x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 39 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 114001 words
  • 117000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 429

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
sosai a muryarta, ka kwainane da kisisina, tana magana tana wani dakewa.

Wani irin nannauyar ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke kafin ya iya komawa saman sofarsa ya zauna.
"Barka da isowa gimbiya kuma tauraruwar mata".
Ya faɗa muryarsa cike tab da tsantsar so da kuma kaunarta.

Wani irin ɗan iskan shu'umin murmushi kaɗan ta saki wanda ya kara fito da tsantsar kyanta, hakan kuma ya kara tafiya da imanin bawan Allah Yusuf.

Shi ma abokinsa ya ƙasa iya kawar da kallonsa daga kanta, gata ƴar caras da ita.

Juya waɗan nan fararen dara daran idanuwan nata ta yi kafin ta ɗan ja gajeran numfashi.
"Yauwa barka dai malam Yusuf, fatan ka zo lafiya?".

Ina ai ta gama tafiya da imaninsa, kara rikicewa ya yi a in da ya amsa mata da lafiya lou da hanzari.

"Bari na zuba maku ruwan sha ko?".
Ta faɗa ba tare da ta kawar da waɗan nan shegun idanun nata daga kan Yusuf ɗin ba.

Da mamaki kuyangun da suka rakota suka bita da kallo, wannan yarinaya akwai shegen makirci, ita da ko kanta bata zuwaba ruwan sha idan zata sha, komai yi mata kuyangun nata suke yi, bata son yin aiki ko kaɗan, amma wai take cewa bari ta zuba mashi ruwan sha? Duk dan ace tana son shi kenan? Kai Sarina duniya.

Ni ko na ce ko ina su twin's? Ko me suke shiryawa Yusuf bawan Allah? Ga shi dai ya gama afkawa gogin sonta, sai Allah sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA ne kawai yasan me waɗan nan Team ɗin suke shiryawa, sai mun haɗu da ku gobe idan mai dukka ya kai mu, amma fa akwai kallo ba kaɗan ba, dan nasan za'ayi dirama a cikin wannan KINGDOM ɗin yau, dan haka ku gyara zama!!.


🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍



🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)







🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 25/7/2024.....✍️📚🌹




For information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








E____________22🔥




Malam Yusuf dai ya ƙasa iya cigaba da magana, kallonta kawai yake yi, ikon Allah ikon gaske, abokinsa da ya zo rakiya ma sai kallonta yake yi, wannan da a tare suka ganta to ba shakka zata raba abotansu, dan sai sun yi faɗa a kanta, yanzu ma waye san gaibu? Ai sai Allah, bamu san me gaba zata haifar ba, amma dai koma me wannan abokin ya faɗa dayawa, Allah kaɗai yasan me yake tunani a cikin zuciyarsa kuma.

Saboda shegen makirci irin na Sarina har da ɗan saukowa ƙasa kaɗan ta hau zuba masu ruwa yadda kuka san irin tana son shi kamar ta cinye shi ɗanyen nan, shi ma ya zaci haka ne, har da wani cewa.
"Gaskiya na jima ban shiga farinciki irin na yau ba, bana jin kishin ruwa, amma saboda ke ce zaki zuba mun ruwan ko dukka kika ce na sha zan shanye".
Ya yi maganar a nutse, da alama yana da nutsuwa sosai.

Wani ɗan iskan shu'umin murmushi ta yi mai kara rikita mutun, a zahirin gaskiya saboda ma bata saba da yin murmushi ba, sai yazama sam murmushi bashi da gurbin zama a saman face ɗinta, ko ta yi baya yi mata wani kyau, amma da yake malam Yusuf sabon shiga ne, sai yazamana shi murmushin nata ya zama mashi wani abin na musamman, kuma sai yake ganin kamar idan ta yi murmushin nan har wani haske parlourn yake karawa.......... E ba shakka kai kam ka shiga tarkon Team ɗin nan na marasa jin magana, duk kuma wanda ya shiga hannun waɗan nan team ɗin to wlh sai dai Allah ya fitar da shi, yara ne yadda kuka san babba mai shekaru 50 wanda ya sha gwagwarmayar rayuwa ne yake shirya masu plan, ba zaka taɓa yarda cewa su ne suke shirya wasu abubuwa ba, saboda abin ya wuce tunanin mutun, idan zasu yi mugunta sai su juye su zama na Allah, su zama mutanen kirki, tsabar kuma sun iya basajan idan suka zama mutanen kirkin ma ba wanda yake iya ganewa, kai waɗan nan yara idan suka girma kada ka yarda ka shiga hannunsu, dan mutuwa ba makawa zaka yi.

Cikin tsantsar rangwaɗa mai jan hankalin ta miƙewa Yusuf cup mai ɗauke da ruwan da ta zuba mashi. Bawan Allah jiki na rawa ya karɓa, tuni ya kai bakinsa ya fara sha yana zuba mata godiya. Haka ta sake zubawa ta miƙawa abokin nasa ma. A hanzarce shi ma ya kai hannu ya karɓa, daga yanayin yadda take zuba wannan ruwa ma kawai ya isa yasa ka fahimci bata iya aikin siɗiɗi bare saɗaɗa ba, kawai iyayi ne.

Saman sofar ta koma ta zauna tare da ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, cikin wata iriyar voice mai sanyaya zuciyar mai sauraro ta fara magana daki daki.

"Malam Yusuf ka sauko ku ci abinci, ga abubuwa nan mun tanada maku".

Irin wannan voice da ta yi magana da shi ɗin nan sam ba zai iya tsalleke tayinta ya ce ba zai ci wannan kayan cima ba, dole ya amsa mata da.
"Okey gimbiyata".

Wani irin fari da ido ta sake yi mashi kafin ta ce da kuyangunta dake tsaye ta bayansu su zuba mashi abin da yake ra'ayi, dan a gaskiya bata iya serving na abinci ba, ruwan ma da yaya ta yi? Already kun san ita ko tsinke bata ɗagawa, komai sai dai ayi mata, so bata iya ba, shiyasa tasa kuyangun su yi masu.

A hanzarce suka karɓi umarninta, ba ɓata lokaci suka zo suka fara serving ɗinsu, a wannan lokacin ne kuma Yusuf ya sami damar iya gabatar mata da kansa tare da abokin nasa da suka zo a tare.

Bawan Allah abokin nasa bai yi kasa a gwiwa ba kuma bai bari kansa ya yi marfi ba ya yi maza ya ce.
"Gimbiyarmu Please kina da sister? Allah dai yasa ba ke kaɗai bace".

Ba tare da ta kalli in da yakeba ta bashi amsa, idan baku manta ba ita bata cika ɗaga idanu ta kalli mutane ba, bare ma kuma mutanen da ta raina class ɗinsu, ai gani take yi ma kallonsu kamar ɓata idanuta zata yi, hakan yasa sam bata kalli in da yake ba, shi ma Yusuf ya ci sa'ar akwai abin da aka shirya mashi ne yasa ake kallonsa, ba dan haka ba ina mai tabbatar maku Sarina ba zata ɗaga idanun ta kalli in da yake.

"Yes ina da sisters ma dai ba sister ba, sai dai sun tafi school, amma idan kana son ganinsu sai na nuna maka pic's ɗinsu ai".

Cikin rawan jiki kamar wani mazari ya buƙaci da yana son kallon hotunan sisters ɗin nata, dan har ga Allah ya afka kogin madarar kaunar jinin Akka....... Ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce aikuwa kana ruwa, dan ba Sarina ba, duk wanda ya ce zai yi soyayya da jikokin wannan tsohuwa in ma mace or namiji wlh yana ruwa, dan wasu murɗaɗɗun mutane ne, ko Zunaira da kuke gani kamar shiru shirun nan idan aka zo batun maza bata da daɗin sha'ani, bare su hjy Chuchu, duk kusan haka suke, babu wanda ya taɓa kula wani namiji a cikinsu, gani suke yi ma kula maza zubar da class ne, bare ma Aneesa ƴar Mama, ita ma kusan halinta ɗaya da Sarina a ɓangaren rai'na mutane, Fanan kuwa cewa ta yi sai ta samu namiji kamar yayansu zata yi aure, yayansu wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya nake magana, yayan Jawad mai suna Rizwan kenan, yana ƙasar Dubai, to shi ne wai sai namiji irinsa idan ta samu zata yi aure, ko shi ɗin wani irin hali gare shi da yasa ta ce sai irinsa zata aura? Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA, koma wani irin hali gare shi lokaci ne zai nuna mana, ga shi kuma yayanta ne uwa ɗaya uba ɗaya bare ace a haɗasu aure kawai, hakan ba zai yi wu ba.

Wayar Mammie ɗinta da yake a hannunta ta ciro ta fara duba mashi hotunan su gimbiya Zunaira, ko a jikinta bata damu ba zata nuna mashi hoton, dan tasan idan ma a cikin ƴaƴan King ne wato su Chuchu, Zunaira or Aneesa zai zaɓa ya yi a banza, dan wlh bai isa ya tinkari King da wannan zance ba ato.

Fito mashi da hotunansu a lokacin da Gimbiya Chuchu ta kammala primary school zata shiga secondary ta yi, a lokacin sun shirya gagarumin party sosai, an gayyaci manya daga ƙasashe da dama, sun sha kyau iya kyau, an yi hotuna anyi kyaututtuka da abubuwa daban daban, so iya waɗan nan hotuna na partyn kawai ne a wayar Mammie ɗin nata, dan na gaya maku ita Mammie ba kaunar jinin King take yi ba, har ga Allah bata son su Zunaira, kawai dai dan ba yadda zata yi ne, amma ta tsanesu kamar ta kashesu, wanɗan nan hotuna da kuka ga ta ajiye su a wayarta ma ta ajiyesu ne saboda akwai ƴaƴanta Sarina and Fanan a cikin hoton, da na su Zunaira ce kawai wlh ba zata ajiye ba, tsab zata gogesu munafukar mata.

Miƙa mashi wayar ta yi a kan ya karɓa ya kallesu, a dai'dai lokacin kuma su kuyangunsu suka gama zuba masu abincin.

Ƙasa saman haɗaɗɗen carpet ɗin suka sauko domin fara cin abincin. Hannu ya kai ya karɓi wayar domin ya kalli hotunan.

Yusuf kuwa abincin ya fara ci domin ta gaya mashi idan ya ci zata yi farinciki, ya ce ta sauko su ci tare, ta ce tom su fara zata sauko.

Shi kuwa Abokin nasa yana kyallah idanu yaga hotunan taurarin King Zuhair haba sai ya ruɗe, idanuwansa suna a tsaye kyam a kan Gimbiya Zunaira ƴar auta, shi ai yaga mata, ina sai ya ga ashe Sarina ma ba wata kyakkyawa bace idan aka dangantata da Zunaira da kuma Chuchu, sun fita kyau nesa ba kusa ba, sai dai Zunaira karamar yarinya ce, kuma shi baya jin kamar zai iya jiranta ta girma, yanzu yana da 28 years a duniya, ita kuma 11, ace ya jirata nan da shekaru 7 zuwa 8 haka, gaskiya da kamar wuya, ita ma dai Chuchu koda ya ce yana so zai yi jiran shekaru 4 zuwa 5 kam, dan 14 years ke gareta, Aneesa mai 15 years ma nawa take? Duk cikinsu dai Fanan ɗin ce sai kuma Sarinar suka isa aure, shi kuma Fanan bata yi mashi ba, dan kyawun Gimbiya Zunaira da Chuchu sun dishashe kyan kowa da yake a cikin hoton, su biyu ne taurarin da suka haska kowa, so shi a ɗaya daga cikinsu yake so a bashi mata.

Taɓa shi Yusuf ɗin ya yi yana faɗin. "Ya dai? Bata yi maka bane?".

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Yi kai, ai ni naga mata".

"To mu gani". Yusuf ɗin ya faɗa.

Miƙawa Sarina wayarta ya yi yana faɗin. "A'a ba zaka gani ba, kai baga naka Gimbiyar a gabanka ba? Me kuma zaka ce zaka ga wata? Gaskiya ban yarda ba".
Yaki nuna mashi su ne kawai dan yasan yana ganinsu zai kallin kyan Sarina ya dishashe a idanunsa kamar yadda ya gani a yanzu shi ma, hakan yasa ya ki bashi ya gani.

Ko a jikinsa Yusuf bai damu ba, shi dai Sarina kawai yake kallo abinsa.

Ƙasa saman carpet ɗin ita ma ta sauko, duk dan ta nuna mashi kulawa ta kuma nuna yes tana kaunarsa, shi kuwa ya saki baki ya ɗauka haka abin yake.

A ɓangaren su twin's kuwa, kwance suke a saman katafaren bed nasu, Omaid yana rike da tsadaddiyar wayarsa yana latsawa, shi kuma Obaid ya yi shiru tare da ɗaura hannunsa ɗaya a saman lallausan kumatunsa, da alama duniyar tunani ya afka, ga dukka alamu jikinsa a mace yake, ya yi kwanciyar ruf da ciki ne, while ya saka wani haɗaɗen pillow na ƙayatattcen bedsheets da yake shinfiɗe a saman bed ɗin nasu a kirjinsa, hakan yasa ya ji daɗin yin kwanciyar ruf da cikin. Luxury bedroom kenan, ɗakinsu duniya ne, katafaren bed guda biyu ne a cikin room ɗin, komai na jikin bed's ɗin iri ɗaya ne, komai da yake cikin room ɗin bibbiyu ne kuma iri ɗaya, harta bedsheet iri guda kuyangunsu suke shinfiɗa masu a kullum idan suka zo yi masu gyaran ɗaki, idan muka leƙa cikin toilet ɗinsu ma komai bibbiyu ne, luxury jacuzzinsu guda biyu ne, haɗadɗen glass bathtub showernsu ma guda biyu ne, kai komai nasu dai guda bibbiyu ne iri ɗaya!.

Jin shirun ya yi yawa ne yasa Omaid ya ɗago da kallonsa izuwa kan ɗan uwan nasa. Ɗan zaro ido ɗaya ya yi tare da ɗage gera guda.
"Blood what are thinking like that naga ka zauna so silent?".
Ya faɗa yana ƙoƙarin kashe wayarsa da yake latsawa, domin ya maido da hankalinsa a kan ɗan uwan nasa da kyau, dan ya ji me matsalar.

"Pleasure am thinking about this our plan, you know Yah Jaish is around, kuma shi Yah Jaish he has a very very shape brain that within a few minute zai iya kamamu, ni bana son shan wahala fa, kafa san halinsa sarai da mugunta, zai bamu punishment over".
Ya yi maganar cikin wata iriyar makirar murya, kamar wadda ya karaya da gaske! Ko da yake dama shi Obaid da sauki a kan Omaid, Omaid shi ne shugaba, bashi da tsoro ko shakka!.

Shiry Omaid ya ɗan yi na ƴan sakani kafin ya ce.
"Why are you worry your self like that? Ka manta da cewa mun yi shiri mai kyau ne? I think by this time ma yakamata ace komai ta fashe, kayi feel free blood".

Ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan yin shiru kamar mai tunanin wani abin, yadda kuka san malamin islamiya ya faɗa jarabawar Ubangiji, irin ya fawwalawa Allah komai nashin nan, to haka Obaid ya yi, ya wani koma kamar Allah sarki bawan Allah.

Hannu Omaid ya kai da nufin ya rungoma shoulder ɗinsa, dan yaga kamar ya shiga damuwa, sai dai bai kai ga taɓa shi ba sai ga Obaid ɗin nan ya fashe da wani irin makiri kuma shu'umin dariya kamar wani zararre, kamar ba yanzu yake cikin halin Allah sarki ba.

Da kallo Omaid ya bishi da shi, dama yasan da wuya Obaid ya karaya a kan abu, kawai salon sabon iskanci ne suka samo.

"Why are you laughing like that?".
Cewar Omaid, ya yi maganar kuma yana kare mashi kallo.

Cigaba da dariyarsa mai sauti ya yi, tsabar dariyar muguntar ma ta yi yawa har da birgima a saman lumtsumemiyar mattress ɗin nasu, ya wani dafe ciki, da alama wani shaiɗancin ya tuna.

"Blood stop this laughing and tell me what are you laughing for?".

Miƙewa zaune ya yi tare da dafe cikinsa sosai, tsabar dariya har da hawaye suka cika mashi idanu.

Pillow Omaid ya ɗauka ya fara bugunsa da shi yana faɗin.
"Please blood stop it now, ni bana son haka fa, ka gaya mun reason na dariyar sai nima na taya ka, amma kana ta yin abu kai kaɗai".
Ya yi maganar cikin ƙaguwa na son ya ji me Obaid ɗin yake yi wa dariya haka har da hawaye.

Ganin yadda ɗan uwan nasa ya ƙagu da ya ji menene yake yi wa dariyar yasa ya daure ya tsagaita dariyar. Murya cike da shakiyanci ga kuma dariya da yake faman dannewa ya fara magana.

"Pleasure ba komai bane ya saka ni dariya face this guy called Yusuf, da wani gemunsa kamar na uncle Rahab, irin shi ustadz like Yah Muzaffar, kaga time da suka fito daga cikin car ɗinsu ina jinsa wai har da cewa baya son ɓata lokaci, da sauri zai sanya daddynsa asaka masu rana shi da Aunty Sarina, har da wani cewa tun da ita ta yi mashi ai ba wani jira da sun ga juna sai aure, wani useless da shi har yana da zaɓi, bari ma dai yanzu zai ji kansa a prison, a nan ne zai ga aure da wuri, hancinsa like Akka nose".

(Innalillahi da ji kunsan waɗan nan twins ɗin basa shiri da Akka, wai harda zagin hancinta irin na Yusuf, kai twin's sai shirin Allah 😅 Akka ma ashe tana layin waɗan da basu kauna, yo dama su ina zasu kaunaci mafaɗaci wanda zai takura masu?)

Dariya Omaid ya kwashe da shi, cikin dariya yake faɗin. "Not only nose ɗinsa ne like na Akka, even his head ma kato ne like Akka own, ka ji kazami wai zai auri Aunty Sarina, an gaya mashi ita ɗin class ɗinsa ne? Amma gaskiya i pity this guy more, ina ga yau gunduwa gunduwa da shi ma dad zai yi, ai prison ma ya yi mashi kaɗan".

Shiru Obaid ya yi kamar mai tunanin wani abin, hannayensa dukka biyu ya kai saman kumatunsa ya tallabosu kamar mai tunanin wani abin, ya ɗan tsuke fuska alamar tausayawa.

"Obaid are you okey?". Omaid ya yi maganar tare da ɗan matsowa kusa da shi ya kuma dakatar da dariyar da yake yi.

"Pleasure yanzun nan naji tausayin guy ɗin ya shiga rai'na, yana ɗan masu muryar faɗa aji a ƙasar amma zai shiga prison? Gaskiya i pity him, amma dai ba zamu fasa yin abin da muka yi niya ba, gobe ya sake zuwa neman aure a gidan su zakuna bakwai, sai ya sha jibga wajen commander ZAFAR, daga nan dad ya ce a yanke mashi hukuncin zama gidan prison for 10 years".
Yana kai karshen maganar kamar abin haɗin baki kamar kuma
End Ads