fasa kirjinta ya fitowa waje, saboda tarin tsoro da kuma danasani na amsawa wannan mata da e zata yi wannan aiki da ta yi, ga kuma tunanin rabuwa da Jasrah! Ko sallama basu yi ba abin gwanin ban tausayi, sannan ga shi yanzu an kawota waje an barta ita kaɗai.
Juyawa ta yi gabas da yamma kudu da arewa bata ga alamar wani halitta mai rai a arear wajen ba, wani sabon tsoron ne ya kara dira mata a cikin ranta. Juyowa ta yi tana kallon wannan prison door ɗin, ji take yi kamar ta yi knocking na door ɗin da karfi har sai an zo an buɗe mata ta koma ciki, dan komawarta ciki shi ne mafi a'ala a gareta. Sai dai kuma tana tsoron yin knocking na door ɗin, gudun kada ya haifar mata da wani gagarumin matsala.
To wai me mutanen nan suke nufi da ita ne da suka barta a wajen gidan yarin?. Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana.💘
Ta kai almost 10 mins tsaye katsake a wajen, ta kasayin gaba ta kuma kasa yin baya, ta rasa duk wani ƙata ɓus, tunani da tsoro duk ya dabaybayeta baiwar Allah.
"Let's go".
Tamkar saukar aradu ta ji wannan murya ta bayanta an faɗi ta zo su tafi. A razane ta juyo mai gabaɗaya.
Wata jibgeiyar hajiya ce da daloli suka yi mata mubaya'a, kuɗi suka jiƙata sharkaf ne tsaye a bayanta sanye cikin wata dakakkiyar tsadaddiyar bakar jallabiya tare da nikaf a face ɗinta, kafafunta na a sanye cikin booth mai tsada, ga wani bakin glass a face nata, kusan dai irin shigar matar ɗazun, sai dai matar ɗazun ƴar siririya ce, wannan kuma jibgegiya, tana da tsoka a jiki sosai, ta ci ta ƙoshi, wannan irinsu ake kira da hajiya two seater, masu haɗiye sofa two seater a wajen zama.
Sosai Leesharh ta ƙara razana fiye da tunanin mai tunani, sam bata ma san lokacin da ta fara kallon matar from head to toe ba, saboda ita dai bata taɓa kallon mace mai kibar wannan mata ba, wani irin kerma na tsoro jikinta ya fara yi, ta kasa koda iya ɗaga kafafunta bare ta isa ga wannan matar.
Ganin haka yasa ita matar ta ƙariso gareta tare da riƙo hannunta, ta jata da nufin su bar wajen.
Ƙasa iya tafiya Leesharh ta yi, da alama suman tsaye a wajen ta yi, yau taga tashin hankali, babban damuwarta ma shi ne kada ace shikenan an rabata da Jasrah ba tare da sun yi sallama ba, in kuwa haka ne wlh ancuceta an zalunceta, haka ake yi ne? Zasu rabasu babu ko excuse!.
Ganin Leesharh fa ba iya tafiya da kafafunta zata yi ba dan duk jikinta ya yi wani irin muguwar la'asar kamar wadda aka zarewa laka, hakan yasa wannan mata ta sanya hannu ta ɗauketa cancak kamar baby ta wuce da ita!.
Kara razana Leesharh ta yi da wannan mata, duba da yadda ta ɗauketa cak abinta.
Cikin wani ɗan ƙurƙuran abin hawa wannan mata ta sauke Leesharh, abin hawan anyisa kamar bayan kunkuru tare da wata ƴar runfa a samansa, ta gaban kuma kamar keƙen hawa yake. Lokacin da wannan mata ta shiga cikin wannan ɗan ƙurƙuran abin hawan sai da ta jijjiga sosai, saboda ƙibar matar nan Masha Allah kawai za'a ce. Cikin harshen larabci ta ce da mai abin hawa ya ja su tafi. Ba ɓata lokaci ya ja suka wuce. Sun yi tafiya mai nisa har sai da suka bar arear AAJ, sannan wannan mata ta buƙaci da mai wannan ƴar ƙurƙuran abin hawan da ya dakata su sauka.
Ba musu ya dakata suka sauka, ga mamankin Leesharh sai taga matar bata biya mai abin hawan kuɗinsa ba kawai ta saɓeta a shoulder ɗinta suka fara takawa da kafa. Shi kuwa mai wannan ƴar ƙurƙura ya gurgura abarsa ya kara gaba, da alama bakinsu ɗaya, duk cikin basaja ne.
Bata sake sauke Leesharh a ko'ina ba sai a gaban wasu irin jiga jigan motoci masu masifar kyau da ɗaukar hankali. Sai dai sun ɗan yi tafiya mai nisa kafin su iso wajen waɗan nan motocin, ba zaka taɓa cewa waɗan nan motoci wata alaƙa ce ta kawo su AAJ ɗin ba, ita kuwa ainahin matar da ta fara yin magana da Leesharh ɗin tana cikin AAJ ɗin tana cike wasu takardu tare da bawa shugaban gandurobobin wasu takardu da ta zo da su ta sanya hannu, da alama yarjejeniya ce a kan sun karɓi Leesharh, ga dukkan alamu takardun da matar ta zo da su daga sama suka fito, ma'ana daga manyan madafun iko suka fito. Gaskiya akwai cakwakiya ta gasken gaske kuwa, ku dai gyara zama sosai!.
Cikin ɗaya daga cikin waɗan nan shirga shirgan dankara danƙaran motocin wannan mata ta sauke Leesharh a gidan baya kenan. Idan ka kalli motocin in the first place ba zaka taɓa yin zaton da akwai mutane a cikinsu ba, saboda bakar glass da suke da shi, sannan babu wani motsi da zai nuna maka cewa akwai mutane a cikinsu.
A tunanin Leesharh dukka babu mutane a cikin waɗan nan motoci, sai da aka sauketa a cikin ɗaya daga cikinsu ne taga wani shirgegen bodyguard, farin balarabe tas da shi sanye da face mask a fuskarsa, shi ne driver wannan mota da aka sanyata.
Ita kuwa wannan mata hajiya two seater, wata mota na daban ta shiga, tana shiga kuma ko second ɗaya ba'a ƙara ba motocin suka tashi a jere kamar abin haɗin baki. A wani irin haukace suka tashi, da wani irin mahaukacin gudu suka bar arear wajen.
Izuwa yanzu Leesharh ta gama saddakarwa da cewa lokacin mutuwarta ne kawai ya yi ba makawa, jikinta sai ɓari yake yi kamar mai zazzaɓi. Motoci guda goma ne cif dama, haka suka rinƙa sharara uban gudu kamar zasu tashi sama, kai daga gani kasan ba lafiya.
Cikin ikon Allah suka samu damar isa katafaren shinfiɗaɗiyar titin da zata sadasu da unguwar Dubai Hills Estates, a luxurious area kenan, area ce ta manya manyan shegu masu faɗa aji a faɗin ƙasar, area ce da tun farkonta har izuwa karshenta take da matakan tsaro sosai, lafiyayyun securitys masu jini a jika ne suke tsaron arear, dogayen benaye masu matuƙar haɗuwa ne a ko'ina na faɗin yankin, babu karamar gida ko ɗaya a arear, dukka gidan manyan kai ne, tsayawa zayyana maku haɗuwar wannan unguwa ma ba zai yuwu ba, ku dai kawata a ranku ya zai kasance, amma dai ya haɗu iya haɗuwa.
Tun da waɗan nan motocin suka danno kai cikin unguwar duk securitys dake arear suke aikin sara masu, da alama motocin gidan wani babban shegene mai faɗa a ji!.
Kai tsaye wani tampatsetsan gida na gani na faɗa waɗan nan motoci suka nufa, tun daga kan yanayin tsarin ginin wannan gida kasan ba na ƙananan mutane bane, gini ne da ya amsa sunansa aljarnar duniya, hawa ɗai ɗai har hawa huɗu ne ginin, ga wani irin fitillu masu haske da suka kara fito da ainahin tsantsar kyan wannan gidan.
Da akwai abubuwar kawata idanu sosai a wannan area da kuma wannan gida da waɗan nan mutane suka shiga da Leesharh, dan idan ka tsaya kalle kalle ma sai ka kwana ka wuni baka yi abin da ya kawoka ka wuce ba, saboda haɗuwa ta ko'ina fa ya haɗu.
Kai tsaye tampatsetsan harabar parking space na gidan motocin suka nufa. Izuwa yanzu Leesharh ƙwaƙwalwarta ta dai'na gane mata komai, ta daina ɗaukar komai, sai dai ido kawai take bin ko'ina suka gifta da shi.
Suna kashe motocin wasu mata guda biyu da suke sanye cikin jallabiyas dark blue har ƙasa, da kuma nikaf a face nasu suka ƙariso wajen motocin. Tamkar sun san motar da Leesharh take a ciki, ita kawai suka nufa, suna zuwa ba ɓata lokaci suka ɓalle marfin motar suka buɗe, ɗaya daga cikinsu ne ta roki hannun Leesharh ta fito da ita.
Suna fito da ita kuma waɗan nan motoci suka sake tashi ba ɓata lokaci suka bar wannan gida tare da hajiya two seater a ciki, ita bata fito ba.
Cikin katafaren gidan suka nufa da Leesharh da ta zama kamar mutun mutumi, bayan idanu da kuma numfashinta babu wani abin da yake motsawa a jikinta baiwar Allah, sai jan kafafu take yi ta bisu izuwa cikin, suma sai jan hannayenta kawai suke yi, basu da karfin iya ɗaukarta, dan ƴan sirara ne su ɗin ma, basu da wani ƙiba saɓanin hajiya two seater, hakan yasa suka jata izuwa ciki kawai.
Duk wata mace da zaka gani a cikin wannan gida to tana sanye da nikaf, duk da cewa hakan kusan ɗabi'ar wasu dayawan larabawan ne, amma su waɗan nan nasu akwai ayar tambaya sosai. Mata sosai ne a cikin gidan, sai ayyukan gabansu suke yi, babu mai kula wani!. Lafiyayyun securitys ne masu gadin wannan gida, daga gani kasan gidan wani shegen ƙusa ne a ƙasar.
Kai tsaye wani haɗaɗɗen elevator suka nufa da Leesharh, hawa na karshe suka haura da ita. A wani katafaren luxury parlour suka dakata, parlourn ya ji komai na more rayuwar ɗan adam.
Wata hamshaƙiyar macece take zaune a saman sofa set mai matuƙar kyau da laushi, ita ma sanye take da wani haɗaɗɗen jallabiyarta launin white color, sannan ga nikaf a face ɗinta ita ma, baka iya ganin komai nata face yatsun hannayenta da suke farare kal kal kamar madara, kafafunta ma na sanye cikin safa baka, iya yatsun hannun ne kawai a waje.
A gabanta waɗan nan mata suka kawo Leesharh suka zaunar, sannan suka sanya kai suka nufi waje ba tare da sun furta ko uppan ba.
Wani irin kerma da jikin Leesharh yake yi ne yasa hankalin wannan mata gabaɗaya ya karkata izuwa kanta. Ɗan kyafta idanunta ta yi alamar tana son tabbatarwa shin da gaske ne take ganin jikin Leesharh na kerma haka?.
Ganin da gaske ne yasa ta ɗan yi gyaran murya, cikin harshen larabci ta fara magana. "Yunwa kike ji ne A'isha? Naga jikinki na kerma".
Jin muryar matar tare da jin yadda ta ambaci ainahin sunanta yasa Leesharh ta kara tsorata sosai, sai kuma a yanzu ta sami dama tare da jin cewa zata iya yin magana, ta ɗan ji kwarin gwiwa kaɗan, a ruɗe take faɗin. "Dan girman Allah ku mayar da ni AAJ, wlh ni nafasa yin wannan aiki, ba zan iya ba, ku mayar dani wajen ƴar uwata Jasrah". Magana take yi amma bata san me take faɗa ba, saboda a tsananin ruɗe take, tana magana tana zaro waɗan nan dara daran idanuwan nata.
Daga ta bayanta ta ji wata murya mai kamar saukar aradu ya daki dodon kunnuwanta tana cewa. "A'isha Aliyu Haidar, calm down mana, menene abin ruɗewa da tada hankali har haka?".
A matuƙar razane ta juyo da kallonta izuwa wajen da wannan murya ta fito. A hankali matar take saƙo kafarta tana taka haɗaɗɗen tiles na floor ɗin kamar bata son takawa, daga ɗaya daga cikin bedroom da suke a cikin parlourn ta fito, sanye take da wasu kananan kaya da suka kama jikinta sosai, wandon jeans fari tas da ƴar riga mai karamar hannu, ta ɗaura after dress a saman kayan, sai dai bata ja zip ɗin after dress ɗin ba, ta barshi ana ganin kayan da yake a ciki, ga wani munafikin nikaf da yake a face ɗinta.
A ruɗe Leesharh ta miƙe tsaye jiki na kerma ta fara faɗin. "Yauwa Aunty dan girman Allah ku mayar da ni AAJ, wlh ni ba zan iya wannan aiki ba, tsoro nake ji". Tana magana tana zaro idanu kamar an tare ɓera a lungu, dama ga idanun nata dara dara ba'a magana, duk wanda ya ganta a wannan hali da take a ciki sai ya tausaya mata, dan ta ruɗe sosai baiwar Allah, tana tsaka mai wuya. Duk da a AAJ wannan mata da nikaf ta je wa Leesharh, hakan bai hana Leesharh ta iya gane ta ba ta hanyar jin muryarta, sarai ta gane wannan mata da ta yi magana a yanzu ita ce ta je wajenta a AAJ, shi ne ma yasa ta miƙe a ruɗe take sanar da ita cewa ita ta fasa yin wannan aiki.
"Very very sharp brain little girl! Gaskiya Leesharh kina da ƙwaƙwalwa, a cikin nikaf kika kalleni a karon farko, haka zalika yanzu a karo na biyu ma a cikin nikaf muka haɗu, amma kin iya gane ni? Abin da mamaki kuma is so nice, wonderful and interested, hakan ya kara tabbatar mun da zaki iya yin wannan aiki, saboda kaifin brain ɗinki".
Matar ta yi magana cikin wani irin salo da ɗan adam ba zai iya fassara wani irin hasashe ko kuma kudurine a cikin zuciyarta ba, komai kaifin ƙwaƙwalwarka ba zaka gane ina suka dosa ba, saboda yadda suke fitar da magana sai sun taunata sosai da sosai suke sakinta, daki daki one ofter the other.
"Aunty please ki tausaya mun, wlh ba zan iya wannan aiki ba, na fasa yi, ki ji tausayin maraicina". Ta faɗa hawaye zafafa suna bin ƙuncinta, sai a yanzu ta sami damar yin kwallah baiwar Allah.
Sheeeee. Matar ta furta tare da sanya yatsarta ɗaya a saman lips nata dake cikin nikaf, a hankali ta ƙariso gabar Leesharh ɗin.
"Leesharh why are you suffering yourself for what you know you have to do it, tun da kika amsa zaki yi wannan aiki har kuma kika bari muka gaya maki wani irin aiki ne to fa dole sai kin yi shi! Babu wanda ya taɓa jin sirrinmu kuma ya ce ba zai yi aikin ba, kin yi kaɗan". Cewar wannan hajiya da take zaune.
My people's ina da wani tantama, anya idan Leesharh Allah yasa ta kammala masu wannan aiki ba'a kamata ba asirinta bai tunu ba ta tsira daga gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen da ranta su zasu barta da ranta kuwa? Ga dukkan alamu sun nuna duk wanda ya ji sirrinsu baya rayuwa, to kenan ita Leesharh me makomarta idan ta yi wannan aiki ta kuma samu nasarar kammalawa lafiya ba'a kamata ba? Kunga kuwa ita dai ta ji sirrinsu, ta ji komai, idan wani abin ya sami Ramish ma ta san sune sila. Shiyasa fa na ce maku wlh akwai cakwakiya da yaki ba kaɗan ba a part ɗin su Leesharh ɗin nan.
Riƙo hannunta wannan mata da ta je wajenta a AAJ ta yi, a saman sofa ta zaunar da ita tare da cewa.
"Mummy ki bari na yi magana da ita mana, kada ki saka baki please, ai zata yi. Leesharh kina ji ko? Ki saki jikinki, anjuma wadda zata koya maki aiki da abubuwan da suka dace dan ki yi basaja da kyau zata zo ta fara koyar dake komai, zaki zauna a gidan nan a kallah one to two weeks kina koya, sai kin goge sosai zamu san ta yadda zaki shiga gidan Sheikh Abu Abdussalam, kada ki damu babu wani abin da zai faru kamar yadda na gaya maki tun farko, ai na gaya maki zan kula dake koda kina a gidan Sheikh Abu Abdussalam ɗin ne, kin manta na ce maki muna da ma'aikata a can gidan ne? To kada ki damu babu abin da zai sameki, ki saki jikinki, na yi maki alkawarin lafiya lou zaki koma gida wajen ƴan uwanki tare da ɗimbin dukiya mai tarin yawa da zaku je ku gina rayuwarku ta inganta".
Tana zuba kalaman yaudarar tata zuciyarta na fargabar jin amsar da Leesharh ɗin zata bata.
"Aunty ni wlh ba zan iya ba, tsoro nake ji, dan girman Allah ki mayar dani wajen ƴar uwata Jasrah".
Tana magana har wa lokacin hawaye na cigaba da bin ƙuncinta, zara zaran gashin idanun nan nata sun jike sharkaf da hawaye, idanun nata sun yi jajir da su gwanin ban tausayi.
A dake wannan hajiya dake zaune saman sofa wadda wannan matashiyar mata ta kira da mummy ta ce. "A'isha kina son Aliyu Haidar ko baki son shi?".
A ruɗe kuma a hanzarce Leesharh ta amsa masu da. "Wlh Aunty in son babana sosai kamar yadda shi ma yake sona".
"To in dai kina son Aliyu Haidar dole sai kin yi wannan aiki, idan ba haka ba zaki rasashi rasawa ta har abada".
Ƙara ruɗewa sosai Leesharh ta yi, cikin tsananin tashin hankali ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta da yake harba mata pat, pat kamar zai fasa kirjinta ya fito, ba komai bane ya hassasa mata hakan face tsoro.
"Aliyu Haidar yana hannunmu, ba kuma zamu sake shi ba har sai kin kammala mana aikin mu, abu ɗaya idan kika saɓa mana ki sani a jikin babanki zamu fanshe".
Hajiyar ta sake yin wannan magana cike da iya gaskiyarta.
A ɗan shagwaɓe wannan matashiyar matar ta ce. "Why now mummy? Ai da kin barni da ita ma zata yi aikin ba sai kin saka baki ko kin gaya mata babanta yana a wajen mu ba".
"Ki ɗauketa ku bar parlourn nan, bana son na sake ganinta har sai an gama koya mata komai idan za'a kaita gidan Abu Abdussalam sai mu yi bankwana". Cewar Hajiya, tana kai karshen maganar kuma ta miƙe ta nufi ɗaya daga cikin bedroom da suke a cikin parlourn.
Binta da kallo wannan matashiyar matar ta yi har sai da ta shige ciki, sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da miƙewa tsaye, cikin mutunci ta riƙo hannun Leesharh ɗin a kan ta zo su tafi ta kaita
room ɗinta.
Bata da wani zaɓin da ya wuce ta bita, dan tun da ta ji furucin wannan hajiya a kan babanta sai ta ji ta sanyawa ranta dole zata yi wannan aiki, dole ta aikata shi ko dan ta tsiratar da rayuwar mahaifinta da shi kaɗai ya rage mata a duniya.
Ni kuwa na ce to Allah yasa idan kin kammala aikin su cika maki alkawarinsu na sake ku ku koma ƙasarku lafiya ke da baban naki, amma fa akwai cakwakiya, ace irin wannan tampatsetsen gida da dollars ta zauna masu sosai ɗin nan ne suke neman leƙar asirin wani? Daga gani kun san ba dan kuɗi zasu yi hakan ba, dole sai dai ransa ko wani abin makamancin hakan, da alama mummunar gaba ce a tsakaninsu, dole akwai abin da Ramish ɗin nan ya aikata masu da suke neman ɗaukar fansa, to koma