kawai ba sai ka sake yi mata wasu tambayoyi ba". Cewar wannan mata da take aikin gogewa Leesharh ɗin hawaye.
"Tayaya zaki ce mun kada na tambayeta? Idan na bata maganin da bai yi dai'dai da ciwon nata bafa? In fact ma kin taɓa ganin garwashin wuta yana da kafa ne da zai tashi ya shiga bakin mutun haka kawai? Ke baki ga yadda ta ruɗe daga tambayarta ba, dole akwai abin da ya faru a rayuwar wannan yarinya na shekara ɗaya da ya wuce, yana da kyau mu san menene". Dr ya bata amsa.
"Dr Suhail bana son jin dogon magana, kawai kayi aikinka kada ka sake tambayarta, idan kuma ba zaka yi aikin bane sai na kira Dr Bakir na sanar da shi ya turo mun wani likitan". Ta yi maganar a gasale. Da alama ranta ya ɗan sosu da jin kalaman Dr na neman son jin tarihin Leesharh, ta ga alama kamar ya ji tausayin yarinyar kuma yana son janta a jiki ya taimaka mata, shi ne ta yi saurin taka mashi birki!.
"Am sorry, bari na dubata na yi mata abin da ya dace". Ya bata amsa tare da fara gyara alluran barcin.
Da kyar Leesharh ta tsaya aka yi mata alluran. A takaice dai Dr Suhail ya dubata ya kuma yi mata abin da ya dace, sannan ya basu magunguna da zata rinƙa sha, a hankali hankali voice ɗinta zai koma normal, daga haka ya yi masu sallama ya tafi.
Ita kuma wannan matashiyar mata miƙewa tsaye ta yi tare da zubawa Leesharh dake ta faman barci idanu tana kallonta, kamar mai tunanin wani abin, kamar kuma tana ɗan jin tausayinta. Ta ɗauki a kallah 5 mins a haka kafin ta sa kai ta nufi waje.
Leesharh kuwa, babu sallar mangariba bare issha, sai barci take yi sakamakon wannan allura da aka yi mata, ba ita ta farka daga wannan barcin ba sai wuraren asuba.
A hankali ta waro idanunta da suke jajir dasu saboda barci, jikinta duk ya yi mata nauyi, da kyar ta iya miƙewa zaune, har wani irin jiri ta fara ji, kanta na sara mata, cikin matsananciyar kasala ta miƙe ta nufi cikin toilet.
Alwala ta ɗauro ta zo ta yi sallar mangariba, dan a tunaninta yanzu mangariba ce, saboda taga ɗan haske haske, sai take ganin kamar yammace irin an fara kiraye kirayen sallar mangaribar nan.
Baki a ɗauke da sallama Auntyn tata ta shigo cikin room ɗin, hannunta na a rike da akwati mai bala'in kyau da kuma wata envelope mai ɗan girma. Leesharh dake zaune a saman dadduma ce ta fara binta da kallon mamaki.
A bakin bed matar ta zauna tare da faɗin. "A'isha idan kin idar da sallar ki zo".
Miƙewa ta yi daga kan daddumar tare da naɗeta ta mayar cikin wardrobe ɗin, sannan ta zo gaban matar ta tsugunna tana faɗin gata nan, duk jikinta ciwo yake yi mata tana son ta je ta yi wanka, dama bata yi wanka bane wai dan kada lokacin sallar mangariba ta wuce ta, kun san shi gajeran lokaci ne da shi, to a tunaninta yanzu mangariba ne ta yi sauri ta ɗauro alwala kawai da nufin idan ta yi sallah sai ta yi wanka tare da ƙara ɗauro wani alwala ta yi sallar isha.
"Tashi ki zauna a saman bed ɗin". Matar ta faɗa.
Ba musu ta miƙe ta haye saman bed ɗin abinta.
"To A'isha, wannan akwatin kayan sakawarki da zaki yi amfani da su ne a gidan Abu Abdussalam idan kin je, akwai komai a ciki, na tabbata ba zaki buƙaci komai ba, wannan envelope ɗin kuma takardun makaranta ne a ciki, dama na gaya maki mai girma Abu Abdussalam baya ɗaukar jahilai aiki, daga irin masu diploma ne suke mashi aiki, kema ba karamar wahala muka sha ba kafin mu samu su amince su karɓeki aiki da kwalin secondary school, dan ma dai muna da hanyar da ba za'a iya kin bukatarmu bane yasa Abu Abdussalam ya yarda, dan haka ki mayar da hankali, ga takardun makaranta nasa an buga maki, nasan kin yi karatu from primary two Jss two, babanki ya gaya mana, so yanzu dai waɗan nan takardu har da result na waec ne a ciki, na primary da komai da komai yana ciki, kuma da first class kika fito, already takardunki sun kaiga mai girma Abu Abdussalam, ya gani kuma ya yarda ya shaida, yanzu zan damkamaki su a hannunki ne kawai dan wata kila watarana za'a buƙacesu a gidan, so ki ajiyesu da kyau a wajenki, sannan ki yi ƙoƙari wajen aiki cikin nuna wayewa da ilimi, kinga result ɗinki sun nuna ke first class ce mai ƙoƙari sosai, so kada ki je ki yi masu kauyanci da shirme".
Jinjina mata kai Leesharh ta yi tare da yi mata alkawarin In Sha Allah zata kula sosai. Shafa kanta matar ta yi tare da sanya mata albarka. A takaice dai haka ta kara gaya mata komai da komai tare da gaya mata wasu dabarun, sannan ta bata takardun tare da ce mata ta yi wanka ta shirya yanzu za a kaita gidan wadda zata kaita gidan Abu Abdussalam ɗin.......Tirƙashi! Wadda zata kaita gidan ma gidanta daban?.🤔
Miƙewa matar ta yi ta nufi waje, ita kuwa Leesharh toilet ta nufa, a gurguje ta yi wanka ta zo ta hau shiri, a nata tunanin fa lokacin sallar isha bata yi ba, saboda tana cikin room, bata ganin rana.
Ɗaya daga cikin tsofaffin kayan da ta saba sakawa ta sanya, abaya ce black color mai kyau, ta gyara gashin kanta da ya sha wanki da gyara a wajen wannan mata mai koya mata aiki, ta feshe jikinta da perfume mai daɗin kamshi, ita da kanta tasan ta yi kyau sosai, amma sai fargaba da faɗuwar gaba take ta ji a ranta.
Bayan ta kammala shirinta fes ne ta nufi wajen window dan ta leƙa wajen harabar gidan. Tana yaye labule ta buɗe window me zata gani? Sai ganin rana ta yi ɓaro ɓaro, a lokacin ma karfe bakwai ta kusa. Zaro idanu waje ta yi tana mamaki, ita da take jiran lokacin sallar isha ta yi? Ashe bata san tuni asuba ma ta wuce ba.
A hanzarce ta dawo cikin room ɗin tare da shinfiɗa dadduma ta tada sallah. Isha ta fara biya kafin ta yi asuba, tana idarwa bata kai ga yin addu'a bama sai ga wannan mata ta shigo, ta zo ɗaukarta ne su tafi.
A hanzarce ta yi addu'a ta shafa tare da naɗe daddumar matar ta riƙo hannunta suka nufi waje bayan ta ɗauka mata wayarta da yake a saman bed in da ta ajiye tun daren jiya bata sake bi ta kai ba. Wasu mata guda biyu ne suka zo suka ɗauka mata akwatin kayanta izuwa harabar gidan. Sai kallonsu da mamaki take yi, ta gane masu aikin gidan ne, dan a aikin kitchen da aka koya mata tana ganinsu a kitchen ɗin suna nasu aikin suma, yanzu ita damuwarta ɗaya shi ne taga ina waɗan can hajiyoyi guda biyu da suka rako wannan matashin jiya? Tasan dai su ba ƴan aiki bane, duba da yanayin kayan jikinsu, hamshaƙai ne a gidan, to ina suke?!.
Suna tafiya wajen parking space na gida wannan mata tana yi mata bayanin aikin da aka ɗauketa zata yi a gidan, ba komai bane face yin mopping na babbar parlourn gidan in da family suke haɗuwa su ci abinci, daga nan sai gyaran bedroom na yaran gidan, shikenan aikinta, banda wankin toilet, akwai masu wankin toilet, iya gyaran room ɗin ne kawai.
Sosai ta kasa kunnuwa tana sauraron matar har suka isa wajen motar da zai ɗauketa izuwa gidan wadda zata kaita gidan aikin.
Rungumarta matar ta yi tare da yi mata fatan nasara kafin ta kara karfafa mata gwiwa, sannan ta bata wayarta da ta kashe mata shi already, daga haka suka yi sallama ta shige cikin motar, wancan hajiyar mahaifiyar wannan bata ko leƙo in da suke ba. Har motarsu ya bar gidan bata kalli wannan hajiya ba, yau kwana uku kenan ma bata haɗu da wannan hajiya face to face ba, ko ina take zuwa oho mata.
A takaice dai wani dakareran gida aka sake kai Leesharh, a nan ne wani mota ya ɗauketa tare da wata hamshaƙiyar hajiya dake sanye cikin abaya tare da nikaf ita ma suka nufi gidan ABU ABDUSSALAM BIN BADEEN tare da wasu bodyguards guda biyu da suka yi masu rakiya.........
Kai tsaye unguwar.............
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
Kai tsaye unguwar.............EMIRATES HILLS motarsu Leesharh ta nufa........ Ku daga jin sunan arear kun san bana ƙananan kai bace ba, area ce wadda take da gamayyar kera keran haɗaɗɗun high rise building da manyan ƙasashen duniya take ji da su, duk wata ƙasa da ta amsa sunanta ƙasa to tana takama da ire iren waɗan na high rise building ɗin, gini ne wadda zaku gansa kamar da glass zallah aka yi sa, luxurious area ne dake ta farko a cikin faɗin DUBAI, babu ƙananan gine gine ko guda ɗaya a gabaɗaya arear, dukka luxurious gine gine ne na manyan shegu a ƙasar, ta ko'ina shinfiɗaɗiyar titi ne mai ji da lafiya har kofar gidaje, ga hasken lantarki ta ko'ina, tsayawa zayyana maku haɗuwar wannan area ma sam ba zai yi wu ba, domin baki ma ya yi kaɗan ya faɗesa, ga wasu mahaukatan cameras ta ko'ina dake ɗauko duk wata abu da zata gifta a wannan area, gabas da yamma kudu da arewa Cameras ne.
Wasu irin jiga jigan zaratan lafiyayyun securitys dake tsaron arear tun daga farkonta har karshenta kawai ma ya isa ya sanya hantar cikin bawa ya kaɗa, kowani security ka gani fuskar nan tasa kamar ta saniya, a tuɓune, a fusace, kamar waɗan da aka aikowa da saƙon bakar takarda ta albishir da shiga cikin wutar jahannama, sam babu annuri ko miskala zarratin a tattare da su, ga wasu shegun bindigu a hannunsu. Sai dai securitys ɗin kala kala ne, ciki akwai ƴan'sanda ma, abin ku da Defence minister, duk wata kaki a kasarsa take, dole ai kuga kaki kala kala a gidansa. Sai kai komo suke yi wasu daga cikinsu, da alama komai ƙanƙantar motsi suka ji sai sun duba.
(Ni kam nace dole waɗan can ƴan leƙen asiri na matan can su kasa iya basu information a kan gidan Abu Abdussalam bin Badeen, irin wannan tsaro dake a arear ma kawai?🤔 Ina ga gidan kuma?🤔)
Ganin waɗan nan securitys kawai sai da ya sanya hantar cikin Leesharh ya yi wani irin kaɗawa, duk da tana cikin mota amma ta tsare hanya da kallo, da alama tana son sanin tsakanin gidan da aka ɗaukota da wannan gidan ya tazararsu take, Leesharh ba dai wayo ba. Sai dai ganin waɗan nan securitys ɗin yasa ta mance duk wasu abubuwan da ta gani a hanyar zuwa dan riƙesu a matsayin yadda zata gane hanya ko watarana, ta manta komai tsabar shiga tashin hankali, sai ma da ta ji cikinta ya yi wani irin murɗawa mai bala'i zafi, nan take ta nemi nutsuwarta ta rasa, tunani ta fara yi asirinta ya tonu gata can a hannun waɗan nan dodannin securitys ɗin suna cin namar jikinta ɗanye. Ai bata san lokacin da ta kurma ihu a cikin motar ba, ta ɗauka da gaske ne ake yagar namar jikin nata.
Sai da matar ta taɓa ne ta farga ashe dai tunani ne. Wani irin wahalallen yawu ta haɗiye tare da fara yin danasani mafi muni na karɓar wannan aiki da ta yi tun daga yanzu, tun ma bata kai ga shiga cikin gidan ba ta fara yin nadamar zuwanta duniya, tunani take yi kawai ta shiga uku ta lalace! Shikenan karshenta ne ya zo, idan asirinta ya tonu a irin wannan gida ace gata an kamata a matsayinta na ƴar leƙen asiri ai shikenan ko gata namar jikinta ba zai samu na agasa shi ba, a ɗanye zasu cinyeta, yau ta shiga uku ta lalace!! Ashe su Jasrah sun yi gaskiya, sune ainahin masoyanta da suka hanata karɓar wannan aiki!.
Duk da sanyin Ac dake a cikin wannan danƙareriyar mota ita fa Leesharh zufa ce ta fara tsastsafo mata a gabaɗaya face ɗinta, kukan mutuwa a cikin zuciyarta kawai take yi, ta yi tsuru tsuru idanu sun rena fata, har buƙatar shiga toilet ta fara ji ya kamata saboda yadda cikinta yake murɗa mata ga kuma dukan uku uku da kirjinta yake yi, kunsan mara gaskiya fa shi tsoratarsa daban take da kowa!.
Sosai wannan mata ta lura da halin da Leesharh ta shiga, amma sam bata kula taba, domin kuwa tasan duk wanda zai shiga gidan Abu Abdussalam bin Badeen to fa sai ya razana makamancin haka, bare kuma ita da tazo da zallar rashin gaskiya? Ai tama yi ƙoƙari da bata saki fitsari a wando ba, leƙen asiri ta zo yi wa masu farautar ran ɗan gidan fa aka turota ta yi, tab ai kunga idan akwai abin da ya fi fitsari a wando ma yi zata yi.
Bata ma kara tsananin tsorata ba sai da ta ga sun dimfari wani katafaren luxurious High rise building wanda ya fita daban da sauran gine ginen dake arear, kuma jiga jigan securitys sun fi yawa sosai a wajen, design na ginin ma kawai abin kallo ne, ba wai gini ne da aka yi shi dogon bene kamar na yau da kullum ba, a'a shi wannan idan ka gansa sak design ɗin world, wato duniya yake, ya yi matuƙar ƙawatuwa kuma ginin ya zauna ya zanu da kyau, ya fita iya fita.
Duk ba shi bane ya ƙara ɗagawa Leesharh hankali, masu tsaron titin da zata sadaka da cikin wannan hamshakin ginin ne suka ƙara ɗaga mata hankali da har suke ƙoƙarin sanya zuciyarta ta buga. Wasu irin jiga jigan bodyguards ne waɗan da kallonsu a wajen Leesharh da sauran marasa gaskiya kai har ma da masu gaskiya waɗan da suke da karamar zuciya dai'dai yake da kallon mutuwa, fusatattun fuskokinsu kawai ya isa ya sanya mutun tsumar tsaye. Sanye suke cikin baƙaƙen kaya sidif, wasu irin shegun securitys shoes ne a kafafunsu, shi ma baki, irin waɗan nan takalmar ne da idan sun takeka da shi sai mutuwa, ga wasu uban black glass da suka zuba a ido kamar ka kurma ihu idan ka gansu, fararen larabawa ne tas waɗan da babu ɗigon baki ko kaɗan a fatarsu, dayawansu suna da dogayen gemu bakin kirin, sannan gasu da tsawo tare da cikar halitta ta jarumai.
Tun daga ɗan nesa da katafaren gate na gidan wani shirgegen bodyguard ya ɗagawa motarsu Leesharh jan wuta, alama su dakata daga in da suke kada su ƙariso, aikin wannan bodyguard ɗin kenan, idan sun san da zuwanka to wannan bodyguard zai ɗaga maka wata farar wuta dake a hannunsa jikin wata kyakkywar na'ura mai bala'in haske, to idan kaga ya ɗaga wannan farar wutar alama ce ta sun sami labarin zuwar wannan mota mai kira kaza da numberta kaza, shi ne zai ɗaga maka wutar alamar ka ƙariso bakin gate su cajeka, ba wai zaka wuce ciki bane, no, wannan farin wutar iso ake maka izuwa bakin gate, sannan wasu bodyguards ɗin su caje motarka tsab ta hanyar amfani da na'urori da komai ƙanƙantar abin zargi bata ɓoyewa, idan suka gama caje motarka tsab, sannan su baka damar wuce gate na farko izuwa na biyu, a nan ma sai ka sake tsayuwa amsa wasu tambayoyi tare kuma da a kara dubaka da kyau, sai sun tabbatar lafiya lou sannan su baka hanya ka wuce ciki izuwa katafaren parking space na gidan.
Idan kuma suka ɗaga maka jan wutar nan, to alama ce ta basu san da zuwan wannan mota ba, ba a gaya masu mota kaza mai number kaza zata zo ba, so dan haka tun kana dimfaro gate ɗin gidan zasu ɗaga maka jan wuta, idan kaki dakatawa a wajen to fa zasu sanya bindiga su harbi tayar motarka ne babu ruwansu, so is better for you da ka dakata tun wuri, in kaƙi jiki magayi.
Da yake ita wannan mata tasan da dokar gidan sanka sanka, sai ta sanya driver ya dakatar da motar. Wani irin kukan kura cikin Leesharh ya kara yi na tsoro, dan a tunaninta ko asirinta ne ya tonu, tun bata ma fara aikin ba har ta fara tunanin asirinta ya tuno, kai a gaskiya rashin gaskiya sam bai yi ba a rayuwar nan, idan baka da gaskiya a waje dai kana cikin tsaka mai wuya, fargaba da faɗuwar gaba ba zasu barka ka zauna lafiya ba, kullum kana cikin tunanin asirinka zai tonu, Allah ka rufa mana aisiri kasa mu kasance cikakkun masu gaskiya a duk in da muke, ko dan mu samu zaman lafiya da zuƙatanmu.
Wayarta matar ta ciro daga cikin jakarta mai shegen kyau da tsada. Massage ta shiga kan wani contact da aka rubuta Hajiya Babba. Gajeran rubutu ta rubuta mata tare da tura mata, sannan ta koma ta jingina da jikin kujerar motar.
Ita dai Leesharh sai haɗiyar wahalallen yawu take yi dan bushewa da wuyarta ya yi saboda tsoro, fargaba da razana yasa maƙoshinta ya bushe ta fara jin ƙishi, ga tsoro yasa bata iya haɗiyar yawun nata ma, bama ya fitowa ta nemesa ta rasa.
Almost 10 mins da tura saƙon da wannan mata ta yi sannan ne wannan bodyguard ɗin ya ɗaga masu farin