ai da tana koya mana abubuwa sosai har da su karatun Alqur'ani mai girma".
Maimaita sunan Alqur'ani mai girma ya yi tare da tambayarta wani littafi ne kuma Alqur'ani mai girma?. Ɗauko wani ƙaramin Alqur'ani na mum ɗin nasu mai English translation ta yi tare da dawowa kusa da shi ta miƙa mashi tana faɗin ga Alqur'ani nan.
Da yake yarinya ce babu ruwanta da yana da tsarki ko bashi da shi, kawai ta miƙo mashi full Alqur'ani izu sittin abinta. Shi kuwa da yake bai ma san menene bane sai ya sanya hannu kawai ya karɓa tare da fara dubawa.
"Kamran you said that you have some surprise for me, kuma baka bani ba". Ta kai karshen maganar tana zama a kusa da shi.
Yana kan duba farko farkon Alqur'ani ya amsa mata da close your eyes na baki. Ba musu ta kai ƴan kyawawan fararen tafukan hannunta ta rufe fuskarta tana ɗan murmushin da yasa dimples ɗinta suke lotsawa sosai.
Juyo da kallonsa a kanta da kyau da kyau ya yi tare da rufe Alqur'ani ya rike da hannunsa na dama. Ganin yadda take ɗan murmushin dimple ɗinta yana lotsawa ne yasa ya sanya karamar yatsarsa a ramin dimple ɗin nata yana faɗin. "Irin na Mammana". Idan baku manta ba Mamma tana da dimples.
Kara faɗaɗa murmushinta ta yi idanu a rufe. "Ka kaini in ga mammarka ɗin". Ta faɗa ba tare da ta buɗe idanu ba.
Ɗauke hannunsa daga saman face ɗin nata ya yi tare da fito masu da kayansu da ya ɓoye a ƙugunsa wajen da yake ɗaure wuƙarsa.
"Mamma ba zata zama abu mai daɗi da zamu iya gani ba, haɗuwarku ba zata yi kyau ba, dan haka ki bar batun yanzu, maybe wani lokaci zan gwada".
Daga jin yadda ya yi maganar zaka san ya yi ta ne kawai, amma ba cikin daɗin rai ba, Pretty tasa ya ji wani irin a ransa, sabuwar tunani a kan meyasa mamma bata son yin taimako ne ya dawo mashi a cikin kwakwalwarsa, ya yi iya tunanin da zai yi domin ya gano dalilinta na kin taimakawa mutane, amma ya kasa iya ganowa, kuma babban abin ban mamakin a nan shi ne, ita tana bala'in kaunar Kamran ɗin kamar ta yi mashi numfashi, amma bata son kowa, bata tunanin cewa kamar yadda take son ɗan nata kowa ma haka yake son nasa? Ita dai a'a nata ɗan ne kawai mutun, saura duk a banza suke, wannan abin da ɗaure kai sosai wlh.
"Meyasa ka ce haka?". Cool voice ɗin Sweetie ne ya katse mashi tunanin da yake yi.
Nisawa ya yi kafin ya ce. "Wani lokaci zan gaya maku, now Pretty open your eyes?".
A hanzarce ta janye tafukan hannayenta da ta rufe fuskar nata tare da waro idanun nata waje. Miƙa mata kayan dukka ya yi tare da bin face ɗinta da kallo, yana fargabar ta ce kayan basu yi mata ba, dan ita fa na gaya maku bata suturta abu, in dai bai yi mata ba ƙaramin aikinta ne ta dubi idanunsa ta ce bata so basu yi kyau ba, da dai Sweetie ne zata hakura ko da basu yi mata ba ta yaba su, amma Pretty wlh ba zata yabi abin da bata so ba, tab ai ko a gaban abin zata ce bai yi mata ba, sai dai dik abin da zai faru ya faru.
Wani irin cool murmushi ta saki wanda ya kara bayyanar mata da kyanta sosai. "Kamran kamar kasan irin kayan nan naka yana yi mun kyau sosai idan na gansa a jikinka". Ta faɗa tana warware kayan ta gani.
Ɗan yatsarsa ya kai saman wannan ɗan ƙaramin lips ɗin nata na kasa, a hankali ya ɗan shafi lips ɗin nata tare da faɗin. "Me ya ji maki ciwo a nan Pretty?".
Ɗan turo bakin ta yi kafin ta amsa mashi da. "Waƴan can mugayen dodannin ne mana, da suka ɗaga ni sama da gashin kai'na zasu ɗaurani a saman dokinsu, sai wannan mutumi ya harbesu da wani abin irin naka da zaka koya mun harbin nan, da ya harbesu shi ne suka sake ni na faɗi kasa bakina ya ɗan fashe, da mutumin ya zo ne sai ya ɗaga ni ya ce na gudu".
Shoulder ɗinta ya ɗan rungumo tare da ɗan jawota jikinsa kaɗan, sannan ya sanya yatsunsa guda biyu na hannun da ya rike da Alqur'ani nan ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, sam yaki yarda ya kalli cikin idanunta, hannunsa kawai ya sanya ya ɗan buɗe ɗan bakin nata domin ya ga ciwon da ta jin da kyau.
Hakorinta ne suka ji mata ciwo a lips ɗin tata, amma ta ciki ne, kaɗan ne ya fito ta waje, sai ka lura sosai ma zaka iya gane cewa ta ji ciwo a wajen, da yake shi Kamran ɗin tana a cikin ransa shiyasa ya yi saurin gane cewa an ji mata ciwo, kuma sau da dama ya fi yawan kallon ɗan bakin surutun nan nata, idan ya kallah yana tuna ranar da aka haifeta ta rinƙa ihu, hakan yana sanya shi shiga cikin nishaɗi........😅
Kamran dai ya kasa mantawa da ranar da aka haifi Pretty ta rinƙa ihu, wato har nishaɗi yake ji idan ya tuno da ranar, lallai kuwa Pretty zata sha gori idan ta girma ta zama ƴan mata ta fara yi mashi yanga, zai ce ke dallah mai kuka kawai yi mun shiru......😅
Kallonsa sosai take yi har cikin idanu, shi kuma ya zubawa ciwon nata idanu yana kallon yadda hakwaranta guda biyu suka haɗu suka datse namar wajen har ya yi jini, ga wajen ya yi jajir ya kuma ɗan kumbura, tunanin ciro mata magani ya fara yi, dan ba ya jin zai iya jure komai ƙanƙantar ciwo a jikinta ba tare da ya nema mata magani ba.
Slowly ya dawo da kallonsa a saman face nata gabaɗaya, ta wani tsare shi da idanu tana jiran ta ji me zai ce, har da wani kara kwanciya mashi a jiki, dama yaya lafiyar kura bare kuma ta yi zawo? Dama bai janyota jikinsa bama ta iya kwanciya bare kuma ya janyota da kansa, ai shikenan kuma ta samu gado da katifa har ma da pillow.
Ganin yadda take kallon cikin kwayar idanunsa sosai ne yasa ya hura mata iskar bakinsa a ido, a tunaninsa hakan zai sanya ta rufe idanun nata. Ga mamakin sa kuma sai yaga ko kyafta idanun ma bata yi ba bare asa ran zata rufe su, yadda kuka san ta sume ido a buɗe, kawai kallonsa take yi...... Dole ya ce idanuta suna rikita shi, wanna yarinyar akwai abubuwan mamaki sosai a tattare da ita, koya aka hurawa mutun iska a cikin idanu sai ya ɗan ji wani iri, wani ma harda kwallah yake yi saboda iskar, wani kuma a take zai datse idanun, amma ita kunga ko kyaftawa ma bata yi ba bare asa ran zata rufesu.
Ba ƙaramin mamaki ta bawa Kamran ɗin ba, sake hura mata iskar ya yi a karo na biyu yana mai cigaba da kallon idanun nata. Ko gezau bata kyafta ba. Tsoro ne ya ɗan kamashi kada ace sume mashi a jiki ta yi, da sauri ya ɗan girgizara tare da ambatar sunanta.
Nisawa ta yi tare da amsawa tana sakin wani irin cool murmushi. Nannauyar ajiyar zuciya shi kuma ya sauke tare da cewa. "Kekam ba mai iya maki, yanzu me kika tsareni da ido haka?".
Hannunta ɗaya ta kai ta dafa shoulder ɗinsa ta gaba tare da gyara kwanciyarta a jikin nasa ta ce. "Yanzu me na yi?".
Yadda ta gyara kwanciyar tata sai gurun wuyarta ya fito sosai. Yatsunsa biyu na hannun da yake rike da Alqur'ani mai girma ya kai saman wuyar tata yana faɗin. "Pretty wannan tsokar da take a wuyar nan taki tana yi mun kyau over, tana kara maku kyau sosai har Sweetie, amma kuma kamar mum ɗinku bata da shi ita".
Girgiza kai Pretty ta yi, cikin sauri ta ce. "Kasan mum ɗin mu ne?".
Sai a lokacin ya san ya yi suɓutar baki, ƴan kame kame ya fara yi yana son waske mata kada ta gane shi ne wanda mum ɗin nasu ta ce su nemo.
Tsare shi da ido ta yi, sai gabaɗaya ya tsargu ya rasa me zai ce. Ƴan hannunta ta kai saman karan dogon hancinsa ta ja da ɗan karfi har sai da ya ce wash. "Amsa me, kasan mum ce?".
Girgiza mata kai ya yi alamar a'a bai san ta ba, kawai tunani yake yi kamar ita bata da gurun wuyar. Da yake dukkansu yara ne sai ya yi wasa da ƙwaƙwalwarsu ya waskar da zancen, sai dai fa ita Sweetie ta fahimci akwai abin da baya son su sani, tabbas ko dai shi ne wanda mum ta ce su nemo, ko kuma dole da biyu yake zuwa wajen nasu, ko dai yama san in da mum ɗinsu take kawai baya son gaya masu ne, shi ne tunanin da Sweetie take yi.
"Kamran bari na ɗauko maka wani rubutu da Mum ɗinmu ta yi, ta ce mu bawa wannan mutumi idan muka gansa, sai kuma wani littafi karami da ta ce shi ma mu bashi, yanzu bari na ɗauko maka takardan tun da ka iya karatu sai ka karanta mana mu ji me mum ta rubuta". Cewar Pretty sarkin kauɗi, ta yi maganar tare da yunƙurawa ta bar jikinsa.
Da kallo kawai ya bita, har cikin ransa yake jin duk wani magana da zata yi, zazzaƙar voice ɗinta yana ratsa shi sosai da sosai.
Wannan envelope ɗin da ya ɗauka ranar shi ta ɗauko mashi, a saman gado ta zauna tana faɗin. "Sweetie in nunawa Kamran ya karanta mana mu ji me mum ta ce?".
Sam Sweetie bata so hakan ba, bata so ace Pretty ta ɗauko wannan ajiya ba, saboda mum dai ta ce sai wannan mutumi kawai zasu bamawa, amma ta je ta ɗauko shi, ga shi ba halin ta ce mata ta mayar da shi kada ta nuna mashi, zai ji babu daɗi tun da yana wajen, da baya nan ne, amma a gabansa ba zata iya cewa kada a nuna mashi ba, dan haka bata da wani zaɓin da ya wuce ta ce. "Ki nuna mashi iya takardan kawai, sauran abubuwan kuma duk ki barsu a cikin envelope ɗin".
To ta amsa mata da shi, cikin hanzarce ta fara fito da abubuwan da suke a ciki, ba iya takardan da aka yi rubutu bane kawai a ciki, har da wasu ring guda biyu iri ɗaya sak, da wasu chain suma gida biyu irin ɗaga, irin siraran chain ɗin nan ne, kansu akwai tambarin ɓauna kamar tambarin gidan sarauta, haka shi ma ring ɗin da yake a cikin, shi ma yana ɗauke da wannan tambari, akwai dai karikitai a ciki, sai wani littafi mai kama da diary, da alama tarihin rayuwarta ta rubuta a ciki ko makamancin haka.
Wata farar takarda dake nannaɗe ta fito da shi, sannan ta kwashi duk sauran abubuwan ta mayar ciki tare da rufe envelope ɗin ta ajiye a gefe guda.
Warware takardan ta yi tare da cewa Kamran zo ka gani. Ba musu ya taso hannunsa rike da Alqur'ani ya dawo kusa da su ya zauna. Ita dai Sweetie shiru abinta baiwar Allah.
Shinfiɗe takardan a gabansu ta yi tare da cewa ya karanta masu su ji.
Fara karanta rubutun da aka rubuta cikin harshen turanci ya yi, amma kafin ya fara karantawa sai da ya tsaya ya tsare rubutun da idanu sosai, yadda kuka san ba hanu bane ya rubuta shi, kamar computer ce ta rubuta, rubutun ya tsaru sosai da sosai, komai daki daki.
"Gaisuwa da fatan alkhari a gare ka Kamran, nasan da izinin Allah saƙona zai iso gareka, ban yarda da kowa ba a rayuwata sai kai, ga amanar ƴaƴana na baka, na san zaka kula mun da su sosai, a yanzu basu da kowa a duniyar nan sai Allah sai kuma kai, zan so kasan tarihin rayuwarsu ko in ce rayuwata, akwai wata littafi da na ajiye maka a tare da wannan saƙo da kuma wasu abubuwa, a nan zaka sami dukkan wata amsa a kan rayuwata, daga karshe ina mai yi maku fatan alheri tare da yi maka albishir da idan Pretty ta girma na baka aurenta duniya da lahira, ita kuma Sweetie ka rike mun ita tamkar kanwarka na jini, na gode sosai godiya mara iyaka". Shi ne abin da yake rubuce a jikin wannan takarda.
Slowly ya ɗago da idanunsa bayan ya kammala karanta saƙon, saman face ɗin Pretty ya sauke fararen idanun nasa, while ita ma shi take kallo har cikin idanu. Cikin nutsuwa da sanyin muryar ya ce mata. "Pretty menene kuma aure? Na ji mum ɗinku ta ce ta bani aurenki".
Ya kai karshen maganar yana cigaba da kallonta.
"Kamran ɗan sake karanta mun layin farko na sakon bari na kara ji". Cewar Pretty, ta yi maganar kamar wata mai cike da ɓacin rai.
Bai kawo komai a ransa ba, sam bai fahimci ya yi suɓul da baka ba, kawai ya sake fara karanta mata. "Gaisuwa da fatan alkhari a gareka Kamran........"
Dakatar da shi ta yi a wajen tare da sake tambayarsa wani suna ya karanta a wajen?. Sai a lokacin ya fahimci ya saki layi wajen karanta sunansa da yake rubuce a wajen, abin gwanin ban dariya, shi gabaɗaya ma ya mance da cewa ya ɓoye masu shi ne wanda suke nema, to yau dai fa Pretty ta kamo shi tsamo tsamo, ba sauran waskiya kuma.
Ƙasa ya sunkuyar da kansa tare da ɗan fara shafa hular da yake a kansa, ƙasa ƙasa ya ce. "Kila wani Kamran ɗin ne mai irin sunana, amma bani bane".
A ƙule Pretty ta yi kansa tare da kai hannunta dukka biyu ta riƙo kunnuwarsa, da karfi ta fara ja tana faɗin. "Ashe ma wani Kamran ɗin ne ko? Har yanzu baka tuba ba kenan? Ba zaka dai'na yi mana wasa da hankali ba?".
Da yake da karfin take jan mashi kunnuwan nasa hakan yasa ya ji zafi ya ziyarcesa, da sauri ya janyota ta faɗa jikinsa tare da cire ƴan hannayen nata daga kunnuwar nasa yana faɗin. "Haba mana, ki bari kada ki cire mun kunnuwa, da zafi fa".
Kuka ta saka mashi har da hawaye, ita a dole ta ji haushi ya yi masu karya. Ita kuwa Sweetie cikin nutsuwa ta ce. "Kamran da gaske kai ne ko ba kai bane? Please kada ka yi wasa da zuciyoyinmu ka ji? Kai mutumin kirki ne sosai, na tabbata ba zaka so ka ganmu cikin ƙunci ba, so please ka gaya mana gaskiya".
Yana ƙoƙarin ƙanƙame Pretty dake son tashi daga jikinsa ta nufi waje, sai kuka take yi hawaye wani na bin wani ya amsa mata da cewa. "Da gaske ne Sweetie, ni ne, na ɓoye maku hakan ne ba dan komai ba sai dan naga zaku iya ganeni da kanku ne ko ba zaku gane ba, amma kuyi hakuri kin ji?". Ya kai karshen maganar dai'dai lokacin da Pretty ta kwace kanta tare da barin jikin nasa, ta diro kasa daga saman bed ɗin ta nufi waje tana kuka sosai.
"Pretty sarkin rigima, to me abin kuka kuma? Ai daɗi ma yakamata ta ji tun da mun ganoka yau, shiyasa mana kake kula damu sosai, dama mum ta gaya mana zaka kula damu sosai" Cewar Sweetie.
"Haka ne Sweetie, amma ku yi hakuri da ce maku bani bane da na yi". Yana magana hankalinsa na a kan Pretty da ta bar cikin ramin, burinsa kawai ya bi bayanta ya je ya rarrasheta.
"Ba komai Kamran, ai kai yakamata ma mu bawa hakuri". Cewar Sweetie baiwar Allah.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya miƙe tsaye tare da ɗaukar kayan da ya kawo masu wadda Pretty ta zubar da su a kasa ta nufi waje, ya ɗaura kayan a saman gadon tare da ajiye Alqur'ani hannunsa a kan gadon yana faɗin. "Bari na bi bayan Pretty ina zuwa yanzu". Yana kai karshen maganar bai tsaya jiran me zata ce ba ya nufi wajen shi ma.
Yana fitowa ya fara waige waige ta ina zai hangota, a hankali ya fara takawa yana naman ta ina take wannan yarinyar.
Can saman dutse wajen ƙorama ha hangota, ta takure jikinta waje guda, da alama a tsorace take da zamanta a wajen, kawai dai karfin hali ne yasa ta zauna, irin ita ta yi zuciyar nan, ta yi fushi. Dariya ma ta bashi, gata da tsoro kuma ga ban tsoro.
A hankali ya lallaɓa ya nufi wajen nata, har lokacin kuma gawarwakin warriors ɗin yana wajen, sai dai ba ta gefen da Prettyn ta zauna ba, ta can gefe ita Pretty ta je ta zauna, da yake wajen yana da matuƙar girma sosai.
Ta yi shiru ta zubawa ruwa idanu tana kallon yadda yake zuba gwanin ban sha'awa, ga hawaye a saman fuskarta. Ruwan wannan ƙoramar yana da matuƙar haske sosai, tankar yake.
Sam bata ji motsin mutun ba sai ji ta yi an rufe mata idanu ta baya. A tunaninta warriors ɗin ne suka dawo, dama a tsorace take da zama a wajen, kawai dan tasan Kamran yana nan, kuma zai biyo bayanta ne ma yasa ta daure ta cije ta zauna a wajen, ba dan haka ba ina ba ita ba fitowa yau.
Wani irin ihu ta kurma har sai da arear wajen ya amsa, a dubu ɗari ta fara ƙoƙarin tashi ta gudu, dan kwata kwata bata kawowa ranta cewa Kamran ne ya rufe mata idanu ba.
Ganin a garin gudunta tana ƙoƙarin faɗawa cikin ruwan yasa Kamran ɗin ya yi saurin zame hannun nasa daga idanun nata ya yi maza ya riƙo kugunta ta baya. Jikinsa ya janyota dan kada ta faɗa ruwan. Sai ƙoƙarin kwace kanta take yi, dan bata san waye bane, ga shi yana ta bayanta babu halin taga fuskarsa.
"Sarkin tsoro ai sai ki nutsu ni ne to". Ya faɗa yana ɗagata sama zai sauko da ita kasa daga saman dutsen, dan ma kada ta yi ta afka cikin ruwan nan ta sanya shi faɗawa ba shiri, bai shirya shiga ruwa da safiyar nan ba.
Yana sauƙo da ita kasa ta juyo tare da fara kai mashi duka a kirji na tsoratata da ya yi, ya wani zo ba excuse ya tsoratata a banza, ya