x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 28 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 81001 words
  • 84000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 359

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
lokacin cin abincin nasu, duk cikin gidan Gimbiya Zunaira ce kawai bata saka kowa aiki, da kanta take yi komai, sai dai idan sun ganta zata yi aikin ne su yi maza su kwace su yi mata, amma ita ko fruits ɗaukar wuƙa take yi ta ce zata yanka da kanta, sai dai su kwace su yanka mata, ba zaka taɓa jin ko da sunan wasa ta ce wance or wane yi mun abu kaza ba, sam bata da girman kai kamar ba jikar cikakkun modarawa ba!.

BARI MU LEƘA SU KAMRAN WATA KILA KAFIN MU DAWO SUN KING SUN GAMA CIN ABINCIN!!.

🏞️FOREST🏞️

KING OF THE FOREST. Aikin gyaran namar ya kammala tas, sannan ya miƙe ya shigarwa da Mammarsa ciki kamar dai yadda suka saba.

Bayan ya jibge mata su a madafarta ya fito ya nufi wajen da yake yin wanka. A gurguje ya yi wankar nasa ya fito, kayansa da ya saba sakawa na sakar audiga na gonarsu da Mammarsa take saƙa masu ya ɗauko, zuciyarsa cike pam da tunanin su pretty, ita kuma Mamma zuciyarta a cike pam da tunanin me ya kawo mayaƙa cikin wannan daji da har suka farmaki Kamran ɗinta? Kenan hakan na nufin basu da nisa da Masarauta ne ko yaya?.

Abin ya yi mugun bata mamaki ne, yau tsawon shekaru 25 zuwa 26 tana cikin wannan daji! Bata taɓa ganin mayaƙa ba sai yau, tana dai ganin manya manyan maharba suna giftawa time to time, suma tana kan jima bata gansu ba, bayansu kuma bata ganin kowa, sai dai idan hanya ta kwacewa wani ya afko cikin dajin bisa rashin sani. Wannan abin ya ɗaure mata kai kuma ya bata mamaki!.

Fitowa tsab tsab cikin shigarsa mai kyau king of the forest ya yi, ya kara kyau sosai Kamran, sai dai daga ganinsa ba tambaya kasan tabbas yana da yare, dan yanayin fatar jikinsa dama shi kansa, yanayin su Mamma san basu yi kala da larabawa ko Hausa fulani or turawa ba, sai Allah sai kuma mammar tasa ce kawai suka san su ɗin ƴan wace ƙabila ce or daga wasu duniya suke? Nasan kowa a ransa yana tunanin me ya kawosu wannan dajin? Ina mahaifin Kamran tun da dai mace bata haihuwa ita kaɗai? Ni kai'na PRINCESS TEEMA waɗan nan tambayoyi shi ne a cikin rai'na, a wannan daji aka haifi Kamran, kuma da alama tun kafin a haifesa Mamma tana cikin wannan daji, ta yi rayuwa mai tsawo a ciki, to kenan before a tare suka yi rayuwa mai tsawo da baban Kamran ɗin har suka haifesa? Me yasami baban nasa? Ina ƴan uwansu? Idan ita Mamma bata da ƴan uwa to shi baban nasa fa? Ina nashi ƴan uwan? Kun ga dai Mamma jaruma ce, da alama kuma kamar yadda take bawa Kamran training ita ma haka aka bata horo a cikin wannan dajin, to waye kenan? WAƊAN NAN AMSOSHIN ALƘALAMIN PRINCESS TEEMA CE KAWAI ZAI IYA WARWARE MAKU SHI KU DAI KU KASANCE A TARE DA NI, BA ZAKU YI DANASANIN BIBIYAR WANNAN LABARI NA RAWANIN ZALINCI BA IN SHA ALLAH, ZAKU ILMANTU, KU WA'AZANTU, IN FAƊAKAR DA KU, KU NISHAƊANTU MATUKA, AKWAI ABUBUWAN DA IDAN MUKA SHIGA CIKIN LABARIN ZAKU SHA MAMAKI!!.

"Mamma, Mammaaa, where are you?". Cewar Kamran ɗin kenan.

Tana daga zaune a gefen bakin bed nata tana tunani a kan warriors ɗin nan ta amsa mashi da.
"Here I am, what happened? Why kake nemana?".

Yaye labulen sakar dake a bakin kofar ɗakin nata ya yi, kasancewar babu mai yi mashi aski a cikin wannan dajin hakan yasa gashin kansa take da yawa, sai dai mammarsa tana rinƙa yanke mashi tsawon gashin da wuƙa, saboda ya rage yawa kada ya rinƙa takura mashi.

"Mamma i want to go to somewhere here, ba zan jima ba, only 1 hour is okey for me na dawo gida".

Bin shi da kallo kaɗan ta yi kafin ta ce. "What about your food? Waye zai ci maka?".

"Oh Mamma na manta da abincin ne, to zan ɗauki abincin na tafi da shi, dama wani babban kogi na gani mai ruwa sosai a cikinsa ta ganganren can, so the place is very very beautiful, can zan je in yi bule a cikin ruwa".

Tun da ya fara magana tasan karya yake yi mata, domin tasan gaskiyarsa da kuma karyarsa, bai saba yin karya ba shiyasa idan ya yi dole a gane, a haka ma fa wai ya yi kasa da kansa baya son ta kalli cikin idanunsa, dan yasanta da kaifin ƙwaƙwalwa, so baya son ta gano shi, sai dai ya makaro, ita ta haife shi ta kuma renesa tsawon shekaru ashirin da biyar yanzu, dole ta iya gane shi ciki da waje.

Amma sam bata nuna mashi cewa ta gane karya yake shirga mata ba, sai ma ta ce ya je ya ɗauki abincin nasa ya tafi, ta kuma yi mashi hakan ne ba dan komai ba sai dan ta jima tun ɓatar su twins bata gansa cikin farinciki da annashuwa ba sai yau, tun shekaru goma baya da maman twins ta ɓace mashi ya koma wani irin so silent over, daga e sai a'a kawai yake haɗa shi da mamar tasa, ya dai'na sakewa suna hira, ya shiga damuwa sosai ta yadda mammar tasa duk kaifin basirar nan tata ta kasa iya shawo kan damuwar tasa.

So yau ta ga yana cikin annashuwa tare da farinciki, bata son ta ɓata mashi wannan farinciki da ya jima bata gani a saman fuskarsa ba, duk da cewa bata san murnar me yake yi ba, amma dai tasan Kamran ba zai taɓa yi mata abin da zai ɓata mata rai ba! So koma me silar shigarsa farinciki a yau tana maraba da shi, kuma ba zata yi abin da zai kawar masa da farincikin ba, shiyasa ta bar shi ya je duk in da yake so, tasan jarumi ne sosai shi ɗin, so zai kula da kansa.

(Kada fa Mamma ta yi mana wayo, ta yi mana mage mai kwanciyar ɗaukar rai ta bi bayansa ta je ta raba shi da su pretty mu shiga uku💔😥 ni nasan halinta sarai😥)

A hanzarce ya amsa mata da okey Mamma, kafin ya wuce ya nufi cikin wajen madafar tata ya ɗauko abincinsa a cikin wani mazubi mai kyau, sannan ya fito tare da ƙara kwala mata sallama daga bakin kofa akan ya tafi.

Tana daga cikin ɗakin ta ce mashi take care.

Daga haka ya fice daga cikin ƙogon, sam bai nemi Rocky ba, dan yasan yau Rocky yana can yana ta fama da cin nama, so ba kula shi Rockyn zai yi ba, gara mashi kawai ya yi tafiyarsa.

Kai tsaye wajen su pretty ya nufa, sai daɗi yake ji a cikin ransa. Cikin nutsuwa a hankali ya shiga cikin wajen nasu, dan yana rike da abincinsa a hannu, kada ya yi ya zubar da abincin.

Kwance ya iskosu a saman bed ɗin nasu, pretty tana karanta wani littafi wanda sai Allah sai kuma mum ɗinta tare da alkalamin PRINCESS TEEMA ne kawai yasan a ina suka samo wannan littafin, ga littafin dai na addu'oe ne.

Jin motsin mutun yasa pretty ta ɗago kai, ɗan wannan ɗagowa da ta yi yasa kumatunta suka ɗan motsa, hakan ya bayyanar mata da kyakkyawar dimple nata da ya ƙara bayyanar da kyan fuskarta.

Ganin shi ne yasa ta yi saurin miƙewa zaune tana binsa da waɗan nan idanun nata masu jefa bawan Allah cikin ruɗu ya kuma rasa nutsuwarsa.

"Pretty motsin me nake ji haka ne?".
Cewar Sweetie dake kwance.

"Wannan mutumin na ɗazun ne ya sake dawowa".
Ta bata amsa tana mai zuro ƴan kyawawan fararen kafafunta kasan gadon.

Yunƙurawa Sweetie ɗin ma ta yi ta miƙe zaune tana jin wani irin babu daɗi a cikin ranta, yau karo na farko da ta ji zafin ciwon makantarta, da sam bata damu da dole sai idanunta sun buɗe ta kalli abu ba, saboda a cewarta to ko idanun sun buɗema ai daga mum ɗinsu sai pretty kawai zata gani, wadda kuma ta saba ganinsu kullum, amma yau an sami sabon mutun wadda bata sani ba kuma bata taɓa ganinsa ba, kash ba halin ta ganshi, abin ya yi mata mugun ciwo yau, har ga Allah tana son ganin wanene shi ɗin.

A saman wata dutse mai ɗan girma kaɗan dake cikin wajen Kamran ya zauna yana faɗin.

"How's your body Sweetie?".

Kamar zata yi kuka, har idanunta sun ciko da ruwan kwallah na rashin gani ta amsa mashi da. Alhdulillah.

Maimaita kalmar Alhdulillah ya yi kafin ya maido da kallonsa a kan pretty dake ta faman kallon kwanon abincin dake hannunsa, bata taɓa ganin irin kwanikan ba, shi kuma bai taɓa jin kalmar Alhdulillah ba, so dukkansu da abin da suke mamaki a yanzu.

"Let's go now ko?". Cewar pretty sarkin sauri.

"Go to where?".
Ya tambaya yana mai da kallonsa a kan littafin da suke karantawa. Allah idanun Kamran suna da matuƙar kyau sosai, sai ma idan yana kallon abu, sai kaga idanun suna ɗaukar hankali sosai.

"Neman wannan mutumin da mum ta ce mu nemosa, you forget that you said zaka taimaka mana to fine him ɗazun ba?".
Har wa yau pretty ce ta bashi wannan amsa.

"Yeah i will going to help you ku same shi, but now ku zo ku ci abincin Mammata".

Da sauri Pretty ta mayar da kallonta a kan Sweetie dake faman girgiza kai alamar su ba zasu ci abincin ba, dan basu yarda da shi ba, kuma da alama mum ɗin su ta ja masu kunne a kan mutane, dan ga shi sai ɗari ɗari suke yi da shi, sam basu saki jiki da shi ba.

Ganin Sweetie tana girgiza kai ba tare da ta yi magana bane yasa pretty ta ɗan shagwaɓe fuska kamar zata yi kuka ta bashi amsa da.
"We can't eat".
A shagwaɓe ta yi maganar. Hakan ba ƙaramin kara mata kyau ya yi ba, duk sai ta sa Kamran ya ji wani irin bawan Allah.

Why?. Ya tambayesu yana mai do da kallonsa a kan Sweetie, dan ya lura ita ce mai sanya Pretty yin abu, idan ta ce ba zasu yi abu kaza ba to Pretty ma ba zata yi ba, idan kuma ta ce za su yi abu, to Pretty zata amsa su yi.

Ita ce babba kamar yadda ya yi tunani tun farko, kuma ta fi Pretty tunani da nutsuwa, and then ita tun ainahi bata cika fita waje ba, koda yaushe tana a tare da mum ɗinsu lokacin da mum ɗin take nan, hakan yasa ta fi Pretty sanin abubuwa sosai, and kuma kafin mum ɗin su ta ɓace kullum tana gaya masu cewa Pretty ta bi Sweetie sau da kafa, idan ta bita tamkar ita mum ɗin ta bi, duk abin da Sweetien ta ce mata to maza ta yi shi, hakan yasa kuka ga idan Sweetie ta ce a'a, to Pretty ma zata ce a'a.

"We can't eat your food be cause we don't know you, kuma mum ta ce kada mu yarda da kowa, kada mu yi magana da kowa, ko mutun ya yi mana magana kada mu amsa, sai dai ta ce mana akwai mutun ɗaya da idan muka ji zuciyarmu ta yarda da shi to mu yarda da shi, dan mai taimako ne, and kuma ta ce lallai mu nemo wani wanda ya taɓa taimaka mata a dajin nan". Cewar Sweetie kenan.

"If that's the case then why kuka yi accepted nawa time da na shigo nan? Why kuka yi magana da ni? Kenan kun karya maganar mum ɗinku? Ba ta ce kada ku yarda da kowa ba? Kada ku yi accept nawa sai wannan da ta ce ku nemo, why ni kuka yarda da ni?".

Sweetie ɗin ce ta sake amsa mashi da. "Bamu yarda da kai ba, and we didn't accept you, kawai bamu da yadda zamu yi ne?".

Yana ƙoƙarin sake yin magana Pretty ta riga shi da cewa.
"Ni dai ina ji a jikina kai ne wanda mum ta ce mu nemo, and kuma zuciyata ta yarda da kai, please don't play with our heart, idan kai ne wannan mutumin tell us, idan kuma ba kai bane please nan ma ka gaya mana, ni dai har cikin rai'na i really accepted you".

Haƙiƙa hakance, ta yarda da shi, ita ma Sweetie ɗin har cikin zuciyarta ta yarda da shi, kawai ita Sweetie da yake ta fi Pretty dogon tunani sai ya zamana bata son gaya mashi cewa sun yarda da shi, a ƴan kananan shekarun nan nata wai zata bari ne sai taga gudun ruwansa sannan ta gaya mashi cewa ta aminta da shi, yarinya mai wayo. Shegen wayo ke gareta kamar me!.

Tun a karon farko suka ji ya kwanta masu a cikin zuƙatansu, kuma kuwa kunsan Kamran yana da shiga rai, and then ko dan kyan zuciyarsa da son taimako dole a so shi, kada ku manta haɗuwarsu ta farko ma taimakon Pretty ya yi, badan shi ba ai da yanzu babu ita ta mutu, kunga kuwa ko dan wannan taimako da ya yi masu dole su ji suna son shi, and kuma dole su fara tunanin ko shi ne mai taimakon da mum ɗin su ta gaya masu? Sau da dama suna ganin maharba suna giftawa ta cikin dajin, idan sun gansu ɓuya suke yi dan kada su gansu, haka mum ɗinsu ta koya masu, kada su yarda wani ya gansu, su rinƙa ɓuya idan suka ga mutane, to a takaice dai duk maharban da suke gani suna giftawa basu taɓa jin koda mutun ɗaya daga cikinsu ya kwanta masu a cikin zuciyoyinsu ba sai Kamran ɗin, hakan yasa suka fara tunanin ko dai shi ne mum ɗinsu ta ce su nema?.

"I can't play with your hearts Pretty, not even you, ni bana cutar da kowa ko mai ƙanƙantar cuta, so feel free with me, yanzu dai ku zo ku ci abincin Mammata sai mu fita waje neman mutumin ko?".

Kallon Pretty Sweetie ta yi tana jiran ta ji me ƴar uwar tata zata ce.

"Okey zamu ci, amma ba'a gabanka ba, sai ka fita waje". Cewar Sweetie ɗin.

Da okey ya amsa masu kafin ya miƙe ya miƙowa Pretty abincin. Sai da ya ji wani irin shock da bai taɓa ji ba a jikinsa na haɗuwar hannayensu wajen karɓar abincin. Amma sai ya daure ya nufi hanyar fita daga cikin wajen.

A wannan karon sam yaki yarda ya juyo su haɗa idanu da ita, dan ɗan taɓa hannunta da nasa hannun ya yi bisa kuskure ma tasa ya ji kamar ba shi ba, dan haka sai ya yi ficewarsa kawai abinsa.

Yana fita Pretty ta kalli ƴar uwar tata kafin ta fara magana a nutse.
"Sweetie Allah wannan mutumin shi ne Mum ta ce mu nemo, na ji hakan a jikina, dama kin ji mum ta ce idan mun gansa zamu ji zuciyoyinmu sun yarda da shi, to ni dai na yarda da shi, ban san ko ke baki yarda da shi ba".

Nisawa ta ɗan yi kafin ta amsa mata da cewa. "Pretty na fiki yarda da shi, zuciyata ta aminta da shi, amma kada mu yi sauri, mu jira mu gani, kinga mum ta yi mana kashedi sosai a kan yin abu cikin gaggawa, gaggawa aikin shaiɗan ne, duk kuma wanda ya yi gaggawa a kan abu sai ya tabka danasani".

"Hakane, to amma Sweetie idan dai har kin yarda da shi kema why not ba za mu bashi saƙon da mum ta ce mu bashi idan muka ganshi ba? Kawai na ɗauko mu bashi, nasan ya manta mum ne shiyasa ya ce mana ba shi ba ne muke nema, amma tun da mum ta ce saƙon yana ƙunshe da abubuwa dayawa masu girmaa cikinsa kila idan muka bashi yana dubawa zai tuna da mum ɗin".

"Pretty kefa baki jin magana, wai ba yanzu na ce maki mum ta hanamu yin abu cikin gaggawa ba? Kina ji fa bai yarda cewa shi ne wanda muke nema ba, taya za'ayi mu ɗauki saƙon da mum ta ce mana sai lallai wannan mutumi da ya taimaka mata ɗin zamu bawa ki ce mu bawa wanda bai yarda shi ya yi taimakon ba? Kina son mu saɓa maganar mum kenan?".

"A'a bana son mu saɓa maganarta, dama dai kawai dan na ji ta ce idan mun ji ya kwanta mana a rai to shi ne, shiyasa na ce ko ya manta da mum ne idan muka bashi saƙon zai tuna".

Shiru Sweetie ɗin ta ɗan yi kafin ta ce. "A'a ba zamu bashi komai ba, ba zamu ma nuna mashi kamar an bamu wani abin mu bawa wanda muke nema ba, mu bari har sai ya amsa da bakinsa shi ne wanda muke nema, kuma sai ya rantse mana da Allah".

(Ni kuwa na ce idan ya san Allah kenan ba! To fa ga shi shi Kamran ya ɓoye masu shi ne ya taimaki mamarsu dan wani dalili nasa na kansa wadda bai bayyana ba, ga shi su kuma mamar tasu ta basu saƙo su bashi, ko saƙon menene?.....🤔 Wannan sai alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana kawai zai warware maku wannan cakwakiyar, ku dai cigaba da bibiya, bamu fara komai ba, sai a gaba zamu yi ainahin shiga cikin labarin cikin labarinmu, yanzu duk muna faro foundation!!. Amma kuma fa da gaske idan bai gaya masu shi suke nema ba ba zasu taɓa bashi wannan saƙon ba, to fahhhhhhhhh)

"Tom shikenan Sweetie yadda kika ce haka za'ayi, yanzu ya zamu yi da abincin da ya bamun nan?".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Jeki ki juye shi a cikin bowl, ki dawo mashi da kwanonsa, mu ba zamu ci abincinsa ba, na ce mashi zamu ci ne kawai dan kada ya yi wani mummunar tunani a kanmu, ko kuma ya ja baya da mu ganin kamar bamu yarda da shi ba, na nuna masa zamu ci ne dan ya kara sakin jiki damu har mu gane wanenen shi mu kuma san idan shi ne wanda muke nema".

(Ka ji yara kanana da shegen wayo da
End Ads