"Tom shikenan tun da baka son zancen, nasan maganinku ai, bari su Ramish ɗin su zo, kun kusa dai'na yi mun yawon tsakar dare a cikin gida".
Guntun murmushi ya yi kafin ya ce. "Wai ni daddy daga ina ma kake samun information a kanmu ne? Wai duk yadda muka yi fitar sirri ranar sai da kasan mun fita ko? Kuma wai ya aka yi kasan ina hira da Jannat a ɗakin Akka?".
Cikin zolaya ya amsa mashi da. "Ka bari Akka ta kamaka a cikin room nata kana soyayya, a nan ne zaka gane ta in da nake samun information, kasan halinta ai, zaka yi bayani randa ta riƙeka".
"Daddy soyayya kuma? Ni fa kawai hira muke yi da su, dan su ɗebe mun kewa".
"Hirar ce har da yiwa autata wayo ku korata ta tafi ta baku waje ko?".
Shafa kansa ya yi yana murmushi, yanzu dai kam ya rasa abin faɗe domin ya kare kansa, shi dai ba zai yarda soyayya suke yi ba, dan ba yanzu ya so bayyana soyayyarta ga kowa ba, ita kanta ma bai bayyana mata bare sauran familyn, ai ba yanzu ba a cewarsa.
"Ka rasa abin faɗe don cigaba da kare kanka ne?". Ya yi maganar yana ɗaga mashi gera.
"Ni daddy barci ma nake ji, kuma da gaske ni da Jannat babu wani abin da yake a tsakaninmu, wai ni yaushe na kori auta ne ma? Daddy masu baka bayanin nan sun yi mun sharri".
Hararar wasa ya wurga mashi kafin ya ce. "Ko? To ce maka nayi akwai masu bani bayananku ne? A kan me zan buƙaci mai saka mun ido a kanku bayan ina da rai'na da lafiyata? Kawai duk abin da kuke yi ne yana cin karo da a lokacin ina wajen, da idona nake ganin komai, wai shin anya ma amsar da ka bawa Abbas gaskiya ce kuwa? Jawad sanadiyyar Jannat ka fara koyan karya ko?".
"Daddy barci nake ji sosai, in je in kwanta please?". Ya yi maganar ƙasa ƙasa irin a ce da gaske yana jin barcin.
Gefensa King ɗin ya nuna mashi tare da cewa. "Zo mana ka kwanta, yau kuka fara yin barci a nan ne? Zo mu kwana tare".
A hanzarce ya girgiza mashi kai yana faɗin. "No daddy zan je room ɗina in kwanta......."
Katse shi cikin zolaya ya yi da cewa. "Ba zaka iya yin barci ba sai ka yi wa Jannat addu'a ko? To je kayi mata sai kazo mu kwana tare".
Miƙewa ya yi tare da nufar kofar fita yana faɗin. "Allah daddy kai da daddy idan kuka saka mutun a gaba babu daɗi, ni yanzu fa na gaya maka gaskiya babu komai a tsakaninmu".
Still cikin zolaya King ya ce. "To ai dama ni bance ba gaskiya ka gaya mun ba, sannan kuma ni ban ce akwai komai a tsakaninku ba, kawai dai idan ta yi tsami zanji ai".
Ficewa ya yi yana murmushi, daddy ya gama gane komai, amma ya tsaya sai waske mashi yake yi saboda wata banzar dalilinsa na cewa sai gaba zai bayyanar da soyayyarsa................... Allah sarki rashin sani yafi dare duhu, da yasan bala'in da yake tinkarosa a gabansa da cikin daren ba sai gobe ba zai gayawa King gaskiya ya kuma ɓukaci da a ɗaura masu aure gobe da safe, amma bai sani ba!.
Yana fita part na King kai tsaye nasa part ɗin ya nufa, wanka ya je ya yi tare da shiryawa cikin tsadaddun kayan barci riga da dogon wando launin brown, ya yi kyau sosai a cikinsu kasancewar yana da hasken fata, yau sai ya kara fitowa sak uncle Abbas, shi ma gashin gerarsa ta kusa haɗewa irin na Jaish, sai zuba kamshin perfume mai daɗi yake yi.
Wayarsa ya ɗauka tare da fitowa waje. Bai zame ko'ina ba sai ɗakin Chuchun kamar yadda kin ya faɗa kuwa.
Yau auta bata cikin ɗakin, tana tare da Mommarta tun bayan da suka gama cin abincin daren.
Tura kofar ya yi ya shiga tare da yin sallama ƙasa ƙasa. A lokacin kuma ta kammala shiri cikin kayan barcinta kenan, ta hau gadon hannunta rike da waya tana ƙoƙarin kiran layin Rizwan, dama hira suke yi ta ce mashi bari ta yi wanka kada dare ya yi sosai, shi ne ya ce idan ta kammala ta kira shi.
Ta yi matuƙar kyau sosai cikin riga da wandon barcin nata, ga su launin dark purple, kasancewar jajir yasa kalar ya yi mata kyau, sannan sleeping dress ɗin nata sun zauna a jikinta cif cif, ta ɗaure arab hairnta kashi biyu, a kowani bakin jelar gashin nata ta ɗaure shi da rebbon white color, saboda kada ya warware, gashin nasu yana da tsantsine sosai, hakan yasa dole suke ɗaure bakin jelar gashin da rebbon. Da alama sleeping dress ɗin nata basu da hula, dan bata sanya ba.
Jin sallamarsa haɗe da turo kofar yasa ta kai kallonta bakin kofar tare da dakatawa daga kiran Rizwan da take ƙoƙarin yi.
Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Yah Jawad baka yi barci ba?".
Cool murmushi shi ma ya maido mata tare da maido mata da tambayar tata. "Kema baki yi barci ba?".
Kai ta gyaɗa mashi tare da ajiye wayar tata a gefe ta juyo da kallonta mai gabaɗaya a kansa. "Yah Jawad to meyasa baka yi barcin ba?". Ta tambaya tana zuro da kafafunta kasan gadon.
"Kasa yin barcin na yi, barci yaki zuwa, shi ne na ce bari na zo mu yi hira". Ya yi maganar tare da harɗe hannayensa a saman kirjinsa, sannan ya jingina da jikin door ɗin kofar, hakan yasa kofar ta rufe kirif sosai.
Wani irin daɗi ta ji da jin kalamansa na cewa ya kasa yin barci ne ya zo su yi hira, tana son kasancewa a tare da shi yanzu da ya dai'na takura mata.
Vibrate ɗin wayarta da ta ji ne yasa ta kai kallonta kan wayar. Yah Rizwan, shi ne sunan da yake yawo a saman screen ɗin wayar, ji ta yi ba zata iya ɗaga kiran ba, saboda a gaskiya tun da har Yah Jawad ya tako kafarsa ya zo har in da take domin su yi hira dan ya kasa yin barci, to dole ta bashi lokacinta su yi hirar. Dan haka sai bata ɗauki kiran ba har ya yanke, yana yankewa kuma ta kashe wayar gabaɗaya tare da dawo da waɗan nan fararen idanun nata a kansa.
Ya zuba mata idanu yana ta kare mata kallo ya jingina da jikin door. "Yah Jawad meyasa kake ta kallona haka?".
Kamar bakinsa na yi mashi ciwo, a hankali ya motsa lips ɗinsa ya furta. "Saboda kin yi kyau sosai".
Daga in da yake ya jiyo saukar ajiyar zuciyarta, alamar ta ji daɗin maganar.
"To Yah Jawad ka shigo mana". Tana magana tana murmushi mai kara mata kyau.
Girgiza mata kai ya yi alamar a'a, kasa kasa ya ce. "Ba sai na sai na shigo ba, ganinki daga nan ma ya wadatar".
"To ni in zo ne?".
Girgizara mata kai nan ma ya yi. "Ba zaki juri tsayuwa ba ai, dan haka yi zamanki a saman bed ɗinki daga nan ma ina iya kallonki da kyau".
"Yah Jawad zan iya tsayuwa mana, bari na zo, dan ni bana ganinka da kyau". Ta kai karshen maganar tare da sauƙowa kasa ta nufo shi.
Tun da ta miƙe ya kara kura mata ido from head to toe yana kallonta, kayan barcin sun yi mata kyau sosai. A kusa da shi ta zo ta tsaya tana faɗin. "Yah Jawad Allah kai ma kayi kyau sosai, kalar sleeping dress ɗin nan naka ya yi maka kyau".
Can kasa kamar mai raɗa ya ce. "Da gaske?".
Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e. Ji ya yi duk jikinsa ta yi la'asar, ya kasa motsawa daga jikin door ɗin, yana son ya ɗan karkato su fuskanci juna da kyau, amma ya kasa, saboda wani irin kasala da ta rufe shi.
"Yah Jawad ya naga kuma kamar kana jin barci?". Ta faɗa tana jingina da jikin bangon kusa da door ɗin.
Nisawa ya yi kafin ya ce. "Ke ki ka ja mun jin barcin ai".
Zaro idanu ta yi tare da cewa. "Ni kuma?".
Lumshe idanu ya yi dan ba ƙaramin kara tafiya da imaninsa ta yi ba da ta zaro idanu.
"Ganinki yasa har na fara jin barci". Ya bata amsa da ɗan buɗe murya.
"Tom ka je ka kwanta".
Girgiza mata kai ya yi alamar a'a. "Meyasa?". Ta tambaye shi da mamaki. "Saboda ganinki ya fi barcin daɗi".
A wannan karon ta ɗanyi mamakin jin hakan, bata damuwa a duk lokacin da ya ce mata ta yi kyau, dan tana ɗaukar hakan a matsayin yabo na yaya da kanwa ne, amma yanzu da ya ce ganinta ya fi barci daɗi sai ta ji kamar Rizwan ne ya yi maganar, dan shi ma yana gaya mata hakan wani lokaci, idan ta ji yana hamma alamar mai jin barci, idan ta ce ya kwanta ya yi, sai ya ce mata hira da ita ya fi barcin daɗi....... Tirƙashi.
Ta luluƙa duniyar tunani bata ankara ba sai ganin hannunsa ta yi saman fuskarta, shafa face ɗin nata ya yi yana faɗin. "Tunanin me kike yi my sister da har ina magana baki ji ba".
Da yake dai akwai yarinta sosai a tattare da ita sai ta kawar da wancan tunanin tare da sakin cool murmushi. "Babu tunanin da nake yi".
Ƴan hannayenta ya riƙo cikin nasa hannun guda ɗaya, wasa da yatsun hannun nata ya fara yi yana faɗin. "Jannat da gaske yau kin yi mun kyau fiye da kowacce rana".
Zata yi magana suka ji knocking na kofar room ɗin. A tare suka zaro ido ita da shi dukka. Abin gwanin ban dariya.
Janyota jikinsa ya yi, a kunne ya raɗa mata koma wanene ya zo kada ta yarda ta gaya mashi ita da waye a cikin ɗakin, bari ya ɓuya a cikin toilet ɗinta. Shi a cikin zuciyarsa yana tunanin King ne ko kuma Mummynta, cikin biyun nan, dan yasan auta kam izuwa yanzu ta yi barci, ba zai lamunci wani ya kama shi a ɗakinta almost 11 na dare ba, duk da suke matsayin iyayensa sun san halinsa ciki da waje, su suka renesa, amma dole shaiɗan zai raya masu wani zargin a ransu idan suka gansa a irin wannan lokacin a ɗakinta, so maganin bari kada a fara, kada ya bari su kama shi ma bare shaiɗan ya raya masu wani abin.
Da sauri ya saketa tare da raba jikinsa da jikin door ɗin ya nufi cikin toilet. Sai da ta ga shigarsa sannan ta dai'dai nutsuwarta tare da ɗan ja baya daga wajen kofar, ƙasa ƙasa ta ce. "Wanene?".
Murɗa handle ɗin door ɗin aka yi tare da turo kofar, dama ɗazun kofar taki buɗuwa ne yasa aka yi knocking, saboda kunga Jawad ya jingina da ita, shiyasa taki buɗuwa.
Jin ba'ayi magana ba an turo kofar ne kawai yasa ta ɗan zaro idanu..............
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 12/9/2024.....✍️📚🌹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
Jin ba'ayi magana ba an turo kofar ne kawai yasa ta ɗan zaro idanu tana jiran kawai taga wanene?.
Tun kafin ya shigo kamshin perfume ɗinsa ya isar mata da saƙon wanene, hakan yasa ta ɗan sauke ajiyar zuciya tare da ɗan sakin fuska.
"Jannat me kike yi har yanzu baki kwanta ba? Almost 11 something fa yanzu, kuma me ya tsayar dake a tsakiyar ɗakin?". Ya jefa mata tambayar tun bai ƙarisa shigowa ciki ba.
Ƴan kame kame ta fara yi, bata iya karya ba, bata son kuma ta karya maganar Yah Jawad, ta rasa me kuma zata ce.
"Jannat ba da ke nayi magana bane? Ko baki da lafiya ne?".
Lokacin guda ta gyaɗa mashi ta sake girgizawa, alamar e bata da lafiya kuma a'a lafiyarta lou. Shiru ya ɗan tsaya ya zuba mata ido da kyau yana kallon yadda take ƴan kame kame, zallar rashin gaskiya ne a tattare da ita.
"Ina Jawad?". Ya jefa mata tambayar ne dan yana son fahimtar wani abin!.
A ɗan ruɗe ta ce. "Daddy ni ma ban gan shi ba". "Keda waye a room ɗin da naga kamar alamar ba ke kaɗai bane? Kuma na je room ɗin Rahilarh na tatda Auta a can bare nace ke da ita ce".
A hanzarce ta amsa da. "Daddy bani da kowa bane, ni kaɗai ce a ciki, ban jima da fitowa wanka bane, yanzu na gama shirin kwanciya, dama yanzu zan kwanta".
Da hannu ya yi mata nuni da saman bed ɗinta. "Jeki kwant to bari na yi maki addu'a, ita ce ta kawoni dama".
A hanzarce ta juya kamar dama jira take yi ya ce ta je ta kwanta.
Binta da kallo ya yi zuciyarsa na ayyana mashi ba ita kaɗai ce a cikin ɗakin ba, koma ita kaɗai ce to tabbas Jawad bai jima da barin ɗakin nan ba, dan akwai kamshin perfume nasa a ɗakin, ga rashin gaskiya dake tattare da ita sosai.
A gefen bedside drawer ya zauna tare da karanto addu'oin kamar yadda ya saba yi masu kullum, ya tofa a hannunsa ya shafeta da shi, sannan da kansa ya janyo mata lallausan katuwar bargonta ya lulluɓeta. Cike da tunani a ransa ya miƙe ya ɗauki wasu remote guda biyu dake cikin bedside drawer. Ya yi amfani da ɗaya wajen kashe wutar ɗakin, ɗayan kuma ya yi amfani da shi wajen rage gudun Ac. Cike da kaunar ƴaƴan nasa ya yi mata good night.
Tana daga cikin bargo ta amsa mashi da daddy Allah ya tashe mu lafiya. Amin ya amsa da shi kafin yasa kai ya fice izuwa ɗakin Gimbiya Aneesa ƴar Mama. A kowacce dare haka yake binsu ɗaya bayan ɗaya yana yi masu addu'a tare da dubasu ya tabbatar suna cikin aminci, abin gwanin ban sha'awa, yana sauke hakkinsa a matsayinsa na uba, ƴaƴa mata sai da kula sosai!.
Yana ƙoƙarin janyo mata kofar ɗakin nata ya rufe ne wayar Jawad daga cikin toilet ta fara kara alamar shigowar kira. Ɗan dakatawa ya yi yana son tantance kirar waya ce ko menene? Da yake wayar bata da ƙara kamar android phone. Mamaki ne sosai ya bayyana a kan fuskarsa, shiru ya ƙasa kunne yana sauraro.
Bai kai ga tantance komai ba Jawad ya yi saurin ciro wayar daga aljihun wandon sleeping dress ɗin nasa, cikin hanzari ya katse karar yana sauke ajiyar zuciya.
Jin shiru ne yasa King ɗin ya yi tunanin ba ringing na waya ya ji ba, kila gizo abin ya yi mashi, dan haka sai ya ja mata kofar ɗakin nata ya wuce, sai dai har ga Allah zuciyarsa na tunanin kamar Chuchu ba ita kaɗai bace a cikin ɗakin, amma sai ya yi ƙoƙarin kore tunanin tare da shiga wajen Aneesa.
Ɓangaren Jawad ɗin kuwa. Ganin sunan Yah Rizwan ne yake yawo a saman screen ɗin wayar tasa yasa bayan ya ji fitar King ya rufo kofa sai ya yi ƙoƙarin picking. Sai dai bai kai ga ɗauka ba wayar ta katse. Fara ƙoƙarin bin call ɗin ya yi sai ga kiran ya sake shigowa.
Kallon kansa a jikin mirror dake gabansa ya yi, hannu ya kai ya ɗan shafi face ɗinsa kafin ya yi picking.
"Ka fara barci ne my brother?". Rizwan ya jefa mashi tambayar bayan ya yi sallama kenan.
"A'a Yah Rizwan ban yi barci ba, lafiya?"
Daga ta cikin wayar ya jiyo saukar ajiyar zuciyar ɗan uwan nasa. "Lafiya lou, amma Jawad ya na ji voice ɗinka haka? Baka da lafiya ne?" Cike da kulawa sosai ya yi maganar.
Rizwan da Jawad suna kaunar junansu fiye da tunaninku, yanzu haka King ne ya gayawa Rizwan ɗin yana zargin kamar akwai abin da yake damun mashi marayarsa, shi ne yasa Rizwan ɗin ya kasa barci ya kira shi domin ya ji menene yake damun ɗan uwan nasa, ba zai iya yin barci ba in dai bai san menene yake damun Jawad ɗin ba.
One thing da ban gaya maku akan Rizwan and Jawad ba shi ne, Jawad and Rizwan fa uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, dukkansu ba Mammie bace ta haifesu, Mammie matar uncle Abbas ta biyu ce, Sarina ita ce ƴarta ta fari sai Fanan wadda take son Jaish ya aura kenan, ita bata da ɗa namiji. Jawad King Zuhair ne ya renesa, tun ranar da aka haifesa yana cikin tsumma uncle Abbas ya baiwa King shi, shiyasa kuka gansa baya a part ɗin uncle Abbas yake tare da Jaish, tsakaninsa da Jaish kwana uku ne kacal ratar, kusan rana ɗaya aka haifesu kenan, so a tare suka taso, tare suka yi wasa, dan King ya haɗawa Momma sune a Dubai, dan kun san ita a can taken haihuwa, haka kawai King ya zaɓi da ya bata Jawad ɗin ta haɗa da Jaish, ita ma tana ra'ayin rikesa yasa ta roƙa, ko da zata dawo sai ta barosu a can, tare suka yi komai, makaranta da komai har zuwa lokacin da suka dawo ƙasar, wannan dalilin yasa kuka ga suna kaunar junansu shi da Jaish ɗin over.
Sannan Rizwan yana kaunar Jawad fiye da tunaninku, dan shi kaɗai yake da shi, ban san dalilin Mammaien na son haɗasu faɗa a kan mace guda ba, suna matuƙar kaunar junansu, ta zo ta cusawa Rizwan kaunar Chuchu bayan tasan Jawad yana sonta. Shi kuma Rizwan yana yi mata biyayya ne saboda a ganinsa ta riƙe shi tsakani da Allah,