x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 357

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ziyara sai ka ɗauka wani hamshakin biki ake yi, su yi ta murna suna farinciki.

Sai shirin zuwa wajensa gabaɗaya ƴaƴan king Zuhair suke yi, Gimbiya Chuchu da ta fi kowa zaƙuwa ta gansa sai ƙoƙarin shiri take yi, yanzu ta fito daga wanka, ɗaure take da ɗankaramin towel da bai gana rufe mata cinyoyinta ba, tana rike da haɗaɗɗiyar wayarta kirar iphone 15 pro max, sai ɗaukar hoton face nata take yi.

A duniya Chuchu tana kaunar hoto, ko barci ta tashi sai ta ɗauki kanta a hoto, ita bata da wata matsala a rayuwarta, bata bi da kan kowa, gata da shegen son gayu, ga bala'in son jiki, kamar mage haka take, komai da kuka sani kuyankunta suke yi mata, wanka da saka kaya ne take yi da kanta, sai sallah da cin abinci, banda haka tsabar son jikinta bata son ɗaga koda tsinke, sai dai ta cancaɗa kwalliya ta haye saman bed abinta, gimbiya Chuchu ƴa ce ga Mummy, wato uwar gida kenan, kanwar Jaruma Gimbiya Raseesa ce, sai dai ita Chuchu bata da jarumtar, sai lalaci da son jiki, bata gado ƴaƴarta da mahaifinta king Zuhair ba, raguwa ce mayyar son jiki.

Sai kashewa kanta hoto take yi abinta, a ɓangaren Akka take, dan ta fi yawan zama a wajen, part na mamanta ma idan kun ganta a wajen to wani abin ta je ɗauka, kullum tana part na kakarta abinta. Hakan yasa kayayyakinta da sauran abubuwanta suka yawaita a part na kakar tata.

Sai da ta ɗauki hotunanta kala kala wajen kala goma, a haka ma wai tana sauri zata je wajen uncle Abbas ne, badan haka ba da dani da ku ba zamu iya kirga hoton da ƴar tahaliƙarnan zata ɗauka ba, dan mayyar hoto ce.

Wasu irin shegun tsadaddun lotions ta shafa a jikinta, tana shafawa tamkar bata son taɓa skin ɗin nata, saboda shegen son jiki, bata son wahala yarinyar nan sam, bata son abin da zai taɓa wannan kyakkyawar jikin nata.

Wasu tsala tsala kaya ta ɗauko, doguwar riga ce wadda ta sha kwalliya na wuce misali, kasancewar ba wata babba bace sai bata sa breaziya ba, dan bata wuce 14 years ba a yanzu, bata saka bra, haka take tsara kwalliyarta abinta, sai dai fa da yake akwai ta da halittar jiki mai kyau, idan ka kalleta sai ka yi tsammanin 16 years take da shi, tula tulanta suna cike fam da su, ga shape sosai tana da shi.

Tana ƙoƙarin zura rigar a jikinta bayan ta zuge zip ɗin kasa ne karfen bayan wuyar rigar ya maƙale mata a gashin kanta, da yake babu ɗankwali a kan nata, ta tara wannan gashin nasu na larabawar ta ɗaure a tsakiya, ta zuba jelar a bayanta, hakan yasa karfen rigar ta iya kama gashin nata.

Ƙoƙarin cirewa ta fara yi, amma ina ta kasa, ga rigar ta rufe mata fuska. Sunan Gimbiya Zunaira ta fara kira, dan tasan ita ce kawai za'a samu a part na Akkar by this time around.

Tana ta ƙoƙarin cire karfen tana kuma kiran sunan Zunaira. Shiru Auta bata amsa mata ba, bata ma san cewa auta kam tana fada a halin yanzu ba, tana can ta haye jikin uncle Abbas tana zuba shagwaɓa abinta.

Ƙoƙarin jan rigar ta yi ta cire shi daga saka shi da ta fara yi, a tunaninta idan ta cire rigar zata iya cire karfen daga gashin kanta.

Bata kai ga cire rigar ba ta ji an sanya hannu ana ƙoƙarin cire mata karfen da ya kama gashin nata, rigar ta rufe mata idanu, bata iya ganin wanene?.

"Auta tun ɗazun ina ta kiran sunanki sai yanzu zaki zo ba? Da na faɗi fa? Kina ganin sai da na fara zura rigar a jikina karfen ta saƙalomin gashina, rigar ta ki wucewa ta karisa shiga jikina, ta tsaya ni baga saka riga ba ba kuma ga iya cireta ba, idan nace zan tafi izuwa wajen Akka kuma faɗuwa zan yi".

Tana maganar ne ba tare da ta san wanene a wajen ba, a duk tunainta auta ce.

Cire mata karfen rigar ya yi tare da karisa saukar mata da rigar a jikinta, sannan ya sanya kyawawan hannayensa yana mai ja mata zip ɗin rigar sama kafin ya kama wannan ɗan karfen da ya saƙalo mata gashin kan nata ya haɗa shi da ɗan uwansa ya mannesu, dama kamar botir suke.

Da sauri ta juyo dan jin kamshin perfume nasa bai yi kama dana auta ba, bugu da kari kuma ba a amsa mata maganar da ta yi ba, da auta ce to tabbas zata amsa mata maganar tata.

Tana juyowa suka yi ido huɗu da Jawad, tsayayyen namiji mai jini a jika, matashi mai 25 years a duniya, ɗa ne ga uncle Abbas, shi ne second born nasa, kyakkyawa ne sosai, ba sai na sake gaya maku ba, gabaɗaya ƴaƴan Akka wato mahaifiyar king Zuhair, ƴaƴanta kyawawane, haka zalika ma jikokinta, cikakkun larabawane jinin Modarawa, hakan yasa suke da kyau sosai kamar su suka yi kansu, sai dai wannan yafi wannan kyau, wannan kuma ya fi wannan haske, haka suke!.

Ɗan kasa kaɗan ta yi da kanta tana ƴan kame kame, dan duk a tunaninta auta ce, da ta san shi ne ba zata yarda ya saka mata kayan ba, wani tunani ne ya faɗo mata cikin ranta, yanzu shikenan Yah Jawad ya kalleta daga ita sai towel? Waye ma yasan tun yaushe yake wajen? Kila tun da karfen ya riƙe mata gashi yake kalleta.

Shiru ya tsaya yana kallonta ba tare da ya yi magana ba, sai ma zura hannayensa da ya yi a cikin aljihun wandon suit dake a jikinsa, da alama daga office ya fito, dan shigar zuwa wajen aiki ne a jikinsa, white suit ce mai bala'in kyau, sai white cover shoe masu bala'in tsada a kafafunsa, daga ta ciki kuma safa ce baka, kyakkyawar bakin gashin kansan nan a kwance luf, ta gaba har gaban goshinsa, ta baya kuma har bayan wuyarsa, sai sheki gashin yake yi, ha sha gyara, ga wani daddaɗar kamshin da yake zubawa.

Daga Akka har marigayi King ABDUL MALIK duk suna da tsawo sosai, hakan yasa daga ƴaƴansu har jikokinsu suke da tsawo sosai, so haka shi ma Jawad yake da tsawo, ga cikar kirar karfi na lafiyayyun maza.

"Yah Jawad ina wuni?".
Ta faɗa murya na kerma, dan ita tsoronsa ma take ji, saboda bashi da wasa da yara, kuma bashi da yawan magana, haka zalika sam bashi da fara'a ko kaɗan, wannan dalilin yasa suke jin tsoronsa.

Nisawa ya yi ba tare da ya amsa mata gaisuwar tata ba, sai cewa ya ya yi.

"Meyasa baki rufe kofar ɗakin ba?". Kasa kasa ya yi maganar.

Cigaba da muzurai ta yi tana wani ƴan kame kame, sam bata san lokacin da ta fara murza ƴan yatsun hannunta ba, dan bata da abin yin da ya wuce haka.

"Am.... In... Dama na manta ne.... Kuma dama muna tare da auta ce, ta ce mun tana zuwa ne ta fita, shiyasa ban rufe kofar ba, dan ina tunanin zata dawo".
Yadda take magana muryarta na rawa, words ɗinta suna rarrabewa, hakan zai kara tabbatar maka da ba ƙaramin tsoronsa suke ji ba, dan fa da gaske ne bashi da wasa kuma baya ɗaukar wasa.

"Lafiyarki kam ko?". Ya tambaya yana mai cigaba da kallonta, ya ji ne sai famar in'ina take yi mashi a magana, sai ka ce ya ce zai zaneta ko wani abin, duk ta bi ta ruɗe mashi.

"Lafiya lou".

Ta bashi amsa still voice nata na kerma.

"Ina zaki je haka? And ina Akka? Dan na shiga ɗakinta bata nan?".

Sai a lokacin ta ɗan ɗago da dara daran idanuwanta a hankali dan ta saci kallonsa, jin bai yi mata tsawa ba, ya yi magana cikin sanyi murya, kuma bai ce ta yi laifi ba, sai hakan yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Ajiyar zuciyar da ta sauke sai da yasa shi ya ɗan kara kwanto da kansa kaɗan yana kallon face nata, ya fita tsawo sosai, so a yadda ya tsaya a gabanta ɗin baya samun damar ganin face nata da kyau, sai dai tsakiyar kyakkyawar bakin gashinta yake kallo.

"Akka ni ban san in da ta yi ba, ɗazun dai na barta a cikin bedroom nata".
Ta bashi amsa tana lallaɓawa a hankali tana ɗago idanunta dan ta saci kallonsa, tana son ganin yanayin face nasa.

"Ke kuma nace ina zaki je haka?". Ya yi maganar yana ɗan ja baya daga kusa da ita, saboda ya sami damar ganin face nata da kyau.

"Part na Mammie zan je, uncle Abbas zan je gani".
Ta bashi amsa dai'dai lokacin da take ɗago idanu zata saci kallonsa. Kash bata san cewa kallon face nata shi ma yake yi ba, hakan yasa tana ɗago kai suka yi ido huɗu da shi, karaf suka kalli juna cikin ido.

Da sauri ita ta yi ƙasa da nata idanun, shi kuma still dai yana kallonta bai cire idonsa ba, ga idanun nasa kamar na Akka, manya manya kamar ball.

"Bani wayarki". Ya faɗa tare da ciro hannunsa guda ɗaya daga cikin aljihun wandon nasa.

A hanzarce ta miƙo mashi wayar, dama tana rike da wayar idan baku manta ba.

A hankali ya dawo da kallonsa a kan wayar da ta miƙo mashi. Ganin yadda hannun nata yake kerma ne yasa ya mayar da kallonsa a saman fuskarta.

"Lafiya kike kuwa?". Da mamaki ɗauke a saman fuskarsa ya wurga mata wannan tambayar, dan yaga yadda hannun nata yake ta famar kerma.

"Lafiya lou nake wlh Yah Jawad".

Shiru bai sake magana ba, ya kai hannu ya karɓi wayar tata tare da juyawa cikin nutsuwa ya nufi waje da wayar.

Yana fita ta faɗa saman katafaren bed ɗin dake a ɗakin tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, hannunta dukka biyu tasa ta dafe kirjinta dake ta faman harba mata fat, fat, fat, saboda tsoro, sai ajiyar zuciya take saukewa, tamkar wadda ta sha gudu ta ƙoshi.

Ta ɗan jima a haka kafin ta furta. "Ko me kuma zaka yi da wayata Yah Jawad?".

Auta ce ta shigo cikin ɗakin bakinta a ɗauke da sallama. Da sauri ta kariso ciki tare da hayewa saman bed ɗin tana faɗin.

"Aunty Chuchu tashi kiji me daddy da uncle Abbas suka ce".

Miƙewa zaune ta yi tana faɗin. "Rabu dani auta, kada ma ki gaya mun abin da suka ce, dan yanzu ma zuciyata a kusa take, kina gaya mun wani abin na tsoro suma zan yi, yanzun nan Yah Jawad ya fita daga cikin ɗakin nan, ba jiya Aunty Sarina ta ce ya kwace mata waya ba? To nima yau ya kwace mun tawa, sai dai ni bai mun faɗa ba, ita kuma Aunty Sarina kin ji ta ce ya yi mata faɗa sosai a kan wayar".

Cikin halin nuna ko in kula Autar ta bata amsa da cewa.
"To shi Yah Jawad me zai yi da wayoyinku da ya kwace?".

"To ko zaki je ki tambayo mana shi ne me zai yi dasu?". Ta faɗa tana zuro kyawawan kafafunta kasan gadon, dan ta miƙe ta karisa shirinta na zuwa wajen uncle Abbas.

"Kai Aunty Chuchu rufa mun asiri, ni na isa in je in ce mashi me zai yi da wayarku ne? Dama dai uncle Taheer ne ko kuma su Yah Obaid".

"Saboda kin rai'na su Obaid ɗin ba?".

Ƴar murmushi ta yi kafin ta ce. "Yah Obaid fa Momma ta ce shekaru biyun da suka bani ma bai cika biyu dai'dai ba, shekara ɗaya ne da wata takwas suka bani, yanzu su basu cika 13 years ba ai, ni kuma na cika 11 years".

Cigaba da yin shirinta ta yi tana faɗin. "E lallai auta kin girma, wato ji kike yi kusan ɗaya kike da su ko? Wlh bari Omaid ya jiki, kin san halinsa da shegen son girma, ranar har da cewa ya yi wai ya girme ni".

Dariya sosai autar ta yi, Obaid and Omaid akwai shegen son girma kamar me, sai dai kuma kash sun yi rashin sa'a sune kanana, auta kawai suka fi shekaru a gidan, amma sai su dage su ce sun fi su Chuchu shekaru.

Ƙarisa shirinta tsab ta yi, sai ta fito a cikakkiyar jinin sarauta, ta ɗauko wani dankareran alkyabbarta fara tas ta ɗaura a saman doguwar rigar tata, ga rigar launinta baki ne, sai alkyabbar ta zauna sosai, ta yi kyau sosai da sosai. Feshe jikinta da daddaɗar Dubai perfume nata ta yi kafin ta fito da wani kyakkyawar tsadadden cover shoe na ƴaƴan sarakuna ta sanya a fararen kafafunta, cover shoe ɗin launin white color ne kamar alkyabbar jikinta.

Hular alkyabbar ta sanya a kanta kafin ta nufi hanyar fita daga cikin ɗakin tana cewa auta ta zo su yafi wajen uncle Abbas.

Da saurin autar ta miƙe ta rufa mata baya. Elevator suka hau zuwa kasa. Suna sauka kasa suka nufi part na uncle Abbas ɗin, part ɗin yana ɗan gefe da nasu ne.

Ƴan'sanda da sojoji ne cike ta ko'ina a arear part ɗin, dan fa uncle Abbas babban ɗan siyasa ne wanda yake a matsayin vice president mai ci a yanzu, mulki a hannunsu take, kasancewar KINGDOM OF POWER tana da manyan ƙusoshin gwamnati da suka fito daga cikinta ne yasa masarautar ta kara karfin iko tare da karfin faɗa aji a duniya, dan babu wani gwamnatin da zai kawo masu wargi, dama can shi King Zuhair gwammati bata ishe shi kallo ba.

Duk in da suka zo wucewa sai sojoji da ƴan'sandan sun sara masu, saboda kowa yasan su waye ne su ɗin.

Kai tsaye cikin part ɗin suka nufa, kowani kofa suka je sai ɗan'sanda ya buɗe masu kofar, a haka har suka isa wajen elevator, nan ma wani ɗan'sanda ne tsaye a wajen.

Shiga ciki suka yi tare da nufar hawa ta biyu abinsu, sai hira suke yi tamkar wasu taurari, ba zaka taɓa cewa ƴaƴan kishiyoyi bane su ɗin, sun haɗa kansu sosai, da yake ma dukkansu basu da matsala, basu ɗauki duniya a bakin komai ba, ba ruwansu da wani zancen ai su ƴaƴan kishiyoyi ne, iya abin da suka sani kawai shi ne ubansu ɗaya, kuma suna girmama mahaifiyar kowa daga cikinsu tamkar ita ta haifesu, su biyun nan na ce maku sun fita zakka a cikin ƴaƴan king Zuhair, suna da banbanci dasu Fanan, Sarina and bloody sosai, bama su haɗa hanya ba.

Kai tsaye babbar parlourn uncle Abbas suka nufa, bai jima da dawowa daga fada ba, yana zaune a tare da Jawad suna hira, da alama saboda zuwan nasa ne ma yasa Jawad ɗin ha dawo daga office, ya zo su gaisa da mahaifin nasa su ɗan yi hira. Ita kuma Mammie wato mahaifiyarsu Jawad ɗin bata wajen, da alama tana cikin part nata.

A kasa saman wata lallausan Turkey carpet suka zauna, carpet nan ta amsa sunanta, ga laushi ga kyau da tsada, naunin ash color mai duhu kalar luntsuma luntsumar sofas dake a cikin parlourn, parlourn dai ba sai na gaya maku ba, kunsan ya haɗu over, ya ji komai na more rayuwa.

Jawad yana zaune a saman sofa mai zaman mutun biyu, shi kuma uncle Abbas yana zaune a saman sofa mai zaman mutun uku, babu maraba a tsakanin fuskar Jawad da ta mahaifinsa, suna kama sosai, sai dai Jawad da yake sabon jini ne ya fi uncle Abbas kyau sosai, kyansa ya fi fitowa sosai.

One think about familyn marigayi King ABDUL MALIK, kusan gabaɗayansu idanuwansa mai design na kifi ne, irin idanun nan ne da zaka gansu tamkar zanen ice fish mara bindi, ga idanun nasu dara dara kuma farare tas, duk sun gado marigayi.

Cikin girmamawa gimbiya Chuchu ta ɗagawa uncle Abbas gaisuwa.

Wani irin fara'a ce ta bayyana mashi a saman fuskarsa.
"Ku tashi ku zauna a saman sofa, a saman sofa ma ku dawo kusa da ni".

Shi ne abin da ya ce dasu, mutumin kirki, su kuma yaran kirki, sun sami tarbiya sosai. Ba musu suka koma saman sofar da yake zaune a kai suka zauna.

Cikin girma da arziki suka gaisa da shi, sai murmushi yake yi ya jawo auta jikinsa. Ko kallon in da suke Jawad bai yi ba, sai ma fitar da wayarsa da ya yi ya fara aikin latsawa.

"Yah Jawad ina wuni." Cewar Auta.

Ba tare da ya ɗago da kallonsa daga kan wayar ba ya amsa mata a takaice da lafiya.

Shiru Chuchu ta ɗan yi tana tunanin ta gaishe shi ne ko dai ta yi shiru tun da yanzu ba jimawa suka gaisa. Ganin cewa auta ta gaishe shi yasa ita ma ta ce.
"Yah Jawad ina wuni?".

Ita ma ba tare da ya ɗago da kallonsa ba ya amsa mata da lafiya a taƙaice.

Sai satar kallonsa Chuchun take yi, tana son ganin a ina ya ajiye mata wayarta ne? Me kuma zai yi da ita? And ina wayar Aunty Sarina ma da ya karɓa jiya?.

Uncle Abbas ɗin ne ya katse mata tunanin da take yi ta hanyar tambayarsu ya school. Da murna suka amsa mashi da school Alhdulillah. Daga haka ya shiga tambayarsu yasu Momma da sauran abubuwa, suka kama hira dai a kan gidan da kuma familyn.

Miƙewa Jawad ya yi ya fice daga cikin ɗakin ya basu waje abinsa.

Nima na haɗa kayana zuwa wajen KAMRAN, wata kila kafin mu dawo sun gama hirar gari sun shiga wani sabgar.

🏞️FOREST🏞️

A hanzarce Kamran ya ƙarisa wajen da wannan yarinyar ta shiga. Da sauri Rocky ya rufa mashi baya.

Yana zuwa bai yi wata wata ba ya sa hannu kamar yadda yaga ta yi shi ma ya buɗe wajen.

Wayam cikin babu kowa kuma babu komai sai wani tsani mai ɗan tsawo da aka kyara shi da itace da yake a bakin ramin, shi ake takawa a sauka ciki.

Babu tsoro babu komai Kamran ya afka ciki ramin abinsa, dan shi burinsa kawai ya kalli Mum twins, bai san ya yanayin wajen yake ba, bai san menene a cikin wajen ba, shi dai kawai ya afka, wannan shi ne komai ta fanjama fanjam.............


🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







End Ads