x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 434

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
hayaniya da matsalolin rayuwa na yau da kullum, kullum a cikin farinciki suke, su bama su san da akwai wasu mutane da suke rayuwa a wajen dajin ba, bare har su san da wasu matsalolin.

Ajiyar zuciya Mamma ta sauke tare da yin hamdala ga Allah subhanahu wata'ala da ya bata yaro mai biyayya irin Kamran, yana da bala'in zuciya na wuce misali, ga saurin fushi, sai dai kuma duk fushin da yake a ciki da zarar yaga Mamma a cikin ɓacin rai shi zai danne nasa fushi ya kwantar da kai da murya dan ya ganta a cikin farinciki, shi ɗin mutun ne mai tsananin son mahaifiyar tasa, bashi da burin da ya wuce ya ganta a cikin farinciki, ita ce komai nasa, ita ce duniyarsa, ta sha ɗawainiya da shi, ta sha fama da shi, ta wahala wajen renonsa, ta tsaya sayin daka tare da jajircewa wajen ganin ya samu komai na rayuwa kamar kowani yaro, ta mai da shi jarumin sadaukin, ta gina mashi rayuwarsa a kan jarumta da rashin tsoro, bai san wani abu wai shi tsoro ba kamar dai ita ma Mamma, rayuwarsu gwanin ban sha'awa abin koyi ga al'umma.

Fitowa ya sake yi hannunsa ɗaya mai lafiyar na rike da kayan abinci.

A kusa da ita ya zo ya zauna tare da ajiye mata abincin a gabanta yana kallon fuskarta, while ita ma shi take kallo, kamar nace zan rabasu.

Wani irin gurnanin Tiger ne ya fara tashi daga bayan kogon nasu. Ko a jikinsu tamkar basu san da cewa Damusa ce take kuka ba, abincin kawai Mamma ta fara bawa Kamran ɗin a baki kamar wani ƙaramin yaro.

A wani irin mahaukacin gudu wani shirgegen damusa ya hauro saman dutsen, yana da girma sosai ga cikar razanarwa a tattare da shi, ƙosasshe ne mai lafiya, ganinsa kawai ya isa ya sanya bawa haɗiyar zuciya ya mutu, dan ba ƙaramin Tiger bane ba, sai wani girgiza yake yi yana jijjiga jikinsa, tamkar wanda ya taso daga barci, kunsan haka Tigers suke yi idan suka taso daga barci ko kuma suka ci suka ƙoshi, to haka suke yi.

Kai tsaye wajen Kamran ɗin ya nufa, yana zuwa ya kwanta a kusa da shi yana wani zuro da harshe waje, da alamu sun saba sosai.

Hannunsa guda ɗaya Kamran ɗin ya ɗaura a saman Tiger yana faɗin.
"Mamma kin ga Rocky tun jiya da ya yi fushi da ni sai yau ya dawo ko?".

Tana ɗebo mashi wani abincin ta bashi amsa da cewa.
"Kai ne baka kyautawa Rocky, shiyasa yake yawan yin fushi da kai".

Buɗe baki ya yi ta zuba mashi abincin da ta ɗebo ɗin, a hankali ya cigaba da tauna yana faɗin.
"Amma kuma Mamma ai ba zai iya fushi dani mai gabaɗaya ya tafi ya barni ba, dole idan ya yi fushin ma sai ya sake dawowa, yanzu ma ba ga shi nan ya dawo ba, ni ai bani na je na nemosa ba, idan ya isa ya tafi mai gabaɗaya ya barni mana".

Girgiza kai kawai ta yi, dan tasan komai wuya komai daɗi Rocky ba zai taɓa rabuwa ba Kamran ba, saboda wani lokaci dabbobi sun fi mutane amana, yau tsawon shekaru goma shabiyar kenan tun ranar da aka haifi Kamran ɗin suke tare da Rocky, a tare suka yi wasa a wannan dajin, so tasan kome Kamran ɗin zai yi mashi ba zai taɓa rabuwa da su ba, sai dai wani ikon Allah, idan Kamran ya yi mashi ba dai'dai ba, sai ya yi fushi ya tafi, amma anjuma kaɗan zai sake dawowa abinsa, kullum suna a tare.

Kun san Damusa da Zaki daban daban suke, ita Damusa tana iya haura sama da shekaru ashirin tana rayuwa a duniya, ita kuma Zaki bata kaiwa sai wani ikon Allah, wannan zafin zuciyar nasu da wannan kukan da suke yi shi ne yake yawan kashe Zakunar, so su basu rayuwa mai tsawo sosai kamar Damusa, kun san sunfi kowace dabba zafin zuciya, to shi ne yake hallakasu basu jimawa a duniya, fatan kun gane?.

Abincin ta cigaba da bashi yana ci yana shafa jikin Rocky ɗin, shi ma yana tsananin kaunar Damusan, dan yana da amana ga kuma taimakonsu da yake yi, baya barin sauran muggan namun dawa su cutar da su.

Bayan ya kammala cin abincin ya ƙoshi ne ya miƙe tsaye yana faɗin.

"Mamma am coming, I want to go to somewhere, is very close".

One thing about KAMRAN yaruka biyu kawai yake ji a rayuwarsa, daga yaren da ya yi wa maman ƴan biyun nan magana da farko, sai kuma English, yarika biyun nan kawai ya iya.

"Kamran kada ka yi nisa fa, sannan ka dawo da wuri, dan anjuma kaɗan kai da Rocky zaku je ku farauto mana nama, bamu da ɗanyar mama, kuma ina son gasa mana da daddare".

Jinjina mata kai kawai ya yi tare da sa kai ya wuce.

Da ɗan gudu Rocky ya rufa mashi baya. Da kallo Mamma ta bisu, tana tsananin kaunar ɗan nata, shi ne duniyarta, abin da yasa bata hana shi fita ba shi ne, tasan cewa kullum suna zuwa yawace yawacensu shi da Rocky, sai dai basu taɓa yin nisa da ita, da ta kwala mashi kira zai amsa, kun dai ga ɗazun da yake wajen Maman twins ta kira kuma ya amsa, to haka suke, baya taɓa yin nisa da ita, dan yasan bata son hakan, bata son yin nisa da shi.

Ta ɗan jima a wajen tana zaune kafin ta miƙe ta nufi cikin ƙogon nasu, dan ta je ta cigaba da yin ƴan aikace aikacenta.

Shi kuwa Kamran, kai tsaye wajen mum twins ya nufa abinsa, dan matar ta tsaya mashi a ransa, yana son ya koma ya sake dubata ita da ƴaƴan nata.

Sai binsa da takun ƙatsaita Rocky yake yi, yana wani irin jijjiga jiki, irin shi ne shugaban nan.

Turus Kamran ya ja birki a lokacin da suka isa wajen da mum twins ɗin take. Zallar madarar mamakice ziryar ta bayyana mashi a saman face nata, ɗan zaro idanuwansa waje ya yi yana kallon wajen da kyau, gani yake kamar ba wajen bane ba.

Mamaki ya lulluɓe shi ya ƙasa gaba ya ƙasa baya, while shi kuma Rocky ya yi gaba abinsa yana son wucewa ya je ya shiga cikin bukkar.

Ganin Rockyn zai shiga ciki ne yasa shi ya ɗan farfaɗo daga sumar mamakin da ya afka.

Da sauri ya ƙarisa ciki dan ya kara tabbatarwa da kansa abin da yake gani. Tabbas ba gizo bane, kamar yadda mum twins ta sha madarar mamakin ganin an taimaka masu an gyara masu komai, haka shi ma ya sha wannan madarar mamakin.

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idanuwansa suka sauka a kan mum twins da babynta, da farko ya ɗauka basu nan ne, ganin suna nan yasa ya ji wani sanyi ta ratsa shi.

Da sauri ya ƙarisa kusa da mum twins ɗin yana mai gayawa Rocky kada ya ce zai shigo cikin ɗakin nan ya ɓallah masu abubuwa, dan kofar shiga ma ta yi mashi kaɗan, idan ya ce zai shiga kaf zai karya itatuwan da aka kafa a bakin kofar, dan haka ya tsaya a waje.

Wani irin gurnani ya yi alamar bai ji daɗi ba, Kamran ya hana shi shigowa yaga ne a ciki.

(Ga ji mun Rocky da gulma😒 wato suma sun san gulma fa😅)

Jin motsin mutun a kanta ne yasa ta yi saurin waro fararen idanuwanta waje, dan taga wanene.

Duk da cewa ɗazun da ya taimaka mata ita da baby's nata suka fita daga cikin ramin nan bata a cikin hayyacinta, amma hakan bai sa ta ji tsoron ganinsa ko makamancin haka ba, sam bata iya gane face nasa a ɗazun ba, tana cikin wani hali, bata san wanene a kanta ba lokacin.

Ganin shi cikin nutsuwa da kamala sosai a tattare da shi ne yasa ta kura mashi idanu tana mai binsa da kallo.

Tsugunnawa a gabanta ya yi, cikin sanyin murya ya tambayeta wanene ya yi mata dukka wannan abin? Ko dai ita da kanta ne ta yi?.

Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a ba ita ce ta yi ba, amma bata iya buɗe baki ta yi mashi magana ba.

Sake shiga cikin kogin madarar mamaki ya yi, amma sai ya daure ya kawar da mamakin nasa tare da ce mata.
"Zaki iya tashi zaune?".

Nan ma girgiza mashi kai ta yi alamar.

"In ɗaga ki?".

Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a bata buƙatar ya ɗaga ta.

Zai sake yin magana ɗaya daga cikin baby's ɗin nan ya fara motsi haɗe da kuka kaɗan kaɗan.

Kusan a tare ita da shi ɗin suka kai kallonsu a kan yaran.
Wannan mai black cuiry hairn ne dai yake motsi tare da kukan.

Da sauri Kamran ɗin ya kai hannunsa ya ɗan ja towel da aka lulluɓesu zuwa kasa kaɗan, ɗan girgiza babyn ya fara yi.

Ai kuwa yana taɓa babyn kamar ya ce ya kara ihu, wage baki ya yi ya fara zunduma ihun da gasken gaske, dama already kun ga da kuka ya zo, sarki ne wajen zuba kuka, dan haka kuwa sai ya cika masu kunne da ihu.

Runtse idanuwanta gam maman nasu ta yi, har can cikin ranta take jin wannan kukan nasa, wani irin zafi zuciyarta take yi mata.

Hannu biyu Kamran yasa zai ɗauki babyn, ai kuwa bai kai ga ɗauka ba ɗayan baby mai golden white hair ya fara ihu shi ma.

Kasancewar daga Kamran har maman tasu basu san cewa tun da aka haife shi bai yi kuka ba, sai kukan nasa bai basu mamaki ba, sai ma rikita Kamran ɗin da suka yi, ya rasa me zai yi masu, ya kuma rasa wanne zai ɗauka daga cikinsu.

Allah sarki uwa da ƴaƴan, jin kukansu su dukkansu biyu yasa ta ji ba zata iya jurewa ba, ciza laɓɓanta da karfi ta yi tare da yunƙurawa dan ta miƙe zaune.

Da sauri Kamran ya juyo da kallonsa a kanta.

Wani irin wahalallen kara ta saki tare da dafa kasa da iya karfinta tana son tashi, nan take har wani irin zufar wahala ya fara tsastsafo mata, daga gani kasan tana jin azaba ba kaɗan ba, dama kuma ai dole ta ji azaba, suka da kifiya a ciki ai ba wasa ba, dan ma ta auna arziki ne ba kaɗan ba, ba dan haka ba ai da ta jima da mutuwa, kuma kunga wanda ya harbeta da kifiyar bai harbeta a in da zata cutu sosai ba, ya mata da sauki.

Kamran sarkin tausayi, duk zafin zuciyarsa akwai tausayi sosai, har cikinsa yake jin wani irin matuƙar tausayinta ya lulluɓe shi, ji yake yi kamar yasa hannu ya ɗagata, amma sam bata son ya taɓata, sanin tana gudun ya taɓata ne yasa ya hakura ya jure yana ganinta cikin wannan hali bai yi yunƙurin taimaka mata ba, ya bita da kallon cike da tausayawa fal a face nasa.

Bai kuma hanata miƙewa ɗin ba, duk da yasan tana da ciwo a cikinta, kasancewar yaga anyi mata aiki sosai a kan ciwon ne yasa sai bai hanata ba, amma kuma duk da wannan magani sosai da aka zuba mata, yana da kyau ta sami kamar kwana uku bata motsawa sosai, dan wajen ya ciko da wuri, sai dai ina, hakan sam ba zai yiwu ba, saboda yaran nan nata, da alama rigimammune number ɗaya, dan sarakan kuka ne, ita kuma ba zata iya jure jin kukan nasu ba, hakan yasa zata miƙe zaune dan ta san ta yadda za'ayi ta basu nono.

To ya Ubangiji ka sakawa iyayenmu da gidan Aljanna, ya Allah kamar yadda suke sadaukar da abubuwansu da dama masu matuƙar mahimmanci wani lokaci ma har da rayukansu a kanmu, ya Allah kasa su zamana daga cikin al'ummar da annabi zai fara ceta a ranar gobe kiyama, ka bamu ikon yi masu biyayya sau da kafa a kan dai'dai.

Da kyar da suɗin goshi ta iya tashi zaune, ta jingina bayanta da jikin itatuwan da aka haɗa masu ɗakin, tsabar azaba har wani irin jajir idanuwanta suka yi, tamkar wadda ta sha kuka na tsawon lokaci ta ƙoshi, zufa cigaba da tsastsafo mata yake yi a gefe da gefen face nata, fuskar nan tata tamkar wadda aka watsawa ruwa.

Ta datse lausasan laɓɓan bakinta gam da hakwaranta, ta kuma datse idanuwanta gam tana girgiza kai alamar azaba take ji sosai.

A hankali take sauke numfashin da yake fito mata tamkar wadda ta sha uban gudu ta ƙoshi, sai a lokacin kuma ta ji nauyin kayan jikinta ya ragu, alamar an rage mata kayan jikin nata. Tana son buɗe idanuwanta ta bi jikin nata da kallo, amma ta kasa iya buɗesu, saboda azaba, ji take yi kamar idan ta buɗe kara karuwa raɗaɗin ciwon zai yi mata.

Sosai Kamran ya yi matuƙar jinjina mata, dan kuwa ta yi namijin ƙoƙarin na wuce misali, ba kowa ne irin abu haka zai faru da shi kuma ya iya miƙe zaune a yau ba, sai wanda yake da matuƙar jarumta, da alama jaruma ce sosai ita ma, dama idan baku manta ba a baya na gaya maku da alama jarumace, da alama an sha fama da ita sosai kafin a iya kaita ƙasa.

Duk jarumta irin na Mammansa yau dai Kamran ya jinjinawa maman twins ma, bai taɓa tunanin aduniya za'a sami jaruma mai tafasasshen jini irin Mammansa ba, sai ga shi yau ya ganta duk da bata kai Mamma ba, dan ita Mamma karshe ce, jarumtarta tamkar wani sadaukin yaki haka take, macen da zata yi faɗa da Damusa ai kunga ba ta wasa bace ba!.

Su dai baby's da yake basu san halin da ake ciki ba, sai tsallara ihu suke yi abinsu, ko a jikinsu, duk sun sa Kamran ya shiga ɗimuwa, ya rasa waye za rarrasa, sun rikita bawan Allah, duk da dama can ba iya rarrashin ya yi ba, yana dai kwatantawa ne, kunga shi kaɗai ne a wajen Mamma, bai da kani ko kanwa bare ace yana ganin yadda Mamma take renonsu shi ma ya koya.

Da hannunta ɗaya ta dafe wajen ciwon nata, ɗayar hannun nata kuma idanuwanta a datse gam ta fara yi wa Kamran ɗin nuni da ya bata baby's ɗin, ba halin yin magana, baki na datse gam.

A hanzarce ya ɗauko wannan mai bakin curly hair ya miƙa mata, dan yafi tsala ihu, babyn nan tamkar maƙoshinsa zai fashe, saboda iya kuka.

A karkace Kamran ya ɗauko shi ya ɗaura mata a saman cinyarta. Jin babyn a jikinta yasa ta sauke wani irin wahalallen nauyayyar ajiyar zuciya, alamar ta ji sanyi ya ratsa cikin zuciyarta.

Da kyar ta iya tallabo babyn ta fara kiciniyar bashi nono duk da bata da tabbacin tsabtar jikinta, ita dai burinta kawai ta shayar da su su daina wannan ihu, dan a tunaninta yunwa suke ji sosai ne yasa suke irin wannan uban ihu haka.

Shi dai Kamran yana son taimaka mata, sai dai babu hali, dan kuwa bazata taɓa yarda ya taɓa jikinta ba, sanin hakan yasa ya kawar da kansa daga kallonta ya cigaba da girgiza ɗayan babyn dan su sami saukin wannan ihun da yaran suke rera masu.

Shi kuwa Rocky ya yi kwanciyarsa a bakin kofar shigowa, sam ba haka ya so ba, ba yadda ya iya ne kawai, yana jin maganar Kamran sosai.

(Hmmm Damusa dai ki sabo ne! Duk da akwai masu amana kamar yanda yake a ko'ina akwai masu amana dana banza, Allah dai ya tsare mana su Kamran, kada wata rana Rocky ya rasa abinci ya yi ram da su😅.)

Da kyar ta iya fitar da nonon ta sakawa babyn abaki. Ai kuwa kamar jira yake yi ya fara sha babu kakkautawa, Allah sarki ashe da gaskiyarta, ashe tasan me suke yi wa kuka, uwa kenan! Babu biyunta a duniya!.

Mamaki ne ya kama Kamran sosai na ganin yadda wannan babyn ya yi shiru yana shan nono, sai a lokacin ya lura da babu wannan alkyabba ta jikin Maman twins ɗin wanda kuma yasan dai ya fitar da ita daga cikin ramin nan da wannan alkyabbar a jikinta, to ko waye ya cire mata shi?.

Ya tambayi kansa da kansa. Ƴar waige waige ya fara yi ko zai ga ta in da aka ajiye mata alkyabbar tata, sai dai ina, bata babu labarinta.

Shiru ya nutsa cikin tunaninsa yana tunano a ina alkyabbar to? Waye kuma ya ɗauketa?. Sai a lokacin ya tuna da cewa ba iya alkyabbar bace kawai, akwai sarka, abin hannu, da kuma ɗankunnenta na zallar madarar gold, suma ina suke? Dukka babu ko zobbe a wajen, bayan kuma shi yasan da hannunsa ya kwaso mata su daga bakin ramin ya biyota da su zuwa wannan wajen time ɗin da take ja a kasa da zasu zo wajen.

Da hannunsa ya ajiye mata su a kusa da ita a lokacin yana yi mata sannu, to ina suke yanzu kuma? Abin da ban mamaki sosai gaskiya, kuma ga dukkan alamu ba wai satarsu aka yi ba, babu ma ɓarawo a wannan daji, tsawon shekaru 15 ɗin nan daga shi sai Mammansa ya sani suke rayuwa a cikin wannan dajin, sai baƙin maharba idan sun zo wucewa, sai kuma idan hanya ta kubcewa mutun ya faɗo cikin dajin, ko su maharba ba kasafai suka cika shigowa cikin wannan dajin ba, dan akwai manyan namun dawa a cikinta, idan suka yi wasa su da suka zo farauta to za'a faraucesu kamar kuda da bujumin sa, hakan yasa sam basu gigin zuwa dajin farauta, sai time to time.

Wannan dalilin yasa abin ya ɗaurewa Kamran kai ya kuma bashi mamaki, to wani ɗan albarkan ne kuma ya kwashi kayan maman twins? Allah masanin gaibu.

Sai da ta ji alamar barcin babyn dake a hannunta ne ta kara sauke nauyayyar ajiyar zuciya, ya sha ya ƙoshi sai barci.

A hankali ta waro idanuwanta waje, sun yi jajir da su kamar wuta, baiwar Allah fuskarta duk a kumbure kamar ba ita ba.

Zubawa babyn idanu ta yi tana mai karewa ɗan kyakkyawar face nasa kallo, ga dukkan alamu wannan baby mai golden white hair yana da matuƙar hakuri sosai, domin kuwa wannan jijjiga shi da Kamran yake yi yana ɗan bubbuga shi a hankali hankali yasa ya hakura ya yi shiru kamar babu shi a wajen, saɓanin mai black hair nan, ai shi ko jijjigawar ma baya jin ana yi, ihu kawai abinsa,
End Ads