Ƙasa da kai Hoorain ya yi, har wa yau yana cikin kayan yakinsa tare da wannan hula da ta hana a kalli face ɗinsa, sarai ya lura da Jaish bai so auta ta yi mashi magana ba, hakance ma tasa ya iya bakinsa bai amsa mata ba, sai dai ya bita da kallo ta ƙasan ido kawai, yarinyar tana burgesa yadda ta fito daban a cikin ƴan gidan, bata da girman kai ga girmama mutane.
Sai da suka ɗan wucesu ne wannan mayakin da suke a tare ya taɓa shoulder ɗin Hoorain ɗin tare da faɗin. "Kabi a hankali abokina".
Jinjina mashi kai Hoorain ɗin ya yi tare da cewa. "Nagode manta kawai mu cigaba da maganar mu".
Ya yi maganar kamar dai yadda ya saba yinta cikin sanyin murya kuma ƙasa ƙasa kamar baya son yi.
Ita kuwa auta a duniya tana son ganin face ɗin Hoorain, sai dai duk kuma lokacin da ta ce mashi ya cire wannan hula ta kallesa sai wani abin ya gifta a tsakaninsu ya hana shi cirewa, tana jin daɗin kasancewa da Hoorain ɗin a matsayin mai bata tsaro sosai, saboda yadda yake kula da ita ya fi sauran mayakan da suke kula da su Gimbiya Chuchu.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
A ɓangaren su Aneesa kuwa, kamar dai yadda suka saba ne, kullum in suka haɗu da Sarina waje guda matuƙar iyayensu basu a kusa to fa rabuwarsu bata daɗi, dan haka a wannan karon ma Yah Jaish yana fita suka dasa daga in da suka tsaye da surutan nasu, ko wacce sai shegen son girma da nuna isa da izza.
Fanan da ta lura zasu cika mata kunnuwa sai ta miƙe ta nufi waje abinta, dan ba zata iya ba, ba yau bane farau. Ita ma Gimbiya Chuchu gyara kwanciyarta ta yi tare da basu baya tana fuskantar headboard na gadon, dan ma kada su takura mata sosai sai ta janyo duvet ɗin Akka ta rufe har kanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, abokiyar hirarta wato auta ta tafi, dama ita idan ba da auta ba bata cika yin hira da kowa ba, ɗan gara ma Fanan, wani lokaci suna hira sosai, amma Sarina da Aneesa wlh babu mai iya halinsu sai su, murɗaɗɗun mutane ne wanda ba zaka taɓa gane ina alkiblarsu take ba.
Duk kuma faɗar da zasu yi fa a iya baki ne kawai yake tsayawa, ko da sunan wasa basa daka hannu a jikin juna, ba wai kuma dan basu iya faɗar ba, ina ai su faɗa a jininsu ma take, kawai dai basu taɓa ko da gwadawa bane, dan sun san zasu daku dukar mutuwa ma kuwa a hannun Jaish in suka yi faɗa, ina ga bugun da zai yi masu ko ganga iyaka, hakan yasa sai suke tsayawa a iya surutan nasu kawai.
Yanzu haka suka yi surutun nasu tsab suka kammala ba tare da ɗaya ya taɓa koda alkyabbar jinin ɗaya ba. Aneesa ce ta fara miƙewa ta fice daga cikin ɗakin. Ita kuwa hjy Sarina sai ta gyara ta kwanta a saman bed ɗin tare da cigaba da taɓa wayar Mammie abinta.
Da daddare misalin karfe 9 kowa ya kammala cin abincin darensa, masu saurin yin barci ma har sun yi barci, wasu kuma suna shirin yin barci.
Akka tana part na uncle Abbas, dan tun da yamma ya ce kansa na yi mashi ciwo, kuma gobe yake son komawa, so Akka tana wajensa, ta je duba ciwon kan nasa.
Gimbiya Chuchu ce kawai kwance a saman bed ɗin Akkar, ita kuwa Gimbiya Zunaira tana wajen Mommarta yau, ta je ta wani haye mata saman bed tare da tada kai da cikyarta suna ta hira na tsakanin uwa da ƴa, kamar wasu ƙawaye, sai shafa lallausan bakin arab hairnta momma take yi, tana ta bata labarin ƴan uwata su uncle Rahab kenan da suke can Dubai.
Ita dai Momma har ga Allah tana wahala rayuwarta a wannan masarauta, shiyasa take yawan zuwa Dubai, ko da kuma ta gayawa mahaifinta ga abin da yake faruwa da ita, sai dai ya ce mata ta kara tsananta addu'a sosai, yau tsawon shekaru talatin kenan tana fama da wannan matsala, sai dai yana yin sauki, ya fi taso mata ne a duk lokacin da ta samu ciki, har ta haifi wannan ciki tana fama da wannan mahaukacin razanar da ita da ake yi, ba kalar halittar da bata gani, wani lokaci idan abin ya yi tsamari har suma take yi, sai an danganata da likitoci, amma kuma idan bata da ciki tana fin shekara biyu zuwa uku bata ga wani abin tsoro ba, sai jefi jefi.
Da yake tana tsananin kaunar gimbiya Zunaira sai aka fi yawan tsorata da fuskar Zunaira ɗin, da tsakar dare zata jiyo muryar autar tata tana ta faman kuka a cikin toilet, idan ta tashi ta je ta duba kuma sai ta ga yes fuskar Zunaira ɗin ce, amma kuma babu gangar jiki, sai jini dake zubo mata daga hancinta, bakinta izuwa wuyarta, wani lokaci idan ta taso daga kan gado da addu'ar tashi daga barci, sai bata tsorata zaka ji ta furta sunan Allah sai abin ya ɓace, amma duk ranar da ta manta bata tashi da addu'ar tashi daga barci ba to ba shakka tana mahaukacin razana har ta kurma ihu, kuma abin baya ɓacewa sai dai ya kara razanar da ita, baya rabuwa da ita har sai ta samu ta furta wata addu'a ko sunan Allah. Haka baiwar Allah take ta fama, ta kuma ƙasa iya gayawa King Zuhair ga abin da take fuskanta, mahaifinta kawai ta iya gayamawa, shi ma kuma da alama saboda babban malami ne sosai kuma sarki mai karfin iko ne yasa abubuwan basu iya rufe mata baki a kansa ba, ta iya gaya mashi. Ko mahaifiyarta bata iya gayawa ba.
Sai hira suke zubawa kamar wasu ƙawaye, a haka Jaish ya shigo ya samesu, sanye yake da kayan barci masu bala'i kyau da tsada, already ya nemi izinin shigowa ta hanyar turo mata massages a wayarta, saboda ko da ya zo parlourn bai sami su kuyanga Mama Haulat ba, sai kawai ya turo mata sako, ta kuma amsa mashi da ya shigo, shi ne yasa ya shigo.
Kasancewar suna a saman bed sai shi kuma ya zauna a saman bedside drawer kusa da lamp dake a kunne yana bada wuta light green.
"Good evening my Momma".
Ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa.
Alhdulillah ya bata amsa kafin ya ce da auta. "Which amsa kenan?".
Ɗan turo baki ta yi kafin ta ce. "About my journey to Dubai, ina son dawowa a tare da yaya Omar ne fa".
Shiru ya yi mata bai amsa ba, dan ya rigada ya yanke hukunci babu in da zata je, abin da next week Omar ɗin zai dawo, dan haka ta jira shi a nan kawai.
Hannun Mommarsa da take ta faman shafa lallausan gashin auta ya riƙo cikin nasa, a hankali ya zura mata wani haɗaɗɗen dankareran diamond ring irin nata da ya cire mata ranar, dama idan baku manta ba ranar ya cire mata nata ring ɗin saboda ya yi mata kaɗan, to shi ne ya yi waya wa a powerful king of Dubai ya aiko mashi da wani irin wannan sak, wato kakansa kenan wanda ya haifi Momma ɗin kuma uncle ga King Zuhair kani ga Akka kenan, dama idan baku manta ba na gaya maku King Zuhair Momma ƴar uncle ɗinsa ce ya aura, aure dangi ne.
Sosai ta ji daɗin wannan ring ɗin, wani sanyi ne ya ratsa mata zuciya yadda ƴaƴanta suke nuna mata so, ya cire wancan da kasa ya kuma kawo mata mai ɗan girma ya saka mata, baban abin birgewa ma ko da ya sanya mata ring ɗin sai da ya ɗan sumbaci hannun nata da wannan ɗan ƙaramin bakin nasa, sannan ya ce.
"Momma ring bai taɓa burgeni ba before, but a hannunki is so very very beautiful da har na ji ina sha'awar sakawa ni ma, you're so special our Momma". Cikin nutsuwa tare da sanyin murya ya yi maganar.
Wani irin madarar daɗi ne ta ji ya kara lulluɓeta, yabo yana da daɗi, amma kuma irin yabon da Jaish yake yi mata ya fi na kowa daɗi. Shi kuma Jaish ɗin a duniya iya ita da King kaɗai ya iya yabawa, ko auta idan ta yi kwalliya suka haɗu ta tambayesa ta yi kyau, kai kawai yake gyaɗa mata, wani lokaci ko kallon kwalliyar tata ma baya yi, amma idan Mommarsa ce ya rinƙa yabon kyanta kenan koda bata yi kwalliya ba, ita da King kaɗai ya iya yabawa a duniyarsa, bayan su ko kansa bai iya yabo ba, yo shi da a duniya ma kwata kwata da mutane huɗu zuwa biyar yake iya buɗe baki ya bawa amsa, saura sai dai ya bisu da ido ko kuma ya gyaɗa masu kai, idan kun ji ya buɗe baki yana magana voice nasa na ɗan fita da sauti kaɗan ma to da Mommar ce ko King, su biyun nan yake yi wa magana har voice nasa ta ɗan fita, saboda baya son ya zamana ya yi masu magana basu ji ba sai sun sake wahalar da kansu wajen sake tambayarsa me ya ce? Baya son haka shiyasa yake ɗan buɗe murya idan zai yi masu magana, bai ɗauki iyayen nasa abin wasa ba, sune komai nasa, yana bala'in kaunarsu fiye da komai, da da hali ma ina ga har abinci zai rinƙa tauna masu dan kada su sha wahala.
"Yah Jaish baka yi magana ba". Cewar auta, ta yi maganar a shagwaɓe sosai.
"Baby I will think about it, ki bari zuwa gobe".
Ya bata amsa yana sakin hannun Mommar tasu.
"Allah ya yi maka albarka my son". Cewar Momma.
Da Amin ya amsa mata kafin ya sake cewa. "Momma zan iya tafiya ko kina buƙatar wani abin?".
Girgiza mashi kai ta yi alamar bata buƙatar komai zai iya tafiya.
Miƙewa tsaye ya yi tare da kai hannunsa ya shafi lallausan kumatun auta da ta tsare shi da idanu.
"Sarkin kallon mutane ayi addu'ar barci kafin a kwanta".
Ya faɗa haɗe da ɗan jan karan dogon hancinta.
Wani irin cool murmushi ta sakar mashi har sai da dimples ɗinta suka lotsa, wani irin sihirtacen kyau ne ya kara bayyana a saman face ɗin nata, dama ita fa ba baya ba wajen kyau, wlh ta fi su Jaish ɗin dukka kyau, yadda kuka san duk an haɗe mata kyansu ne aka cure waje guda aka bata, idan ka gansu dai dukka zaka san cewa ƴaƴan Momma ce saboda jini ba wasa ba, amma dai ta fisu kyau har twins Obaid and Omaid, Yah Omar dukka, ita ce tauraruwarsu.
Ɗan yatsarsa karami ya ɗan saka mata a ramin da dimples ɗin nata suka lotsa, ya ɗan danna wajen kafin ya ce. "Naki ya fi na kowa kyau a gidan, kin yi mana wayo".
Ya yi maganar kasa kasa tare da ɗauke hannunsa daga saman face ɗin tata. Sai binsu da kallo Momma take yi, gwanin ban sha'awa abin, akwai soyayya da kauna mai karfi a tsakaninsu. Daga King har Momma dukka suna da dimples, hakan yasa gabaɗaya ƴaƴan Momma suke da shi, ita ma Gimbiya Chuchu tana da shi, amma Gimbiya Aneesa ƴar Mama bata da shi, uncle Abbas yana da shi, amma su Sarina duk basu da shi, Akka ce tushen dimple ɗin nasu, duk da ta tsufa idan tana magana zaka gansa a face nata ɓaro ɓaro.
Hannunsa auta ta kama ta ɗan sumbata kafin ta ce. "Take care Yah Jaish, kaima kada ka manta ka yi addu'a, nima kuma zan yi, Momma zata kara yi mun kona yi barci, kuma nasan daddy ma sai ya zo ya yi mun, dan baya taɓa yin barci ba tare da ya zo ya yi mun addu'a ba, ina fa samun addu'oi sosai".
Nufar kofar fita ya yi yana tafiya a nutse, sai da ya kai tsakiyar ɗakin ya kusa bakin door ɗin ya ce. "Ni ma baki san ina dawowa na yi maki addu'a bako? Ai ke ƴar gata ce, bana jin a gidan nan akwai wanda baya yi maki addu'a".
Ya kai karshen maganar dai'dai lokacin da ya fice daga ɗakin, bai jira amsarta ba, dan baya buƙatar ji, idan ya biye mata zasu iya kwana a wajen, auta bata gajiya da magana.
"Mommana dama Yah Jaish yana dawowa ya yi mun addu'a idan na yi barci?".
Gyaɗa mata kai ta yi alamar e tare da faɗin. "Harda Yah Jawad duk suna zuwa bedroom naki su yi maki addu'a, amma idan a nan kika kwana basu zuwa, dan basu son takura mun suka ce".
Shiru ta ɗan yi kafin kuma ta ɗan shagwaɓe fuska tare da faɗin. "Allah sarki suna sona sosai".
Yadda ta yi maganar sai da ta sanya Momma sakin murmushi, wai Allah sarki suna sonta sosai, ashe ma ita bata san cewa ita ɗin kamar bugun zuciyarsu take ba, bata san cewa sun fi sonta fiye da kansu ba, saboda kyawawan halayenta irin na King yasa take da mugun shiga rai, harta Mama da take bata shiri da Momma tana kaunar Zunaira, wannan suna na Zunaira ma Mamar ce ta zaɓa mata a lokacin da aka haifeta, yarinyar ce dole ta shiga ran mutun, saboda yadda take bata ɗauki duniya a bakin komai ba, bata ɗauki abubuwa da zafi ba, komai nata very calmly and softly conduct.
Cigaba da hira ita da Mommarta suka yi har izuwa lokacin yin barci, dama already tana shirye cikin kayan barcinta masu bala'in kyau da tsada, riga da wando launin maroon color. Barci ne ya ɗauketa kwance a saman laps ɗin mommar tata, fuskarta ɗauke da annuri tare da murmushi mai kara mata kyau ko da tana barci.
Shiru Momma ta yi tana karewa face ɗin nata kallo kamar mai tunanin wani abin. Ta ɗauki a kallah tsawon mintuna 10 a haka tana kallon fuskar ƴar tata ba tare da kyafta idanu ba. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin nan cikin dabara ta sauketa daga saman laps ɗinta tare da sanya mata pillow, sannan ta sauko kasa daga saman bed ɗin, dan ta je ta yi wanka ta yi shirin kwanciya.
Bata kai ga shiga toilet ɗin ba sallamar King kasa kasa ya daki dodon kunnuwanta, ya biyo sahun ƴarsa, ya je bedroom ɗinta bata nan, ya leƙa na Chuchu bata can, babu kowa ma a ciki, dan Chuchu ɗin ma tana wajen Akka, hakan yasa ya nufo nan kai tsaye kawai, ba zai iya yin barci ba idan bai yi wa Zunaira addu'a ya shafa mata ya kuma tabbatar tana cikin aminci ba.
Sanye yake da arab jallabiya fara tas a jikinsa, ga arab hairn nan nasa a kwance luf har gaban goshinsa, King ba dai kyau ba, kyakkyawan balarabe ne ajin farko, ga wani bakinkirin ɗin saje mai bala'in laushi da kyau kwance luf a gefe da gefen face ɗinsa, kyakkyawar gemun nan nasa ta sha gyara, sai sheki take yi sosai, ga wani haɗaɗɗen gashi da ya kewayo ɗan red bakinsa, ba ƙaramin kyau ya kara mashi ba, farar fata da bakar gashi ku kunsa dole ya ɗauki ido, ga kuma dara daran idanu masha Allah, gashin gerarsa har kamar zasu haɗu da juna saboda cika, suna kwance luff suma kamar an zana mashi su, sai sheki suke yi........ (Har na ji zan iya yi wa Momma kwace🥱🌝 sai dai ina tsoron commander ZAFAR😥)
Tsare Momma da waɗan nan dara daran idanun nasa ya yi yana kare mata kallo tare da harɗe hannayensa a saman wannan Lion chest ɗin nasa, King fa ansha fama a fagen yaki a lokacin da mahaifinsa King ABDUL MALIK yake raye yake kuma rike da karagar mulki, idan baku manta ba na gaya maku ya taɓa rike commander mayakansu a lokacin, so har yanzu a buɗe yake kamar yana mai cigaba da karɓar horon yakin.
"Barka da shigowa ranka ya daɗe". Momma ta faɗa cikin girmamawa, sai kallon juna suke yi, ita bata cire idanunta daga kansa ba, shi kuwa dama kunsan ba kawarwa zai yi ba.
(Ni kam na ce mada dai a manta auta tana ɗakin😌🌝)
Shiru suka kurawa juna idanu na a kallah mintoci uku kafin kuma a tare su sakarwa da juna cool murmushi kamar abin haɗin baki.
"Ka fara ko?". Momma ta faɗa tare da sa kai zata wuce cikin toilet abinta.
"In dai zan shigo ki cigaba da yi mun irin wannan tarba to ba zan canza hali ba".
Ya faɗa tare da nufar saman bed ɗin nata wajen Zunaira kenan yana cigaba da sakin murmushi kamar ba King sarkin zafin rai da iya tsare gida a fada ba.
"Shi ne baki rufe mun sanyin idaniya ta da duv ba ko? Kika barta sanyin Ac na ratsa mun ita sai ta yi mura ko? Zan rama mata".
Ya kai karshen maganar tare da hayewa saman bed ɗin, a kusa da ita ya zauna tare da fara tofa mata addu'a kamar yadda ya saba.
Ita kuma Momma ta shige cikin toilet, dan in ta biye mashi tsab zasu iya kwana a tsaye suna yi, su ɗin ƴaƴan kawu da gwaggo ne, Akka gwaggon Momma ce, akwai wasa sosai a tsakaninsu, abokan wasa ne, hakan yasa wani lokaci King ɗin yake tsokanarta sosai