ya shigo ba, hakan yasa ta fara jin fargaba da faɗuwar gaba. Room ɗinta ta wuce da sauri dan ta je ta ɓoye abubuwan da bokan ya bata da ta sanya a cikin jakarta.
Tana ajiyewa ta yi maza ta dawo parlourn, da yake bata da gaskiya ko da ta je ajiye jakar sai taga kamar baban Zainab ɗin ya biyo bayanta yana leƙarta, hakan yasa ta yi saurin ajiyewa ta fito, abin ku da bata saba ba, duk sai ta bi ta tsargu tana neman tonawa kanta asiri, ta rasa a ina zata sanya ranta.
Saman sofa mai zaman mutun ɗaya ta zo ta zauna tare da ce mashi sannu da dawowa, tsoro da fargaba yasa ta manta da cewa faɗa suke yi, ta manta da cewa tana fushi da shi bata yi mashi magana.
Yana jinta amma bai amsa ba, ya yi kamar bashi a parlourn, dan iya ɓacin rai ta ɓata mashi rai, tun karfe 11 ya dawo gidan domin ya ɗebe mata kewa, ya dawo ya cigaba da rarrashinta tare da bata hakuri kamar yadda ya saba, amma sai ya zo ya ga bata nan, kuma bata sanar da shi ga in da zata je ba, ya kira numberta a lokacin suna kan dutse babu network, ya gwada numberta ya fi sau hamshin, amma bata shiga, ya kira number Aunty Hauwa ma bata shiga, ya je gidan Aunty Hauwar Khadija kanwar mijin Aunty Hauwar ta ce mashi Aunty Hauwa bata nan tana wajen business ɗinta na yawon bin gidan dillalai, ita kuma maman Zainab bata zo gidan ba, bawan Allah ya shiga damuwa sosai a kan to ina ta je tun da bata je gidan Aunty Hauwa ba? Ya dai san bata san kowa ba, bata kuma zuwa gidansu Haidar, gara ma gidan hajiyarsa wani lokacin yana kaita su kuma dawo a tare, baya yarda ya barta a can, dan yasan hajiyarsa zata takura mata, a tare suke zuwa su gaisheta su kuma dawo a tare.
Bawan Allah nan ya yi tunani sun fi kala ɗari a kan ina taje? Wani zuciya ya rinƙa raya mashi cewa kila ta yi fushi ne ta shiga mota ta koma gidansu, ya kira mamanta cikin hikima ta yadda ba zata yi zargin komai ba ya tambayeta ko ta yi magana da maman Zainab da safe ne? Da maman ta tambayesa lafiya? Sai ya ce lafiya lou kawai dama maman Zainab ɗin ce ta tambayesa a kan zata je gida shi kuma ya hana, shi ne ta ce sai ta gayawa mama, to shi ne ya kira ya ji idan ta kawo kararsa ya bada hakuri. Bawan Allah.
Murmushi kawai mahaifiyar tata ta yi tare da gaya mashi bata kira ta kawo kararsa ba ya kwantar da hankalinsa, rabon ma da su yi waya tun shekaran jiya, hakan yasa ya fahimci lallai ba garinsu ta tafi ba, dan da garinsu ta nufa dole zata sanar da mamarta, ya kira Sadiq da ya baro a kasuwa ya tambayesa ko ta gaya mashi zata je wani waje?.
Mamaki ne sosai ya kama Sadiq ɗin, domin kuwa bai taɓa jin maman Zainab ta fita har baban Zainab ɗin ya nemeta ba, abin ya ɗaure mashi kai, haka dai ya bawa baban Zainab ɗin amsa da a'a ai shi ta kwana biyu ma bata yi mashi magana tun lokacin da suka yi wannan faɗar.
Da okey kawai baban Zainab ɗin ya amsa mashi tare da katse kiran. Yana katse kiran Sadiq ɗin ya hau kiran numberta dan ya ji a ina take? Amma ina number bata shiga, babu network.
Tunani baban Zainab ya fara yi a kan to kodai dama haka take yi kullum ne? Abin ku da shaiɗai ko ya ya samu kofa sai ya cusa maka wani mummunar tunanin, sai ya fara raya mashi cewa ai dama kullum idan ya fita ita ma fita take yi ta tafi yawonta, sai yau ne Allah ya nufa dubunta ya cika ya kamata, wannan tunani shi ne yafi tsaya mashi a ransa sosai, kawai burinsa yanzu ya ji ina take zuwa to?
Kamar zai yi hauka haka ya rinƙa nemanta har wajen karfe 1 na rana, sannan ne ya hakura ya dawo gida ya kwanta, sallar azahar ma yau a gida ya yi, damuwa tasa ya kasa iya zuwa masallaci ya bi jam'i, ya rasa ina zai sanya ransa bawan Allah nan, ta ko'ina ba sauki, ga hajiyarsa a gefe ga kuma maman Haidar, yanzu kuma maman Zainab ta kawo mashi sabuwar bala'i, kunga kuwa ai bai yi laifi ba da ya shareta da ta dawo! Yana ma da ƙoƙarin da kuma hakuri tare da juriya, idan wani namijin ne wlh kina yin sallama zai fara sauke maki buhu buhun masifa a kan gidan uban waye kika je ba tare da izininsa ba? Amma shi sai ya yi shiru yana mai cigaba da haɗiyar bakin cikinsa a ransa, ya yi kamar bai ganta ba, da alama kuma ya yi hakan ne dan baya son ya yi magana da ita cikin fushi da ɓacin rai, yana da ilimi, yasan cewa idan mutun yana cikin fushi ya buɗe bakinsa to tabbas sai ya yi danasani, hakan yasa bai kulata ba, sai ya huce tukun nan.
Ta kai almost 20 mins a zaune a wajen bai ko ɗago idanun ya kalleta ba, idanunsa na a kan Tv kamar mai yin kallo da gaske, alhalin ba wani kallon da yake yi, duniyar tunani ma ya afka, yo bakinciki ma ina zata barshi ya iya yin wani kallo? Ai babu wannan zance kuma.
Da dai taga bashi da niyar kallon in da take ma bare ya yi mata magana sai ta miƙe ta nufi kitchen domin ta girkawa ƴaƴanta abinci sun kusa dawowa daga school. Farar shinkafa ta dafa masu, already tana da miyar steew ɗin da ta yi da safe, so sai ta ɗauko shi ta sake ɗumamawa, ta zubesu a kulolinta kamar yadda ta saba ta kwasa izuwa cikin parlourn.
Tana kokarin shirya abincin su Khadija suka shigo, sun dawo daga school, lemun kankana da abarba ta haɗawa baban Zainab na daban kamar yadda ta saba haɗa mashi, sai dai a yau ta zuba mashi maganin da boka ya bata, tana zuba maganin jikinta na kerma, hannunta na ɓari har ta ɗan zuzzubar da maganin a wajen, abinku da bata saba ba, tana yi tana leƙo wajen kitchen ɗin, dan sai taga kamar baban Zainab ɗin yana yi mata laɓe ne, sai taga kamar ya ganta, duk ta ruɗe zata tonawa kanta da kanta asiri, shi kuwa baban Zainab bawan Allah yana can cikin parlourn suna zuba hira da su Khadija, sai dai daga jin yadda yake magana zaka fahimci kawai ƙaƙalo maganar dan dole yake yi, dan kawai yaga ya kwantarwa da ƴaƴan nasa hankali kuma matsalar da yake a tsakaninsa da mamarsu bata shafesu ba, yana ƙoƙarin yaga bai ɗauko matsalar mamarsu ya shafa masu ba, yasa su rasa farincikinsu da kulawar da suke samu daga garesa a kullum ba.
Bayan ta kammala haɗa mashi lemun ta shirya a saman try ɗin jug ɗin tare da cup's ta ɗauka sai cikin parlourn, sam bata ji tsoron kada su Khadijah su sha ya zamar masu matsala ba, ita dai bukatar ta ya biya taga abubuwa sun dai'dai ta mata kamar da....... Ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce ki kauce hanyar Allah kuma ki yi tunanin abubuwa zasu dai'dai tun maki? Lallai kin tabba babban kuskure kuwa, domin wane mutun, babu wanda ya isa ya ga dai'dai idan ya sauƙa daga kan haryar Allah, ai yama kullah da rashin daidai kenan har sai ya tuba, idan kuma bai tuba ba haka zai mutu cikin ƙunci da baƙinciki, ya je lahira kuma ya girbi abin da ya shuka, Allah ka kiyashemu sauƙa daga kan hanyarka, Allah ka tsaremu kaucewa faɗar ma'aiki, ka kare mu daga sauka daga turbar da ma'aikinka ya ɗauramu, duk wuya duk daɗi ya Allah ka tausaya mana ka barmu da imaninmu, ya Allah cikin jarabarwa da zaka yi mana kada ka haɗa mana da raunin imani tare da tawakkali.
Kamar yadda ya saba shan lemun ya kuma ci abincin haka yau ma ya ci ya sha, sai dai fa yau ɗin ya ci ne kawai saboda su Khadija, ba dan haka ba bai da niyar cin girkinta yau, bama yau ba bai da niyar sake cin girkinta har sai ta gaya mashi in da take zuwa, idan ta gaya mashi kuma sai ya bincika yaga da gaske ne ko karya, dan haka kawai ya ji hankalinsa sam yaki ya kwanta.
Bayan sun kammala cin abincin, har da su Khadijah duk sun sha lemun baban nasu, miƙewa ya yi tare da nufar room ɗinsa, ita kuma maman Zainab jiki ba kwari ta zo ta tattare wajen, ta shiga damuwa sosai na ganin yaki ya kulata, har ta yi tunanin ta bisa ɗaki ta bashi hakuri, sai kuma ta sake cewa bari ta barshi tun da ya sha maganin nan, wata kila zai sauko ya zo ya fara yi mata biyayya................ Babbar magana, akwai case kuwa ba karama ba, ga su Khadija ma dai sun sha magani, ko me zai faru? Mu dai je zuwa zamu ga komai dallah dallah, kun san ni dama da iya yi maku komai dallah dallah ta yadda zaku fahimta da kyau da kyau, to mu dai je zuwa, na yi gaba sai kunzo!.
Shirin komawa kasuwa ya je ya yi tare da fitowa, bai yi mata sallama ba ya sa kai ya fice izuwa harabar gidan. Da sauri Zee and Khadijah suka bi bayansa.1k ha ciro daga cikin aljihunsa ya basu a kan su sai wani abin idan sun je islamiya, ya san ba'a rabasu da kayan kwalama.
Sai zuba mashi godiya tare da adduar a dawo lafiya suka rinƙa yi, ita kuwa maman Zainab ta maƙale a windown parlourn tana leƙansu, ji take yi kamar ta je ta bashi hakuri, amma kuma idan ta tuna ya sha magani sai ta ce ina babu wani hakurin da zata bashi, da kansa zai kawo kansa gabanta yana mai ƙasƙantar da kansa a ƙasa, a nan ne zata zuba mulkinta ita kuma. Babbar magana.
Tana ji tana gani ya fice ya tafi kasuwa, su Khadijah kuma suka dawo cikin parlourn, room ɗinsu suka nufa domin su yi wanka tare da ɗauro alwala su yi shirin zuwa Islamiya, dan lokacin sallar la'asar ta kusa, saura kaɗan, suna yin sallah kuma zasu wuce Islamiya.
Ita ma mamar tasu nata room ɗin ta shiga ta kwanta, dan ta huta, duk a gajiye take, dutsen nan da suka hau ya ja mata ciwon kafafu................ Ni kuwa nace har da uban ciwon kafafu ma zai ja maki ai, ai kafafu ma kaɗan ne ba dai saɓon Allah ba?.
Sai da suka kammala shiri cikin uniform ɗin islamiyarsu, sannan suka yi sallar la'asar, dan a lokacin an kira, bayan sun idar da sallar lafiya lou suka zo suka yi mata sallama a kan sun tafi islamiya, kuɗin kayan miya kamar yadda suka saba ta basu su sayo mata a hanya idan suna dawowa, daga haka bata sake yi masu magana ba, suma karɓa kawai suka yi suka wuce abinsu, dan sun san kwana biyun nan fa gidan nasu sai addu'a kawai. Yara masu hankalin manya kenan, kullum cikin yiwa iyayen nasu addu'a suke yi bayin Allan!.
Tamkar Khadija zata dawo ta ce mata an kira sallar la'asar, sai kuma ta fasa saboda kada ta yi mata faɗa ta ce ai ita ba kurma bace tana ji. Haka suka wuce Islamiyarsu, gwanin birgewa idan suna tafiya islamiya, cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kai daga ganinsu kasan tarbiya ta ratsasu sosai.
Maman Zainab kuwa barcinta ta hau yi ba tare da ta yi sallah ba, dan ta ci mugun wuyar hawa dutsen, duk gaɓɓan jikinta ciwo yake yi mata, hakan yasa da ta kwanta ta ƙasa iya tashi, sai kawai ta hau barci ƴar kaniya.
Ɗan tsokaci, saɓon Allah komai ƙankantarsa yana mugu mugun nesanta bawa da Ubangiji tare da raba shi da imani, barema saɓon Allah mafi girma wato shirka, haɗa Allah da wani kenan, kun dai san maman Zainab tana da ƙoƙari wajen yin ibada, amma da yake ta saɓawa Allah kunga har abin ya fara shafar ibadarta, ko a jikinta ta kwanta tana barci lokacin sallah, to haka saɓawa Allah yake, kishiyoyi ne da rabaka da Ubangiji, daga nan kuma zaka ga komai yana taɓarɓare maka, please ƴan uwana mata, zan yi amfani da wannan dama na ja hankulanku sosai, duniya dai ba matabbata bane, kwana nawa ya rage? Lahira ita ce madauwamiya, kada ki je garin neman duniya ki ɓata lahirarki wadda kuma ita ce madauwamiya, duniya tamkar kasuwa muka zo ci mu koma gidan gaskiya, duk daɗi duk wuya kada ki taɓa yarda ki rasa lahira, gara maki ki rayu cikin ƙunci na tsawon rayuwarki da ki lalata lahirarki, Allah ka karemu da kariyarka, ka shiga cikin lamuranmu, ka dafawa musulmi da musulunci, ka kara ɗaukaka musulunci da musulmai bakiɗaya, ya Allah ka jikanmu, ka tausaya mana, kai mana rahmarka, dama kai arrahman ne kuma arrahim, ka gafarta mana, dama kai algaffar ne, mai gafartawa bayinsa a duk lokacin da suka ƙasƙantar da kai suka nemi afuwa, ya Allah ka kawo mana zaman lafiya a duk in da muke. Ku ce amin a cikin zuciya!.
Bari mu leƙa wani wajen, wata kila kafin mu dawo baban Zainab ya dawo mu ga result ɗin maganin bokan ya ake ciki?!.
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
🏞️FOREST🏞️🌼
After some days. A cikin ƴan kwanakin nan da suka suɗe, Kamran sun yi muguwar sabo da su Pretty, kullum yana zuwa kamar yadda ya saba, har yau kuma ya kasa iya tambayar mammarsa menene aure, tun da ya tambayeta menene Alhdulillah ta ɓata rai sosai kamar zata maresa, ta kuma tsare shi a kan dole sai ya gaya mata a ina ya jiyo wannan kalmar ta Alhdulillah? Da kyar ya iya shawo kanta ya gaya mata cewa wasu maharba ne suna wucewa ya ji suna faɗin Alhdulillah, shi ne yake son sanin ma'anarta, warning ta yi mashi sosai a kan babu ruwansa da jin abubuwan da mutane masu wucewa zasu faɗa, a wannan rana dai sam bai je wajen su Pretty ba, saboda mamma ta yi mugun ɗaukar zafi na jin kalmar Alhdulillah ta fito daga bakinsa, hakan yasa ni PRINCESS TEEMA na kara sakawa mamma ayar tambaya a kai, duk yadda aka yi tana da sani a kan addinai ba iya musulunci kawai ba, tana da sani sosai a kan har sauran addinan, dole akwai wani abin da yasa ta ce ita bata yarda da addini bama kwata kwata, ita bata da addini, yadda ta ɗauki zafi daga jin kalmar Alhdulillah ya nuna tasan ma'anar kalmar.
Shi kuwa Kamran a bakin su Pretty yake yawan jin wannan kalma ta Alhdulillah, sai ya yi gangancin tambayar mamarsa bai tambayi su Pretty ɗin ba, tun da yaga ta ɗauki zafi sosai haka sai ya ji tsoron yi mata tambaya a kan menene aure, dan gudun kada ya zamana shi ma auren wata magana ce babba da zai ja mashi a rabashi da su Pretty, duk abin da zai sanya a rabasu baya kaunar ko jin makamancinsa, dan sun zama wani ɓari na rayuwarsa, wani abu guda ɗaya da ya lura da shi shi ne, duk wani abin da zai fito daga wajensu Pretty yana cin karo da ra'ayin mammarsa, ma'ana zaka tarar da Mammarsa ta tsani jin makamancin wannan abin, abin har ya fara bashi mamaki yana kuma ɗaure mashi kai sosai, hakan yasa ya fara zargin lallai Mammarsa tana da sani a kan irin wannan addini nasu su Pretty, sai dai ya barwa zuciyarsa wannan tunani, saboda baya son ya ɓallo ruwan da zai rabashi da sanyin idaniyarsa wato su Pretty, ga shi mum ɗinsu ta bashi amanarsu, ai kunga nauyi ya karun masa a ka, dole ya zage dantse wajen kula da su.
A ƴan kwanakin nan da suka shuɗe sun yi muguwar sabo da shi na ƙin karawa, har ta kai ta kawo yanzu sai ya zo suke cin abinci a tare, suna fita waje filin ƙoramar nan su yi ta wasa, a yanzu yana koyawa Pretty harbi da kifiya, sakamakon ya rage jin feeling da yake yi, hakan kuma ya samo asaline saboda maganin da mammarsa take basa ba tare da saninsa ba, so yanzu idan ya taɓa Pretty baya jin abin sosai.
Yanzu ya koya mata busar wannan sarewar tasa da yake kyarawa da abin ayaba, ya koyawa Sweetie ma, idan suka zauna a wajen ƙoramar nan yana koyawa Pretty harbi da kifiya ita kuma Sweetie tana yi masu busa mai daɗi, abin gwanin birgewa, wani lokaci ya goyi Pretty su hau saman bishiya su ciro mangoro, Sweetie tana ƙasa tana yi masu busa, sai dai su ciro su zo su wanke mata su bata ta sha.
Sai dai fa har yau har gobe Pretty dai taki yarda da Rocky, taki yarda su zama abokai, ta ce babu wannan magana, kowa ya tsaya a matsayinsa, Kamran dai bashi da zaɓin da ya wuce ya yi masu iyaka idan yana son zaman lafiya, baya yarda ya bar Rocky ya taɓata, dan yana taɓata zata haukace masu ne a wajen.
Taƙa tsantsan sosai Kamran yake yi wajen zuwa wajen nasu, dan kada Mamma ta gane shi. A yanzu warriors ɗin nan sun ɗan rage shigowa cikin wannan dajin, yau tsawon kwanaki biyar kenan Kamran bai haɗu da ko mai kama da su ba. Gawarwakin warriors ɗin da wannan jarumin sadaukin mutumin ya kashe su ma duk Kamran ɗin ya jefasu cikin ruwan dake gudu har izuwa wajen babban teku ruwan ya tafi da su.
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
Gari ya yi sanyi, rana ta yi yamma ta kusa faɗuwa, inuwa ta sauko a dajin, ƴelwar ni'imar iska tana kaɗawa a ko'ina, iska ce mai matuƙar daɗi da ratsa jiki, dogayen bishiyoyin sai kaɗawa suke yi, ba iska bace ta ruwan sama, ba kuma iska bace ta hunturu, iskace ta bishiyoyi suke kaɗawa, yanayin gari ya yi matuƙar daɗi musamman ace ga masoya, dajin ta yi shiru sai sautin kukan tsuntsaye ne yake tashi