Kai kai kai, Guyson fa akwai madarar kyau kam, kamar Gimbiya Zunaira yake, sai ma daya haɗe rannan, sai kyan ta kara bayyana so masha Allah, kamar ka yi ta kallonsa ba gajiyawa, da ya ɗaure fuska sai ga shin gerarsa suka haɗe waje guda, hakan ba ƙaramin kara tsatso mashi kyansa ya yi ba, waɗan nan fararen idanun nasa idan ya zaro maka su sai ka gudu saboda girma ga kyau.
Cikin girmamawa wannan matashi ya amsa mashi da babu abin da ya yi mata, haka ya iskota tana kuka shi ne yake rarrashinta. Da alama wannan matashi yasan Guyson sosai duba da yadda ya bashi amsa cikin girmamawa.
"Leesharh meyasameki kike kuka?". Ya yi tambayar yana maido da kallonsa a kanta.
Tana kan goge hawayen da suka ki dagatawa da zuba, ta ruɗe ta rasa wani amsa zata bashi. Shin ta ce mashi kewan babanta ne yasa take kuka ko yaya? Amma idan ta ce mashi kewar babanta ne zai iya sanyawa ya ce a kaita wajen baban nata ta gansa sai a dawo da ita, to a ina zata ga baban nata kenan? Ta sake jefawa kanta tambaya, ta rasa me yakamata ta ce mashi, tasan ƙaramin aikinsa ne duk abin da ta ce ga shi shi ya sakata kuka shi kuma ya ce a nemo wannan abin, ya zata yi kenan?.
Can wata wani dubara ta faɗo mata, cikin hanzari ta amsa mashi da. "Wani kwaro ne ya shiga mun cikin idona, shi ne ya sanya ni yin kuka".
Murya a ɗan kausashe ya ce. "Ta ya aka yi aka samu kwaro a cikin hall ɗin nan? Dole masu gyaran hall ɗin nan su sha punishment, domin kuwa basu yi aikinsu yadda ya dace ba ga shi suna cutar da mutane". Ya kai karshen maganar tare da ciro handkerchief daga aljihunsa ya miƙa mata a kan ta goge hawayen nata, sannan ya yi mata sannu kafin yasa kai ya wuce ya barta tsaye a wajen, ya sha alwashin in aka gama taro dukka masu aikin gyaran hall ɗin sai sun sha punishment, a kan me basu yi aikinsu da kyau ba har suka bar kwari suka iya shigowa cikin wajen suna cutar da bayin Allah?. Da alama Guyson yasan darajan ɗan Adam sosai da sosai.
Ita kuwa tsoro ne ya kamata na ganin cewa zata ɗauki alhakin masu gyaran wajen, bayin Allah basu san komai ba zasu sha punishment a banza, ta shiga damuwa sosai a kan hakan, danasanin yin wannan karya da ta yi ta fara yi, tana yi tana goge hawayen nata da handkerchief ɗin da ya bata, tana kuma shaƙar daddaɗar kamshin dake jikin handkee ɗin.
Katseta da yi mata sannu wannan matashi na bayan nata ya yi. A ɗan razane ta juyo da kallonta a kansa, da alama ta manta da shi yana wajen, hakan ne ya razanata.
Sannu ya kara yi mata yana wani binta da kallo kamar wani tsohon maye. Da yauwa kawai ta amsa mashi, cike da tsoro tasa kai zata bar wajen. Ƙoƙarin dakatar da ita ya yi, da alama yana da wani plan a kanta. Kin tsayawa ta yi domin idan baku manta ba ita Leesharh tana aiki ne bisa umarnin masu nikaf, sai abin da suka ce take yi, dan haka kula maza baya daga cikin tsarin aikinta, hakan yasa ta yi saurin barin wajen.
A hanzarce ta fito daga hall ɗin, tana tafiya tana waige waige kamar maras gaskiya, kirjinta sai dukan uku uku tara tara yake yi, addu'a take yi kawai Allah yasa wannan matashin kada ya biyota, sai zuba uban sauri take yi, a ƙagare take da ta isa wajen elevator ta koma sama ta je ta yi kwanciyarta a room nata dan yau dai aiki ba zai yiwu mata ba.
A garin waige waigen baya da take yi bata ankara ba sai ji ta yi ta yi karo da mutun. Har wani irin jiri ta ji tana ƙoƙarin faɗuwa saboda bata rike jikinta da kyau ba.
Da kyar ta iya kama kanta ta tsaya tare kuma da ƙoƙarin ɗaga idanu dan ta kalli da waye ta yi karo. Daddaɗar kamshin perfume ɗinsu ne ya daki kofofin hancinta. Kusan kamshin perfume ɗin irin na Ramish, hakan ne ya haifar mata da faɗuwar gaba tun bata kalli wanene bane.
Cikin tsoro ta ɗago idanunta da suke jajir har sun ɗan kunbura saboda kuka. Dai'dai lokacin da ta ɗago kai shi kuma Obaid ya yi yunƙurin kai mata mari saboda buge shi da ta yi, har ta sanya wayarsa ya faɗi a ƙasa.
Riƙesa Omaid ya yi dan yasan wlh marinsu ba shi da daɗi sam sam, idan ya mari yarinyar nan ai sai ta suma, duk wanda waɗan nan twins ɗin suka mara fa baya sha ta daɗi, sam marinsu bashi da daɗi. Hakan yasa Omaid ya riƙesa.
Ita sam bata damu da yunkurin kai mata marin da Obaid ya yi ba, ruɗani ma suka jefata, tunani take yi wai shin a gaban madubi take kallon mutun biyu maimakon ɗaya ne ko dai yaya ne? Taga sun yi muguwar kama, ka rantse da Allah mutun ɗaya ne, sun ruɗar mata da ƙwaƙwalwa...... Ni kuwa na ce ba ke kaɗai ba, yayyunsu ma ba iya rabesu suke yi ba bare ke bare, ai su kaɗai suke iya rabe kansu sai Mommarsu, ko King da yake matsayin ubansu baya iya rabesu, sai ya kira Obaid da sunan Omaid, ya kira Omaid da sunan Obaid, Allah ya yi masu halitta ne iri guda sak, ta wannan kamanceceniya da take a tsakaninsu suke amfani su ruɗar da mutane a kullum, baka isa ɗaya daga cikinsu ya yi maka laifi ka ce zaka iya gane wanda ya yi ɗin ba, wane kai, sai dai idan zaka haɗesu dukkansu biyu ka basu punishment, amma gane mai laifi a cikinsu ba abu bane mai yiwuwa.
"Who're you and what are you doing here?". Cewar Omaid ɗin, ya yi maganar kuma bai saki hannun Obaid da ya rike da kada ya mareta ba. Da farko dai sun cewa Guyson ba zasu zo gidan ba, amma daga baya suka ce zasu halarci walimar, shi ne fa Abu Abdussalam ya tura tawagar motoci aka ɗaukosu. Sun ci gayu cikin ƙananan kaya, ga wasu booth da suka sanya a kafafunsu masu kyau da tsada, already kunsan su komai masu iri ɗaya suke sanyawa, harta gyaran gashin kansu iri ɗaya suke yi.
"She looks like a criminal, ban yarda da ita ba". Cewar Obaid, ya yi maganar yana zame hannunsa daga riƙon da ɗan uwan nasa ya yi mashi.
Su suna ta maganarsu ita bata ma a tare da su, duniyar tunani ta luluƙa, ta ruɗe ta rasa gane wai mutun biyu ne a gabanta ko dai ɗaya ne a gaban mirror, sam bata jin abin da suke faɗe ma.
Na gaya maku waɗan nan twins ɗin giveted ne, ƙwaƙwalwarsu kaifi gare shi ga saurin gudun aiki, cikin lokaci ƙanƙani suke iya gane abin da babba baya ganewa, da kallo ɗaya Obaid ya yi mata ya ji ya fara zarginta, bai ma san wacece ita ko me take yi a cikin gidan ba, amma har cikin ransa ya ji tabbas wannan yarinyar maras gaskiya ce.
(Da su twin's a gidan Abu Abdussalam suke da kuwa akwai cakwakiya, dan kuwa cikin minti ɗaya zasu gano Leesharh.😅 Yara kamar wasu aljanu🤔😅)
"Yeah you're right blood, the way she's walking she's totally criminal, and see her eyes like she want to kill someone innocent". Cewar Omaid.
Tsawa Obaid ya daka mata a kan wacece ita?.
Can masu dai, ita bata ma jin me suke faɗe, hankalinta ya yi nisan kiwo. Wani irin raɗaɗin azaba da ta ji ya ziyarci dukkannin ilahirin sassan jikinta ne yasa ta dawo daga tunanin da ta afka. A wani irin mahaukacin razane ta sanya hannu ta dafe ƙuncinta in da Obaid ya sakar mata mari, ji take yi kamar ba'a duniya take ba, nan take ta fara ganin wani haske yana mamaye ko'ina a wajen, ɓangaren da ya mareta ɗin kunnenta ya daina jiyo mata sautin komai. Dama twin's basu shiga aikin special weapons and tactics bama ya marinsu yake da azaban zafi bare kuma su da suke karɓar horo kullum, ga aikin wahala, ai dama idan suka mareka sai ka ji kamshin lahira, to ita dai Leesharh ta ɗan ɗana.
Ƙoƙarin kara mata wani marin Obaid sarkin saurin hawa ya yi, dai'dai lokacin Guyson ya iso wajen, ya fito daga cikin gida wajen Yah Ramish.
"Kai Obaid me ta yi maka zaka mareta?". Guyson ya jefa masu tambaya, while shi kuma Omaid ya riƙe hannun Obaid ɗin dan kada ya kara mata wani marin, yasan idan ya barshi ya kara mata to fa sai dai a kwasheta ranga ranga bayan ta zuba kashi da fitsari a wando.
"Yah Omar who's she?". Cewar Omaid. Omaid fa da kuke ganin nan ya iya takunsa, ya fi Obaid iya tsiya, sai dai shi yana danne zuciyarsa baya saurin hawa, baya yarda ransa ta ɓaci har zuciya tasa ya fita hayyacinsa, sarai yasan me yake yi, da ƙwaƙwalwarsa yake aiki over, ya iya takunsa sanka sanka, yanzu dai kunga shi Obaid har ya arzuƙa, dan sun yi magana bata amsa masu ba har ya fusata ya mareta, shi kuwa Omaid kun ga kamar ma bai san ana yi ba, saboda tsabar iya taku da basaja.
"Ayya she's our new house girl, sabuwar maaikaciya ce fa, kuma innocent girl ce, bata da hayaniya, kawar Lil sister ce ma fa". Cewar Guyson.
Kawar da kansa Obaid ya yi tare da sauke hannunsa daga yunƙurin kara mata marin da ya yi niyar yi Omaid ya tare, cikin ɓacin rai ya ce. "Wannan ba house girl bane ba, criminal ce maras gaskiya, she looks like green snake under green grass".
Omaid zai yi magana Guyson ya riga shi da cewa. "Anyway, koma dai menene kuzo mu tafi cikin hall, wai bama kunce ba zaku zo ba? Ya aka yi kuma kuka zo?".
Guyson bawan Allah, yasan da cewa halin kannen nasa sai su, shi sam bai ɗauki zancensu da wani mahimmanci ba na kiran Leesharh da green snake under green grass da suka yi, dan yasan su fa yaran nan sam sam basu son zaman lafiya, idan basu kaunar mutun ba kalar sharrin da ba zasu yi mashi ba, dan haka sai ya ɗauki abin a zaman cewa basu kaunar Leesharh ce kawai yasa suka laƙa mata wannan suna. Bai san sun fishi gaskiya ba, su fa jami'ai ne, yau tsawon almost shekaru 8 suna a special weapons and tactics academy, a matsayin horon da suke yanzu zasu iya gane ɓarawo cikin dubbannin mutane, horo mai rai da lafiya suke samu, ba makarantace ta kananan kai ba, kun san su kuma da basira, hakan yasa makarantar take alfahari da su sosai da sosai, su ɗin su kaɗai ne tamkar ya dubu a cikin school ɗin nasu. Shi kuwa Guyson da yake karatun computer engineering ina zai gane hakan? Ai babu wannan magana, ba abin da zai gane, su kam sun san duk wasu lago na mutun maras gaskiya.
Da kyar Guyson ɗin ya iya jansu suka bar wajen, har suka bar wajen kuma Leesharh bata dawo cikin hayyacinta ba, ta maru kam ba karya, duk da take chocolate color sai da shatin yatsu biyar ɗin Obaid ya fito ruɗu ruɗu a face ɗin tata, ta ji hannun manya, wannan ma dan ba marin Omaid ta sha ba, da na shi ne ina ga suma zata yi ko mutuwa mai gabaɗaya, dan Omaid ya fi Obaid sanin gurbin mugunta, dama kunsan ko da twin's ɗin a mahaifa guda suka fito ba daban daban ba dole ɗaya yana fin ɗaya wasu abubuwa, to Omaid dai ya fi Obaid wayo, iya shege, iya taku, zafin zuciya, iya sarrafa zuciyarsa, kai da komai ma.
Ta jima sosai a wajen kafin ta fara jin kamshin dawowa cikin hayyacinta. Sai a lokacin kuma ta iya durkushewa kasa a saman gwiwowinta a wajen ta saki wani marayar kuka, wani irin zogi da azaba ne yake ratsa kashi da ɓargon jikinta, har yanzu kuma ta kasa iya tantance wai Obaid da Omaid mutun biyu ne ko dai mutun ɗaya ta gani?.
Ta ɗauki a kallah tsawon good 30 mins s wajen kafin nan ta iya miƙewa tsaye, tana sharar kwallah ta nufi cikin gida. Allah sarki Jasra mai cewa Leesharh bata da saurin kuka to yau ta zo taga Leesharh na sharɓar kwallah kamar ruwan fanfo aka buɗe.
Elevator ta haye ta nufi sama, sai goge kwallar take yi amma yaki dakatawa daga zuba, zogin wannan mari nasa yaki sakinta, tunani take yi su waye su Obaid kuma?. Can zancen wannan matashiyar mata mai nikaf ɗin ya faɗo mata a ranta in da take cewa. "Akwai wasu twin's a gidan, kada ki yarda ki haɗa hanya da su, kada ki takalesu ko wata gardama ta haɗaku, saboda kaifin ƙwaƙwalwarsu zasu iya harbo jirginki". Tuna tattaunawarta da matar yasa ta fara zargin to ko sune waɗan da aka yi mata gargaɗi a kansu? In kuwa sune to ai ta kwaɓe aiki, dan kuwa ga shi dai gardama ce ta fara haɗasu, kuma tun da suka fara cewa suna zarginta to da wuya su kyaleta, idan ma basu fara yin practical na aikinsu a kanta ba... Akwai cakwakiya kam.
Tana haurawa sama ta nufi hanyar da zai sadata da part ɗinsu, tana tafiya zalo zalo kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Kamar daga sama ta tsinkayo muryar Ramish da tun da ta ji ta sau ɗaya ɗazun ya tsaya mata a ranta. Waya yake yi cikin harshen turanci, da alama kuma da abokan aikinsa yake wayar, yana tsaye a gabanta in da take tunkara kenan, sai dai bata ƙarisa wajen ba, da alama wayar ce ta fito da shi daga babbar parlourn izuwa wannan waje.
Cikin hanzari ta ɗan ja da baya kaɗan ta laɓe wajen wani ɗan lungu na kusa da babban parlourn, tattara dukkan nutsuwanta ta yi ta kasa kunne tana sauraron abin da yake faɗa, ba wani gane turancin sosai take yi ba, amma Allah yasa yana maganar yana haɗawa da larabci, hakan yasa tana fahimtar abin da yake faɗa sosai da sosai, ta fahimci ina maganar tasa ta dosa.
NI KAM NA CE LEESHARH FA TA FARA AIKINTA KENAN, TO KAFIN MU JI ME RAMISH YAKE FAƊE BARI MU LEƘA SABON GIDAN BABAN KHADIJA MUGA ME AKE AIKATAWA SAI MU DAWO.
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
GIDANSU KHADIJAH 💔😥
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 9/9/2024.....✍️📚🌹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
Ana dirama a wannan gida dai'dai gwargwado, domin kuwa Hauwa fa ita ce ta bawa maman Zainab ɗakin da zata zauna, gini ne da baban Zainab ya yi ta gabaɗaya rufi ɗaya, manya manyan bedrooms guda huɗu ne a cikin ginin, kowanne da toilet ɗinsa daga ciki, sai parlor a tsakiyarsu, akwai katafaren kitchen a cikin, kofar kitchen ɗin yana ta wajen dining area. Daga waje ta baya kuma akwai Bq, ginin dai ya tsaru sosai, gini ne na zamani, kasa tiles sama pop, ga manya manyan Ac a parlourn da kowa room na gidan. Kitchen ɗin ma already anyi fixing na komai, drawers ɗin duk an yi fixing ɗinsu, harta gas da komai da komai an sanya.
Hauwa da kanta ta zaɓawa maman Zainab ɗakin da yake ta kusa da dining area, wai shi ne ɗakinta, sannan ta bawa su Zainab ɗakin da yake kusa da na mamar tasu wai shi ne nasu, sura room guda biyun kuma ta ce ɗaya nata ita da baban Zainab, ɗayan kuma a bar mata shi zata yi amfani da shi ba yanzu ba.
Nan fa maman Zainab ta ce bata isa ba, dan bata ga dalilin da zai sa ace Hauwa ce zata zaɓa mata ɗakin da zata zauna ba, kunsan mu fa mata haka halinmu yake, mun tsani muga wata macen tana nuna mana ta fimu iko da abin da muka san mu muka sha wahala a kansa, da farko maman Zainab ta ce zata danne zuciyarta ta hakura kome Hauwar zata yi ba zata kulata ba, zata kawar da kai, amma ina ba zata iya yin hakan ba, domin kuwa mu mata bamu da karfin zuciyar jurar ganin kishiya ta nuna ta fimu iko da komai na gida.........😌🙃🌝
Hakan yasa maman Zainab ta ce ina wlh Hauwa bata isa ta zaɓa mata ɗakin da zata zauna ba, ta gama shan wahalar baban Zainab ɗin, su juri wahala a baya domin su gina kansu rana tsaka kawai wata banza ta zo ta ce zata nuna mata ta fita iko da wannan ribar wahala da suka sha? Wlh wannan ne kuwa ba zai taɓa yiwuwa ba.
Ita kuwa Hauwa ta ce yama yiwu ya gama. Baban Zainab wanda tun da suka shigo gidan ya kama hanya ya wuce room ɗinsa bai ma san me ake ciki ba, ya barosu a parlourn ne suna ta dirama. Cikin gatse Hauwa ta fara gaya mata magana.
"Wannan ɗakin shi na zaɓa maku, kuma a cikinsa zaku zauna, idan ba haka ba sai dai ku kwana a waje, dan ba zaku kwana mun a parlour bama, saboda wani lokaci tsakar dare ina fitowa mu ɗan yi hira da mijina idan barci yaki zuwa, so ba zaki kwana mun a parlour mu fito hira mu sameku ba, dan