x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 37 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 108001 words
  • 111000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 361

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ta yi a saman gwiwowinta, wani irin azaban zafi da gwiwowin nata suka yi mata ne yasa ta saki ƴar kara tare da yin zaman dirshan a cikin elevator, ba zata iya cigaba da tsayuwa bane, ƙafafun nata ba zasu iya ɗaukarta ba.

Cike da bada umarni ba tare da ya kalli in da take ba ya ce "Stand up! Kada kuma naga kin yi mun tsayuwa wani iri, stay straight kamar koda yaushe! Daga nan har cikin hospital zaki je da kafarki, and lastly clean all this tears da yake a saman kumatun nan naki, kada ki yarda ki bari na sake ganin wani tears a saman face ɗin naki komai ƙanƙantarsa".

Kai Yah Jawad ma ya iya mugunta, Akka ce fa ta tambayeta ita kuma ta faɗa, shi ne zai kara azabtar da ita? Allah ya saka mana, sai mun haɗu gobe idan my dukka ya kaimu my people's, Love you all guy's ❤️💘🔥



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)







🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 24/7/2024.....✍️📚🌹




For information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








E____________21🔥








Kasa miƙewa ta yi, saboda yadda ta yi zaman dirshan ɗin ba zata iya tashi ba, ga kafafun nata ciwo suke yi mata sosai, hakan hasa ta kara sautin kukan nata tana mai cigaba da yi mashi magiya da ya yi hakuri ta tuba ba zata sake ba! Ya dubi girman Allah ya yi hakuri, gabaɗaya hawaye ya gama jike mata face nata izuwa yanzu, ta ci kukan har ta fara ƙoshi.

Dai'dai lokacin kuma elevator ta yi ƙasa da su, buɗe kofarta ya yi da nufin ya fita waje in yaso sai ya yi abin da ya dace.

Ai kuwa yana buɗe kofar suka yi ido huɗu da uncle Abbas, zai je wajen Akka ne daga nan ya wuce su gaisa da su Mummy, dan tun da ya zo bai leƙa su mum ba a matsayinsu na Aunty's ɗinsa matan wansa, so shi ne zai je wajensu, ga wani jibgegen ɗan'sanda shirye cikin kayan aiki rike da wata lafiyayyar jibgeiyar gun a hannunsa, fuskar nan tasa sam babu alamar mutunci a tattare da shi, ya haɗe gerar sama da ta ƙasa, face kamar an naushi kashi, no mutunci.

"Good morning daddy".
Ya faɗa ƙasa ƙasa, yaki yarda kuma ya ɗago kai su haɗa idanu da daddyn nasa, dan ya san zai sha harara tun kafin ma ya tambayesa me ya sami Gimbiya Chuchu ta yi zaman dirshan a cikin elevator kuma take kuma haka?!.

Aikuwa ya gudu ne bai tsira ba, domin kuwa uncle Abbas bai amsa gaisuwar tasa ba, kwata kwata bai ma ji gaisuwar ba, hankalinsa gabaɗaya yana a kan Chuchu dake ta faman kuka, hakan yasa sam bai ma ji cewa Yah Jawad ya ɗaga mashi gaisuwa ba!.

"Jawad what happened to her? What did you did to her?".
Uncle Abbas ya faɗa fuskar a ɗauke da mamaki, dan kukan da ta yi ba kaɗan bane, ta sha kukan ta ƙoshi har wani shessheƙa take yi, ya yi maganar kuma tare da shigowa cikin elevator da sauri fuskarsa a ɗauke da alamun ɓacin rai.

"Dad i don't do anything to her, kawai kafafunta ne suke yi mata ciwo, Akka ta ce na kaita hospital, wannan shi ne dalilin yin kukanta".

Sam uncle Abbas bai sake bi ta kansa ba, yana shigowa ya tsuguna a gabanta tare da kai fararen tafukan hannayensa ya fara goge mata hawayen yana mai tambayarta me ya sameta? Me take yi wa kuka har haka?.

Da farko kamar zata gaya mashi gaskiyar abin da ya faru, amma tuna cewa yanzu ma faɗawa Akka gaskiya da ta yi ga shi nan Yah Jawad ɗin ya sake wahalar da ita, hakan yasa ta ɓoye gaskiyar dan kada ta sake shiga wani azaban.
Cikin rawar murya ta ce.
"Uncle my legs, ciwo suke yi mun, na kasa iya takawa ne".

Hannunsa ya kai saman kafafun nata yana faɗin. "Meyasameki a kafar taki har take yi maki ciwo haka?".

Ɗan satar kallon Yah Jawad ɗin ta yi kafin ta sake sunkuyar da kai ƙasa.
"Faɗuwa a bathroom na yi".
Ta faɗa tana sunkuyar da kai ƙasa.

Daga yanayin yadda take satar kallon Yah Jawad yasa uncle Abbas ya fahimci tabbas Yah Jawad ɗin ne ya yi mata wani abin, shi ne makasudin wannan ciwon nata, dan haka sai ya miƙe tsaye yana karewa Jawad ɗin kallo, da yake shi mutun ne mai ilimi sosai sai bai ce mashi komai a gabanta ba, dan kada ya ja mashi reni a tsakaninsu.
"Tun da ba zata iya takawa ta yi tafiya da kafafunta zuwa parking space ba, kai kuma ba zaka iya ɗaukarta ba bari na kira Jaish ko kuma Taheer ɗaya daga cikinsu ya zo ya ɗauketa, sannan idan kun kaita asibitin duk abin da yake damunta you should let me know da sauri".

Ya kai karshen maganar tare da ciro wayarsa daga aljihun rigarsa domin ya kira ɗaya daga cikin waɗan da ya kira sunansu su zo su ɗauketa.

A hanzarce ya ce.
"Daddy me zaka yi kuma?".

"Taheer zan kira ya zo ya ɗauketa dan ba zata iya takawa ba, Jaish ma ba zan wahalar da kai'na wajen kiransa ba, dan nasan halinku ɗaya ne da shi, kuma idan ka dawo office kazo ina son yin magana da kai".
Ya kai karshen maganar yana wurga mashi wani irin kallo wadda za'a iya fassarata da sai na rama mata.

"Kai daddy ni yanzu na ce maka ba zan iya ɗaukarta bane? Nawa take kwata kwata?".

Hararar wasa ya wurga mashi kafin ya ce. "Aww dama zaka iya ɗaukarta kenan? Shi ne ka bar mana ita zaune cikin sanyin nan tana kuka kana sauraron kukan ko? Ku canza hali wlh".

Shiru dai ya yi bai sake yin magana ba, sai ma zura wayarsa a aljihu da ya yi tare da duƙowa kanta kaɗan, ya saɓeta sai saman shoulder ɗinsa, yasan idan ya biyewa daddyn nan nasa sai su ɓata sama da awa a wannan wajen, haka suke kamar abokai, uncle Abbas yana da wasa da dariya dasu sosai fiye da King Zuhair ma, shi kamar ba daddynsu ba, yadda kuka san abokinsu ne.

"Da ka bari na kira Taheer ya ɗauketa ai".
Uncle Abbas ya faɗa yana binshi da kallon zolaya.

"Daddy have a wonderful day, love you more".
Shi ne abin da ya faɗa tare da sa kai ya fice da sauri abinsa, dan kada daddyn nan nasa ya ɓallo mashi ruwa ana zaune kalau.

Da kallo uncle Abbas ya bishi da shi, sai da ya kalli wucewarsu suka bar arear wajen, sannan ya ce. "Zaka zo ka same ni ne, sai na rama mata, ku baku da aiki sai azabtar da ƴaƴan mutane".
Ya kai karshen maganar tare da gyara tsayuwarsa a cikin elevator, sannan ya gyara babbar rigar dakakkiyar shaddar dake a jikinsa, ɗinkin ta zauna zam zam a jikin nasa, ya yi wa kayan kyau, da alama wani waje mai muhimmanci sosai zai je, domin idan ba haka ba uncle Abbas bai cike saka manyan kaya har da babbar riga haka ba, ya fi yawan sanya suit sai kananan kaya, da yake ma yanayin jikinsa, suna da kyan jiki sosai, ba zaka taɓa cewa shi ne ya haifi su Jawad ba, idan ya shiga cikinsu ma sai ya saje da su abinsa.

A bakin elevator ya bar wannan ɗan'sandan, domin babu wani security da ya isa ya keta ya shiga part na King.

A ɓangaren shi kuwa Jaish, bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga cikin bedroom na King.

Zaune saman wannan haɗaɗɗiyar carpet na gashin jimina ya isko King yana shan haɗaɗiyar hot coffee da Gimbiya Rahilarh wato Mommar Jawad ɗin ta haɗa mashi, ta saba bashi coffee da sassafe ya sha kafin lokacin yin breakfast ɗinsu ya yi.

Kusa da daddyn nasa ya zo ya zauna. "Good morning daddy, how was your night?".

Miƙa mashi cup ɗin coffee ɗin dake hannunsa yana sha King ɗin ya yi, dan yasan ƴaƴan Momma dukka mayun shan coffee ne, a jininsu yake, yanzu haka shigowar Gimbiya Zunaira cikin ɗakin sai da ya bata ta sha kafin ta fita, za kuma ta sake zuwa wajen Momma ta sha, kullum safiya aikin kenan.

Sai tashin tiriri coffee ɗin yake yi. Karɓa Jaish ɗin ya yi tare da kaiwa saitin ɗan bakinsa, kaɗan ya ɗan kurɓa ya sake muƙowa da daddyn nasa abinsa.

"Ya isheka ne?".
King ya tambaya yana mai kai hannu zai karɓi cup ɗin.

"No dad, bai isheni ba, sai dai nafi son kai ka sha ne, Momma kai ta kawowa, for sure nasan nawa yana cikin bedroom ɗinta yanzu haka".

"To ai na Mommarka daban na daddynka ma daban, nawa ya fi nata daɗi ai".
Yana magana yana tsare Jaish ɗin da idanun.

Nisawa kawai ya ɗan yi, har gobe daddynsu ba zai canza ba, wai nasa yafi na Momma daɗi, bayan kuma ita ta haɗasu dukka, tsammashi fa shi ma ta yi, ba shi ya yi da kansa ba! Haka yake cewa, sai ma sun zauna da Momman waje guda, sai ya rinƙa ce mata dukka ƴaƴansa shi suka biyo, sai ya zaɓi waɗan da suka fi kyau sosai a cikinsu ya ce sune masu kama da shi, ai Momma ita bata da wani kyau sosai, ya fita kyau, kawai ya aureta ne saboda uncle ɗinsa, kuma fa ba haka bane, daga cikin KINGDOM OF POWER yake shiryawa ya tafi har Dubai zance a wajenta lokacin da yake neman aurenta, yana mutuwar sonta, amma yanzu saboda zolaya sai ya rinƙa cewa ai ya fita kyau, kuma ita ta makale mashi ta ce idan ba shi ba mutuwa zata yi dan taga kyakkyawa, wasu abubuwan ma ai ba za'a tunosu bane, da irin kaunar da ya nunawa Momma idan sauran matansa suka ji ai ba zaman lafiya, zasu ce ya yi son kai, ita kuma Momma idan ya ce bata da wani kyau hasken fata ne kawai, lallaɓawa yake yi da ita, sai ta yi ta biye mashi tana cewa ta fishi kyau, hakan ne kuma yake yi mashi daɗi yasa kullum sai ya zolayeta, abin gwanin birgewa!.

"Daddy zan je wajen Momma daga nan zan wuce office".

Kai mashi cup ɗin coffee ɗin a saitin ɗan bakinsa King ɗin ya yi yana faɗin.
"Ka kara sha kaɗan".

Wannan coffee dai da albarka take, Gimbiya Zunaira ta sha, King ɗin ya sha, ga Yah Jaish ma yanzu ya sha, da twins Obaid da Omaid za su shigo yanzu da su ma sai sun sha.

Ba musu ya karɓa ya ƙara sha ba mai yawa sosai ba, sannan shi ma da kansa ya sawa daddyn nasa cup ɗin a baki yana faɗin.
"Dad take it all, kasan kai fa Momma ta kawowa, idan har ta samu baka sha dayawa ba zata ɓata rai".

Da sauri ya ce. "Ni kuma da ta ɓata rai ai gara na shiga filin daga mu buga yaki, dan haka bani kayana".
Ya kai karshen maganar tare da karɓar cup ɗin daga hannunsa.

"Dad you really love Momma fa over".
Ya faɗa tare da fara yunƙurin miƙewa.

"Kai idan ka ce love ma ai ka rage, ita ɗin rayuwata ce, ƴar albarka ce".

Shi dai Jaish miƙewa tsaye ya yi abinsa tare kuma da ɗan duƙowa ya mannawa King ɗin sunbata a goshi, ba dan yasan wanenen Jarumin mahaifin nasa ba ai da ya bashi number ɗaya a matsayin masoyan duniya, ita ma Momma bata da wani magana sai nasa, shi dai Jaish suna cika masu kunnuwa da zancen love ɗinsu da suka yi a baya, shiyasa da sun fara yake kara gaba abinsa, dan ya lura kowannensu mutuwan wa juna yake yi.

"Dad na wuce, pray for me".
Ya yi maganar tare da nufar hanyar fita abinsa!.

Addu'a sosai King ya yi mashi cike da so da kauna. A cikin zuciyarsa yake amsawa da Amin ɗin, daga haka ya fice waje.

Yana fitowa suka haɗu da uncle Abbas da yake ƙoƙarin shigowa bedroom na King ɗin, gaisawa suka yi cikin girmama juna tare da nuna tsantsar so da kauna, suna kaunar uncle Abbas ba karya.

Addu'a sosai shi ma ya kwarara masu kafin su yi sallama da Jaish ɗin ya wuce part na Mommarsa domin ya je ya sha coffee kamar yadda ya saba. Shi kuma uncle Abbas ya wuce ciki wajen King kenan.

Shiru part ɗin nata babu kowa sai kuyangun da suke ta faman yi mata hidima, sai kai komo suke yi, part ɗin tsab tsab da shi, sai tashin kamshin room freshener mai kwantar da hankali yake yi.

Ƙasa gabaɗaya kuyangun dake cikin parlourn suka zube a saman gwiwowinsu suka fara zuba mashi gaisuwa. Kamar dai yadda aka saba ne ko kallon in da suke bai yi ba, ya sa kai ya nufi saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna a parlourn kenan.

Kuyanga mama Haulat ce ta ƙariso gabansa cikin sauri tare da zube gwiwowinta a ƙasa tana ɗibar gaisuwa.

"Yi mun sallama da Momma". Shi ne kawai abin da ya faɗa, daga haka bai sake magana ba, kuma bai kalli in da take ba.

A hanzarce cikin rawan jiki ta miƙe ta nufi cikin bedroom ɗin, ita kaɗai ce mai shiga har cikin bedroom ɗin Gimbiya Rahilarh, sauran kuyangun a iya parlourn kawai suke tsayuwa.

Zaune saman waɗan nan shinfiɗu na alfarmar ta isko Momma, ta sha kwalliya cikin wata dakakkiyar tsadaddiyar lace mai bala'in kyau launin pink color mai ɗan duhu, ba ƙaramin kyau ta yi ba, farar mace da kaya pink color akwai ɗaukar idanu, kalar yana hawa da skin ɗinta sosai, hannayenta wuyarta dukka shake suke da abin ado na zallar madarar gold masu bala'in kyau da tsada, ga tsadadden haɗaɗɗen alkyabbarta launin white color, white ɗin ma irin up white ɗin nan mai haske sosai, sai ta kara tsantsara kyau na wuce misali.

Wasu haɗaɗɗun Dubai set of cup's ne a gabanta, ga hot jug ɗinsu, cup ɗin sun haɗu makurar haɗuwa. Daga gefe kuma wani haɗaɗɗen kwandon kayan fruits ne mai shake da fresh fruits ɗin sosai a cikinsa.

A gabanta Mama Haulat ta zo ta tsugunna, cikin girmamawa ta dukar da kanta ƙasa tana jiran izinin yin magana.

"Haulat menene yake tafe da ke?".
Ta faɗa cikin sanyin murya kamar Gimbiya Zunaira ce ta yi magana.

"Dama Yah Jaish ne yake neman iso, yana parlourn".

"Ki ce mashi ya iso".

A hanzarce ta miƙe cikin rawan jiki ta nufi wajen. Kai tsaye gabansa ta sake komawa ta zube gwiwowinta a ƙasa kafin ta gaya mashi Momma ta ce ya shigo.

Tun bata ƙarisa maganar ba ya miƙe ya wuceta abinsa, dan lokaci ya ɗan tafi, yana son ya je office da wuri.

Baki a ɗauke da siririyar cikakkiyar sallama ya shigo cikin bedroom ɗin.

Yadda Mama Haulat ta barta bata motsa daga wajen ba, tana zaune, daga zaunen ta amsa mashi sallamar tasa tare da yi mashi izinin shigowa.

Kai tsaye kusa da ita ya zo ya zauna tare da ɗaura wayarsa a saman wani haɗaɗɗen throw pillow dake kusa da shi.

"Good morning our lovely Momma".
Ya faɗa yana kai hannu zai ɗauki cup ɗaya ya zuba coffee da yake a gabanta.

Karɓar cup da ya ɗaukan ta yi.
"Morning my son how was your night?".
Ta faɗa tana zuba mashi coffee ɗin da kanta.

Alhdulillah ya amsa mata da shi tare da tambayarta ta tashi lafiya?.

Zuba mashi coffee ɗin ta yi dai'dai yadda tasan yake iya shanyewa, sannan ta fara bashi a baki kamar ƙaramin yaro, bai karɓa ya sha da kansa ba, dan idan da sabo ai ya saba, sau da dama idan zai ci abu, in dai a gabanta ne to ba shakka sai ta bashi a baki, hakan yasa bai ma damu ba, ya fara buɗe ɗan bakinsa yana karɓa kawai. Akwai soyayya mai karfi mai kuma kayatarwa a tsakanin King Zuhair, Gimbiya Rahilarh da kuma ƴaƴansu.

Haka ta cigaba da bashi coffee ɗin suna hira cike da so da kauna, har gobe dai yana da matukar kunya, baya bari su haɗa idanu da mutane shi dai!.

A ɗayan ɓangaren kuwa, Gimbiya Sarina ce zaune a tsakiyar katafaren bed ɗinta, da alama yanzu ba jimawa ta tashi daga barci, gabaɗaya wannan gashin nata na larabawan a watse, ya basu mata har ta gaban fuskarta, kayan barci riga da wando launin sky blue ne a jikinta.

Wayar Mammie ɗinta ce a hannunta, call take ta aikin dannawa twins Obaid and Omaid, a kan su zo su sameta su shirya wani plant, dan yanzu Mammienta ta fita daga cikin bedroom ɗin, ita ce ma ta tasheta daga barci, yau a part ɗin iyayen nata ta kwana, uncle Abbas ya ce akwai wani ɗan amininsa da ya ganta ya ce yana so, dan haka zai zo suka ga juna ta shirya, ɗa ne ga Attorney general of the federation, dan haka ta shirya anjuma zai zo, ita kuma sam bata son kowa, bata kula samari, bama ta son a kawo mata zancensu, shiyasa duk wanda ya zo neman aurenta sai ta haɗa baki da twin's sun yi mashi wata muguntar da idan ya tafi ba zai sake dawowa ba, haka suke yi, to shi ne yanzu ma take kiran numbersu, su zo maza, duk tana wani birkice, dan uncle Abbas ya yi ta yabon yaron, wai yaron kirki ne,
End Ads