x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 47 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 138001 words
  • 141000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 423

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
kanta, jiki na kerma ta fara gyaɗa mata kai alamar ta yarda ta amince tun ma bata ji wani irin sharaɗi bane, ita dai burinta ma kawai ta bar wannan gida, ko bara zata yi a bakin titi in dai zata bar wannan gida to zata amince da koma wani irin sharaɗi za'a sanya mata, bata damu da sai wannan mata ta bata dukka wannan daula da ta lissafa mata ba, ita dai ta fita daga gidan nan kawai.

"Good girl, wani aiki zaki yi mun, ba aiki bane mai wahala, kuma ba jimawa zaki yi kina yin aikin ba, da zarar kin yi mun shi dai'dai shikenan angama zaki sami duk waɗan nan abubuwa dana kirga, kina amincewa ko yanzu ne zaki bar wannan gida ba tare da kin kara one mins ba, amincewarki ne kawai yanzu zai fitar dake a yau ɗin nan". With full confidence matar ta yi maganar.

Shiru Leesharh ta ɗan yi, kamar zata ce wani abin, sai kuma bata yi wani tunani ba ba kuma ta ji wani irin aiki bane, idanunta ya rufe da son fita daga AAJ, hakan yasa ta gyaɗa kai alamar ta amince zata yi wannan aiki da bata san menene bane.

"Kin amince zaki yi mun wannan aiki?". Matar ta tambaya muryarta cike tab da tsantsar farinciki mai nuna alamun ta jima bata shiga farinciki irin haka ba, ga tsantsar ƙaguwa a voice ɗin nata.

Ƙara gyaɗa mata kai Leesharh ta yi alamar yes ta yarda ta amin zata yi wannan aiki da bata ji ko menene ba.

"Kin san wani irin aiki zaki yi mun ne? Bashi da wata wahala fa".
Matar ta sake faɗa cike da murna da farinciki.

Girgiza kai Leesharh ta yi alamar bata san wani aiki bane.

"Ba wani aiki mai wahala bane, so nake.............

Ko masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu, amma ku wani aiki kuke ganin wannan mata zata sanya Leesharh da har ta yi mata alƙawarin maƙudan dunbin dukiya har haka?🤔 Anya wannan mata akwai alkhari a tattare da ita kuwa?🤔 Ga shi dai ta rufe ko'ina nata ba'a iya ganin wacece!🤔 To dai shikenan su kuma nasu wasan yanzu zai fara kenan, 🥱 na yi ta nan.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍



🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)






🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 1/8/2024.....✍️📚🌹




For information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








E____________26🔥


🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼

"Ba wani aiki mai wahala bane, so nake kawai ki shiga jikin wani, ina son ki shiga jikinsa ta yadda duk wani abin da yake yi zan samu labari, na sha wahala sosai kafin na samu yarinya irinki wadda take da duk wasu qualities da nake da buƙata wanda kuma nake ganin zai iya jefa Ramish a cikin tarkonmu".

Ɗan dakatawa da yin magana ta yi cike da fargabar kada Leesharh ɗin ta ce ba zata iya yin wannan aiki ba, ta kafeta da idanu ta cikin glass ɗinta tana karewa fuskarta kallo tare da karantar yanayin ta, bata san ya zata yi ba idan Leesharh ɗin ta ce ba zata iya yin wannan aiki ba.

Cike da kirsa tare da ƙoƙarin yin amfani da ƙarancin shekarun na Leesharh ɗin ta cigaba da yin magana kamar haka.

"Na san da cewa baki jin daɗin zaman wannan gida, na san da cewa kina cikin kunci da takura, na san da cewa kina cikin wahala, na san da cewa baki da burin da ya wuce ki fita daga cikin wannan gida, to dukka wannan zai faru ne kawai idan kika amince da tayi na, bafa cutar da kowa zaki yi ba"

Sake dakatawa da yin maganar ta yi tana jan numfashi tare da kara kurawa face ɗin Leesharh idanu.

Ni kuwa nace babu rami me ya kawo maganar rami? Me ya kawo zance ba cutar da kowa zata yi ba?......🤔 Anya wannan mata ta kulla gaskiya kuwa? Anya ba so take ta kai Leesharh ta barota ba? To wai waye ma shi Ramish ɗin? Kuma meyasa take son a yi mata leƙen asiri a kansa? Me suke nema daga garesa?.

"Leesharh zaki samu jin daɗin rayuwa sosai da sosai, zaki samu farinciki fiye da tunaninki, zaki sami kuɗi ki taimaki duk wanda kike so, just kawai amsa me with your full confidence that zaki iya, nasan cewa zaki iya shiyasa na zo wajenki, ban zo nan ba sai da na binciki tarihin rayuwarki, and ke ƙaramar yarinya ce, babu wanda zai yi tunanin ga abin da kika je yi a gidan, taimako fa zaki yi, wasu ne suke son cutar da shi mu kuma zamu bashi kariya ta hanyar sanin duk wani motsinsa, ta hakance kawai zamu taimakesa, kinga kema kin taimaka mashi kenan".

Cike da kwarewa a iya juyar da tunanin mutun ta yi maganar, sai dai fa tana magana ne tana fargabar amsar da Leesharh zata bata, domin ta gama saka duk wani hope ɗinta tun kafin ta zo a kan cewa lallai Leesharh zata yi mata abin da take so, amfani zata yi da karantar shekarun Leesharh, dan tasan ƙaramar yarinya kamar Leesharh babu wanda zai yi tunanin leƙen asiri ta je yi, da alama wutar ɗaukar fansa ne yake ruruwa a cikin zuciyarta, shi ne kuma take son ta yi amfani da Leesharh domin cikar burinta. Hmmmm akwai babban yaki da cakwakiya kuwa a gaba, ga shi ko face nata bata bari an sani ba, wato idan ma an kama Leesharh ita kaɗai ayi mata duk hukuncin da za'ayi mata, wannan mata bata kullah gaskiya ba, akwai babban wasa a wannan waje.

"Leesharh say something now, shin kin amince?".

Shiru ta ɗan yi kafin ta ɗago da idanunta da suke cike taf da kwallah, muryarta na rawa, da alamar tsoro sosai a saman face ɗinta, hannayenta dukka kerma suke yi, hakan zai kara tabbatar maka da tana tsorace. Magana ta fara yi cikin rawar murya ga shi dama ba fita sosai voice ɗin nata yake yi ba, sai abin ya kara kwaɓewa.

"Ni Aunty duk wata dukiya bata dameni ba, ni bana da buƙatar komai a duniyar nan da ya wuce na je naga kabarin mamata daga nan na koma ƙasarmu, ƙasarmu nake da burin na koma naje na nemo ƴan uwana da kuma mahaifina, please Aunty ki taimaka mun na koma ƙasarmu zan yi duk abin da kika ce".

Wani irin nannauyar ajiyar zuciya wannan mata ta sauke da jin amsar da Leesharh ɗin ta bata, ranta ya yi haske da jin cewa Leesharh zata iya yin komai domin ta bar wannan gida ta koma kasarsu, har wani walwala ne ya bayyana a face nata, da yake tana sanye da nikaf hakan yasa ba za'a gane ba, hankalinta ya kwanta yanzu, ta samu damar da zata cinma burinta da abin da take hari a nata tunanin kenan, ko da yake bata zo wannan gidan yarin wajen Leesharh ba sai da ta shirya ta kuma san labarin Leesharh ta san da cewa zata iya aikata komai idan aka bita ta yadda ya dace, idan aka yi wasa da tunaninta, dan yarinya ce mai jajircewa a kan burinta da aikinta.

"Good Leesharh, haka ake son mutun mai zuciyar jajircewa juriya da hazaƙa, naji matuƙar daɗi da ya kasance zaki yi komai domin mahaifinki, kada ki damu kina gama aiki zan mayar dake ƙasarku ba tare da ɓata lokaci ba, ai uba ya wuce wasa Leesharh, ke ɗin yar baiwa ce Allah ya yi maki albarka".

Ɗan dakatawa da kalaman yaudarar tata ta yi tana kara kallon face ɗin Leesharhr, dan kowa yasan dai waɗan nan kalaman nata na yaudara ne, so take yi ta yi amfani da ƙarantar shekarun Leesharhr haƙanta ya cinma ruwa, daga gani bata ƙullo gaskiya ba.

Da Amin kawai Leesharh ta amsa mata ba tare da ta ɗago da kallonta ba, tunanin a ina zata yi wannan aikin kawai take yi.

"Kina jin yadda aikin zai kasance, zaki je gidan ne a matsayin ƴar aikinsu, suna da masu aiki da a kallah zasu kai mutun 50, amma dukka wannan ba damuwa bane, ni nasan ta yadda zan shigar dake gidan a matsayin mai yi masu aiki, zan saya maki sabuwar waya, ba kin iya amfani da ita ba?".

Ta dakata tana jiran amsa.

Girgiza mata kai Leesharh ta yi alamar a'a bata iya amfani da wayar ba.

"Okey wannan dukka ba matsala bane, ni zan sanya a koya maki komai, dama ba'a haka zaki je masu ba, dan su masu yi masu aiki ma sai wanda yake da degree or diploma, ba kananan kai bane suke yi masu aiki, sai na sanya an koya maki abubuwa na a kallah wata guda, kafin nan na shirya ta yadda zaki yi ki shiga gidan, babu ruwanki da kowa a cikin gidan, ko sauran ma'aikatan gidan ban yarda ki rinƙa yi masu magana ba, kada ki yarda ki sake da kowa, muna da ma'aikata a gidan da zasu kula da ke, dukkansu manyan mutane ne da ba zasu iya shiga jikin Ramish ba, shiyasa na zaɓoki, Ramish kawai zaki saka mun ido a kansa, ban ce ki kira kowa da wayar da zan baki ba, haka zalika ban ce ki bawa kowa number wayar ba, nima kuma ba zan kiraki ba, idan ina da buƙatar yin magana dake ni nasan ta in da samu haɗu mu gana, wayar da zan baki zan baki ita ce kawai dan abu biyu, na farko domin akwai abin da zan sanya a cikin wayar dan ya tayaki aikin da zaki yi domin mu kammala da wuri, na biyu kuma wani lokaci ki rinƙa ɗauka mun Ramish ɗin a video idan suna irin tattaunawa mai mahimmancin nan, kuma da zarar kin turo mun video ki goge shi a wayar, ko da yake ma time to time zan rinƙa canza maki wayar, wannan ba abin damuwa bane na san ta yadda zan shirya komai".

Ɗan dagatawa da maganar ta yi tana jiran ta ji me Leesharh ɗin zata ce.

"Aunty to ni da nake matsayin ƴar aiki ya za'ayi na iya sanin lokacin da suke tattaunawa mai mahimmancin? Kuma ai idan zasu yi tattaunawa ba'a ko'ina zasu yi ba ko? In dai haka ne ya za'ayi na san in da zasu yi tattaunawar?".

Ɗan ƙaramin tsaki ta ja kafin ta cigaba da cewa. "Aikin da zan samo maki ba kamar sauran ƴan aikin gidan bane, an gaya maki a banza na zaɓeki ne? Akwai dalilan da yasa na zaɓeki wadda ban gaya maki ba, kina da kyau, kina da diri da sai an tara mata 100 ba'a sami goma masu irin dirinki ba, da wannan zamu yi amfani mu sanya shi ya saki jiki da ke ko kuma ku sami kusanci sosai har haƙanmu ya cinma ruwa".

Shiru Leesharh ta ɗanyi, abinku da kananan shekaru, sai bata kawo komai a ranta ba, bata ma san waye zata yi wa wannan shisshigin da leƙen asirin ba, ita dai tun da ance mata taimako zata yi ai shikenan, bata san me za'ayi mashi da ake buƙatar sanin duk wani halin da yake a ciki ba, ita dai burinta na son komawa ƙasarsu ya rufe mata idanu da har take jin cewa tabbas zata iya yin komai a kan hakan.... Babbar magana, in kuwa haka ne akwai kura ba kaɗan ba.

"Tunanin me kike yi Leesharh?".
Ta faɗa a ɗan tsorace, tana tsoron kada Leesharh ta ce ba zata iya ba ko ta karaya.

Girgiza mata kai ta yi tana faɗin. "Bana tunanin komai".

Kada ku mance duk maganar da Leesharh zata yi sai wannan mata ta ɗan ɗauki lokaci mai ɗan tsawo tana jujjuya maganganun a cikin ranta, dan ta fahimci abin da Leesharh ɗin ta faɗa da kyau da kyau, na gaya maku maganar tata ne baya fita sosai, hakan yasa ba'a gane me take cewa sosai.

"Kada ki yi tunanin komai my sister, ba wani abin da zai faru In Sha Allah, zaki gama wannan aiki lafiya ki kuma koma ƙasarku wajen babanki da ɗinbi dukiya sosai lafiya lou, ba zan bari wani abin ya sameki ba, na yi maki alkawarin, ki yarda da ni taimakon zaki yi".

"Na yarda dake Aunty, na kuma yarda da duk abin da kika faɗa, sannan na yarda da zan yi maki wannan aiki".

Wani irin cool ajiyar zuciya ta sauke jin kalaman yarinyar, sai kuma ta ɗan ji wani irin yar a ranta, ba komai bane yasa ta ji hakan face tasan da cewa in dai asirin Leesharh na leken asiri ya tuno to ba makawa kasheta zasu yi har lahira, hakan yasa ta ɗan ji wani iri a cikin ranta, amma da yake abin da suke buƙata kuma yake a gabansu suna ganin cewa yafi ran Leesharh ɗin mahimmanci, sai ta saki wani irin shu'umin murmushi tare da cewa.

"Tom shikenan jeki ɗakinku ki shirya ki kuma yi bankwana da kawayenki anjuma zan dawo na ɗaukeki mu tafi".
Yadda ta yi maganar with her full confidence sai ka rantse da Allah ba'a gidan yari Leesharh take ba, wai zata dawo ta ɗauketa kamar ba ita aka yankewa hukuncin kisa ba, hakan na nufin koma wacece wannan mata ba kananan mutane bane, dole manyan kai ne suke ƙoƙarin tura Leesharh ga halaka.

Miƙewa Leesharh ta yi jiki ba kwari, dan yunwa take ji sosai, da kyar take iya jan kafafun nata ta nufi kofar da zai mai data izuwa ɗakinsu. Da idanu matar ta bita da shi tana yi mata wani irin kallo mai wuyar fassaruwa.

Har ta kai tsakiyar office ɗin, sai kuma ta juyo tare da cewa. "Aunty a gidan waye zan yi aikin?".

Wani shu'umin murmushi ta ɗan saki kafin ta ce. "A gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen zaki yi aiki".

Jinjina mata kai kawai ta yi da yake ita ba ƴar ƙasar ba ce, bata san wanenen Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen. Wucewa ta yi ta nufi waje ranta fes zata fita daga wannan gida a yau.

Nannauyar ajiyar zuciya wannan mata ta sauke kafin ta ce. "Lokacin ka ya fara daga yanzu Ramish, time ɗimu ya yi".
Ta yi furucin nata a fili, cike da farinciki tare da full confidence sosai ta yi furucin nata.

Ita kuwa Leesharh sai murna take yi ta koma room ɗinsu. A yadda ta bar Jasrah haka ta dawo ta sameta, ta buga uban takumi tana tunanin ina aka kai Leesharh.

Tana ganinta ta yi maza ta miƙe tsaye, nan take farinciki ya bayyana a samar face ɗin tata, har wani ƴar murmushi ta sakar mata kafin ta ce.
"Alhdulillah nagodewa Allah da yasa ba ɗaki suka sauya maki suka rabani dake ba.

A hanzarce Leesharh ta ƙariso ta zo ta rungumeta tana murnar lokacin fitarta daga gidan ya yi.

"Leesharh is there any good news? Naga like you're so happy like ba yadda kika fita ba, ke matsalar ma baki yin dariya bare mutun ya iya fahimtar kina cikin farinciki or not, amma dai a haka nake son kayata, baki dariya ko kina dariya dukka abu ɗaya na sani shi ne i really like you".

Wani irin faɗuwar gaba Leesharh ta ji na jin kalaman Jasrah, ba yau ta fara jin kalaman da suka fi haka daɗi da kyau daga gareta ba, amma na yau ɗin sai ta ji sun ɗaga mata hankali kuma sun jefata cikin damuwa, sai yanzu ta tuna cewa zasu rabu da Jasrah kenan? Shikenan ita zata fita ta bar Jasrah? Kuma nan da one year kashe Jasrah kenan za'ayi? Ba zasu sake haɗuwa ba? Sun rabu kenan har abada?. Ya ilahi ya lillilahi, a duniya duka bayan iyayenta babu wanda ya taɓa nuna mata tsantsar kauna tsakani da Allah kamar yadda ƴar tahaliƙan nan Jasrah ta nuna mata, bata taɓa zama da yarinyar kirki biyun Jasrah ba, yarinya so silent, ga hakuri da tawakkali, ilimin addini da yin aiki da shi, nutsatsiya, ta nuna mata kauna kamar ƴar uwarta na jini, wani lokaci har a baki take bata abinci idan ta ki ci, shikenan yau alaƙarsu zata zo karshe na har abada?.

Wani irin sara mata ta ji kanta ya yi, nan take murnarta ya rikiɗe izuwa bakin ciki, damuwar da bata taɓa shiga makancinsa bane ya lulluɓeta, nan take ta ji wani irin karayar zuciya ya dira mata a ranta, idanuwanta ne suka yi wani irin ciwowa da kwallah tab, nan take kuma idanun nata suka yi jajir kamar wuta.

Sai tambayarta Jasrah take yi akwai labari ne suna a rungumi da juna, amma ina Leesharh ta ƙasa yin magana, sai ma wani irin ciwo da nauyi da kanta ya yi mata, ji take yi kamar kan nata zai faɗi ƙasa.

Jin alamar saukar hawaye a saman shoulder ɗinta ne yasa Jasrah ta yi saurin raba jikinsu domin taga face ɗin Leesharh ɗin da kyau.

Su Sarah dai sai binsu da kallon walaƙanci suke yi, sun tsani Leesharh a rayuwarsu yaran nan, babu abin da ta yi masu, kawai bakar zuciya ce irin tasu.

"Subhanallah Leesharh what's happening? This tears is for what?".
A ruɗe ta yi tambayar tata, tana magana tana zaro idanu, alamar tana ɗan tsorace, dan ita ma bata jin zata iya rabuwa da Leesharh a yanzu, duk da cewa tasan lokaci ƙalilan ne ya rage mata a duniyar ma bakiɗaya, amma bata sanya a ranta zata rabu da Leesharh a yanzu ba, ta fi yin tunanin kasheta da za'ayi ne kawai zai rabasu.

Zama a gefen bed ɗinta Leesharh ta yi tare da buga uban tagumi, kan kace me har hawaye
End Ads