x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 75 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 222001 words
  • 225000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 362

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
dan ƙasa ta yo. Dakatawa da yin karatun ta yi tana zaro idanun nan nata da suke kara fito da tsantsar kyanta.

"Kamran menene yake kara har haka?". A tsorace ta yi maganar.

"I don't know, amma mu je mu duba mana mu gani". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta, shi fa ko tsoro baya ji, wai su je su duba, ita dai Sweetie baiwar Allah tana ciki abinta, ba ruwanta da yawace yawace har sai idan ya zama dole.

"Kamran ina tsoro fa". Ta faɗa tana ƙanƙame hannunsa tare da kara zaro idanu.

Sauƙowa ƙasa daga saman dutsen ya yi tare da juya mata faffaɗar bayansa a kan ta hau ya goyata yana faɗin. "Kada ki ji tsoron komai my Pretty, ina tare dake, mu je muga menene yake kara har haka?".

Ba musu ta haye bayan nasa tana murmushi, idan da sabo ai ya saba goyonta, dan haka sai ta ɗale abinta tare da saƙalo wuyarsa ta kwantar da kanta a gefen shoulder ɗinsa, sai murmushi take saki dimple ɗinta na lotsawa, ga ruwa na zuba mata daga tsakiyar kai, kyalkyawar gashin kanta sai zubar da ruwa yake yi.

Kai tsaye Kamran ya nufi ta wajen da suke jiyo wannan kara a tare da ita. Sai hira suke yi gwanin birgewa har suna ɗan yi nisa. Suna tafiya suna kara jiyo wannan sauti tana kara matsowa kuma tana kara karfin kara.

Sai da suka sake matsawa kusa sosai suka fahimci ashe sautin ƙugin igiyar ruwace mai karfin gaske ne, da alama katafaren teku ce a wajen wadda ta cika take ambaliya sanadiyar wannan ruwan saman, igiyar ruwace ke ƙugi.

A hanzarce ya ƙarisa matsowa sosai, babu ko shakka bare tsoro ya nufi waje. Wannan katafaren tekun nan wanda mum ɗinsu ta faɗo daga ɗaya daga cikin duwatsun dake kewaye da tekun nan ne, sai dai a yanzu iya gane daga ta ina mum ɗin nasu ta fito har ta faɗo ta wannan waje abu ne da ba zai yi wu ba, su bama su san daga ta wajen ta fito ba, so sai basu wani damu ba. Mamaki ne kawai ya bayyana a saman fuskokinsu na ganin tekun a dajin bai sani ba.

Duk zaman Kamran a wannan daji bai taɓa sanin wannan teku ba, sai dai kananan ruwa dake ta wajen tsauninsu, ashe akwai teku mai girman da idan ka bi cikinta zaka je ƙasashe da dama.

"Kamran saukeni na ga tekun nan da kyau". Ta faɗa tana zaro idan, yadda igiyar ruwa ke juya tsakiyar ruwan tekun kawai take kallo. Shi ma Kamran ɗin abin da yake gani kenan, abin ya ƙayatar da su kuma ya basu mamaki sosai. Ba musu ya sauketa dan ta yi kallo da kyau.

"Pretty ina ganin kamar wannan teku ta nan ce hanyar fita daga cikin wannan Forest ɗin ko?".

Ya faɗa yana dawo da kallonsa a kanta, ya jima yana neman hanyar da zata fitar da shi wannan Forest ɗin cikin sauki, ita kuma wannan teku abin da bai sani ba ta kasance kamar border ce, iya kar ƙasashe da damane a wajen, sai dai tabbas ita ce hanyar da zata iya kaisu cikin babbar ƙasar, kuma dai kada ku manta su su Pretty ta nan mum ɗinsu ta fito, kunga hakan na nufin koma dai me ta nan garinsu or ƙasarsu yake. Akwai cakwakiya kenan, da alama su Pretty zasu kai kansu in da ake nemansu ruwan ajallo idan suka yi wasa.

Sai hira suke yi suna ta kallon yadda igiyar ruwa yake jan ruwan har sama sai kuma ya sake sake shi, hakan yakansa ruwan ta bada sauti mai karfin da har suka iya jiyowa ɗazun, sai zancen neman hanya suke yi, Kamran ya kafe a kan shi dai lallai wannan teku a akwai hanya a kusa da ita, ita kuma Pretty ta ce bata ga alama ba, domin kuwa ita dai ruwa take kallo maras iyaka, kuma wlh ita ko kasheta za'ayi bafa zata shiga cikin ruwan nan ba........😅

(Kunga laifinta? Da gaskiyar ruwa ba iyaka haka ace su shiga su ketare?🤔 Ni dai ina bayanta, ko za'a kwasheta kada ta yarda ta shiga😅 ta bar Kamran da Sweetie su je, idan suka isko mutane sai azo da jirgin ruwa a ɗauketa😅😅 saura naji wata magana, shawara na bata🥱😎)

Sun jima tsaye a wajen ruwan sama na jiƙasu, sai da Pretty ta fara rawan sanyi ne ta dube shi. "Kamran sanyi nake ji sosai".

Juyowa ya yi da kallonsa a kanta. "Zo na goyaki mu koma, gobe dole mu dawo wannan waje".

Da sauri ta faɗa jikinsa, sai rawan sanyi take yi sosai, shi ma dai zubar ruwa yake yi.

Ɗagata sama ya yi tare da maida ita bayansa, ya goyata kamar yadda suka zo, dan wannan yarinya ba iya tafiya da kafafunta zata yi cikin bishiyoyi da ciyayin nan ba, sai ta ɓata masu lokaci basu isa in da za su je ba, kuma dama shi Kamran yana jin daɗin goyata idan zasu je yawonsu, saboda hakan zai sa su yi tafiya mai nisa ba tare da ɓata lokaci ba.

Nufar hanyar komawa suka yi, ta kwanta shiru a bayansa tana rawan sanyi, ta wani ƙanƙame mashi wuya. Shi kuma sai tafiya yake yi.

Ko da suka isa bakin ramin nasu sai ya sauketa, miƙo mata wani irin nau'in fruit nasu dake a cikin dajin mai kama da ruman mai kuma kama da Apple haka yake ya yi, ya miƙo mata tare da cewa. "Ina sonki sosai Pretty, ki koma ki cire kayan jikinki ki canza wasu kada sanyi ya kamaki, nima zan je gida, sai gobe, kada fa ki sake fitowa, gobe za mu je yawo sosai".

(Ko a ina ya samo wannan fruit ɗin?🤔 Kila a hanya ya ciro da suna dawowa)

Karɓar fruit ɗin ta yi tare da cewa. "Nima ina sonka Kamran, amma fa gobe kazo da wuri ka ji?".

Jinjina mata kai kawai ya yi, sam baya son rabuwa da su, ji yake yi a wannan yanayi kamar kada ya koma gida, amma ina babu dama, ba hali dole ya koma idan yana son cigaba da kasancewa da su.

Shiru ya ɗan tsaya ya kasa tafiya.

"Kamran lafiya ka tsaya shiru? Ka tafi mana". Ta faɗa tana kallon face ɗinsa.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan ƙaƙalo murmushi kaɗan. "Babu komai Pretty, kawai ina tunanin rabuwa da ku ne, bana son komawa gida na barku".

Shiru ta ɗan yi itama, jikinta ya yi sanyi, har ga Allah bata son rabu da shi ita ma, amma ya zasu yi? Dole su rabu, idan ba haka ba su jawa kansu rabuwa ta har abada.

"Nima bana son ka tafi Kamran, nafi son kullum ka kasance a tare da mu, idan ka tafi bana jin daɗi, ina jin kamar bani da lafiya, duk sai in ji wajen zamanmu ya yi mun zafi babu daɗi, shiyasa ka kallah ina fitowa waje in zauna idan baka nan, bana jin daɗin zaman cikin ne". Tana magana kamar zata yi kuka.

Ɗan rungumota a jikinsa kaɗan ya yi tare da shafa kanta dake ta zubar da ruwa. "Idan nazo gobe zamu yi magana, yanzu kinga kije ciki kada sanyi ya kama mana ke, ki canza kaya kin ji ko? Ki gaishe da Sweetie sosai".

Rungume shi ita ma ta yi kafin ta sake cewa. "Goben fa kada ka daɗe, kazo da wuri".

Okey ya amsa mata da shi, sannan ya saketa tare da ce mata ta shiga ciki. Ba musu ta shige ciki, sai dai ta shige ne tana ruwan hawaye, kuma ya lura da hakan, kawar da kansa kawai ya yi, saboda dalilai guda biyu, na farko baya son ya cigaba da tsayar da ita cikin ruwan nan ga kuma ɗanyen kaya a jikinta, sanyi zai kamata, na biyu kuma baya son kara jan lokaci da su kada mamma ta tashi daga barci ta farga baya nan, hakan yasa ya kawar da kai tamkar bai ga tana kuka ba, amma ya ji zafin hakan sosai a cikin zuciyarsa, sai ya ji kamar shi ma ya yi kukan ko zai ɗan ji sanyi a ransa.

Haka ya juya jiki ba kwari ya nufi nasu gidan, yana tafiya yana tunanin hanyar da zai bi ya isa ga mutanen dake wajen dajin nan, sannan yanzu kuma tunanin mahaifinsa ta yawaita mashi a cikin zuciyarsa, ji yake yi lokaci ya yi da yakamata ya tambayi Mamma ina babansa? Tun da yanzu ya gano cewa ba iya macece kawai take haihuwa ba, dole yana da baba, to ina baban nasa? A gaskiya yakamata Mamma ta gaya mashi in da mahaifinsa yake, kullum da wannan tunani yake kwana kuma yake tashi, sai dai ya rasa ta ina zai fara tunkara Mamma da zancen. Tashin hankali kenan.

Tafiya yake yi sam bashi da wani kuzari a jikinsa, da haka ya isa gida. Yana zuwa ya wuce nashi makwancin, kayan jikinsa ya fara kwaɓewa tas. Yana da kyan jiki kam kamar madara duk da Mamma ta fishi haske nesa ba kusa ba, da alama babansa ya yo a kalar fata, fari ne fa shi ɗin ma, amma a gaban mamma gaskiya ba fari bane.

Canza kaya ya yi tare da kwashe waɗan nan ya kai su in da suka dace, ya sanya kaya masu nauyi sosai saboda sanyi, sannan ya kwanta ya ɗauko Alqur'ani da ya ɗauka wajen su Pretty ya fara dubawa yana karantawa, bai leƙa Mamma ba. A lokacin ita kuma ta tashi daga barcin tana cikin madafarta, tana aiki, tasan da cewa ya fita bayanan, domin tana farkawa daga barci makwancinsa ta fara leƙawa dan ta duba shi, sai ta taras baya nan, so bata wani damu ba, dan dama da lallami ta lallaɓa shi ya dawo, so ba zata takura mashi ba.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼

GIDANSU KHADIJAH😥💔

Maman Khadija tana durkushe a wajen tana kuka Khadija na rarrashinta, bata tashi daga wajen ba sai ji ta yi an sake banko masu kofar gida.

Bata kula ba, haka zalika bata bi ta kan son sanin su waye bane, ita masifar da take a ciki ma ya isheta, dan haka sai ta cigaba da rera kukanta da sauti baya fita sai dai ruwan hawaye.

Banko labulen kofar aka yi aka shigo, maman Haidar ce da Maman Hanif sai Hajiyarsu, Haidar yana tsaye daga bakin kofa, shi ma Sadiq ya fito ya tsaya a bakin kofar ɗakinsu yana kallon cikin parlourn, abin da ya fito da shi kuma shi ne irin yadda ya ji sun banko masu cikin gida babu mutunci, so yana tsoron kada su yi wa ƴar uwarsa wani abin, shiyasa ya fito, shi dai yana ganin bala'i kala kala bawan Allah, daga nasu maman Haidar yanzu kuma an koma na Hauwa, wannan irin jarbawa sai ka dage zaka iya cinta, Allah yasa maman Zee tana da juriya da karfin imanin iya cinye jarabawarta.

Tana durkushe tana kuka maman Haidar ta fara surfa mata ruwan bala'i a kan ina su Hauwa ɗin suke? Ta fito masu da baban Zainab ita kuma.

Wani irin kallon takaici mai haɗe da tsananin ɓacin rai maman Zee ta wurga masu. Cikin ɓacin rai da fusata ta ce. "Saboda ni kuka raina shi ne dan kinga ni kaɗai ce zaki fara mun hargagin banza ko? Meyasa ɗazun da kika samu Hauwar baki yi mata ba kika yi shiru? Yanzu dan kinga bata nan ne zaki ce na fito maku da baban Zainab? To na cinye shi ɗanya, sai ku fasa cikina ku ciro shi!!". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye, idanunta jajir kamar wuta, yau tasha kuka, kuma a cike take har wuya da bakinciki, idan su maman Haidar suka yi wasa tana iya yi masu hauka, dan Hauwa ta sanya zuciyarta yanzu ya fara bushewa ta dai'na ganin mutuncin kowa, zuciyarta ta kusa fashewa ta fito waje. Tashin hankali, yanzu wasan zai fara!!.

"Ke Aisha ni kike gayawa magana yau? Ni nake magana kike mayar mun da amsa? A lallai kam kan mage ya fara wayewa". Cewar maman Haidar.

"Ke ɗin nake gayawa, an gaya maki ɗin, zaki iya yin duk abin da ya zo maki cikin wannan banzar ƙwaƙwalwar taki, sannan kuma ke dama a tunaninki rashin wayewa yasa bana mayar maki da martanin duk abin da kika yi mun ko? Ko kina tunanin ina jin tsoron ki ne? To idan ma haka kike tunani kin makaro, tarbiya da ilimi dana samu daga wajen iyayena ne yasa nake darajaki a matsayinki na yar miji, nake baki girma kamar yayata uwa ɗaya uba ɗaya, nake kuma ganin mutuncinki, amma yanzu tun da abin yazama babu mutunci, to kuwa zaki ga ainahin wacece A'isha! Yanzu baki isa kiyi mun na kyale ki ba wlh, a baya kin ci banza, amma yanzu zan nuna maki ba wai ban iya rashin kunyar bane, tarbiya muka kwankwaɗa muka ƙoshi, a gidanku kuma kuka shayar da ni ruwan kwatar ƴancina, to yanzu na sha na ƙoshi, duk wanda ta shirya mu buga to ta zo mu buga daga nan har illa Masha Allah, in dai bata gaji ba, to nima ba zan gaji ba! Duk wadda ta ce mun kule sai na ce mata cas, na dai'na yin shiru tun ba mutuncin kuke so ba!!".

Shiru ita dai maman Hanif ta yi, dan ita dama ba wai ta cika shiga irin wannan shirgin bane, kawai ba yadda ta iya ne, idan maman Haidar ta yayuɓota dole ta biye mata, ko dan ma Hajiyarsu, idan bata shigarwa maman Haidar ba ya zama dole ta shiganwa Hajiyarsu.

Gadan gadan cikin fushi maman Haidar ɗin ta nufeta da nufin ta kai mata mari. Ai kuwa maman Zee bata yi ƙasa a gwiwa ba ta yi cap ta rike hannun nata.

"Wlh idan kika kuskura kika ɗaura hannunki a jikina sai na rama, ashe rashin kunyar taki sai kinga wargi kike yi, meyasa baki yi wa Hauwa ba? Kika yi shiru ta gama cin maki mutunci baki da wani kataɓus! Meyasa kika ja baki kika yi shiru a gabanta? Sai ni zaki yi wa hargagin banza? To nima na dawo daga rakiyarku wlh!!".

Ƙoƙarin kwace hannunta ta fara yi, amma ina maman Zee taki sakar mata hannun, ji take yi ma kamar ta kife munafuka da mari, so take ta sauke haushin da Hauwa ta cusa mata a kansu.

A fusace Haidar ya shigo cikin ɗakin, a haukarsa da rashin hankalinsa wai zai daki maman Zainab ɗin. Ai kuwa yana zuwa Sadiq ya tare shi, dan kuwa ya biyo bayansa, saboda yasan halinsa sarai, tun da yaga ya shige cikin parlourn yasan ba zasu yi da kyau ba, shi kuwa ba zai bari su taɓa mashi ƴar uwa ba, tun da faɗar ba'a kan ƴaƴa bane tsakaninsu da ƴar uwarsa ce yana da damar saka baki ya tare mata, da ace faɗar a kan su Khadijah ne to fa bashi da bakin magana, amma a kan ƴar uwarsa yana da bakin magana. Aikuwa ya tare mata a in da ya ce wlh in dai Haidar ya ɗaura hannunsa a jikinta yau sai ya gwada mashi banbancinsu, jahili wanda bai san me yake yi ba, angaya mashi ana taɓa matar aure ne? Matar mutun kawai kasa hannu kace zaka daketa, ai ko kotu aka je in dai shari'ar musulunci za'a bi sai a ɗaureka har igiya ta yi saura a kan hakan.

Da farko Haidar ɗin ya so kama Sadiq ɗin da kokawa. Amma ina Sadiq ya nuna mashi ya fishi hankali da sanin ciwon kansa a in da ya ce da maman Zee ta wuce cikin bedroom ɗinta ta rufe kofa ta rabu da su, idan suka gama hauƙarsu ba'a kulasu ba za su kama kansu.

Da sauri ta wuce cikin room ɗinta, ta bi maganar ɗan uwan nata. Tana jiyo muryar Hajiyarsu tana cewa to ai ba gidan ubanki bane da zaki shige cikin ɗakin, ki fito ki tafi gidan ubanki marasa kunya marasa tarbiya, wlh sai kin bar gidan nan tun da ku baku da albarka dangin matsiyata, dole ya zo ya sakeki ki wuce gidan ubanki tun da har da ni zaki yi wa rashin kunya, dan kin rai'na taki uwar.

Wato ita fa Hajiyarsu bata san cewa yanzu fa baban Zainab bayan Hauwa baya jin maganar kowa ba, har da wani cewa zata sa ya saki maman Zainab, wlh ana show a wannan gida, ana rikici, ko ya tsohuwar nan zata ji lokacin data ga Hauwa na juya mata ɗa? Mu dai ana yi muna shan Maltina.

Ko juyowa maman Zee bata yi ba bare ta kallesu har ma ta kulasu, tana jin hajiyar tasu ta ce kada ta yarda ta shiga cikin bedroom ɗin nan ta zo ta wuce gidan ubanta, amma ina ta wuce ciki ta banko masu kofa da karfi tare da murza key abinta, irin bata da lokacin sun nan.

Shi ma Sadiq sa kai ya yi ya wuce ya fita abinsa, dan bashi da lokacin biyewa haukarsu a cewarsa, shi a mahaukata ma yake kallonsu, idan sun ga dama su kwana a cikin parlourn suna surfa masifa su dai suka sani, shi dai ya kama kansa abinsa. Baban Zainab ma yanzu ba samun damar ganinsa zasu yi ba bare har su ce ya saki maman Zainab ko su gaya mashi ta yi masu rashin kunya, idan ma sun sami damar ganinsa to ko kallo basu isheshi ba, shi da yake ta Hauwa ina ruwansa da su? Idan ma suka yi wasa sai ya haɗa masu da zagi da kuma duka koma ya ce bai san su ba. Tirƙashi, ana cakwakiya a gidan baban Zainab fa sosai.

Haka suka yi ta surfa uban masifa mai isarsu, da dai suka ga ba mafita sai suka kama kansu, dama shi Haidar already ya bi bayan Sadiq da nufin ya je ya kama shi da faɗa, amma ina Sadiq ɗin yaki biye mashi, dama yaga zai takura mashi sai ya ɗauki wayarsa ya fice daga cikin ɗakin, ya bar masu gidan ma gabaɗaya, sai dai bai yi nisa da gidan ba, dan yana tsoron ya yi nisa kada su yi wa maman Zainab ɗin wani abin.

Haka suka yi ta haukarsu har suka gaji suka hakura suka tafi. Ita kuma maman Zainab tana shiga cikin ɗaki ta ɗauki waya ta kira mamanta dan ta sanar da ita
End Ads