fara yin magana da wannan yaren nasu dai da bamu jin me suke faɗa, Kamran dai yana bala'in son ya ji me suke cewa, amma babu hali, hakan yasa ya zuba masu idanu kawai ya ga me zasu yi idan suka gama maganar nasu, sai alama yake yi wa Pretty da hannunsa a kan ta gudu ta wata hanyar, kada ta koma cikin ɗakinsu, hakan zai sa a gane maɓoyatsu.
Amma ina ita Pretty sam bata ma san yana saman bishiyar ba, bata ganshi ba, ita dama take tsaye tana jiran kiris ta saki fitsari a wando saboda tsoro, ina ita ina wani kallon sama kuma? Har ma ta ganshi a saman! Ai babu wannan zance.
Kamran ya yi nisa cikin tunanin mafita bai ankara ba sai gani ya yi warriors guda biyu sun diro kasa daga saman dawakansu, cikin takun tsantsar jarumta suna taka ƙasa tana amsawa dip dip dip suka nufi Pretty ɗin.
Tana tsaye ta kasa iya guduwa, tamkar wadda aka sarewa gaɓɓan jikinta ko aka dasata a wajen, ba komai bane ya ja mata hakan kuma face tsoro, tsananin tsorata da ta yi ne yasa gabaɗaya gaɓɓan jikinta suka yi la'asar babu laka.
Ganin sun tunkareta gadan gadan ne yasa Kamran bashi da wani zaɓin da ta rage mashi face ya sauko ya fiskancesu gaba da gaba wata kila su yi mutuwar kasko, dan ba zai iya bari su cutar da Pretty ba, ko da kuwa zasu kashe shi, shi da kansa yasan wlh waɗan nan jiga jigan warriors ɗin sun fi karfinsa, ba zai iya yin faɗa da su ba, dama dai su huɗu ne to zai iya cewa zai kashesu, amma har su takwas shi kaɗai ai kowa yasan idan ba aljani ne shi ba wane kaniyarsa ya iya faɗa da su, amma ya zai yi? Da dai su kashe Pretty gara mashi ya sauko su buga da shi ɗin, idan ya so Pretty ta gudu ta samu ta tsira!.
Hakan yasa shi ya diro ƙasa daga saman bishiyar, bai yi tunanin wani hali Mammarsa zata shiga idan aka kashe shi ba, yasan shi kaɗai take da shi a duniyar nan, tana bala'in kaunarsa fiye da tunaninku, ya zata yi da ranta idan aka ce waɗan nan azzaluman sun kashe shi? Ai ina ga ita ma mutuwa zata yi ko kuma ta haukace kawai!!.
Ganin dirowar mutun yasa warrior da suke tunkarar Pretty suka dakata daga tafiyar da suke yi, tare da ɗaura kallonsu a kan Kamran ɗin. Ya yi tsayuwar cikakkun jarumai! Babu alamar tsoro ko kuma sarewa a tattare da shi, yadda kuka san zai iya da su dukkansu.
Ganin irin tsayuwar da ya yi cike da jarumta babu ko ɗar ɗar ne yasa warriors ɗin suka fara tunanin ko dai da akwai abin da ya taka ne?. Amma da yake a fagen daga ba'a ja da baya kuma ba'a nuna tsoro ko shakku, sai hakan yasa suma basu nuna kamar sun ɗan yi mamakin ganin ɗan ƙaramin kwaron ya yi irin wannan tsayuwa a gabansu ba, sai ma waɗan can warriors biyu da suke tunkarar Pretty ɗin suka juyo ta kansa, gadan gadan suka nufesa.
Cikin harshen turanci ya ce da Pretty ta gudu ta wata hanyar ta daban. Ai kuwa yana yin magana ta ji karfi ya zo mata, dan haka sai ta juya a guje ta nufi wata hanya da take ta can gefe, bata koma cikin ramin nasu ba.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ganin ta gudu, sai dai kuma ɗaya daga cikin warriors da suke a saman dawakan nan ya bi bayanta da dokinsa, hakan ya kara tayarwa da Kamran ɗin hankali sosai, dan haka sai ya yi ƙoƙarin hango warriors ɗin dan ya faɗo kasa daga kan dokin. Sai dai kash, bai kai ga nasarar yin hakan ba warriors biyun nan suka capke shi, wani irin murɗe mashi hannu ta baya da suka yi ne yasa bai san lokacin da ya zube ƙasa a saman gwiwowinsa ba.
Da gudu ɗaya daga cikin warriors da suke a saman dawakansu ma ya rufawa wanda ya bi Pretty baya, suka zamana su biyu ne suka bi bayanta, waɗan nan biyun kuma sun durƙusar da Kamran ɗin a saman gwiwowinsa suna ƙoƙarin cutar da shi, a in da ɗaya ya zaro karamar wuƙa yana son yanke mashi maƙogoron wuya, yadda kuka san ya yi masu wani laifi bawan Allah.
Ganin hakan yasa Kamran ɗin ya fara ƙoƙarin kwatar kansa daga hannunsu, dan shi ma dai kun sani ba tayan baya bane wajen iya faɗa, ya san salo da dabarun faɗa sarai. Hakan yasa ya iya samu da kyar da suɗin goshi ya kwaci kansa a hannun warriors biyun nan, gadan gadan ya fara yin faɗa da su yana son kashesu ya bi bayan Pretty dan kada waɗan can su kamata su kasheta. Cikin zafin nama da zafafawa yake faɗa da mutun biyun nan, mutun huɗu kuma suma saman dawakansu suna ta kallon ikon god ikon gaske, basu taɓa tunanin cewa Kamran ya iya faɗa haka ba, kallon ɗan ƙaramin kwaro suke yi mashi, basu san shi ma babban shege bane.
Cikin ikon Allah, Allah ya bashi nasara ya iya kashe mutun ɗaya daga cikinsu, amma fa ya sha abin da ake cewa bakar wahala na kin karawa a hannunsu!!.
Ganin ya kashe mutun ɗaya yasa wani bujumin warriors ya diro ƙasa daga saman lafiyayyar dokinsa, yana dirowa kuma yasa kafarsa da karfin gaske cikin ɓacin rai za zafin nama haɗe da tafasar jini ya taka Kamran ɗin a kirjinsa, hakan yasa Kamran ɗin ya yi baya baya ya faɗi kasa cikin ciyayi, a fusace wannan warrior ɗin ya yi kansa, wata iriyar shaƙa da ya kai wa Kamran ɗin a wuyarsa ne yasa har idanunsa suka firfito waje kamar zasu faɗi ƙasa. Ran maza ne ya ɓaci, ace ɗan ƙaramin kwaro kamar wannan ya kashe masu mutun guda ɗaya? Ai dole ran maza ya ɓaci, dole su gwada mashi banbancin kwanji, dole su gwada mashi akwai maza a gabansa.
Cikin fusata yasa hannu biyu ya ɗago Kamran ɗin sama, ga shi kuma ya shaƙe mashi wuya sosai, so yake ya daurasa a saman wuyarsa ya karya mashi baya shikenan ya kashe shi sun huta, shi ne yasa ya yi mashi irin wannan ɗagawa sama. Shi kuma ɗayan warrior da suka sha fafatawa da Kamran ɗin ya nufi kan gawar ɗayan da Kamran ɗin ya kashe yana ambatar sunansa yana kuma mai da numfashi. Saura kuma suna saman dawakansu, dan a cewarsu sun fi karfin su ɓata hannunsu wajen yin faɗa da Kamran ko su ce zasu kashe shi, ya yi masu kaɗan, kamar kiyashi suke kallonshi a gabansu su........ E manya manya maganin kanana ba, ya yi mazan fama.
Sosai wannan bujumin mayakin ya ɗaga Kamran ɗin sama zai karya mashi baya, shi kuwa bawan Allah Kamran izuwa yanzu ya fita daga cikin hayyacinsa, saboda shake mashi wuya da wannan mayaki ya yi, sai fafutukar neman numfashinsa yake yi ya dai'dai tata..........
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
Ya ɗaga shi sama da nufin ya sauke shi a saman wuyar tasa ya ɓalla mashi baya, sai dai bai kai ga yin hakan ba wata iriyar mahaukaciyar kifiya mai bala'in dafi ta sauƙa mashi tamkar sauƙar aradu a wuyar tasa, irin waɗan nan kifiyoyin ne wadda ake masu shiri na musamman wanda idan aka caki mutun da shi koda a in da ba zata iya kashe shi ba ne to dafin jikinta tsab zai kashe shi, in dai an harbeka da wannan kifiya to fa sai dai wani ikon Allah, amma wlh tsab zaka mutu, ba kai ba iya cigaba da rayuwa, dan da wasu irin poison masu haɗari ake dafa kifiyar na tsawon lokaci kafin a fara amfani da ita.
Ai tana sauƙa a wuyarsa ma bai san lokacin da ya saki Kamran ɗin ya faɗi ƙasa ba, nan take bakinsa ta fara bulbular da wata farar kunfa fara kal kamar wadda ya ci dangerous poison.
Kafin sauran warriors ɗin su yi wani yunkurin tuni ya zube ƙasa yana shure shuren mutuwa cikin raɗaɗin azaba tare kuma da kai hannunsa saman wajen da kifiyar ta cakesa, ga shi dai kifiyar ƴar marama ce ba kamar na sauran mayaka ko maharba ba, amma sai shegen ɓarna ke gareta kamar nuclear.
A dubu ɗari sauran warriors biyar dake wajen suka fara waige waige suna neman ta ina aka jefo wannan kifiya?.
Shi kuwa Kamran sai ƙoƙari ya ja numfashinsa ya dai'dai tashi yake yi, ya ci bakar wahala na shaƙar nan da ya sha a hannun wannan warrior ɗin, har ya fidda rai da rayuwa, sai kuma Allah ya ƙaddara ba zai mutu a hannun wannan bakin azzalumin mayakin ba!.
Suna tsaka da waige waige basu ankara ba sai jin saukar wasu kifiyoyin har guda uku suka yi a saman wuyar dawakansu. Hakan yasa dawakan suka buga wani irin uban haniniya mai tashin kai tare da yin watsi da warriors ɗin da suke a saman nasu, kan ka ce me suma sun zube ƙasa tare da fara yin birgima suna sure suren mutuwa, already shi wancan warrior da aka fara harba a karon farko da kifiyar har rai ta yi hanlinta, ya mutu ya yi sanyi!.
Sauran dawakai biyun kuwa bazama suka yi cikin dajin a haukace suna neman hanya. Su kuwa waɗan nan jiga jigan warriors ɗin mimmiƙewa tsaye suka yi suna masu cigaba da neman ta ina ake watso masu waɗan nan shegun miyagun kifiyoyin masu bala'in haɗarin wadda ba kowa yake iya mallakarsu ba sai shahararre kuma gawurtatcen mai kuɗi ko Basarake ko dai wani mai mulkin?!.
Da kyar Kamran ya iya miƙewa zaune, yau ya ji hannun maza bawan Allah, idanuwansa sun yi jajir kamar wuta, jijiyoyin kan nan nasa duk sun mimmiƙe tsaye cirko cirko, har wasu siraran jijiyoyi ne suka fito mashi a wajen wuyarsa, ga wata uwar zufa da take tsastsafo mashi, gabaɗaya fuskarsa ta jike sharkaf da zufar, har wata ƴar canzawa ya yi cikin ƙanƙanin lokaci?.
Abin mamaki a nan shi ne, duk wannan uwar wahala da Kamran ɗin yake ciki sam bai damu ba, hankalinsa ma yana a kan tunanin Prettya! Yanzu damuwarsa ɗaya shi ne ya samu ya miƙe ya bi bayanta ko zai iya cetonta daga hannunsu, shi ko ya damu wajen neman wanenen ya taimakesa ma bai yi ba, damuwarsa dai Pretty, hakan yasa ya yi ƙoƙari da kyar ta miƙe.
Da kyar da suɗin goshi ya iya tattaro sauran karfin da suka rage mashi ya miƙe tsaye, har wani irin jiri yake gani yana gilma mashi, amma sabosa karfin hali sai ya daure ya cije ya fara ƙoƙarin ɗaga kafafunsa domin ya yi tafiya.
Yana miƙewa warriors biyar da suke a wajen suka kewaye shi tare da zare takubansu, cikin wannan yare nasu suka yi magana a kan duk wanda yake harba masu wannan kifiya ya fito fili mana idan ba tsoro ba! Kuma idan ya cika cikakken namiji ya fito ne su gwabza gaba da gaba ba ya ɓuya yana harbinsu ba! Idan kuma bai fito ba to zasu kashe Kamran ɗin, sannan idan ya sake harbinsu da kifiya ya tabbata mace rago kuma lusari!.
Shi dai Kamran ko kallonsu da kyau ma baya iya yi, wani irin ɗan duhu duhu yake gani, ƙoƙarin ɗaga mafafunsa kawai yake yi dan ya yi tafiya wajen Pretty.
Cikin fusata ɗaya daga cikin mayaƙan ya nufi Kamran ɗin da wuƙa, dan a tunaninsa idan suka yi yunƙurin kashe Kamran ɗin wannan mai harbinsu da kifiya da ya laɓe a wani wajen zai fito.
Ai kuwa hasashensu ya gaya masu gaskiya, dan kuwa wannan mayaki yana ɗaga takobinsa da nufin ya fillewa Kamran kai, kamar wani walkiya haka mutun ya bayyana a gabansa, sai dai lokacin da mutumin ya bayyana shi kuma mayakin baya da rai, domin kuwa wannan mutumi ya bayyane ne tare da fillewa wannan mayaki wuya da wata sharɓeɓiyar takobi dake hannunsa, irin mahaukatar takuban nan ne masu tsawo ga kaifin balai' na wuce misali a hannunsa.
Matashin saurayi da a kallah ba zai wuce 35 years a duniya ba, dakakken jarumin ne na kin karawa, dan daga yanayin bayyanarsa da kuma tsayuwarsa a gaban waɗan nan warriors ɗin ya nuna cewa daka jiya ne shi ɗin bata yau ba, da alama shiga filin daga ba bakuwarsa bace, duk in da ake neman cikakken jarumin namiji to wannan mutumi ya kai, sanye yake da kaya kusan irin na jikin waɗan nan warriors ɗin, sai dai nasa ya sha banban da nasu, nasa ya fi nasu dakuwa sosai da sosai, sannan kuma shi bai sanya hular kayan yakin nasu a kansa ba, ya dai naɗa wata iriyar rawani a kan nasa wadda ta rufe mashi fuska kamar nikaf, sai kwayar idanunsa da suke sak irin na Pretty zaku gani, olive eyes ke gare shi shi ma, bayan waɗan nan idanun nasa babu kuma wani abin da zaku iya gani a jikinsa, kafafunsa suna sanye cikin wasu shegun takalma irin na mayaƙa masu matuƙar kyau ga karfi, a yadda ya yi wannan tsayuwa ya tabbata zaki ne shi ɗin a cikin zakuna. TO FAH, WAYE SHI?!!!.
Gadan gadan ragowar warriors huɗun nan suka nufeshi da yaki, shi kuma ɗayan ya faɗi ƙasa gefe kansa ma ta yi gefe, domin kan nasa wannan matashin ya cire mai gabaɗaya.
Faɗa suka farayi na gaske gaske, kai daga ganin wannan faɗa dukkansu kasan tsoffin hannu ne, sun saba da yaki, domin kowannensu yana faɗa ne cikin kwarewa da nuna fifikon iyawa. Shi kuwa Kamran bawan Allah, lallaɓawa ya yi a in da ya bar wajen nasu ya bi bayan Pretty, shi ita ce kawai a ransa, ita ce damuwarsa.
Ya ɗan jima yana tafiya a kan wannan hanyar da ta bi ɗin, saboda a hankali yake tafiya, bashi da kuzarin iyayin sauri, dan fa babu karya ya wahala a hannun mayakin can, da an kara minti ɗaya zuwa biyu da sai dai gawarsa, shegu ne warriors ɗin can. Tafiya yake yi yana ƙoƙarin dawowa normal, yana jin jikinsa tana warwarewa, ya bar wannan matashi da basu san ko wanene shi ba yana ta fama da faɗa a wajen.
Can ya hango Pretty zaune a saman wani dutse dake kusa da wata ƙatuwar dutse wanda wani dibgefen bishiyar ɗorawa ya fito a tsakanin duwatsun, sai bishiyar ta bada inuwa sosai a wajen, Allah mai iko, Allah mai yin yadda ya so a koma ina ne, yanzu bishiya ce ta fito a tsakanin duwatsu guda biyu kuma har ta girma haka tana bada inuwa, Allahu Akbar.
Ganin ta a zaune a wajen yasa Kamran ɗin ya ji wani irin karfi ya zo mashi, sai ya ji wani irin daɗi da sanyi har cikin ransa, hakan yasa ya nufeta da sauri.
Ita ma tana ganinsa ta miƙe tsaye daga zaman da take yi tana kallonshi har cikin ido. Ɗan kawar da kallonsa daga kan kyakkyawar kwayar idanun nata ya yi, dan kada ku manta suna birkita mashi lissafin ƙwaƙwalwa. Da sauri ya ƙariso wajen nata.
Da ƴar gudunta ita ma ta ƙariso in da yake, tana zuwa kuma ta faɗa jikinsa tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, baiwar Allah dama duk a tsorace take, ta zauna a wannan waje ne kawai dan ba yadda zata yi, duk da cewa bata san wanenen Kamran ba, amma ya fi mata kowa dake a cikin dajin nan sau dubu, dan kuwa shi tun farko da suffar taimako ya zo masu, so hakan yasa take tsananin jinsa a cikin ranta sosai da sosai, wannan dalilin kuma yasa ta rungume shi tana kerman tsoro.
"Pretty are you okey? Where's the warriors?!".
Ya faɗa da wata iriyar kasalalliyar murya wadda da ka jita kasan ta karfin hali aka yi aka ƙaƙalota dan ayi magana. Ya yi magana kuma shi ma yana rungumarta da kyau a jikinsa, dan wani irin kukan da take yi sai ta baka tausayi, da alama taga mutuwa kusa da kusa ne!.
Kasa amsa mashi tambayar da ya yi mata ta yi, sai ma kara ƙanƙame shi da ta yi tana mai kara sautin kukan nata tare da gudun hawayenta.
Ɗan bubbuga bayanta ya fara yi yana mai faɗin. "Is okey Pretty, ki yi shiru".
Ina ta kasa yin shirun. Ganin haka yasa ya raba jikinsa da nata tare da riƙo hannunta suka koma saman dutsen da ta tashi ɗin suka zauna. Nan fa ya shiga rarrashinta yana mai lallaɓata a kan ta yi shiru.
Ɗan rungumota a gefen kirjinsa ya yi yana mai cigaba da bubbuga bayanta alamar rarrashi.
Almost 10 mins suna a haka kafin ya samu ta fara yin shiru, sai wani irin shesshekar kuka mai ban tausayi take yi!.
Sai da ya tabbatar da ta ɗan nutsu ya lallaɓata ta yi shiru, sannan ya sake tambayar a karo na biyu ina mayakan suke?.
Fararen idanun nan nata sun yi jajir saboda kukan da ta sha, abinku da farar fata harta fatar face nata ya yi jajir da shi, hancin nan nata kamar wadda aka kama mata shi da clip na kama kayan na tsawon lokaci yanzu aka saki, ya yi jajir da shi, duk kuma saboda kukan ne.
Kyakkyawar farar tafin hannunsa Kamran ɗin ya kai saman beautiful face yana goge mata hawayen, ta kwanta shiru a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya tare da mai da numfashi, ƴar kaniya taga bala'i ne yau.