x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 48 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 141001 words
  • 144000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 384

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
sun jike mata fuska, sai simtiri suke yi, sun wanke mata fuska sosai, wani irin kukan zuciya ma da take yi tun da uwarta ta haifeta bata taɓa yin irinsa ba, sai dai kuma duk da haka bata jin akwai wani abin da zai dakatar da ita daga fita wannan gida, tana son ta koma wajen ƴan uwanta, ba zata iya hakuri da mahaifinta tare da ganin kabarin mamarta saboda Jasrah ba, haka zalika bata jin kuma kamar zata iya rabuwa da Jasrah ɗin. Tashin sense, dole kuma a ciki ta ɗauki ɗaya.

A ruɗe Jasrah ta zauna a kusa da ita, duk ta rikice tana son ta ji me ƴar uwar tata take yi wa kuka? Me yasameta ko me suka ce mata a office ɗin da ta je. Shoulders ɗinta ta rungumo tana mai cigaba da faɗar subhanallah.

Da taga dai Leesharh ba zata iya gaya mata me suka ce mata ba, dan yarinya ce mai zurfin ciki, sai ta yanke shawarar bari ta yi mata nasiha wata kila idan nasiha ya ratsata zata sami nutsuwa har ta gaya mata abin da yake faruwa, a nutse ta fara magana kamar haka.

"Leesharh duk tsanani yana tare da sauki, duk abin da yake da farko dole yana da karshe, kuma ki sani duk wata second ɗaya da zata wuce a rayuwarmu Ubangiji baya barci yana sane damu, ni bansan me suka ce maki a cikin office ɗin ba, amma dai koma menene nasan ba mai daɗin ji bane, dan abin da yake sanyaki kuka ba ƙaramin abu bane, to koma dai me suka ce maki ina son ki yi hakuri ki fawwalawa Allah al'amuranki, da sannu zai yi mana sakayya, ni har cikin zuciyata ban taɓa yarda da cewa ke kika kashe Oummunki ba, kin kuma ki gaya mun gaskiya yau tsawo shekara guda kenan, amma dai koma me Allah ya fimu sanin dai'dai da ba dai'dai ba da kuma abin da ya dace damu, shiyasa na miƙa mashi ragamar rayuwata, ni bance dole sai kin gaya mun abin da suka gaya maki ba, abin da nake so dake kisani a nan shi ne komai ya yi zafi koda ya fi wuta zafi to maganinsa Allah, duk abin da suka ce maki idan alkhari ne a gareki Allah ya tabbatar maki, idan kuma sharrine to Allah ya wargazar da shi, amma please ki dai'na wannan kuka, mu yi addu'a komai zai koma dai'dai da izinin Allah".
Ta kai karshen maganar ita ma idanunta suna cikowa da kwallah.

Sosai Leesharh ta samu saukin raɗaɗin da take ji a cikin zuciyarta da jin kalaman Jasrah. Haƙiƙa duk abin da Jasrah ta faɗa gaskiya ce, hakan take babu wata tantanma, sai ta ji ta ɗan sami kwarin gwiwar da zata iya gaya mata abin da ya sanyata kuka, dan haka sai ta kai hannu ta goge hawayen da suke a saman fuskarta, cikin voice ɗinta kamar wata yarinya yar shekara huɗu a duniya ta fara korawa Jasrah bayanin abin da yake faruwa daga farko har karshe kamar yadda wannan mata ta gaya mata da yadda suka yi dukka.

Da Aaradiya da Sarah sun mayar da su Tv na kallo, kallonsu kawai suke yi babu kyafta idanun, tunani kawai suke yi da ace sune suka sami wannan damar mana, ai da shikenan komai shar abinsu su bar gidan.

Shiru Jasrah ta yi tana sauraronta, har sai da ta kai aya a maganar tata, tana yi wasu hawaye suna ƙara bin ƙuncinta sosai.

Da yake Jasrah babu mugunta ko ɗigo a ranta, ita ɗin tana sowa ɗan uwanta abin da take sowa kanta ne, sai ta saki cool murmushi ga ragowar hawaye a fuskarta.
"Leesharh ai wannan abin farinciki ne bana kuka ba, ke da zaki fita daga wannan gida, kuma ke da zaki koma wajen iyayenki da ƴan uwanki, to me abin kuka? Ai godewa Allah ma zaki yi sosai, alwala yakamata mu tashi mu yi dan mu nunawa Ubangiji murnarmu, Addu'arki ce ta karɓu wata kila".
Tana magana ne da dukka iya gaskiyarta, tabbas zata sha kukar rabuwa da Leesharh, kuma zata shiga damuwar da bata taɓa shiga ba, domin da ita kawai ta saba a gidan, amma kuma hakan ba shi zai sanya ta tauye gaskiya ko ta hanata cigaba saboda son zuciyarta ba, sam ba haka take ba ita.

Wani irin confidence Leesharh ta kara ji ya dira mata, sai ta ji kaso sittin na damuwar da ta shiga duk ya gudu, ta lura da cewa tabbas Jasrah ta shiga damuwa, amma kuma ta yi ƙoƙarin danne damuwar tata dan kada ta sarewa Leesharh ɗin gwiwa.

Aaradiya da Sarah da yake bakaken zuciya ne da su, kuma basu son Leesharh ta fita gidan ta barsu, sun fi son a kashesu a tare kamar yadda aka yanke masu hukunci tun farko, sai abin ya sosa masu rai over, nan take suka ji koma ta halin ƙaƙa ba zasu bari Leesharh ta fita ta barsu su a kashesu ba, dan haka har suna haɗa baki wajen cewa.

"Ke Leesharh baki da hankali ne da zaki yarda da wannan mata? Wlh kada ki yarda da ita, kila ma kasheki zata je ta yi, gara maki ki zauna a nan wlh yafi maki".

Da yake ita Jasrah ta fisu shekaru kuma ta fisu wayo da ilimi, sai ta fahimci in da suka dosa, ta ganosu hassadace kawai take cinsu, dan haka sai ta ce.
"Da can baya babu wadda ta taɓa bawa Leesharh shawara a cikinku ko? Kuma babu wadda ta taɓa yi mata maganar da zai amfaneta ko? Babu wadda ta taɓa shiga harkarta a cikinku ko? Sai yanzu ne kuke ganin yakamata ku bata shawara kenan?".

Da yake Leesharh har yanzu da sauranta, yarinta yana a kanta sosai, sai taga kamar amsar da Jasrah ta basu bai dace ba, a wawtarta ita gani take yi ai sonta suke yi tun da har suka bata shawara. Wannan shi ne da gaske ne ta yaro kyau take yi bata ƙargo.

Wani kallon uku saura kwata Aaradiya ta wurgawa Jasrah ɗin kafin ta ce. "To uwar kanzagi, ai da yake sunan Jasrah muka kira ba Leesharh ba, ina ruwanki da mu? Dole ne mu bata shawara dan munga zata faɗa halaka".

(Ni kam na ce su shawara manya, Aaradiya manyan kasa😅🥱)

A takaice Jasrah ta amsa mata da cewa. "Ko kuma dan kunga zata fita ba za'a kasheta ba, zata fita ta barku ba, shi ne hankali duk ya bi ya tashi".

A harzuƙe Aaradiya ɗin ta miƙe zaune, nan take ta hayyako da hayakin masifa kamar wadda dama take wuya tana jiran kiris ta zazzageta.

Jasrah bata sake bi ta kanta, ba kuma ta sake maida hankali ta saurari hayakin masifar da take barbalo masu ba, ta toshe kunne tare da maido da hankalinta a kan Leesharh da take ta faman binsu da idanu.

"Leesharh baki gaya mun a gidan waye zaki yi aikin ba? And kuma baki gaya mun wasu irin bayanai na mutumin zaki kwasa ki bawa wannan mata ba, sannan ina son kafin ki tafi ki gaya mun kasar da kike da sunan iyayenki ko da baki bani labarinki ba, zan gayawa kanwata Alveena idan sun kawo mun ziraya watarana ko bana raye ta je ƙasarku ta kai maki ziyara idan ta girma".

Duk wata zuciya mai tausayi sai ta tausayawa Jasrah a wannan gaɓa, sai ta ji wani irin mugun tausayinta, saboda daga jin yadda ta yi maganar kasan kawai ta ƙaƙalo ta ne dan dole, daga jin muryarta kasan e lallai tana cikin matsananciyar tashin hankali da damuwa.

"Aikin da zan yi mata ta ce mun duk wasu motsi nasa tana son ta rinƙa sani, kamar in da zai je da kuma idan ya fita gida, yaushe yake fita? And kafin ya fita tana son sani? Yaushe yake dawowa gida, and idan ya dawo gida ma tana son ta sani da dai sauran dukkan motsinsa, and duk wani muhimmin tattaunawa da zai yi da ma koma waye shi ma tana son ta sani, iya aikin da zan yi mata kenan, batun wajen da zan yi aikin kuma ni ban san a ina bane, ban san wani gida bane, ni dai ta ce mun gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen, so ban san waye shi ba, sai dai ta kaini na gani, batun iyayena da ƴan uwana kuma zan baki..........."

Wani irin jan birki ta yi, ta tsaya cak da maganar tata sakamakon wani irin mimmikewa tsaye da ta ga Jasrah, Aaradiya and Sarah sun yi. Ɗan zaro idanu ta yi tana kallonsu a cike da mamaki.

Ai a dubu ɗari Aaradiya ta diro ƙasa daga saman bed ɗinta, cikin sarkewar murya ta ce. "A gidan waye zaki yi aiki?".

Da wani irin kallon mamaki ta bita da shi kafin ta maimaita mata kalmar gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen.

Wani irin kara Aaradiya ta fasa kamar wadda aka tsinkawa mari, sai kuma ta sake cewa. "Tab Allah ya bada sa'a, ai Leesharh ki je kawai abinki, ashe banza muƙa ɓata bakinmu wajen baki shawarar karki je ma, ai baikamata mu hanaki tafiya ba, ni yanzu ba zaku sake jin bakina a wannan case ɗin ba, lastly dan girman Allah Leesharh kada ki sake yin tunanin kin sanni a rayuwarki, please koda watara za'a tambayeki wa da wa kika sani a rayuwarki ki ce ke baki sanni ba bama ki taɓa ganin mai kama da ni ba".
Tana kai karshen maganar tana wuce ta haye saman gadonta.

A hanzarce Sarah ta karɓi zance da cewa. "Ki haɗa da ni Leesharh, dan girman Allah ko da sunan wasa kada ki taɓa sake tunanin cewa kin sanni".

Ita dai ta yi kasake tana kallon ikon Allah, daga ambatar sunan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen duk sun ruɗe haka? To waye shi?.

Dafa shoulder ɗinta da aka yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka.

"Jasrah wannen Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen ɗin?" Ta wurga mata tambayar a ɗan ruɗe, dan ta tsorata na ganin yadda su Sarah duk suka bi suka ruɗe daga jin sunan mutumin.


Wani irin dogon numfashi Jasrah ta ja tare da saukewa a hankali, shiru ta ɗan yi na a kallah mintuna uku kafin ta sake nisawa ta fara magana a nutse.

"Tabbas ni ba haifaffiyar nan Dubai bace, amma kuma duk wanda ya kwana ya tashi a cikin Dubai dole zai san familyn Badeen, dole zai san wannen Shaikh Abu Abdussalam bin Badeen, magana ta gaskiya ni yanzu na ji ban ma yarda da cewa wannan mata zata iya shigar dake cikin wannan gida ba farko kenan, gidan da aka ce maki tun daga farkon titin da zai kaika cikin unguwar da gidan yake wasu mahaukatan securitys ne wadda ganinsu tamkar ganin mutuwa haka yake, ban taɓa zuwa gidan ba, amma babana yana bamu labarin gidan, ke in takaice maki ko tsuntsuwa waɗan nan securitys ɗin da da hali ba zasu bari ta gifta ta sararin samaniyar wannan gida ba, babana ya ce duniya ne guda gidan, ma'aikata masu yi masu aiki kawai sun fi mutun 50, a hakan ne zaki shiga cikinsu a matsayin mai aiki? Zaratan mata ne masu lafiya da jini a jika, mata masu kirar maza su suke yin girkin wannan gida, to ina mai tabbatar maki duk wani motsin ma'aikatan wannan gida suna sane da shi, wlh Leesharh gwara maki mutuwa a cikin wannan gidan yarin da ki je ki karɓi aikin leƙen asirin gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen, dan naratse maki da wanda rai'na yake hannunsa idan suka kamaki wani irin kisan walaƙancin da zasu yi maki ko kare ba zai shinshini namarki ba, yafi maki sauki ki tabbata a cikin nan da ki fara tunanin zuwa gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen ziyara ma kawai, wannan mata da ta kawo maki wannan aiki ma sam sam babu ƙwaƙwalwa a cikin kanta, da alama mahaukaciya ce".

Izuwa yanzu cikin Leesharh ya gama ɗuran ruwa, ta tsorata sosai da jin maganganun Jasrah, sai zaro idanu take yi, amma sai ta daure ta ce.
"To Jasrah wanenen shi ɗin?".

Da sauri Aaradiya ta ce. "Ni ne nan zan baku wannan amsa, dan ko ita Jasrah magana kawai yake yi bata san wa ake kira da Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen ba, ku saurara ku ji wanenen shi ɗin. Shi ɗin ɗane ga the most powerful King of Dubai, babban Yayan Shaikh Abu Abdussalam shi ne president mai ci a yanzu, shi kuma Abu Abdussalam Defence minister ne, shiyasa securitys kala kala suka yawaita a gidansa, domin duk wani security da kuka sani a faɗin Dubai, duk wani mai kaki (uniform ) da kuka sani to dole da umarninsa zai yi aiki, a ƙarƙashinsa suke, dole umarninsa zasu bi kafin aiwatar da wani abin, yana da manyan brothers har guda uku masu rike da manyan muƙamai masu karfin faɗa a ji a duniya bakiɗaya, amma babban yayansu baya kasar nan ma bakiɗaya, King of Dubai ƴaƴansa maza biyar ne mace ɗaya ita ce Gimbiya Rahilarh (Mommar Zunaira) ita ce kuma auta, su Abu Abdussalam bin Badeen duk yayyunta ne, Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen matarsa ɗaya yayansa uku, mata biyu namiji ɗaya, wannan shi ne kaɗan daga cikin labarin gidan da zaki je leƙan asiri, familyn da manyar ƙasar nan suke tsoron haɗa hanya da su, sai dai muce Allah ya bada sa'a yasa ki samu mutuwa mai sauki a hannunsu......"

Tana rufe baki Jasrah ta karɓi zancen da cewa.
"Wlh Leesharh gara maki ki mutu a cikin wannan gidan yarin da ki mutu a hannun ƴan gidan can in suka kamaki, tab akwai ma wanda ya isa ya shiga gidan leƙen asiri ne?! To wlh ki shafawa kanki ruwan sanyi, meyasa ita matar bata je ta yi aikin da kanta ba? Sai ke zata saka bakar muguwa azzaluma! Kuma meyasa ba zata saka maza manya ko kuma mata manya ba? Sai ke ƴar ƙaramar yarinya? Ai naga manya ne ma zasu yi mata abin da take da buƙata daidai, sune suke da girman da sun san ta yadda zasu zulle kada a kamasu".

Sosai Leesharh ta kara tsorata over, muryarta na rawa ta ce. "Ni ai kinga ta ce mun taimakonsa zasu yi, wai wani ne ma yake son cutar da shi su kuma zasu taimaka mashi, kuma ta ce mun wai manyan maza ko mata ba zasu iya samun damar shiga har cikin gidan ba bare su sami kusanci da shi, da alama baya yarda da kowa, amma ni karama ce babu wanda zai yi tunanin leƙen asiri na je yi, zasu yarda na shiga cikin masu aikin da suke aiki a can cikin gida ba tare da wani damuwa ba haka ta ce mun".

"Hmmmmm Leesharh ya tabbata baki da hankali, waye ya ce maki taimakonsa suke son yi? Idan har taimakonsa suke son yi menene na neman information a kan duk wani motsinsa? Su fito mana kai tsaye kawai su sanar da shi cewa ga wani zai cutar da shi in gaskiya ne, wlh babu wani taimakonsa da zasu yi face cutarwa, sannan maganarki gaskiya ce da kika ce ke kamar yarinyar ce ba wanda zai kawo wani bad tunani a kan ki, kuma za'a iya barinki ki shiga cikin ma'aikatan da suke aiki a can cikin gidan, amma ki sani hakan ba mai ɓulle maki bane wlh, dan yadda kika san aljanu haka familynsu suke, kin san takun sakar da ake bugawa da su a duniya kuwa? Kin san adadin makiyan da suke son kaisu kasa kuwa? Ta ko'ina tarin makiya suke da shi sakamakon riko da gaskiya da suke da shi, suna sane da tarin makinyan su, a haka kuma kuke tunanin zasu yi zaman shiru har wani ya iya shiga cikin ya leƙa asirinsu? Lallaima Leesharh na tabbata makiyan familynsu ne suke son yin amfani dake dan cinma burinsu, ki sake yin tunani da kyau, na tabbata sun hango cewa amfani dake zai basu nasara ne yasa suka buƙaceki, wlh idan kika shiga hannunsu ina gaya maki gawarki ma ba za'a gani ba, mahaukatan karnikan gidan ne kawai zasu cinye namarki ɗanya, wata ƴar figaggiya dake a wajen ne zaki ce zaki je leƙar asirin shegun duniya ko?".

Shiru Leesharh ta yi, gabaɗaya ta shiga ruɗani kanta ya ɗaure, duk ta rasa me yake yi mata daɗi, yanzu ya zata yi?..... Masu karatu ku bawa Leesharh shawarar ya zatayi, shin ta yarda ta yi wannan aiki ne ko kuma ta hakura a kasheta a wannan gidan yarin kawai? Ni dai bari na leƙa su Kamran namu na amana mu gani, wata kila kafin mu dawo Leesharh ta samu mafita, amma kam tana ruwa kusa da kada..........🥱

🏞️FOREST🏞️

Kamran ba dan ya so ba ya tashi Sweetie daga barci, dan su koma gida, saboda ya haura lokacin da yake komawa, ya tabbata idan ya ɗan kara ƴan mintoci Mamma zata fito nemansa, dan haka sai ya tashi Sweetie daga barci, ita kuma Pretty sai dai ya ɗauketa cak, dan san kai irin nasa sai bai tasheta daga barcin ba, ko da yake abokiyar rigimarsa ce, ba son kai bane...........😅

Hannun Sweetie ɗin ya riko bayan ya saɓa Pretty a saman shoulder ɗinsa, da haka suka nufi maɓoyar tasu, ya bar Rocky a wajen yana aikin zuba barci, yasan duk lokacin da ya tashi daga barcinsa zai komo gida.

Da kyar ya iya shiga da Prettyn cikin wannan rami, sai barci take zubawa, da alama yau barcin nata ya yi nauyi sosai. A saman gadon nasu ya kwantar da ita, ita kuma Sweetien ya zaunar da ita a bakin bed ɗin, ba tare da ɓata lokaci ba ya yi maza ya kama hanya tare da yi wa Sweetie sallama.

Kai tsaye gida ya nufa, bai sake bi ta kan Rocky ba, sai sauri yake ta zuba wa kada Mamma ta yi faɗa.

Yana shigowa cikin ƙogon nasu ya wuce ɓangarensa, tunanin Pretty ce kawai a cikin zuciyar tasa.

"Mamma where are you?". Ya faɗa yana
End Ads