x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 24 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 69001 words
  • 72000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 427

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ya ƙaddara akwai auren a tsakanin wannan family, sai kuga Allah ya kawar da wanda ya hana ayi auren ɗin, ya mutu kuma a ɗaura auren zam zam a zauna babu mai hanawa, so da dama hakan tana faruwa, sai kiga mutun yana mutuwa bai fi da sati biyu ba anyi bikin ƴarsa ko wani makamancin haka, so rabo tana kisa har lahira, dan haka mu guji kin abin da Allah ya halakta mu ce mu sai mun haramta.

"To Hauwa in dai haka ne nima sai na hakura kawai na bari baban Zainab ɗin ya yi auren ko?".
Ta yi maganar muryarta a sanyaye, da alama jikinta duk ya yi sanyi.

Wani irin harara Aunty Hauwar ta wurga mata kafin ta sake fara wannan shegen dogon jawabin nata.
"Hakura fa kika ce? Lallai maman Zainab har yanzu baki da hankali! To idan kin hakura ya yi aure hajiyarsa fa? Ita ma haka zaki zauna da ita a tare da amaryar suna yi maki cin kashin da suke so? Kin dai san ƴar cikin dangi zai auro ko? To tasu ce ita ɗin, zasu goya mata baya ne ta taka ki son ranta ba yadda zaki yi, bare kuma ke da basu son ganinki a gidan, ai kin shiga ɗari ma kenan ba uku ba, malama kawai idan zaki tashi tsaye ki nemawa kanki mafita ki tashi tsaye, idan kuma ba haka ba wlh bakinciki ne zai zama sanadiyar ajalinki kin ji na gaya maki, waye ya ce maki yanzu ana zama shiru? Ai a zamanin da ne aka yi wannan haukar, yanzu ko mahaukacin kura aka kwanto maki maza ki yi fito na fito da shege, ke baki ga ko aljani idan kika nuna baki da tsoro shakkarki yake yi ba? Ai kawai haukacewa ƴan iska zaki yi duk kici ubansu, ki gasawa shegu aya a hannu, barema wannan Uwar Haidar ɗin, shegiya mai kafa kamar na shamuwa, saboda ita mijinta soloɓiyo ne ko abinci baya iya neman masu, baya iya ciyar da ita shi ne take yi maki bakinciki da hasada, wannan da ace ba ubansu ɗaya da baban Zainab ba da tsab zata aure shi, shegiyar mata dangin mayu"

Ta kai karshen maganar tana cikin kunar rai, ta kuma kai karshe tare da miƙewa da nufin tafiya.

"To Hauwa ina kuma zaki je?".
Still dai cikin sanyin murya ta yi maganar, da alama jikinta ya yi sanyi sosai.

"Ina zan je kuwa maman Zainab? Gidana mana zanje, me zan zauna nayi maki? Ina ce maki ga shinfiɗaɗɗiyar hanya mai kyau kina ce mun lallai ke ta saman dutse zaki bi ki wuce, ba dole na kama kai'na ba, kuma kada ki sake gaya mun wannan kayan takaici na sirikan naki, tun da ke baki ji, ke kin zama kamar wata jaka kwandon shara, kowa ya ɗebo dattinsa a kanki zai juye, da anyi magana ki ce ke ta Allah, ai kowa ma na Allah ne, kuma a koda yaushe muna rokon Allahn da ya yafe mana zunubanmu ya bi mu da rahmarsa, ni bana cutar da kowa, idan kin ga na gayawa malamai damuwata to cutata aka yi zan kwaci hakkina, a hakan ki gaya mun wani laifi na yi?".
Ta kai karshen maganar tare da nufar kofar fita daga parlourn, tana wani kara ɗaure fuska yadda kuka san ita aka ce za'ayi wa kishi.

Aunty Hauwa ta yi nisa ba zata ji kira ba, ga shegen kaifin harshe, yanzu tana neman ta jefa maman Zainab ga halaka da sunan wai tana sonta, a ganinta da haukarta hakan ce so, saɓawa Allah da shirka ka tura mutun ya yi ai ba so bane.

Shiru dai Maman Zainab ta ɗan sake yi kafin ta ce.
"To Hauwa zan yi tunani a kai, gobe zan zo gidanki mu sake tattaunawa In Sha Allah".

Tana fita waje daga cikin parlourn ta amsa mata da sai kin zo, daga haka ta nufi harabar gidan dan wucewa nata gidan, dama daga wajen kasuwancinta take, akwai wata dillaliya ce a nan unguwarsu Zainab ɗin, to tana zuwa wajenta duba kayayyaki, irin suna harka a taren nan ne, duk wadda ta samu kaya mai sauki zasu raba su sayar dan su sami alkhari, wannan dalilin yasa take yawan kawowa Maman Zainab ziyara, dan a unguwarsu dillaliyar take, so duk time ɗin da ta shigo sai ta biyo mata sun gaisa.

Kamar dai kullum har kofar gida maman Zainab ta rakata tare da bata kuɗin mashi 1k kamar yadda ta saba, daga haka suka yi sallama Aunty Hauwar ta tafi ita kuma ta komo cikin parlourn ta zaune.

Uban tagumi ta buga tare da haɗa gerar sama da ƙasa tana tunanin mafita, da alama zuciyarta ta fara yarda da zancen Aunty Hauwa, abinku da shaiɗan la'anannen Allah, sai ya rinƙa raya mata cewa ita ma amaryar da za'a auro ai tana can wajen malami tana ƙoƙarin a mallaka mata zuciyar baban Zainab, ya zama baya son kowa sai ita.

(Baban Zainab bawan Allah yana can kasuwa yana tunanin maman Zainab ɗin, ita kuma tana nan tana tunanin wata na ƙoƙarin mallake mashi zuciyar😅 kai shaiɗan shege wlh, Allah dai ya kara tsine mashi ya kuma nesantamu da shi, yasa mufi karfin zuƙatanmu. Amma na ce ba yanzu shi ma Haidar fa ba za'a rasa matan da zasu yi kishi a kansa ba ko?😂😅 Mata mutanenmu)

Sai tunane tunane na banza shaiɗan yake kawo mata, har ya sanya zuciyarta ta fara yarda da zantukan Aunty Hauwa, yau har girkinta ya fara ƙonewa tana nan ta afka duniyar tunani.

A hanzarce ta miƙe ta nufi kitchen ɗin, dan kaurin abincin ya iskota har cikin parlourn, tana can tana tunanin lamarin Aunty Hauwa ƴar balaja'u, abin mamakin shi ne tana da mahaifiya a raye, mahaifinta ne ya rasu, a maimakon ta sanar da mahaifiyarta gafa halin da ake ciki, ko banza shawarar uwa ta wuci abin wasa, da ai yanzu zata sami shawara mai ɓille mata, amma ta je tana ƙoƙarin daka ta Hauwa, bayan kuma ita da kanta ta karanta ta san cewa ba'a taɓa cin nasara da saɓon Allah, duk abin da ka haɗa shi da shirka tare da saɓawa mahaliccinmu to wlh wannan abin ba zai taɓa yi maka kyau ba, sai dai ma ya zamar maka bala'i, sarai tasan da haka, amma kishi yana neman rufe mata ido, ga Aunty Hauwa a gefe, sannan ga shaiɗan yana can yana ta faman buga masu ganga, da alama kuma suna shiri takawa wannan gangar ta shaiɗan ɗin rawa. Allah dai ya kyauta ya kuma kara tsaremu da tsarewarsa.

Girkin nata ta sauke tare da ɗaura tukunyar miya a saman gas ɗin. Kamar yadda ta saba haka ta haɗa masu miyar steew tare da zuba komai a cikin kula, sannan ta kwasa zuwa cikin parlourn, sai dai fa duk wannan aikin da take yi hankalinta da tunaninta dukka yana a kan maganganun da suka yi da Aunty Hauwa, tana ta saka da warwara a cikin ranta.

A haka su Khadija suka dawo daga islamiya suka sameta, sosai Khadija ta lura da yadda mamar tasu take sukuku yau, amma bata yi ƙoƙarin tambayarta ko lafiya ba, ta barwa kanta tunanin kawai a cikin zuciyarta.

Yau babansu bai shigo gidan ba har sai da ya yi sallah issha, da kullum sai ya shigo ya yi wanka kafin ya tafi masallaci, amma yau sai da ya yi sallah ya dawo, duk kuma dan baya son shigowa ya kalli face ɗin maman Zainab a ɗauke da damuwa ne, hakan yasa ya yi zamansa a waje sai da ya yi sallar, tun da ya je kasuwa a cikin damuwa yake bawan Allah, ita kawai yake tunani, wlh baya son ɓacin ranta ko kaɗan, kawai ba yadda zai yi ne.

Maman Zainab dai yau ta ki ta ci abincin daren ma, dan bata jin yunwa saboda damuwa, haɗa masu komai dai ta yi sannan ta nufi cikin bedroom nata.

Izuwa yanzu Khadija ta gama fahimtar lallai iyayen nata sun sami gagarumin matsala a tsakaninsu, hakan yasa sai ta yi ƙoƙarin jan babanta da hira dan ya saki jiki ya ci abinci sosai, tasan ba abin da ya fi so irin ya gansu suna karatu sosai, dan haka sai ta ɗauko mashi zancen karatu, ta rinƙa bashi labarin irin karatun da ta sha yau a school. Ai kuwa nan take ya ɗan ware suka fara maganar karatu suna cin abinci, a haka ta ja shi da hira har ya ci abinci sosai wanda bai zata ba, Zainab kuwa da yake hankali bai gama zama ba, da suran yarinta, sai ta zauna tana zuba kallo a Tv tana loda abinci abinta.

A haka suka yi hira su kaɗai har zuwa karfe tara na dare, yau dai Sadiq shi ya shigo ya ɗauka masu abincinsu. Karfe tara na cika su Zainab suka miƙe suka nufi bedroom nasu bayan sun yi wa baban sallama.

"Kada ku manta ku yi addu'a fa". Ya faɗa tare da miƙewa shi ma ya hau kashe kayan kallo da su wutar ɗakin, dan shi ma shiga zai yi tun da maman Zainab bata nan, ba wani hira da zai zauna yi kuma, gara mashi ya je ya lallaɓata ta daure ta fito ta ci abinci, ga shi ko na rana ma bata ci ba..............💔😥

Cikin bedroom ɗin nata ya nufa, ya kuma yi sa'a bata rufe kofar ba, bawan Allah yau ko wanka ma bai yi ba, kuma ta haɗa mashi ruwan wanka kamar yadda ta saba, shi ne kawai bai je ya yi ba, saboda damuwa.

Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga cikin ɗakin, tana kwance a saman bed kamar ɗazun da rana, maganganun Aunty Hauwa kawai take tunawa.

A gefenta ya zauna da nufin ya fara yi mata magana. Amma ina yana zama ta miƙe a hanzarce ta fice daga cikin ɗakin ta bar shi zaune, bedroom nasa ta je ta shiga tare da rufo kofar ta murza key, sai ka ce shi ne ya yi mata laifi, abin da shi ma ba laifinsa bane, amma ta kasa yi mashi uzuri a kan kishin...........MATA MUTANENMU😅😅

Ji ya yi gabaɗaya duniya tana juya mashi, ya rasa menene ma yake yi mashi daɗi a duniyar nan, har wani kara sara mashi kansa yake yi, ya rasa me zai sake yi kuma, jingina da jikin headboard na gadon nata ya yi yana tunanin me zai sake yi kuma? Ni ma na rasa wannan abin da me ta yi kama, dan haka bari na bar waɗan nan ma'auratan na leƙa wani ɓangare, wata kila kafin mu dawo maman Zainab zata ɗan sauko kaɗan........😥💔

Amma kafin mu leƙa KINGDOM OF POWER bari na baku amsoshinku sannan na kara maku haske a kan labarin, masu tambayata mun koma baya ne, ma'ana yanzu labari nake bayarwa ne, amsa ita ce a'a, ni ban koma baya ba, ai idan da zan koma baya na bada labari zan sanar daku, gaba muka ci ba baya ba, masu cewa Gimbiya Zunaira ita ce maman twins saboda suna tunanin mun koma bada labarin baya da ta wuce ne to ba haka abin yake ba, ai kuna gani ina rubutu a kan Gimbiya Zunaira kuma ina rubutu a kan su pretty wato twins, su pretty fa shekarunsu goma a yanzu, ita kuma Zunaira shekarunta shaɗaya, da shekara ɗaya kawai ta fisu, to taya za'ayi ta haifesu fisabilillahi,🤔 so rayuwar FOREST daban rayuwar KINGDOM OF POWER daban, fatan kun gane? Ɓangare biyu ne a wajen ba wai ɗaya ba, so yanzu dai zamu fara shiga cikin sarautarmu domin mu nemo shin ina RAWANIN ZALINCI take? Sai muga ko zamu iya fafatawa da ita.🥱

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

KINGDOM OF POWER💪🔥

Wasu irin shegun shirga shirgan dankara danƙaran motoci masu numfashi ne suka danno hancinsu a cikin Masarautar. Tun da waɗan nan motoci suka danno kai a saman shinfiɗaɗiyar titin dake tsakanin babban gate na shiga da second gate kowani mayaki da kuma bayi suka nemi waje su tsaya, motoci goma ne cif, dukka launin motocin sun kasance maroon color, guda ɗaya na tsakiyar ne kawai black color, waɗan nan motoci tamkar wasu jirage da suka danno kai, kace ba'a kan ƙasa suke tafiya ba, saboda tsantsar kyau, ga ɗaukar idanu, sam kukan motocin baya fita sosai, ba zaka taɓa cewa suna kuka ba, saboda haɗuwarsu, na manyan kai ce.

Kai tsaye part na BARDE suka nufa, basu ja burki a ko'ina ba sai a katafaren parking space na part ɗin mai matuƙar girman da zai iya ɗaukar motoci sama da guda 50.

Suna kashe motocin ba'afi da ƴan sakanninba wasu shirga shirgan bodyguards masu shiga cikin dark ash suit suka firfito daga cikin motoci maroon colors ɗin, bodyguards ne da suka san aikinsu, karfafan gaske ne, babu alamar wasa a tattare da su, aikin kawai suka iya aikatawa, duk suna sanye da face mask a face nasu.

Wani shirgegen bodyguard mai ji da lafiya da karfi ne ya zo ya ɓalle marfin black car ɗin nan, ya buɗeta cikin girmamawa. A take sauran bodyguards ɗin suka ja gefe guda suka tsaitsaya alamar suna jiran na cikin motar ya fito.

Sun ɗauki a kallah good 5 mins da buɗe kofar motar, amma babu wanda ya fito, tamkar babu kowa a cikin motar, su kuwa bodyguards ɗin sun kame waje guda suna jiran ya fito.

Sai da aka kara almost 2 mins, sannan ya sako kafafunsa waje a hankali kamar mai tsoron taka ƙasa. Sanye yake da wata haɗaɗiyar cover shoe irin na gidan sarauta, cover ta haɗu matuƙar haɗuwa, launin white color, sai kyalli duwatsun jikinta suke yi, kun dai san yadda takalmar sarauta suke dai ko? Takalma ne na gani na faɗa waɗan da ake narka maƙudan dukiya wajen sayansu, To haka na kafarsa take, daga ta cikin takalmar yana sanye da uncle sos a kafafun nasa, sai kafar wandonsa da ta kasance wandon jeans blue color. Koma wanenen a cikin motar nan da alama jinin sarauta na gudu sosai a jikinsa, duba da yadda fitowa daga cikin mota ma kawai sai an yi ta da isa da izza, ya shanya bodyguards ɗinsa a tsaye tamkar wasu mutun mutumi, kamar an sassaƙasu a tsaye, shi kuma yana zaune, da alama jinin King Zuhair ne da gasken gaske kuwa.

Ko da ya zuro kafafunsa waje ɗin ma sai da ya ɗauki almost 2 mins kafin ya fito daga cikin motar. Hannunsa na riƙe da waya, da alama tun ɗazun da yake zaune a cikin motar wayar yake latsawa.

Aka ce faɗa ɓatawa ko? To shi ne wannan, dan tsayawa zayyana haɗuwar wannan matashi ma ɓatawa ne.

JAISH kenan. matashin saurayi ne da ba zai haura 25 years a duniya ba, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan cewa e lallai wannan yayan gimbiya Zunaira ce, saboda fuskarsa iri ɗaya da nata, sai dai kwayar idanuwansa da suka bambanta da nata, shi nasa kwayar idanun baki ne, ita kuma nata kunga hazel eyes ke gareta, banbancin idanu ne kawai ya bambanta face nasa da ita, kyakkyawar gaske ne, ga wani haɗaɗen saje da ta kara sawa ya fito a ainahin jinin Modarawan larabawa da gaske, Cikakken namiji ne mai cikar sura tare da haiba da kamala, da ganinsa kasan e lallai shi ma ya taɓa renon commander ZAFAR, gashin kansa na larabawa a kwance luf bakin kirin yana wani sheki, ya sha gyara, da alama ba ƙananan kuɗi yake kashewa gashin nasa wajen gyaranta ba, dan da gani ba tambaya ba gyaran kananan kai ba ce, ta manyan kan ne. Yana da innocent face sosai, so silent ne, sai dai da alama akwai zafin nama da kuma zuciya, baya shiga harkar kowa, nutsatse mutun ne shi ɗin, ga bala'in kamun kai da yasa ake yi mashi kallon mai bala'in girman kai, baya da yawan magana, ga kuma bala'in kunya ke gare shi, sannan baya son ɗaga idanu ya kalli mutane, wasu suna fassara hakan da kunyar da yake da shi, a gaskiya mutun ne mai kunya sosai, dan ko mahaifiyarsu gimbiya Rahilarh baya kallonta ido cikin ido, haka Allah ya yi shi. Bugu da ƙari komai zaka yi wa JAISH a duniya ba zaka wani burgesa ba, irin mutanen nan ne da komai suka fiya yawan burus da shi, ba kasafai abu ya cika burgesu ba, amma fa mayen shan coffee ne kuma, kusan za'a ce abin a jinin gimbiya Rahilarh yake, dukka ƴaƴanta mayun coffee ne na bugawa a jarida, ko tsakiyar rana zaka gansu da cup ɗin coffee mai zafi suna sha, harta gimbiya Zunaira ɗin ma haka take da shan coffee, sai dai kuma basu taɓa shan coffee ɗin kowa sai wanda mamarsu Gimbiya Rahilarh ko kuyanga Haulat suka haɗa, a cewarsu babu wanda ya iya haɗa coffee sai mutane biyun nan, ga su da shegen kyankyani, basu son datti ko kaɗan, saboda su wani lokacin Gimbiya Rahilarh take shiga kitchen ta yi coffee da kanta. JAISH yana kaunar ƴan uwansa da iyayensu sosai, idan kaga yana magana to da ƴan uwan nasa ne, bayan su baya ɗaga idanu ya kalli kowa a cikin gidan, ƴan matan cikin family duk sun saka mashi ido, sai dai kowacce bala'in tsoron tunkararsa take yi, saboda wannan rashin maganar tasa yasa suke ɗaukarsa mai zafin rai sosai, kuma yana da zafin rai ɗin ba sai na faɗa ba, dan kunsan duk mutun mai shiru shiru irin haka fa ba'a magana wajen zuciya da zafin rai, baya ɗaukar wasa, hakan yasa suke shakkarsa sosai, best friend ɗin Yah Jawad ne.........😅

Shigar kananan kaya ce a jikinsa, sai dai ya ɗaura wata haɗaɗiya kuma tsadaddiyar suit fara a ta saman rigar jikinsa, da suit ɗin da takalmar kafafunsa haɗe da rigar jikinsa duk iri ɗaya ne white colors, wando ce kawai blue jeans. Sai tashin wani daddaɗar fitinannen kamshi yake yi.

Cikin takun jarumta haɗe da ƙasaita ta jinin sarauta ya nufi hanyar barin parking space ɗin nasu. A hanzarce bodyguards ɗin nasa suka yi yunƙurin rufa mashi baya.

Kyakkyawar farar hannunsa ɗaya ya ɗaga masu ba tare da ya yi magana ba, alamar baya buƙatar su bi bayansa. Cak suka tsaya kamar gumaka, shi kuwa ya wuce izuwa
End Ads