x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 88 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 261001 words
  • 264000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 364

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
haka in baki son ɗakin da na baki ki san abin yi, ke bari ki ji ko shi kansa mai gidan idan na ga dama yau a waje zai kwana, kuma haka dole zai kwana babu yadda ya iya da ni, ni fa babu yadda kuka iya da ni, na zame maku ƙashin wuya, na fi karfinku sai gani sai hange daga nesa".

Zainab dake tsaye kusa da mamar tata ce ta ce. "Idan kin fi karfinsu ai baki ki fi karfin Allah bako? To da izinin Allah sai rayuwarki ta walaƙanta tun a duniya kafin ki je lahira ki girbi abinda kika shuka, maciyi amana kawai, In Sha Allah idan baki yi hankali ba ni ce nan zan gyara maki zama!". Ta yi maganar tana wurga mata kallon up and down irin wanda take yi wa Haidar idan ya ɓata mata rai, kun san fa Zee ta kware a iya irin wannan ɗan iskan kallo na rai'nin wayo, kamar dan ita aka yi kallon, ga idanun nata kuma manya farare tas, idan ta fara wannan kallo ba'a magana, kallo ne na ƙasƙanci wanda idan ka yi wa mutun sai ya ji kamar bashi da gata, to ita dai Zainab ta kware a wannan part ɗin.

Sai ƙoƙarin rufe mata baki Khadija take yi a kan ta yi shiru kada ta sake jangwalo masu wani bala'in, amma ina Zainab fa taki rufe bakinta har sai da ta kai aya a maganarta.

"Eyeee lallai Zainab kin girma, wuyarki ya yi kwari ya kai yanka, ke ɗin ce zaki gyara mun zama? To uwarki ma mecece a gaba bare ke? Ubanki ma bai wuce na aikesa ya je ya dawo ba bare ke, lallai yarinya kinzo da abin da dukka familynki ba zasu iya ɗauka ba, wato faɗa da ni!!".

Cigaba da wurga mata wannan matsiyacin kallo ta yi tare da cewa. "Ke ɗin wacece ke? Ke ɗin banza ke ɗin hofi, babanmu dai zaki iya aikansa ya je ya dawo kamar yadda kika faɗa ɗin, dan kin shanyesa, amma ni dai wlh nafi karfinki algunguma kanwar shaiɗan kawai!!".

Cikin fushi tare da jin zafin kalaman nata Hauwar ta yi kanta zata daketa. Da sauri maman Zainab ta shiga tsakaninsu ta mayar da Zainab ɗin bayanta. Cikin ɓacin rai ta fara magana. "Wlh Hauwa idan kika ɗaura hannunki a jikin Zainab sai kin gane baki da wayo, sai na tuno maki da lokacin da muke zuwa Islamiya!".

Khadija dai tana tsaye shiru tana ganin wannan iko na Allah, ita kanta ma ciwo yake yi mata, ta gaji da tsayuwa tana son ta zauna.

Birki Hauwar ta ja, cikin kunan rai ta juya fuuu kamar wata kunfa ta nufi ɗakinta in da baban Zainab ya shiga kenan, da alama tana matuƙar tsoron yin faɗa da maman Zainab ɗin, duk da ta san cewa baban Zainab yana nan kuma zai tare mata faɗar, sai dai tasan kafin ya fito ya tare mata ɗin maman Zainab idan ta yi mata duka ɗaya sai ta yi jinya, hakan yasa bata yarda ta yi faɗa da ita idan baban Zainab ɗin ya matsa ko kaɗan ne.

"Zainab ku shiga wancan ɗakin da ta ce naku ɗin ku zauna ina zuwa, ku fa rufe kofa idan kun shiga, kuma ko an buga kofar kada ku buɗe har sai idan ni ce na dawo". Cewar maman Zainab.

Cikin wani irin kasalalliyar murya mai sanyi Khadija ta ce. "Mama ina zaki je?".

Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce. "Ba zan yi nisa ba, yanzu zan dawo, idan na dawo zan gaya maki in da na je". Tana kai karshen maganar bata jira jin me zasu sake faɗa ba ta nufi waje da sauri.

Su kuma suka nufi cikin ɗakin a hanzarce kamar yadda ta umarcesu, suna shiga kuma suka dannawa kofar key.

Da shigansu ɗakin ba'afi da minti ɗaya ba sai ga Hauwa da baban Zainab sun fito daga nasu room ɗin. Sai cika Hauwa take yi tana batsewa, da alama wani munafurcin ta je ta haɗa, ta kwashi karya da gaskiya ta sanar da shi, bawan Allah shi kuwa da already an rigada an shanye mashi ruwan kansa, sai yazama kamar wani yaronta, duk abin da ta faɗa shikenan ya yarda, haka kuma zata taso shi a gaba zalo zalo yana biye da ita, duk abin da ta faɗa ya hau kai ya zauna da shi yake aiki.

Ganin babu kowa a parlourn ne yasa Hauwar ta fara surfa uwar masifa a kan ita lallai ba zata yarda ba sai baban Zainab ya daki Zainab ɗin dan ta yi mata rashin kunya.

Shi kuwa bawan Allah sai hakuri yake ta bata babu kakkautawa, kafewa ta yi a kan lallai sai ya gurzan mata bakin Zainab har sai ya yi jini. Allah sarki Zee baiwar Allah, babanta bai taɓa ɗaura hannunsa a jikinta da sunan duka ba, baya dukansu sai dai rarrashi da lallama tare da nuna soyayya, amma yau Hauwa tana son lallai sai an dirzan mata bakin Zee, akwai cakwakiya kenan.

Sai hakuri yake bata yana gaya mata ai shi bai ga su Zainab ɗin ba, tun da kuma basa nan ta yi hakuri kawai. Sam bata san sun shiga cikin ɗakin ne sun rufe kofa ba, da ta leƙa ɗakin da ta baiwa mamar tasu taga ba kowa sai ta yi zaton fita suka yi, bata yi yunƙurin leƙa ɗayan ɗakin ba.

Ita kuwa maman Zainab tana fita kai tsaye bakin titi ta nufa, da yake gidan nasu bashi da nisa da bakin babban titin.

Yau a karo na biyu Maman Zainab ta sake fita ba da izinin baban Zainab ba, hakan kuma ya faru ne saboda tsananin kunan rai da take ji, idanunta sun rufe bata ji bata gani, shiyasa ake son bawa a kowani lokaci ya rinƙa yawaita addu'ar Allah yasa ya fi karfin zuciyarsa, sannan ku kasance a duk lokacin da ranku ya ɓaci ku yawaita istigfari kuna ambaton sunan Allah, hakan zai sa duk ɓacin ran da zaku shiga ba zaku taɓa yin aikin danasani ba, dan haka ni dai shawarata a gareku ƴan uwana mata har ma da maza, kada ku bari zuciyarku ta fi karfinku, duk wuya duk daɗi kuma kada ku bari ambaton sunan Allah ya kubce daga bakunanku, yawan ambaton Allah ya kan sa ku fi karfin zuƙatanku, kuma yakan kai ku ga nasara tare da cinma burikanku da kuma samun babban rabo duniya da lahira, dan haka kada ku yarda ambaton Allah a kowani irin yanayi ne ya kubce daga gareku!!.

Abin hawa ta hau ba tare da ta gayawa kowa ba ta nufi bayan gari. Zuciyarta tafarfasa yake yi mata tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje, ranta ya yi bakin kirin, idanunta sun rufe sosai, burinta kawai ta isa in da take da buƙata, sai sauke wani irin ajiyar zuciya take yi wanda da gajisa kasan na tsananin ɓacin rai ne, wai ace Hauwa ce ma zata zaɓa mata in da zata zauna ita da gidan mijinta, gidan mijin nata ma wanda ta sha wahala ta juri komai dan su gina gidan? Abin da ciwo kam matuƙa, duk kuma macen da aka yi wa haka ba lallai ta iya ɗauka ba, za'a tara mata ɗari da wuya a samu biyu da zasu iya danne irin hakan su shanye, akwai matuƙar ciwo sosai.

Kai tsaye bayan gari suka nufa, ba tare da ɓata lokaci ba ta yi wa mai mashin ɗin kwatance wajen wannan boka na Hauwar, sai kutsawa cikin dajin yake yi ita kuma tana kara yi mashi kwatance. Da kyar dai suka iya isowa wajen dutsen.

Sauka ta yi ta ce ya jirata bari ta je ta fito, dama sun yi da shi tun kafin ta hau a kan zai kai ta ne ya kuma dawo da ita, hakan yasa ya samu waje ƙarƙashin wata bishiyar kuka mai girma ya yi zamansa bayan ya kashe mashin ɗin nasa kenan. Zuciyarsa cike tab da tunani tare da tarin tambayoyi haɗe da mamaki a kan maman Zainab ɗin.

Bai san wacece ita ba, amma ta bashi mamaki yadda ta ce ya kawota wannan ƙungurmin dajin, tunani ya rinƙa yi tare da tambayar kansa me ta zo yi a nan? Sam bai san da cewa a saman wannan dutse ta baya akwai wani la'anannen Allah ba wai shi boka, wani tsinanne wanda wutar jahannama ke jiran gangar jikinsa idan bai tuba ba, shi dai mamaki yake yi kawai na me zata yi a daji, tunani ya yi ko dai ya salallaɓa ya bi bayanta ya je ya leƙa me zata yi ne domin ya samu abin labartawa a gari.

Hakan kuwa a ka yi, ya miƙe daga zaunen da yake ya fara salallaɓawa ya haye saman dutsen shi ma. Tun bai ƙarisa zuwa wajen ɗan kogon da ya gani a wajen ba ya fara jiyo muryarta tana magana kamar haka.

"Ba ni ce na kawo maka aikin ba dama? Ai kuɗina na biya, dan haka na ce ka warware wannan aiki, idan kuma ba haka ba zan shigar da kai kara ga hukuma, macuci kawai azzalumi, wlh da kai da Hauwa ba zaku ga annabi idan baku tuba ba".

Yana daga zaune saman ɗan buzunsa na tsafin ya amsa mata da. "Ke ɗin ganin annabin zaki yi ne aka ce maki? Nasan kin san da cewa idan mutun ya je wajen boka ba tare da ya yi aiki da abin da bokan ya faɗa ba, zuwa kawai ya yi sallarsa ta kwana arba'in Allah baya karɓa, kin san da haka kuma ai kika zo nan har kika yi amfani da abin da na faɗa na kuma baki, ke muma fa ba wai jahilai bane, bari ki ji in gaya maki gaskiya kafin ka zama cikakken boka sai kana da hadda Alqur'ani mai girma a kanka, sannan sai ka san fassarar ayoyin cikinta, babu wanda Allah ya kafurta a Alqur'ani mai girma har sau biyar sai boka!! Mun san komai kawai take sanin muke yi domin biyan buƙatar kanmu! Kuma hakan ce kaddararmu, Alqur'ani da kike ganin nan tun daga farkon duniya har karshenta akwai magungunar duk wasu cuta da suke a duniya a zamanin da ya shuɗe da kuma yanzu har ma da cutar da zata bayyana nan gaba wadda namu sani ba, Allah bai saukar da cuta ba sai da ya saukar da maganinta, kowacce aya a cikin Alqur'ani da kike ganin nan tana da dalilin sauketa, dan haka ki sani ba wai da ka muke komai ba, duk wani sihiri da zamu haɗa in dai da gaske so muke taci to dole sai da Alqur'ani, dole sai da wasu ayoyin da Ubangiji ya saukarwa mutanen da suka gabata domin kawar da matsalarsu, to mukuma da ita muke amfani domin hassasa matsala cikin al'umma, sihirin da yake jikin mijin kurciya ce, sihiri mai wuyar warwaruwa kenan, ba kamar sauran sihiri da kika sani wadda zata yi kwana arba'in ko makamancinta ta kwance bane, wannan babban aiki ne, dole idan za'a kwanceta sai an dawo da kurciyar, sannan tsakanina da Hauwa akwai amana, dan tana mun abin da ba kowa ba, sai dai idan zaki yi mun abin da take yi mun sai na duba na gani.......".

Zaro ido maman Zainab ta yi tun lokacin da ya fara jawabinsa, kenan dama sun san gaskiya shegu?. Ni kuwa na ce kwarai kuwa babu abin da basu sani ba, shiyasa idan Allah ya tashi kamasu suke cin ubansu! Domin da sanin komai suke aikata duk abin da suke aikatawa, Allah baya kama bawa a cikin aikin rashin sani, amma ka sani ka take sani babban laifine wanda idan Allah ya tashi kamaka baya yi maka ta daɗi, babu wani ɗan iskan boka da ya isa ya yi sihiri ba tare da ayoyin Alkur'ani ba, dan haka ilimi ne da su sarai la'anannun tsinannu, kafirtasu da Ubangiji ya yi har sau biyar a cikin Alqur'ani ma duk sun san da haka shegu, sun karanta kuma sun karanci tafsiri, sun san fassarar ayoyi da dama, wasu ma sun san fasarar kowace aya shegu, amma a haka suke take sani suna cutar da bayin Allah, su yi asiri su ɗaurawa wata cuta, wata su haukatata ta shiga duniya a sake samun wasu la'anannu su yi amfani da ita a haukace dan biyan buƙatarsu suma, kuma duk bokayen ke saka hakan, ga shi nan dai abubuwa kala kala, ga cin zarafin Alqur'ani mai girma da suke yi, wata zasu rubuta mata suratul ali'imran su haɗa da magungunansu su ce ta wanke gabanta da shi, wannan ɓangaren sun fi yiwa karuwai wai dan su kara ɗanɗano, kun ga laifi kan laifi, ga bokanci ka taimakawa zinace zinace ta kara yaɗuwa, wani lokaci su rubuta wata sura daga cikin Alqur'ani mai girma su wanke suce mace ta yi wanka da shi, haka zata je cikin toilet wajen najasa ta yi wannan aiki, wani lokaci da jinin al'ada kazanta zasu rubuta Alqur'ani mai girma su wanke su bawa mace ta baiwa namiji, wani lokaci su rubuta wata sura a paper su ce mace ta sanya a gabanta, aiki dai kala kala na cin zarafin Alqur'ani mai girma duk yinsa suke yi, kuma sarai sun san hukuncin da yake jiransu na yin wannan ɗanyen aikin, amma da yake sheɗan ya yi wa Allah alkawarin sai ya samu parsinjoji na tafiya wutar jahannama, sai ya bi ya yi ta kaɗa masu gangan a kunne yana gaya masu cewa kada su damu su yi ta aikata fin hakan ma, idan sun zo mutuwa sai su tuba, haka sheɗan yake ruɗarsu, su yi ta tsula siyarsu a zuwan zasu tuba kafin mutuwa, sai su fake da cewa ai Allah gafurun rahim ne, sai dai sun manta shi Allah ba'a yi mashi wayo, wane mutun, san da zasu mutu ma basa sani bare har su tuba, time da zai kamasu ma basa sani bare su tuba shegu!!!.

Ganin maman Zainab ta zaro idanu tare da luluƙawa duniyar tunani ne yasa bokan ya sake ce mata. "Kada ki damu mu wannan ita ce kaddararmu da Allah ya kaddaro mana".

Wani irin matsiyacin kallo ta bishi da shi kafin ta ce. "Kuka dai kaddarawa kanku, Allah kam bai ɗaura maku wannan kaddara ba, kowani ɗan iska sai ya gama shirga iskancinsa, ya tsula tsiyarsa son ransa sai ya ce kaddararsa da Allah ya kaddaro masa kenan, to shi dai Allah baka isa ka yi mashi karya kuma ka zauna lafiya ba, azzaluman banza kawai..........."

Dakatar da ita ya yi ta hanyar daka mata tsawa ba tare da ya bari ta gama amayar da zafafan zantukan da suke ƙunshe a cikin cikinta suna cizonta ba.

Maman Zainab akwai karfin hali, ko tsoron wannan boka bata ji ba, ɓacin rai yasa ta fara zazzaga mashi masifa ba tare da jin tsoron kada ya yi mata wani abin ba, bugu da kari tana zaune a cikin muhallinsa tana kwashe mashi albarka.

"Dakata Hajiya, idan maganganu marasa daɗi kika zo gaya mun to tun wuri ina umartarki da ki fita a cikin wajen nan tun ban sauya maki halittar jikinki ba, sha sha sha kawai, ke har kin isa ki zo har in da nake ki ce zaki gaya mun magana? To idan ba aiki zaki kawo mun ba kada na kara ganinki a nan, idan ba haka ba kuma sai na mayar dake kwaɗo ko kunkuru". Yana maganar yana wani irin muzurai da ido, yadda kuka san kwarton da soja ya kama a gidansa, irin shi zai tsoritatan nan, ga idanun nasa jajir da su kamar mutun ya kwakwalesu ya jefar saboda muninsu, hancin nan nasa ba'a magana, a bage yake a saman fuskarsa kamar kan fanfo, ga shi bakin kirin kamar zunubi, bakinsa kamar waga.

Kasancewar ta zo ne domin a kwance wannan aiki da hauwa ta yi wa baban Zee, sai ta ɗane zuciyarta, ta daure ta sassauta muryarta tare da ƙoƙarin kawar da ɓacin ranta ta fara magana a nutse. "Ni ba dukka wannan ne ya kawoni ba, aikin da ka yi wa mijina kawai nake son ka kwance shi kamar yadda ka yi".

To kun san bokaye basu da sirri, dan haka sai ya ce mata. "Ni da Hauwa akwai amana a tsakaninmu, amma idan zaki bani abin da take bani sai na warware".

Da sauri ta amsa mashi da. "E zan baka menene?".

Ba wani ɓoye ɓoye bare kunya ya baje mata komai a faranti. Kanta zata bashi, dan shi ne abin da Hauwa take bashi yasa ya riƙe mata amana, har da wani ɗaurawa da cewa. "Ke kin ma fi Hauwa sura da kaya, kin ga da kin bani sai na warware aikin, kuma zan riƙe maki amana".

Ni kuwa nace wani amana kuma? Na tabbata ita ma Hauwa hakan ya ce mata idan ta bada kanta zai riƙe mata amana, amma ga shi yanzu saboda yaga maman Zainab ta fi hauwa komai da komai har ya tonawa Hauwar asiri, kuma idan da maman Zainab zata bashi kan nata tsab zai iya kwance aikin nan da ya yi wa Hauwar, kun ga kuwa a nan ina amana fisabilillahi? Ko da yake duk aikin da aka ce maka ya saɓawa Allah da Manzonsa ai babu wani amana da tausayi a cikinsa face danasani da nadama maras amfani!!.

Wani irin mahaukacin razana maman Zainab ta yi da jin maganganunsa, nan take ta ji wani irin jiri yana neman kwasanta, wa'iyyazubillah ta furta kusan sau uku. Wani irin tsinanne kallo ta fara bin bokan da shi, wani ƙazami da shi, ai wannan da ta haɗa shinfiɗa da shi gwara ta mutu, da wasu garmar hakwaransa da baya brush kamar na shanu. Wani irin muguwar tsanan Hauwa haɗe da baban Zainab ɗin ne dukka ya kamata, ji ta yi wlh zata iya hakura da baban Zainab har abada tun da ya haɗa shinfiɗa da Hauwa da ta sallamawa wannan ƙazamin la'anannen Allah kanta, waye ya sani ma ko yana ɗauke da wata cuta tun da ya nemeta hakan yana nufin ba da iya Hauwar kawai yake kwanciya ba, yana keta mutuncin mata da dama, daga gani halinsa ne, da wuya kuma idan bai da wata cutan.

Wani irin ƙululun bakinciki ne ta gangaro mata har wuya, kanta dake sara
End Ads