x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 70 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 207001 words
  • 210000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 402

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Zainab a tare da Hauwa, dukkansu sun ci uwar kwalliya, ko daga ina suke haka oho dai.

Sannu da zuwa Sadiq ya yi wa baban Zee ɗin yana bin Hauwa da kallo, sai wani yauki da yange take yi, tana sanye cikin shadda da ya sha ɗinki mai kyau, ko rantsuwa Sadiq ya yi ba zai yi kaffara ba wannan shadda daga shagonsu aka ɗauketa, wato kayan da baban Zainab ɗin ya kwasa ranar da ya je shagon ita ya kaiwa kenan? Sadiq ya tambayi kansa da kansa, lallai akwai cakwakiya ba kaɗan ba. Sai zuba kamshi suke yi suka nufi cikin gidan.

Saboda tsabar mugunta irin na Hauwa ce ta ce sai dai baban Zainab ɗin ya rakota ta gaisa da maman Zainab, dan tana kewar kawar tata, kawai ta yi hakan ne dan ta kara kunsawa maman Zainab bakin ciki, yanzu fa Hauwa bata gidan mijinta, da alama kashe auren ta yi ko wani abu makamancin hakan, yanzu haka daga gidan kanin mahaifinta ta fito, garinsu maman Zainab kenan, ita ma Hauwa dama mahaifinta ya jima da rasuwa, ya riga baban su maman Zainab ɗin ma rasuwa, so already dama a hannun kanin mahaifin nata take, ku ma shi ba mutun ne mai karfi ba, kusan kaso saba'in na matsalolin gidansa ma Hauwar ce take ɗaukar nayinsu, shiyasa duk abin da zata yi yake ganin tana a kan dai'dai, dan yana tsoron kada ya ce bata yi dai'dai ba ta ɗauke mashi tallafi, Allah ka rabamu da mutuwar zuciya. Yanzu ta zubar da ƴaƴan nata wa dangin mijinta ta koma garinsu.

Suna sako kafarsu a cikin parlourn aka sake yin knocking na kofar gidan, a lokacin shi kuma Sadiq yana ƙoƙarin shiga room ɗinsu, dan ya je ya ɗan kwanta ya huta kafin ya fita kasuwa.

A dubu ɗari maman Zainab ta miƙe tsaye na ganin Hauwa a tare da baban Zainab da ta ɗauki kwanaki bata sanya shi a idanunta ba.

Wani irin shu'umin murmushi Hauwa ta sakar mata tare da faɗin. "Gaskiya nayi kewarki sosai maman Zee, yau dai na ce dole baban Zee ya rakoni na zo mu gaisa, zan iya zama a kujerar taki ne?". Cike da kirsa da makirci ta yi maganar, daga jin yadda take magana kuma ba sai an faɗa ba kunsan da biyu ta yisa, ta yi ne duk domin da kara jefa zuciyar maman Zainab cikin ƙunci.

Kallon baban Zainab kawai maman Zee take yi, tamkar bata san da Hauwa a wajen ba. Shi kuwa Baban Zee tamkar bai san da mama Zee ɗin a cikin parlourn ba, wucewa ya yi ya zauna a saman sofa yana faɗin. "Hauwa me ya tsayar dake a tsaye? Ki samu wuri mana ki zauna......". Yanzu fa har su Khadija ma ya mance da su bawan Allah.

Bai gama rufe baki ba aka banko labulen parlourn aka shigo ciki. Ba kowa bace face su maman Haidar, dama tsawon kwanaki yau suna neman baban Zee ɗin basu samu ganinsa ba, shi ne nan suka sanya Haidar da ya saka masu ido duk idan ya ga giftawarsa ya sanar da su, sun zo gidan ya fi sau a kirga suna cin mutuncin maman Zee a kan wai ita ta hanashi zuwa wajensu, basu san ita kanta bata samu ganinsa da ido ba, amma haka suke cin mata mutunci son ransu, sai dai ta bisu da ido kawai. To yanzu kafin baban Zainab ɗin ya zo gida sai da suka fara zuwa kasuwa Hauwa ta kwashi abin da take so, sannan ne suka nufo gidan, a nan ne kuma Haidar ya gansu, shi ne ya yi maza ya sanar da mamar tasa ta hanyar kiranta a waya ya ce mata to ga baban Zainab ya nufi gidansa, shi ne suka biyo sahunsa dan su zo su ji dalilinsa na kin zuwa in da suke, su kira wayarsa ba zai ɗauka ba, ga batun aurensa da suke ta jiran ya zo ya je su gaisa da bappan nasa a samu a saka rana, ayi komai cikin ƙanƙanin lokaci, ƴar bapparsa suke son aure mashi dama, to fa shi ne suke ta nemansa amma shiru, sai yau Allah ya yi suka ji labarin ga shi a gida, shi ne suka kwaso ayari suka yi maza suka zo.

Ko sallama babu suka faɗo cikin parlourn fuskoki babu mutunci, shi kuma Haidar ya tsaya daga bakin kofa. Baban Zainab yana zaune a saman sofa tamkar bai san da shigowarsu ba.

Maman Zainab ce ta ce masu. "Sannunku da zuwa".

Ita kuwa Hauwa wani irin kallon sama da ƙasa ta wurga masu kafin ta ce. "Ya zaku wani shigowa mutane cikin ɗakin babu ko sallama kamar wasu dabbobi? Ko dai ba musulmai bane ku?".

Ɗan zaro idanu maman Zainab ta yi tana kallon Hauwar da mamaki a saman face ɗinta, shi kam baban Zainab ko gezau, bai ma ɗaga idanu ya kallesu ba.

Maman Hanif wato kanwar maman Haidar ita ce ta ce. "Ke kuma wacece? Daga ina kuma?".

Kallon uku saura kwata Hauwa ta watsa masu kafin ta buɗe baki zata yi magana maman Haidar ta rigata da cewa. "Ke maman Hanif ai da baki bata amsa da baki ba, buge bakin shegiya ya kamata ki yi har sai ya fitar da jini, an gaya mata mu sha'anin yinta ne da zata nemi ta gaya mana magana ko ta yi mana rashin kunya?".

A walaƙance Hauwa ta basu amsa, dan dama a kule take da su har wuya, musamman ma maman Haidar, ta tsani matar sosai, tasan labarinsu dukka a bakin maman Zainab, tasan duk irin cin kashin da suke yi wa maman Zee ɗin, shiyasa ita ta ɗaura ɗamarar cin ubansu one by one, da gangan kuma dama ta zagesu daga shigowarsu, dan tana son su fara gwabzawa ne da su tun daga yanzu, duk sai ta saita masu zama tun da su basu da lissafi.

"Ke tsohuwar kokon giya dallah ki rufewa mutane baki, kada ki sake sanya mun baki a maganata, an gaya maki ni Aisha maman Zainab ce? Ba zan ɗauki iskancin ku ba, yanzun zan sanya mata ta san matsayinta, bani da mutunci ko miskala zarratin kuma ban san hanyar in da mutunci take ba, dubeki wata a koɗe dake futu futu kin yi tsufar kokon giya, wlh na zabga maki mari idan baki mai da hankalinki ba, an gaya maki ruwa sa'ar kwando ce? Ke baki ga kalar ba? Na yi kala da waddan tsofaffin kokon giya zasu kawowa wargi ne? Yanzu zan sa ki gane annabi ya faku". Cewar Hauwa.
Yadda take magana tamkar wadda ake karantowa tana faɗa ko kuma wadda aka sanyawa battery, daga ji kasan wannan dama tun ainahi ƴar tijara ce, bala'i da masifa ya jima da samun matsuguni a wajenta.

Tsit maman Haidar ta nutsu, dama tsoron bala'i ke gareta, kawai dan sun rena maman Zainab ne yasa suke cin mutuncinta dai'dai gwargwado, amma banda haka mugayen matsorata ne, to yau dai sun sami dai'dai da su.

Maman Zainab kam sake baki ta yi tana ganin ikon god, ashe dama akwai abin da zai sanya maman Haidar yin shiru a duniyar nan? Wannan shi ne gaba ma da gabanta wai aljani ya taka wuta, duk iskancinta da balai'nta yau dai ga shi ta nutsu tsit ana kwashe mata albarka ba bakin tankawa. Babbar magana, ana dirama a cikin wannan gida.

Haidar dake a tsaye a bakin kofa ne ya yi kanta cikin fushi da nufin dukanta, a cewarsa bai ga dalilin da zai sanya ya tsaya wata ta tsaya tana gayawa mahaifiyarsa maganganu marasa daɗi son ranta ba.

Wani irin tsawa ta daga mashi wadda ya sanya shi jan birki babu shi, a walaƙance ta ce. "Dakata ƙaramin maras kunya, ai kai taka rashin kunyar nafila ce tun da iya nan gidan kawai ka iya baje ta, wlh idan ka yi kuskuren sanya hannunka a jikina duk danginka babu mai kwatarka, sai kun yi danasani mafi girma a rayuwarku".

Sai a lokacin baban Zainab ya saka baki a in da ya dakawa Haidar ɗin tsawa da ya fita mashi daga cikin parlourn ko kuma yanzun nan ya canza mashi kamanni. Babbar magana, a kan Hauwa fa babu abin da baban Zainab ba zai aikata ba, lallai akwai rikici ba kaɗan ba.

Ba ƙaramin kara tsorata su maman Haidar suka yi ba na ganin yadda baban Zainab ɗin ya hayayyako masu dan kawai Haidar ya yi yunƙurin taɓa Hauwa, yana gani Hauwar ta ci masu mutunci bai saka baki ba, amma daga za'a taɓata ya wani hayayyaƙo masu kamar zai cinyesu ɗanye, lallai akwai matsala babba ma kuwa.

Ita kam maman Zee komawa ta yi saman sofa ta yi zamanta tare da buga uban tagumi tana ganin wannan cakwakiya. Tatas baban Zainab da Hauwa suka yi wa su maman Haidar, daga karshe baban Zee ya koresu ma daga cikin gidansa, basu kuma da zaɓin da ya wuce su tafi, dan kuwa a yadda yake ɗin nan tsab zai iya yi wa mace ɗan banzan duka, Allah ma ya rufa asiri basu zo da hajiyarsu ba, abin ya tsaya a iya kansu kawai, ai da anyi ba daɗi.

Haka suka kwashi jiki cikin ruɗu tare da mamaki haɗe da tunanin baban Zainab kam anya lafiyarsa kuwa, a haka suka bar gidan suka nufi gidan Hajiyarsu, dan su sanar da ita halin da ake ciki.

Ita kuwa Hauwa bata bar wannan gida ba sai da ta tabbatar ta ƙunsawa maman Zainab abin da zai hanata yin barci a yau, sannan ta ce da baban Zainab su tafi. Shi kuwa bawan Allah kamar raƙumi da akala haka ya bita zalau zalau suka bar gidan kamar yadda suka zo.

Suna fita maman Zee ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tun daga saman kujera ta zubo kasa saman gwiwowinta tana kuka, Khadija dake zaune komai ya faru a kan idanunta ne ta zo ta rungumeta tana rarrashinta ita ma kuma tana nata hawayen, abin gwanin ban tausayi.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

Idan muka waiwaya Dubai kuwai.

GIDAN ABU ABDUSSALAM BIN BADEEN🔥🌼

Lest cut the story, tsawon wata guda Leesharh tana aiki a cikin wannan gida, amma kuma ko kusa ko alama bata samu ganin wanda ta zo aiki a kansa ba, wato Ramish kenan, bayan Ummie and Sharifa ma sai su Radia babu wani bakon fuska da ta sake gani a cikin gidan, abin ya ɗaure mata kai, ji take yi kamar ta tambayi su Radia ina Ramish yake kuma wanenen shi? Amma da yake bata saki jiki da su ba, bata shiga cikinsu, kuma tana tsoron su zargeta a kan wannan tambaya yasa ta ja bakinta ta yi shiru, kawai ta zubawa sarautar Allah idanu, amma kullum da wannan tunani take kwana, da shi kuma take tashi, ga wayar da aka bata kullum a kunne yake, amma babu wanda ya taɓa kiranta ko ya turo mata saƙo, waɗan da suka bata wannan aiki da alama sun san da cewa ganin Ramish da ido ma kawai ba ƙaramin aiki bane, shi ne yasa basu nemetaba tukunnan, da alama suna samun information a kan wani hali take ciki sosai ba tare da saninta ba, amma su waye masu basu information a kanta? Allah masani. ita dai a yanzu bata san a wani matsaya ma take ba baiwar Allah.

A bangaren shi kuwa Ramish yana nan a cikin gidan, sai dai samin damar ganinsa ne ba kowa ba, ko ita kanta Ummie tana fin sati biyu bata sanya shi a idanunta ba, ba wai kuma dan baya nan ba, no a cikin gidan yake kwana yake tashi, sai dai yadda kuka san wani aljani haka yake, tamkar yasan akwai mayunwatan kuraye dake farautar rayuwarsa a cikin gidan, bawan Allah nan baya tashi dawowa sai tsakar dare yake shigowa cikin gidan, duk balainka da nacinka baka isa kasan lokacin da Ramish yake fita ko yake dawowa ba, zaka iya zaman shekara guda a cikin wannan gida baka haɗu da shi ba, shi ɗin ba kamar sauran mutane yake ba, and kuma ba shi kaɗai bane, matasa ne su huɗu wadda dukkansu babu wanda ya kai 30 years a duniya, cikinsu kuma harda Rizwan yayan Yah Jawad, first born ɗin uncle Abbas kenan, amma fa dukkansu kafin ka samu damar ganinsu wlh kana iya fin shekara a cikin wannan gida, su ɗin ba mutane ne kamar kowa ba na gaya maku.

Wai wanenen Ramish? Bari mu ɗan ji wanenen shi kaɗan wata kila zamu iya fahimtar dalilin da yasa ake nemar rayuwarsa ruwa a jallo.

Ramish dai ɗan King Zuhair ne ba ɗan Abu Abdussalam bin Badeen bane, yayan gimbiya Aneesa ƴar mamace uwarsu ɗaya, wato ɗan mama ne shi kenan. Ramish fa Special weapons and tactics. Wato SWAT, kuma shi ne operation lieutenant ɗinsu gabakiɗaya. Special weapons and tactics, ku daga jin sunan special kun san they're special ɗin ne da gasken gaske, su ɗin wasu irin jami'ai ne da ake basu horo na musamman fiye da duk sauran jami'ai da kuka sani, saboda su idan ka gansu a waje ma to fa abu ya lalace, sai special waje ake turasu aiki, ba kamar jami'an air force, jami'an soja, jami'an ƴan'sanda da sauran masu kaki suke ba, no su they're very special, da farko kasar America ce ta fara kaddamar da Special weapons and tactics, daga baya sauran manyan ƙasashe ta duniya suka kwaikwayesu suma suka kaddamar da su, aiki suke yi kamar agogo, ga ɗan banzan fikira dake garesu, ga zafin nama, cikin ƙanƙanin lokaci suke aiwatar da duk abin da zasu yi, ba iya karfin dantse ne kawai suke da shi dan an basu horo na musamman ba, no su ɗin aiki suke yi da kwakwalensu cikin kwarewa tare da tunani mai zurfi, duk fa idan suka yanke hukunci a kan abu to ko gwamnati bata ja da su, domin ansan gaskiya ce, suna da uban tarin makiya ta gabas da yamma kudu da arewa, saboda sun yi aiki tukuru, sun kashe iyayen wasu, sun kuma jefa iyayen wasu gidan prison, su fa har manya manyan ƙusoshin gwamnati basu bari ba, duk wanda ya keto ta cikin aikinsu to ba makawa zai jisa a in da sai ya yi danasanin zuwansa duniya, wannan takaitaccen bayani ne a kan wanene Ramish, sauran bayanai ya biyo daga baya, kada ku manta shi ɗin jinin Modarawa ne, ɗa ne ga King Zuhair. To amma meyasa ake farautar rayuwarsu har haka? Lokaci ne zai nuna mana komai.

Ramish yana da kani mai suna Bilal wanda ya kasance yaya ne ga Gimbiya Chuchu uwarsu ɗaya, wato ɗan mummy kenan, Bilal air force ne shi, ba sai na tsaya yi maku dogon bayanai a kan su waye air force ba, kun san jami'ai ne da suke sadaukar da rayukansu a kan ƙasarsu, sun fi sojoji shiga haɗari nesa ba kusa ba, su ɗin jami'an sama ne, yakin sama ake turasu, jami'ai ne da ba kowa yake iya yin aikin da suke yi ba, jajirtattun ne kuma jarumai na gasken gaske. Bayan Bilal kawai Dr Raj wanda ya kasance shi ma ɗan mama ne, Kanin Ramish kenan uwa ɗaya uba ɗaya, shi kuma hamshaƙin Medical Dr ne, mutun ne shi da ya san aikinsa, baya kuma wasa da aikinsa, bama sai na ɓata bakina wajen gaya maku cewa yaran King Zuhair basu da wasa ba, ku da kanku kun san jininsu a tafashe yake, sun gada wajen mahaifinsu, Akka da take mace ma da yake jinin Modarawa ne ke gudu a jikinta ita ɗin ma, baku ganinta a zafafe take ne? Tana da zafin nama bare kuma su maza, sam basu da wasa ko kaɗan, kuma idan ka kuskura ka kawo masu wasa a cikin lamuransu yanzun nan zasu saɓa maka kamanni.

Rizwan kuma wato yayan Yah Jawad, kamshaƙin ɗan kasuwa ne wadda yake business tsakanin manyan kasashen duniya, yana da kamfanonin a ƙasashe daban daban, baya da ra'ayin siyasa ko sarauta, haka zali baya ra'ayin kaki, duk da cewa kowace irin kaki ya yi ra'ayi zai iya sanyawa ga jikinsa ya yi aiki, domin kada ku manta da muƙamin uncle ɗinsu wato uncle Abu Abdussalam bin Badeen, shiyasa su Ramish ɗin ma suke da manyan muƙamai a wajen aikinsu, kuma ya haɗu da basu da wasa, jajirtattu ne su ɗin. To shi Rizwan ya zaɓi kasuwanci ne abinsa, shi ne ra'ayinsa. Dukkan ƴaƴan King Zuhair idan ka kallesu ba sai an ce maka ƴaƴansa bane, akwai alamar kamanni ta jini a tsakaninsu, musamman Ramish da kaninsa Dr Raj, suna kama sosai, duk kuma kamannin Akka suka ɗauko, shiyasa suke sajewa da su Abu Abdussalam bin Badeen, sun zama dai duk iri ɗaya.

Wannan shi ne takaitaccen labarin waɗan nan zaratan samari na Abu Abdussalam bin Badeen wanda kuma ya renesu kamar wasu zakuna, suka taso a haka, tun suna kanana suke a hannunsa, shi kuma ƴaƴansa maza biyu basu a tare da shi, suna gidan the most powerful King Badeen, wato gidan mahaifinsa kenan, ƴarsa Sharifat ce kawai a gidan, sai Ummie, yana kaunar King Zuhair ne over, hakan yasa yake kaunar ƴaƴansa ma.

To mu koma kan labarinmu tun da kun ji su waye su Ramish, ɗan mama ne dai, mama sarkin masifa, ƴaƴanta maza biyu ne sai Aneesa ta uku, kuma ga duka yayan nata da Ramish da kuma Dr Raj ɗin duk a Dubai, amma a haka kullum take tsayar da bala'i a kan ita King baya yi mata adalci, ya fi son Momman auta, ɗan adam kenan, ba'a iya mashi, ita fa ƴaƴa maza manya har biyu ke gareta saɓanin Mummyn Gimbiya Chuchu da take da iya Bilal kawai, amma Mummy bata wani damu ba, ita kuma mama sarkin haɗama so take ace ita kaɗai ce take da ƴaƴa maza, kuma fa su Ramish ɗin nata sune manya a kan Bilal ɗin Mummyn Gimbiya Chuchu, idan ma mulki take so ai su zasu karɓi mulki, amma ita dai duk bai yi mata ba, sai ka rasa me take so a duniyar nan kuma, mummy ma fa tana da babban ɗanta na fari kafin Gimbiya Aunty MieMie wanda ya rasu, rasuwa ya yi shiyasa yanzu su Ramish sune manya a kan Bilal ɗinta da yake matsayin ɗanta a uku, sai Chuchu auta. Fatan dai kun gane?.

A kullum baza idanu Leesharh
End Ads