Mamma dake wajen madafarta tana ta aikin soka nama a jikin itace tana saƙalewa a saman dutsen, ta amsa mashi da. "Sai yanzu ka dawo ko?".
"Kai Mamma ban fa jima ba".
Wasu duwatsu guda biyu ta ɗauko masu karfi tare da fara ƙoƙarin kunna wuta ta hanyar haɗa duwatsun tana bugawa, suna bada wuta.
"Ba shakka kam baka jima ba, kazo ka ɓare ɓawon masaran nan".
Tana magana tana ƙoƙarin kunna wuta da waɗan nan duwatsun.
"Am coming Mamma, but before na zo let me ask you something, dan na ƙagu na ji amsar, abin yana damuna".
Yana magana yana cire kayan jikinsa.
"Okey ina jinka sarkin tambaya".
Ta faɗa tare da ɗauko wani tukunyar ƙasa ta ɗaura a saman wutar da ta kunna ɗin, sannan ta duba ruwa ɗan dai'dai misali.
"Mamma this two dys am feeling something da ban san ya zan gaya maki ba, ban taɓa jin hakan a jikina ba sai this time around, and hakan yana faruwa ne...............🥱
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
"Mamma this two dys am feeling something da ban san ya zan gaya maki ba, ban taɓa jin hakan a jikina ba sai this time around, and hakan yana faruwa ne if i........... " Sai kuma ya ja birki da yin maganar, saboda ya kasa iya ƙarisar da cewa hakan na faruwa ne idan ya taɓa wata mace ba ita ba.
Da yake ita Mamma tasan wani lokaci questions ɗin da yake yi mata ba wasu masu amfani bane, kawai ya sanyata magana ne, sai da ta ji ya yi shiru bata sake bi ta kansa ba, ta cigaba da aikin girkinata na dare, ga nama da take gasa masu a gefe, namar gwanin ban sha'awa, kana gani sai ha kaɗiyi yawu.
Shi kuwa kammala cire kayansa ya yi tare da nufar in da zai yi wanka zuciyarsa a cike tab da tunanin yadda zai yi da mamma ta gaya mashi menene yake damunsa ba tare da ta san cewa jikin wata ya taɓa ba, a nasa tunanin gani yake yi bashi da lafiya ne, kada kuma ku manta Mamma babbar likitar gargajiya ce, shi ne ma dalilin da yasa yake son ya tambayeta ko akwai wani magana da zata taimaka ta bashi.......... E lallai ni kuwa nace zaka ga magani...😅
Wankarsa ya je ya yi tare da fitowa ya shirya cikin wasu haɗaɗɗun kayansa masu matuƙar kyau, tas tas da su, Mamma ba dai tsabta ba, shi ma Kamran a yadda ta rainesa kenan, baya kaunar datti ko kaɗan, suna da tsabta sosai da sosai.
Itatuwan da take saƙar kayan sakawa irin na mutanen da ya ɗauko tare da audigar da take saƙawa ya nufo waje gabaɗaya, bai je in da take ba, sai tubka da warwara a cikin zuciyarsa yake yi, yana ta saƙa ta yadda zai yi mata ta gaya mashi me yake damunsa?.
Can wata dabara ta faɗo mashi ya gaya mata yanayin da yake shiga kawai ba sai ya ce mata wata ta taɓa shi ba, tuna wannan dabara yasa ya ɗan saki face ɗinsa keɗan.
Kafa itatuwar sakar tata ya yi tare da zama a saman wata dutse da Mammar tasa take zama idan zata yi saka, shi ma izuwa yanzu ya iya sakar sosai, so ya ɗauko ne domin ya saƙawa Pretty sket da riga masu shegen kyau, bai taɓa saƙa kayan mata ba sai nasa, yau ne farau, so ya sanya a ransa idan ya saka ta yi kyau sai ya sakawa Sweetie ma, idan kuma bata yi kyau ba sai ya hakura. Yasan ba yanzu Mammarsa zata fito waje ba, zai iya kammala saƙa sket ma Mamma bata leƙo ba, dan tana girki, idan ta kammala kuma wanka zata yi ta gyara madafa da sauran sassa na cikin ƙogon, so sai can yamma sosai zata fito, yasan cewa yana saurin yin sakar shiyasa bai ji tsoron kada ta fito ta same shi yana saka kayan mata ta tambayesa waye zai sakawa ba, bai wani damu ba, a hanzarce ya fara saka mata sket, dan shi ya fi girma da cin lokacin. Sai dai fa yanayi kuma yana fargabar kada Mamma ta faɗo mashi babu wani excuse.
Sam ya manta Mamma ta ce ya zo ya ɓare mata masara, da dai baya mantawa da maganar Mamma komai ƙanƙantarta, yanzu kuma su Pretty sun shigo cikin tunaninsa da ƙwaƙwalwarsa suna raba mashi hankali gida biyu, har ya fara mancewa da wasu kalaman Mamma, duniya kenan.
Da sauri sauri yake sakar kamar wani mara gaskiya. Sket ya saƙa mata white color, dan Mamma bata rina audigar ba, farace kawai, sket ɗin ya yi masifar kyau, sai dai ɗan guntu ne da ba zai wuce mata gwiwowinta ba, kamar umbrella ya yi yanayin design ɗin sket ɗin, ta yi kyau sosai.
Cikin sauri ya cireta ya sake mayar da audigar ya fara sakar sket ɗin Sweetie ma. Good one hour ya ɗauka yana yi, iri ɗaya dana Pretty ya sakasu kamar yadda yaga Mamma tana yi wa kanta, sai dai nata manya ne har kasa take yi, shi kuma ya yi masu ƙanana, dan yana ganin kamar zata iya kai masu kasan gwiwa kaɗan.
Rigar Pretty ya fara saƙawa kamar yadda ya fara da sket ɗinta, yana yi yana fargabar kada Mamma ta fito ta same shi yana sakar mata, dan ma ya kwashe skets ɗin ya kai cikin ɗakinsa ya ɓoye, idan Mamma ta gani ta tambayesa kayan waye bai san me zai ce mata ba, bashi da amsa, hakan yasa ya kwashe skets ɗin ya kai room ɗinsa.
Yana kammala rigar Pretty ya jiyo motsin Mamma tana shirin fitowa, ta kammala duk wasu ayyukanta da ta saba yi, a hanzarce ya cire rigar daga jikin itatuwar ya cusata a cikin rigarsa ya ɓoyeta a wajen plat tummynsa, sannan ya saka wata audiga ya kama sakar hula ta karya. Wasa wasa Kamran ya fara koyan karya tun bayan haɗuwarsa da su Pretty, ya kuma koyi ɓoyewa Mamma abubuwa saɓanin da can baya kafin ya haɗu da su Pretty, sam baya ɓoye mata komai.
Sarai Mamma ta lura da cewa yana ɓoye mata abubuwa da dama, amma ta zuba mashi idanu ne tana son taga gudun ruwansa, abinku da uwa kuma abin da bai saba ba, bai saɓa ɓoye mata komai ba, rana tsaka ya koya harda karya kunga kuwa dole ta fahimci canzawar ɗan nata, da yake ita macece mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira sai bata wani damu ba tana bin komai daki daki taga iya ina abin zai kaita.
Shiru ta tsaya a bakin kofar fitowa daga kogon tana kare mashi kallo, ta zuba mashi idanu tamkar mai nazarin wani abin a face ɗinsa.
Sarai yasan da tsayuwarta a wajen, amma sai ya yi kamar bai sani ba, tamkar bai ji motsinta ba, saboda kada ta fara zarginsa, yasan halinta sarai.
Ta ɗauki a kallah good 10 mins tana kallonsa babu ko kyaftawa, shi kuma ya zage yana ta saƙa hula ta karya kamar bai san da ita a wajen ba.
Haƙiƙa wannan kallo da take yi mashi kallo ne da ya ƙunshi abubuwa da dama, kallo ne da ya ƙunshi abubuwa da ba zasu fassaru a bakin wani ɗan adam ba face ita, yanayin fuskarta ya nuna cewa da akwai abin da take tunani sosai da ta tsare shi da ido haka.
"Kamran". Ta ambaci sunansa in a low voice sosai.
Sarai ya ji kiran nata, amma sai ya yi kamar bai ji ba, saboda idan ya nuna ya ji zata fahimci cewa lallai akwai wani abin, zata ce kenan yasan da tsayuwarta a wajen. Da yake shi ma ba tayan baya ba wajen basira, ya ganota, wannan shi ne ɗan na gada ya fi ɗan na koya.
"Kamran".
Ta sake ambatar sunansa da ɗan ɗaga murya kaɗan.
Sai da ya dai'dai ta nutsuwarsa ta yadda ma kada ta gano shi ya yi sakar mata ko ya ɓoye kayan mata a jikinsa, kafin ya juyo da kallonsa a kanta.
"Mamma why are you standing there?".
Ya faɗa cikin nutsuwa.
Shiru ta ɗan yi kafin kuma ta ce. "What's wrong with you?".
Ta yi maganar ne tana kallon cikin kwayar idanunsa da suke ja a yanzu saɓanin a baya da ta san idanunsa farare ne tas.
Wani littafi da ya taɓa karantawa a cikin takardun da take koya mashi karatu ne ya faɗo mashi a ransa, Kamran ya iya reading sosai kamar ba girman Forest ba, Mamma ta koya mashi, tunawa da wani part na short story of love da ya karanta a cikin littafin ya yi, nan take ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da ɗan kwaɓe fuska ya ce.
"Now Mamma kin daina damuwa dani, kina gani na dawo ban ci abinci ba amma ko ki damu, before fa har a baki kike bani abinci idan nace ba zan ci ba".
Wannan magana ba daga zuciyarsa ta fito ba, a cikin wannan littafi ya tuno da ita.
"Yanzu dai tambayarka na yi what's wrong with you ba wai cewa na yi ka gaya mun na damu da kai or not ba".
Ta bashi amsa tare da ƙarisowa in da yake.
"Kanaso ka doje mun ko Kamran? Me kake ɓoyewa?".
Ta yi maganar tare da cire hular da yake a kansa, nan take uban tulin gashin kansa ya watse har bayansa, bashi da mai yi mashi aski bawan Allah, Mammar ce take datse mashi gashin nasa da wuƙa idan ta yi yawa sosai, ga shi kuma da halittar gashi sosai, ya fi mata dayawa gashi, ga gashin nasa a kwance luf yana sheƙi.
Tara mashi kashin nasa ta fara yi tana son ta haɗa ta ɗaure waje guda sai ta ɗauko wuƙa ta rage mashi tsawonsa, dan ta lura ya yi tsawo sosai har izuwa bayansa, hakan yana sanya shi ƴar rama, ita kuma bata son hakan, ta fi son ta gansa ɓul ɓul da shi, wannan dalilin yasa take datse mashi gashin a kai a kai.
"Mamma this two days ina jin canji a jikina sosai, sometimes ina jin kamar sanyin zazzaɓi yana ratsani, and kuma......"
Sai kuma ya yi shiru ya kasa iya gaya mata karshen maganar na cewa gabansa yana tashi ba kamar da ba, bai san me zai ce mata ba.
Sarai ta gane me matsalar tasa tun ma kafin ya sanar da ita, tun ba yau ba ta fahimci yana da karfin sha'awa sosai, sai dai ta zuba mashi idanu ne kawai domin ta ga ko zai iya gane wa ko akasin haka, bata yi zaton zai tunkareta ya tambayeta ba, saboda tasan yana da kunya sosai, ba komai yake iya yin magana a kai ba, yanzu ma idan da yasan menene wlh ba zai yi magana ba bawan Allah.
"Baka barisar da maganar ba ai, and kuma me?".
Ta yi maganar cikin zolaya.
A hanzarce ya ce. "Mammaaaaaaaaa zaki fara ko? Na san kin gane me nake nufi fa, because i know who's my mother, ke ɗin special ce, just kawai ki gaya mun ganyen da zan ciro maki ki haɗa mun maganin, dan gaskiya abin yana damuna".
Ya kai karshen maganar tare da juyowa suna fuskantar juna.
"Ni babu wani abin da na gane, ni likita ce?". Ta yi maganar tana ƙoƙarin barin wajen ta koma cikin ƙogon, dan ta ɗauko wuƙa ta zo ta datse mashi gashin nan nasa.
Cikin hanzari da zafin nama ya riƙo hannayenta cikin nasa.
"Mamma wai yanzu kin dai'na sona ne? Kwata kwata baki kulani sosai".
"Kai da ka girma ni yanzu wani kula ka zan yi? Yanzu fa ka gama mun bayanin lallai da gaske ka girma, shi ne kake son kulawata kuma? Ai sai dai ka kula da ni yanzu".
Ta bashi amsa tana ɗaga mashi gera guda.
Ƴar murmushi ya sakar mata kafin ya miƙe cike da so da kuma kaunarta ya rungumeta a jikinsa, cikin dabara ya zame rigar Pretty da ya ɓoye a wajen plat tummynsa ya mayar ta bayansa, dan kada Mamma ta ji ya ɓoye abu.
"My Mamma you're my world, you're my happiness, you're my everything, ina kaunarki sosai".
Ya faɗa yana kwantar da kansa a saman shoulder ɗinta.
"Kamran this two days ɗin nan kana yin abubuwan da ban saka ka ba sosai".
Ta faɗa tare da raba jikinsu ta nufi cikin ƙogon.
Da sauri shi ma ya nufi ɗakinsa domin ya ajiye rigar na Pretty ya fito, zuciyarsa cike tab da tunanin maganar Mamma na cewa kwana biyun nan yana yin abin da bata sanya shi ba, me hakan yake nufi? Duk sai ya bi ya tsargi kansa, ya afka duniyar tunani.
Kun san ance mutun idan bashi da gaskiya ko yana ɓoye wani abin to fa haka yake, kome zai gani sai ya rinƙa zargin kansa, yanzu dai ita Mamma bada wata manufa ta yi maganar nan ba, hasali ma ta yi mashi harshen damo ne a maganar, abin da take nufi shi ne kwana biyun nan baya yin abin da take saka shi, kunga ɗazun ta ce ya ɓare masara, amma bai yi hakan ba ya zauna saka kayansu Pretty, jiya ta ce ya kawo masu fruits, ya fita ya je wajensu Pretty ya yi zamansa ya manta, kuma da zai dawo ma bai ciro ba, and ya dai'na kawo masu nama a kai a kai, to shi ne harshen domon da ta yi mashi na baya yi mata abin da ta saka shi, amma da yake shi yasan yana ɓoye wani abin, duk sai ya tsargu ya ruɗe yake ganin kamar ta gano shi ne.
"Kamran lafiyarka kawa?".
Voice ɗinta ya daki dodan kunnuwarsa.
Ƴar razana ya yi tare da amsa mata da ba komai. Sam bata son ta fara zarginsa a kan komai, amma zuciyarta ta kasa yarda da canzawar da ya yi kwana biyu, sai take jin lallai akwai abin da yake ɓoye mata, shekaru ashirin da biyar suna a tare bata taɓa ganin canji a tattare da shi ba sai wannan karon, kunga kuwa dole ta damu.
Cike da tunani a zuciyarta ta fara datse mashi gashin kan nasa da kakkaifar wukarta. Shi ma duniyar tunani ya luluƙa, amma fa tunanin Pretty yake yi, face nata yadda take barci a saman shoulder ɗinsa ɗazun kawai yake gani tana yi mashi gizo. Sam bai san lokacin da ya furta sarkin rigima a fili ba.
Sai da ya ji voice ɗin Mamma a cikin kunnuwansa ne ya gane ashe ma a fili ya yi maganar.
"Wacece kuma sarkin rigima?" Shi ne tambayar da ta yi mashi.
Ƴan kame kame ya fara yi ya rasa waye zai cewa Mamma ita ce ƴar rigimar.
Canza mashi topic na hirar Mammar ta yi, saboda ta sanya a ranta tabbas in zai fita zata bi bayansa domin ta ga menene ya canza mata yaro, ta fara tunanin ko dai ya gano wannan mum twins da yake ta yawan maganarta a baya ne a kan ta ɓata, yanzu kuma ya dai'na yin magana tata, to dole da akwai dalili.
Jansa da hira irin na uwa da ɗa ta yi, cike da so da kauna yake amsa mata suna zuba hirar, sai datse mashi gashin take yi tana zubarwa.
Sai da rana ta faɗi suka shiga cikin ƙogonsu, abinci suka ci tare da namar da ta gasa masu, ya kara kyau sosai da Mamma ta datse tsawon gashin nasa ta rage mashi, sai face ɗinsa ta kara wani irin haske.
Bayan sun ci abinci ne suka ɗan taɓa hira kamar yadda suka saba kafin nan kowa ya yi nasa waje ya kwanta.
Mamma tana kwanciya ba jimawa ta yi barci, shi kuwa bai yi barci ba har dare ta tsala sosai, sai juye juye yake yi a saman gadon nasa, shi da kansa ya rasa menene ya hana shi yin barci bawan Allah. Tunaninsa ɗaya kawai shi ne ya tashi ya lallaɓa ya je ya leƙo su Pretty, su kawai yake son gani yasa ya shiga damuwa haka. Sam baya tsoron dare.
Saukar ruwan sama da ya fara gudana a cikin dajin ne yasa ya hakura da tunanin zuwa ganinsu a cikin wannan duhun dare, ya kwanta shiru yana ta tunaninsu har wayewan gari barci ta gagara. Da gari ta fara wayewa ne ya yi maza ya ɗauko abin sakar Mamma ya saƙawa Sweetie rigarta, ya haɗa kayan waje guda ya ɓoye da nufin anjuma in ya fita zai kai masu!.
Da safe kamar yadda suka saba idan suka tashi daga barci haka suka yi, Mamma ta dafa masu abin da zasu ci, ba komai bane face gasasshen nama da kuma ruwan gayyayakin tea masu inganci da ƙara lafiya a jiki. A cikin tea ɗin Kamran sai ta sanya mashi wani ganyen magani green color, kasancewar da zuma suke haɗa tea ɗinsu ba sugar ba, sai yazama ruwan tea ɗin nasu ya yi wani irin orage color mai ɗan duhu, ganyen shayin da suke amfani da shi ya kasance ja ne sosai, so idan suka zuba zuma sai ya ɗan dishashe karfin jan ya ɗan yi kamar orage color, suna da yelwar zuma sosai a cikin dajin, Kamran ne mai ciro masu Mamma kuma ta tace ta zuba a mazubi mai kyau ta ajiye masu suna amfani da shi, zuman da babu mix ko ɗigo a ciki, su ina ma suka san anayi