanu tana kallonsa jin ya ambaci matsala.

Daga ɗayan ɓangaren ya amsa mashi da. "E akwai matsalar babba ma kuwa, amma ba ita ce tasa na kiraka ba, na kiraka ne dan naji ya ka kwana? Ya kuma ka tashi? Jiya ban samu ishasshen barcin kirki ba, saboda tunaninka".

Miƙawa Chuchun cup ɗin coffee ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye ya nufi hanyar fita yana faɗin. "Matsala kuma Yah Rizwan? To matsalar me? Meyake faruwa?"

Bin shi da kallo ta yi har ya ficewa ganinta. Cigaba da cin abin nata ta yi tana tunanin to matsalar me aka samu kenan?.

After some minutes ya dawo cikin ɗakin fuskarsa babu annuri ko kaɗan, da alama Rizwan ɗin ya gaya mashi wani abin da ya ɗaga mashi hankali sosai, jikinsa duk ya yi sanyi sosai kamar ba shi ba. Kusa da ita ya koma ya zauna yana faɗin. "Jannat ci abinci da wuri na kai ki school akwai in da zanje".

Cikin sanyin murya ta ce. "Yah Jawad kai fa? Ba zaka yi breakfast ɗin ba ne?".

Kai ya gyaɗa mata alamar e ba zai ci ba, sannan ya ɗaura da cewa. "Sauri nake yi, ki ci da wuri in kaiki school ke dai, idan na dawo daga in da zan je zan yi breakfast ɗin".

"Yah Jawad meyasameka naga fuskarka ta sauya haka". Ta faɗa tana kallon face ɗin nasa.

Babu komai ya amsa mata da shi, sannan ya fara ƙoƙarin kiran number Jaish domin su gaisa su kuma yi magana, dan basu yi wayaba, ya so ya kira shi tun farkawarsa daga barci, amma bai samu dama ba, ya sha'afa.

Ringing wayar ta yi har ta katse ba'a ɗaga ba, duba time ya yi a danƙareriyar watch dake hannunsa. 7:05 am, yakamata ace Jaish ya tashi barci yanzu ai. Ya faɗa a bayyane tare da sake gwada kiran number.

A karo na biyu ma ba'a ɗaga ba. Knocking na kofar ɗakin da aka yi ne ya ja hankulansu shi da ita izuwa bakin kofar. Kasa ƙasa ya furta wanene?.

Daga wajen kuyangarsa ta amsa mashi da ita ce, tazo tana son fara yin aikinta ne na gyaran ɗaki. "Ki je sai anjuma ki dawo". Ya faɗa yana dawo da kallonsa a kan wayarsa da call ya shigo ciki yanzu.

Mammie, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗauki call ɗin, yana sonta, ya ɗauketa kamar uwa, saboda yana ganin cewa tana son su kuma ta rike su kamar ƴaƴan cikinta.

"Good morning Mammie". Ya faɗa cikin sanyin murya.

Tana daga zaune saman sofa a fatafaren parlournta, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, kamar kullum tana cikin haɗaɗɗen kwalliyar nan nata na alfarma, ga ruwan madaran gwala gwalai da ta zuba wuya da hannu, ta fito a hamshakiyarta, ta ko'ina dai bata da makusa sai bakar zuciyarta, kyakkyawar macece ga iya ɗaukar wanka, sai dai kash, kyan ɗan macijine. Daga gefenta wata hamshaƙiyar budurwace take zaune mai tsananin kama da ita, daga gani ba tambaya kasan kanwarta ce, dan sun yi kama sosai, yarinyar ba zata wuci 25 to 27 years a duniya ba, ita ma kyakkyawace, ga shi ta iya ɗaukar wanka kamar Mammie ɗin, yanzu haka ta sha wanka, duk wanda ya kalleta sai ya sake waigowa ya kalleta, da alama abin ya samo asali ne, duk yadda aka yi ainahinsu ƴan son gayu ne sosai.

"Morning Jawad how was your night?". Ta faɗa tana kallon kanwar tata.

Bayan ya amsa mata sai ta ce. "Kafin ka tafi office ka sameni a parlour mu ɗan yi magana".

Da okey kawai ya amsa mata, katse kiran ta yi tana bin kanwar tata da kallo. "Aliyah lafiya kike cunkushe rai haka?".

Kara tunɓune fuska kanwar tata ta yi kafin ta ce. "Aunty ba dole na turɓune fuska, ni ban san ya zan yi ba, saboda King nake zuwa gida nan, amma har in je fadarsa in gaishesa in fito baya ɗaga idanu ya kalleni, kuma ni ina matuƙar sonsa Aunty"............. Tashin hankali kenan, yau ake yinta, ita King ɗin da kansa ma take so ba ƴaƴansa ba, lallai wannan ta ɗebo da zafi, kai bama da zafi ba ta ɗebo mai tafasa!!.

Wani irin zaro idanun Mammaien ta yi, tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa. "Amma dai Aliyah baki da hankali! Ko dai kin sha wani abin ne yau kafin ki zo gidan nan! King Zuhair ma kike magana ko wani King ɗin da ban sani ba?!". Cikin tashin hankali ta yi maganar.

Kara turɓune fuska sosai ta yi. "Aunty idan ba King Zubair ba wani King muke da shi mai power a ƙasar Tunisia? King Zuhair nake magana a kai mana, kuma shi nake so, shi nake burin aura, In Sha Allah kuma ni ce cikon matarsa ta huɗu! Da ni zai rufe kofa, ko ana ha maza ha mata wlh sai King ya aureni!!". Babbar magana!.

"Aliyah lallai mutuwa kike nema, wlh idan baki yi hankali ba a ɗanya ƴaƴansa zasu cinye namarki, wai ke Aliyah ni da nake nan ina ta faman yadda zan yi in ga King auri Jahiz ɗan autan su King ɗin, shi ne bashi da aure, bai taɓa yin aure, matashi saurayi ne mai jini a jika, ga shi shararren mai kuɗi, duk duniya ta san shi, ya fi Abbas fa kuɗi nesa ba kusa ba, ke in takaice maki ma wlh zai iya fin King Zuhair ɗin ma kuɗi, ga shi sabon jini, shararrene da duniya dukka suna san shi, shi ba iya ƙasar Tunisia ne kawai aka san shi ba, duniya gabaɗaya ta san shi, shararren ɗan kwallo ne da yake bugawa Real Madrid, ke kanki kin san da haka, kin san Jahiz ganinsa da ido ma ba abu bane mai sauki, ko a cikin family na kusa kusa ba kowa yake samun damar ganinsa ba, ni kai'na da nake matsayin matar yayansa ma idan ya zo gidan nan ba samun ganinsa nake yi ba, idan kinga na gansa to yayansa yana nan, nan ne zai shigo wajen yayan nasa, a nan nake samun damar ganinsa, kuɗi iya kuɗi yana da shi, ga shi sabon jini matashi, me kuma zaki buƙata....."

Katseta Aliyah ta yi da cewa. "Sarauta! Yana da sarauta ne? Duk kuɗinsa a banza idan ba shi da mulki, burin mulkar ƙasar Tunisia nake da shi ni ba kuɗi ne a gabana ba, burina in yi mulki, in zama mai faɗa aji, dan haka yasa nake son zama mace ta huɗu da zata rufe kofa a zuciyar King Zuhair....." Tashin sense!!.

"To idan mulki kike so ai magajin masarautar zaki ci burin ki aura, magajin wannan powerful seat ɗin zaki kwaɗaitu da son aura, ga Ramish! Ga Bilal! Ga Suraj! Ga Jaish! Sannan ga Aryan! Ɗaya daga cikinsu yakamata ki zaɓa ai, dan sune zasu gaji wannan kujera mai matuƙar power da karfin ikon, in dai
End Ads