x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 50 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 147001 words
  • 150000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 360

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
mata mix? Ina suka ga sugar a cikin wannan daji? Ai babu ita.

Kamar yadda suka saba yin breakfast bayan sun yi wanka cike da so da kauna haka suka yi yau ɗin ma, suna gamawa Kamran ya ce mata zai je cikin daji yawo, ba tare da jan mashi rai ko ta ce ba zai je ba ta amsa mashi da sai ya dawo ya kula da kansa.

Cike da murna ya nufi ɗakinsa domin ya shirya, ya ɓoye Kayan da ya sakawa su Pretty a jikinsa sannan ya fito ya nufi waje. Da ido Mamma ta bishi har sai da ya fice, sannan ta fara bin bayansa a sese'sese domin taga ina ya nufa.

E TO LALLAI AKWAI CAKWAKIYA, BARI DAI MU JE MU DAWO.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

KINGDOM OF POWER 💪🔥

Zaune Gimbiya Zunaira take a cikin katafaren lambun da yake a cikin family part.

Zaune take a saman ɗaya daga cikin wasu haɗaɗɗun chairs da suke a wajen da aka tanada dan zama a cikin lambun, an kawata wajen sosai da sosai, ga wani irin iska mai matuƙar daɗi da yake kaɗawa a wajen, iska ne ba mai sanyin cutarwa ba, ɗan dai'dai.

Ta tsantsara kwalliyarta cikin shiga ta alfarma ta ƴaƴan manya manyan sarakuna da ake ji dasu, wata shegiyar Dubai gown ce a cikinta launin pink color, rigar ta sha kyau har ta gaji, yanayin tsarin rigar ya yi kama da masu tula tulan breast ne kamar su Gimbiya Chuchu, dan rigar yana da breast part a jikinsa duk da ba mai girma bane, ita Zunaira yanzu ma ta fara kirgan dangi, amma ta sanya shi a jikinta, hakan kuma ya samo asaline saboda tsawon da take da shi, tsawonta ya fi shekarunta, hakan yasa ake saya masu kaya dai'dai girman na su Chuchu, dan shi ne yake yi mata dai'dai tsawon, da kaɗan Chuchu ta fita tsawo, to kun ji in da matsalar take.

Ta yi shiru tana kallon kyawawan tsuntsayen da suke a cikin ɗan kejin dake kusa da ita, irin kananan tsuntsayen nan ne waɗan da suke three colors, akwai brown, akwai blue, sannan yellow, haka kalarsu yake, suna da matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ƴan kanana da su.

Cikin takun jarumta Hoorain ya shigo cikin wajen. Tun daga bakin kofar lambun ta tsare shi da waɗan nan kyawawan fararen hazel eyes ɗin nata tana kare mashi kallo yadda yake taka ƙasa cikin zafin nama, yana shirye cikin kayan yakinsa, hannunsa na rike da wani ɗan ganye kamar flower yana ɗan murzawa. Ga wata shegiyar sharɓeɓiyar takobi a ƙugunsa.

A kusa da ita ya zo ya tsaya tare da ɗan sirinar da kai ya furta.
"Sannu da hutawa ranki ya daɗe". Cikin harshen larabci ya yi maganar.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan saki ƙayatattcen murmushi mai kara fito da tsantsar kyanta tare da faɗin.
"Waye ya gaya maka ina nan Hoorain?".

Ƙara yin kasa da kansa kaɗan ya yi kafin ya bata amsa da cewa. "Abbie ne ya faɗa mun".

Idan ba ka kasa kunne sosai ba ba zaka taɓa jin me Hoorain yake faɗa ba idan yana magana, in a low voice sosai yake magana ɗan tahaliƙin nan, kamar baya son motsa laɓɓansa.

Da yake ita auta ta saba da shi sosai, dan tun tana karama take tare da shi, sai ta saba da maganar nasa, ko yaya zai yi magana tana iya gane me ya faɗa kuma tana jinsa, ita tama saba da jin magana ƙasa ƙasa sosai ai, ga Yah Jaish da Yah Jawad ma, wannan ba shi bane farau.

"Kai Abbie ya cika sa ido, yaushe wai ya ganni na fito har ya gaya maka".
Ta faɗa tana turo baki.

Bai amsa mata ba, dan bai san me zai ce maya ba, shi ba wani iya surutu ya yi ba, idan ka gansa yana magana ma to ka kan yaki ne da sauransu, bayan haka baya wata magana, ko da mahaifinsa commander ZAFAR wato wanda ya kira da Abbie yanzu basa hira, ko dare ne basa wani hira a tsakaninsu, dukkansu sarakan shiru shiru ne, kuma a tare suke kwana, basu taɓa rabuwa, suna manne da juna, amma ba zaki taɓa jin suna wani hira mai tsawo ba, daga tambaya sai amsa kawai ne a tsakaninsu.

"Hoorain kai kullum idan muka haɗu sai na ce maka ka zauna ne?".
Ta faɗa tana mayar da kallonta izuwa kan Gimbiya Chuchu da ta shigo cikin lambun a yanzu, kafa ya ɗan sami sauki, sai wani turɓune fuska take yi kamar wadda aka yi wa dole ta zo wajen, tana sanye da kaya irin na jikin Autar, sai dai ita ta ɗaura kyakkyawar alkyabbarta a saman kayan, ita kuma auta bata ɗaura komai ba, sai ɗan ƙaramin lallausan hula da ta sanya a kanta ta rufe arab hairnta.

Ganin bai amsa mata bane yasa ta sake ce mashi. "Hoorain ka zauna mana".

Cikin girmamawa ya karɓi umarnin nata tare da zama a saman ɗaya daga cikin kujerun da suke a wajen in da take zaune ita ma kenan, wasu irin chairs ne masu bala'in kyau a wajen, a baya idan ta ce mashi ya zauna sai dai ya ce zai zauna a ƙasa, ita ta hana shi zama a ƙasan, ta gaya mashi da shi da su duk ɗaya ne a wajen Allah, dukkansu mutane ne halittun Ubangiji, babu wanda ya fi wani a duniya sai wanda ya fika tsoron Allah, dan haka ita idan yana son su shirya kada ya kara zama a ƙasa, ya zauna a in da take zaune ita ma, hakan yasa yanzu idan ta ce ya zauna sai ya zauna a in da ta zauna ita ma, dan kada ya ɓata mata rai.

A kusa da su Gimbiya Chuchu ta ƙariso ta zo ta zauna, sai turo baki take yi kamar wadda aka yi wa wani abin, da ace Sarina ce ta shigo wannan waje kuma ta sami Hoorain zaune a saman irin chair ɗin da auta take zaune, da rashin mutuncin da zata yi mashi kare ma ba zai shinshina ba, sai ta zagesa fes, sannan ta buga mashi warning a kan kada ya sake, kuma ya sani shi ɗin bawansu ne, a karkashinsu yake, dole a kasansu zai zauna ba wai ya jera da su ba. Amma da yake gimbiya Chuchu ce, sai bata wani damu ba, bama ta bi ta kansa ba, zama kawai ita ma ta yi.

"Aunty Chuchu meyafaru naga kina ɓata rai ne?". Cewar auta.

Kara tsuke ɗan bakin nan ta yi kafin ta ce. "Ni da Yah Jawad ne mana, na je wajen daddy yanzu dan na roke shi zan je Dubai, shi ne Yah Jawad wai na tafi daga nan babu in da zan je, kamar shi na je tambaya".

"Yauwa kin ma tunaninmun bari na je wajen Yan Jaish ya gaya mun ya gama tunanin da zai yi, nima dai ina son zuwa Dubai ɗin ne ai"
Ta kai karshen maganar tare da yunƙurawa ta miƙe.

"Jirani mu fita tare, daga nan na wuce wajen Akka, Allah zan je na gaya mata ta sa daddy ya barni na je".

(Chuchu dai bata daddara ba zata sake kai karan Yah Jawad wajen Akka, da alama ta manta punishment ɗin ne😅 mu dai namu ido)

A tare suka miƙe. "Hoorain zan je wajen Yah Jaish, zaka jirani a nan ne ko zaka tafi?".
Ta faɗa tana kallonsa.

Ƙasa ya yi da kansa kafin ya amsa mata da cewa. "Yadda kika ce ranki ya daɗe".

"Auta sunana ba ranki ya daɗe ba, ko kace mun Zunaira". Ta faɗa a ɗan ƙule.

"Ai babu wanda zai kiraki da Zunaira sai mara kunya". Cewar Aunty MieMie da ta shigo cikin lambun a yanzu.

A hanzarce suka kai kallonsu a kanta, tana shirye cikin kayan masu bala'in kyau da tsada, ga wani dankareran alkyabbarta a sama, daga wuya zuwa hannunta dukka gwala-gwalai ne masu tsada ta kawata kanta da su, ga wani haɗaɗɗen ɗan kunnen hancinta na gold shi ma da ta sanya ɗan karami, sai kyalli yake yi, hakan ba ƙaramin kyau ya kara mata ba, cover irin na hamshaƙan matan sarakuna ne a kafafunta launin golden color, haɗuwa iya haɗuwa, jinin larabawa.

Da sauri auta ta taho ta faɗa jikinta tana sakin murmushi, ita ma Chuchu a hanzarce ta ƙarisa wajenta tana faɗin. "Aunty MieMie ina kika je two days?".

Rungume auta ta yi tare da sanya hannu tana shafa kan Gimbiya Chuchu ta basu amsa da. "Na je na halakci taron makarantarsu Omar da aka gudanar ne na kammala secondary school ɗinsu, yau na dawo".

"Shi ne Aunty MieMie baki tafi da mu ba?". Cewar Chuchu.

"Ban san kuna son zuwa ba ai, nima na wakilci daddy ne, saboda ba zai samu zuwa ba, akwai abubuwa da suka sha mashi kai sosai, uncle Abbas ma bashi da lokaci shi ne na wakilcesu duk da su uncle Rahab sun je".

Gimbiya Zunaira zata yi magana wata kuyanga da ta shigo cikin lambun a yanzu ta katsesu da cewa. "Allah ya kara sawon kwana ranki ya daɗe, Momma tana kiranki, wai ki je parlourn mai martaba ki sameta".

Har suna haɗa baki wajen tambayar waye ake kira? Dan ranki ya daɗe ta ce, kuma dukkansu haka ake ce masu.

"Princess Aunty MieMie ke ake kira".
Kuyangar ta basu amsa.

Shi dai Hoorain yana zaune yana binsu da kallo, sai dai ba kowa zai iya gane cewa yana binsu da kallon ba, baza ma kataɓa yin tunanin yana kallonsu ba.

Raba jikinta dana auta ta yi tare da riƙo hannunta tana faɗin su je su ji me ake kiransu. Ta yi maganar tare da riƙo hannun Chuchu da ɗayan hannunta.

Kai tsaye part ɗin King suka nufa, suka bar Hoorain a zaune a wajen bawan Allah.

Sun sha madarar mamaki na ganin gabaɗaya family a wajen, harda su Sarina, ga Yah Jaish da Yah Jawad ma nan, dukkansu manyan suna zaune a saman tsala tsalar sofas dake a cikin parlourn, su Sarina kuwa suna zaune a saman Dubai carpet dake a tsakiyar sofas ɗin, ga twins Obaid and Omaid a kusa da Gimbiya Fanan.

Cikin mutuntawa Aunty MieMie ta yi sallama tare da wucewa ta zauna a saman sofa mai zaman mutun biyu da yake a kusa da King, tare da zaunar da auta a gafenta kafin ta ɗagawa su Momma gaisuwa.

Kowacce tana dake a cikin alkyabbarta, kowacce kuma tana zaune a saman nata sofar na daban, Mama ta wani tsare gida kamar hakan ce zai sa su ji tsoronta, har da Mammie Yah Jawad a wajen, kowa yana cikin shiga ta alfarma.

Gimbiya Chuchu kuma kusa da King ta zo ta zauna a saman carpet ɗin, ta kwantar da kanta a saman laps ɗin King ɗin. Tana turo baki kamar anyi mata wani abin, sai dai rashin sa'arta na yanzu yasa ta zauna a in da suke fuskarta juna ita da Yah Jawad, da zarar ta ɗago kai shi zata fara kallah, shi ma kuma haka, sam bata lura da hakan ba har sai da ta ɗan ɗago da kanta da nufin ta kalli su waye da suwaye ne ma a cikin parlourn, tana ɗago kai kawai karaf suka haɗa idanu da shi, a dai'dai lokacin shi ma ya ɗago idanu dan ya saci kallonta, dan shigarta ta yi mashi kyau.

Cikin sauri ta yi ƙasa da nata idanun ta fara ƙoƙarin matsawa daga saitinsa ko da kaɗan ne.
Shi ma kawar da nasa kallon ya yi izuwa kan King, ga mamakinsa sai ya ga King ɗin ma shi yake kallon, abin gwanin ban dariya. Duk sai ya ji ya tsargu kuma, sai yake ganin kamar kallon tuhuma King yake yi mashi, alhalin kuma ba haka bane, shi ma King ɗin ya ɗago ido ne kawai sai kallonsa ya sauƙa a kansa, ba wai haka kawai ya kalle shi ba.

Kamar dai wani mara gaskiya sai ya yi saurin kawai da kallonsa daga kan King ɗin yana jin gabaɗaya a takure yake, izuwa yanzu shi da kansa ya fahimci ba iya burgesa kawai Chuchu take yi ba, sama da hakan ne, akwai dai abin da yake ji dangane da ita.

Shi kam Jaish da tun ɗazun yake aikin latsa waya bai ma san me ake ciki ba.

Twins kuwa sai wani ƙus ƙus suke yi ƙasa ƙasa, wani lokaci su yi ƴar kurma kurma kamar wasu munafukai.

Gyaran murya King ya yi tare da fara yin magana a nutse. "Nataraku a nan ne kan abubuwa biyu zuwa uku. Na farko shi ne akan abin da ya faru da Sarina, abin sam bai yi daɗin ji ba, ga shi har ya saka mun ɗan uwana (uncle Abbas) ciwon kai, sam ban ji daɗin hakan ba, shiyasa na taraku domin na ja maku kunne a kan ban yarda wani ya sake zuwa wa wani daga cikinku da zancen yana son ƴaƴana har kuma ku yi mashi jagora zuwa cikin gida na wajen ƴaƴan nawa ba, ban yarda da hakan ba! Ku kyaleni idan sun kai munzalin aure ni zan zaɓa masu maza da kaina, koma ya kuke da mutun bana da buƙatar ku kawo mun shi cikin gidan nan da sunan wai yana son ƴa ta, dukka dukka ma nawa Sarinar take da Abbas zai takura kansa da zai ta yi aure? To ni bana da buƙatar irin hakan ta sake faruwa, ku kyale mun ƴaƴana su huta, sai dai ni ina tunanin wannan yaro Yusuf ba lafiya yake ba, amma dai koma menene Zafar zai yi masu abin da ya dace, wannan shi ne maganata ta farko. Ta biyu kuma Obaid and Omaid zasu koma Dubai gobe, duk da ba'a buɗe makarantarsu ba ko ma nace basu wuci sati ɗaya da yin hutu ba, amma za su koma bisa son hakan da mahaifiyarsu take yi, ta ce tana son su koma yafi mata, so zasu koma. Sai magana ta uku, Omar zai dawo nan da kwana uku, Mommynku ta buƙaci da zata shirya mashi gagarumin walima na murnar dawowarsa, na kuma bata izinin yin hakan, ina gaya maku ne domin na fita hakkin kowa".

Ɗan dagatawa ya yi da maganar yana sauke numfashi tare da bin fuskokin matan nasa da kallo.

Shi dai Jaish har ga Allah bai ga wani abin da zai sa a kirashi cikin wannan al'amari ba, shi ba aboki yake da shi bama bare ace ko abokinsa zai ce yana son kanne nasa har ya yi mashi jagora zuwa gidan, to shi ko da ace yana da aboki ma ya isa ya yi mashi jagora zuwa neman aure ne? Wlh bai ga wanda ya isa ya sanya shi ya yi mashi jagora zuwa wajen mace ba, a ganinsa ba'a haifi mutun ba.

"Akwai wani mai abin faɗa ne?".
King ya katse su da wannan tambayar.

Siririn tsaki Mama ta ja kafin ta ce. "Ranka ya daɗe ni ina son a gaya mun menene banbancin su Chuchu da su Obaid da duk wanda Rahilarh zata haifa sai ta ce bata son ya zauna da ƴan uwansa a nan sai dai a Dubai? Menene a gidan da nata ƴaƴan ba zasu zauna ba sai namu? Ko mu namu ƴaƴan ba mutane bane? Ko dai nata ƴaƴan sun fi namu daraja ne?".
Da iya gaskiyarta ta yi maganar.

Ita kuwa Momma ba wani dalili bane yasa ta buƙaci su Obaid su koma Dubai face wannan matsala dai da take fuskanta a cikin gidan, kwana biyun nan tana yawan mafarkinsu a cikin wani mawuyacin hali ne yasa ta buƙaci da su koma kawai ko hankalinta zai kwanta.

(Ni kuwa na ce bama dole ki gansu a cikin mawuyacin hali ba, yara basu ji, sai dai su yi ta kwasa wa kansu alhakin mutane suna biyewa Sarina suna kwasan hakkin waɗan da basu ji ba basu gani ba, yara kamar an canza maki su lokacin da kika haifesu🤔 ai in a kansu ne ma fin haka zaki gani baiwar Allah😅)

Da yake Momma jinin Modarawa ce ba'a masu su kyale, sai ta ce da Mama ɗin. "To ai naga duk tushe ɗaya ne ko? Kina iya mayar da su Chuchu ɗin Dubai ɗin kema idan kina da buƙata, saboda suma ai kakaninsu ne a can ɗin, babu wanda ya hanaki yin haka, dan haka sai ki cire idanunki a kan rayuwata, haka nake son ƴaƴana su kasance, tun da ba ke kika haifa mun su ba kina iya jan baki ki yi mun shiru".

Akka dake zaune saman nata sofar ta wani dake tare da ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ne ta karɓi zancen da cewa. "Idan ma baku yi haka ba ai sai na ce Zuhair ba mata ya aura ba".

Karo na farko da Yah Jawad ya ji dariya ta so ta kubce mashi, wannan tsohuwa Akka akwai iya tada bom, a maimakon ta shiga cikin lamarin ta sasanta, amma kun ji wai idan basu yi hakan bama ba mata bane.

Shi dai Jaish haushi har wuya yake ji ta iso mashi, dan shi sam baya son zama a taron mata, yasan fin haka ma zasu aikata, su yi abinsu su bar mutun da ƙuncin zuciya ba abin da ya damesu, ai mata duniya ne, kome za'ayi masu kishin nan dai yana nan, ba zai taɓa tafiya ba, kai ko cire zuciyar mace ka yi ka wanketa fes da ruwan zam zam ka sake dawo mata da shi a kan kishi gobe sai kaga wani bakin halin........😅

"Daddy zamu iya tafiya?". Cewar Yah Jawad, dan ya lura abin na mata ne take shirin motsawa, wato kishi, dan haka gara su kama kansu kada a kashesu da kuncin zuciya.

Shiru King bai basu amsa ba, ya dai zuba masu idanu yana ganin su, dama haka yake yi, sai sun yi sun gaji yaje saka baki.

"Bayan kin asirce shi ya zama ƴaƴanki kawai yake gani da daraja ta ina muke da ƴan cin zaɓarwa ƴaƴanmu in da muke son su yi rayuwa? Ai ke kaɗai ce mai wannan dama, zalunci dai komai daren daɗewa yana da karshe". Cewar Mama.

Omaid ne ya kalli Mama ɗin cikin ɓacin rai ya amsa mata da. "Mama ko Momma ta zaɓa mata in da zamu yi karatu ko bata zaɓa mana ba mu dama bamu da ra'ayin yin rayuwa a cikin kingdom ɗin nan, wajen su mai ran karfe su Uncle Rahab and uncle Abu
End Ads