kaga ta yi mashi abin da ya ɓata mashi rai to wlh babban akasi aka samu, banda haka kullum tana ƙoƙarin ganin ta kiyaye bata yi abin da baya so ba, shiyasa shi ma duk abin da bata so yake ƙoƙarin kiyayewa, mutun ne shi mai ilimi, yasan da cewa a duniyar yanzu idan mutun ya faɗi ya mutu idan ba yana da makudan kuɗaɗe ba to babu wanda zai kula ƴaƴansa da matarsa ma bare har ya yi ƙoƙarin tallafa masu, mutun yana raye bai mutu ba ma idan bashi da dukiya babu mai kula shi ba mai zuwa gidansa bare kuma idan ya mutu, in kaga family suna rige rigen ɗaukar yara idan mahaifinsu ya mutu to wlh ya mutu ya bar masu dukiya mai yawa ne, nan ne zakuji har faɗa ake yi a kan ɗaukarsu, da zarar kuma ancinye dukiyar gadon shikenan za'a fara yi wa ƴaƴan riƙon sakainar kashi, a barsu suyi ta gantali a bakin layi, mai ƙoƙari ne ma zai sanyasu a islamiya, wannan mai mutunci sosai daga cikin ƴan uwa kenan, mara mutunci ma ai sai dai ya turasu wajen uwarsu idan ya kammala cinye dukiyar, ta je can ita ta karita da su, idan ma zasu mutu su mutu!.
So shi baban Zainab yana da dogon tunani, hakan tasa ya yi wa kansa plan tun yana da rai, plan da zata inganta mashi rayuwar ƴaƴansa da matar tasa ko bayan babu shi, wannan dalilin yasa baya da sha'awar tara ƴaƴa da mata, rashin haihuwar maman Zainab ɗin ba daga ita bace, daga shi ne wanda ya dakatar masu da shi ita ma ba tare da saninta ba, sam bata sani ba, ta dai ga haihuwarta ya dakata, da yake tana da tawakkali kuma sai bata buƙaci jin ba'asi ko kuma ta tuhumi wani ba, sai ta ɗauka a matsayin Allah ne ya dakatar mata da shi, dan tasan babu wanda ya isa ya dakatar da haihuwa har sai idan Allah ya rigada ya rubuta su ɗin kenan zata samu.
Babban burin baban Zainab shi ne, idan ya kammala masu ginin nan nasu suka koma, the second abin da zai yi shi ne ya sanya Maman Zainab ɗin a harkar kasuwanci sosai da sosai, this is the best way na farko da zai fara gina rayuwar iyalansa, abin da yasa ya yi plan ɗin hakan kuma shi ne, ya san cewa a duniya idan kowa zai guji rike mashi ƴaƴa saboda talauci to banda mahaifiyarsu, ita ce duk wuya duk daɗi zata zauna da su, zata iya yin kwana biyu tana kwana da yunwa in dai ƴaƴanta zasu ci abinci, zata iya kwana a waje bakin kofa ƴaƴanta suna cikin ɗaki idan ɗakin ya yi masu kaɗan, zata iya zama a cikin ruwan sama, rana, da kuma iska su kuma ta ajiyesu a inuwa idan filin ba zai ishesu ba, uwa ita kaɗai ce ba zata taɓa bari rayuwar ƴaƴan da ta sha wahala ta haifosu ta renesu ya tagayyara ba, sai dai idan babu yadda ta iya ne, amma ba zai taɓa yiwuwa ta barsu a gantale ba.
Wannan dalilin yasa baban Zainab ɗin yake planing ɗin ita ce ya dace da ya fara ingantawa tun yana raye, ita ce ya dace da ya fara ginawa a kan komai nasa, ya koya mata kasuwanci tun yana raye, ya kuma bata makudan kuɗaɗe na jari, tun yana da rai ta ginu ta tsaya da kafafunta, hakan zai sa ko bayan ya mutu, idan ma ƴan uwansa sun cinye gadon yaran, to uwassu tana da abin yi, kuma nata dukiyar dai babu wani daga cikin ɗan uwansa da ya isa ya zo ya kwace mata shi da sunan gadon yara, yasan wacece maman Zainab sarai, shi ne yasa baya da wata damuwa zai ninke makudan kuɗaɗe ya bata jari tare da nuna nata yadda zata yi.
A tsarinsa ba wai ita ce zata fita ta yi business ɗin ba, a'a amintattun daga cikin ƴan uwanta ko kannenta zata ɗauko ta ɗaura a kan kasuwancin nata, kowani sati ta rinƙa yin lissafi da su tana cire ribar tana zubawa a cikin account nata, idan ta ga dama ta kara bunƙasa kasuwancin da ribar, shi dai a matsayinsa na cikakken ɗan kasuwa zai yi ƙoƙarin ya bata shawarar da ta dace game da kasuwanci a koda yaushe, sannan kuma zai sanar da ƴan uwansa cewa wannan dukiyarta ne da aka bata na gadon mahaifinta da ya rasu ta fara kasuwanci da shi, zai yi hakan ne kuma gudun fitina, kada azo idan ya mutu ace wannan dukiya da take juyawa ma nashi ne a kwace, yasan halin mutane, to wannan shi ne plant ɗinsa ta farko kenan game da familynsa, shiyasa baya son aurar wata mata, dan baya son bayansa su walaƙanta.
Bawan Allah shi da yake da tunani kenan, da ya yi ta aure yana haifar ƴaƴa gara mashi ya inganta rayuwar waɗan da yake da su a gida ta yadda ko bayan ya mutu ba zasu sha wahalar rayuwa ba, amma a duniyarmu ta yau magidanci ya bawa matarsa jari a cikin gida ta yi sa'anaa ma gani yake asarace, kuma idan ta tambaye shi buƙatunta ba biya mata yake yi ba, idan ta nemo jari ta fara kasuwancin ma wani mijin saboda mugunta sai ya san yadda ya yi ya cinye mata jari, wani ma sai ya rinƙa hanata isashen kuɗin cefane yana cewa ta cika zai biya ko makamancin haka, da haka jarin nata yake karewa, sun gwammaci su je su yi ta karo aure kamar wasu bunsuraye, sun gwammaci su yi ta tara yara dayawa su kasa riƙewa, yara su zama ba boko ba Arabic, su saki ƴaƴa a layi babu ɗaya kanin biyu, yara duk su girma ba ilimi bare sanin yakamata, mahaifiyarsu baiwar Allah tana can ta kashe kanta a neman masu abin da zasu ci bata wani zama ta basu tarbiya sosai, duk su taso babu tarbiya su zama ƴan iska, wasu ma ƴan shaye shaye, wasu daga haka suke ɗaukar makamai su fara sace sace suna addabar al'umma, wlh da kowanu uba tun farko yana kula da ƴaƴansa ya sakasu makarata ya basu ilimin addini dana boko, to wlh da yau babu ɗan iska ko guda ɗaya a duniya, duk ƴan iskan nan jahilai ne, ba Arabic bare boko, wani ko karatun fathiha bai iya ba, kuma ya girma ya zama matashi an fara rubuta mashi zunubi, ba gasu nan zube a layi ba, sai anyi magana kuce annabi ya ce a hayayyafa dayawa dan ya yi alfahari da al'ummarsa ranar gobe kiya ma, tambayata a nan shi ne da ƴan iskan annabi zai yi alfahari ne? Ai wlh ka haifo ƴan iska sai dai ka je cikin kabari kana kwance kana fama da azaba su kuma suna duniya suna kara labto maka wata azabar, wlh kasani in dai baka bawa ƴaƴanka tarbiya ba, to duk abin da zasu aikata kana da kaso a ciki, kana kabari kana karɓar azabar da suke aikatawa a duniya, ka je lahira Allah ya ce maka ya ka yi da amanar da ya baka? Nan idan baka bada amsar da ake buƙata ba ka sake karɓar wani sabon gashi na musamman, annabi bai ce kowa ya haifi ƴaƴan da ba zai iya kula da tarbiyarsu ba, ko shin kansa karin aure annabi ya ce in kasan ba zaka yi adalci ba ka tsaya a kan guda ɗaya, domin kuwa in dai ka yi rashin adalci aranar gobe kiyama a mai shanyayyen ɓari guda na jikinka zaka taso, amma sai kaga wasu shaiɗanun mazan da sun kara aure uwar gidansu da suka sha gwagwarmaya a tare ta zama bola kayan banza, su rabu da ita tana gantali tsakanin layi da gidajen maƙota dan neman abin da zata ci ita da yara, su watsar da yara su gasu bunsuraye iyayen son mata, wlh ku ji tsoron Allah, abu guda ɗaya Ubangiji ba zai manta ba sai ya tambayeku, idan ku kun manta shi Ubangiji ba zai manta ba, duk sai ya bi ɗaya bayan ɗaya ya tambayeku, Allah dai kasa mu dace.
(Yau dai za'a ga rubutun alƙalamin nawa ta yi zafi, abin ne yana bakanta mun rai in ga yadda maza suke walaƙanta mata a kan karin aure, wannan abin da ciwo yake wlh🥲 Allah dai ka haɗamu da abokan zama na gari masu ƙoƙarin bin tarihin manzon Allah kuma suna koyi da shi tare da litattafan musulci haɗi da Alqur'ani mai girma.)
Mu koma kan labarinmu.
Idan ran maman Zainab ya yi dubu to fa ya ɓaci a wannan lokaci, wani irin tukukin bakinciki ne ya taso mata daga ciki ya tsaya mata a wuya, zuciyarta har wani irin tafasa yake yi mata, sam bata san lokacin da ta ce mashi.
"Allah zai saka mun duk abin da suka mun, na so su, na kaunacesu tsakani da Allah, babu abin da na yi masu, babu abin da na tare masu, Allah ya gani ina yin iyakacin bakin ƙoƙarina wajen ganin na yi komai na tsakanina da Allah, amma me nayi masu da suke son sai sun cutar dani a rayuwata? Me nayi masu? Ya Ubangiji kamun sakayya cikin gaggawa!".
Tana magana tana hawaye, ta kai karshen maganar tare da miƙewa tamkar zata faɗi kasa, saboda tukukin bakin ciki, a hanzarce ta wuce izuwa cikin bedroom nata tana kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Already baban Zainab yasan za'ayi hakan, fin haka ma ya yi tsammani, dan yasan ta tsani kishiya, bata son maganar, yanzu shi yana cikin wani hali, duk ta in da ya je babu sauki, maman Zainab ta yi fushi, mahaifiyarsa ma ta fusata, kota ina babu daɗi, duk sai ya ji ba zai iya komawa kasuwar bama, haka zali ka ba zai iya tunkarar Maman Zainab a yanzu ba, zai barta ne sai ta huce kaɗan, yanzu ko ya tunkarata ba zata saurare shi ba, ba kuma zai sami abin da yake so ba, idan ba sa'a bama sai su yi faɗa sosai a tsakaninsu, shi mai ilimi ne, yasan idan ran mace ya ɓaci to kada ka tunkareta a lokacin, dan zaku yi ɓarattciya ne kawai, saboda a lokacin kome zaka gaya mata ba zata fahimta ba, idan ka samu ta saurareka ma kenan, zuciyar mace karama ce, kuma a kusa zuciyar take, idan ranta ya ɓaci babu abin da ba zata iya aikatawa ba, sai dai daga baya ta yi dana sani.......(Kamar aljanu haka muke idan ranmu ya ɓaci😅😅😅 mun san komai 🥱)
Dan haka sai ya koma ya kishingiɗa a saman kujerar yana tunanin rayuwa, kansa sai wani irin sara mashi take yi tamkar zata fashe gida biyu, har wani irin jiri yake gani, idanuwansa duk sun yi jajir saboda ɓacin rai, ya rasa me yake yi mashi daɗi a duniyar nan, bugu da ƙari ga auren Khadija and Haidar, sannan ga shi mamarsa ta ce nan da wata ɗaya da ita da amarya zasu koma sabon gidansa in da ya ci burin ya rayu da maman Zainab rayuwa mai daɗi, dan ta juri akwai da babunsa, ta zauna da shi tun yana talaka bai da komai, kai akwai lokacin da ita ma take ciyar da shi, harta maman Haidar ta ciyar, amma saboda rashin godiyar Allah shi ne suka saka mata ta wannan hanyar, abin sam babu daɗi, ya so ya aurar da Khadija da Zainab ga nagartattun maza da suka san ciwon kansu, sai ya zauna daga shi sai mamansu a sabon gidansu su sake more amarcinsu a karo na biyu babu kowa, babu wanda zai damesu, suyi rayuwar farinciki, ya saka mata da abin alkharin da ta yi mashi a baya, amma duk mamarsa ta rusa komai, ina shi ina soyayya mamarsa tana gidan fisabilillahi? Ai babu wannan zance!.
A haka su Khadija suka dawo daga school a tare da Sadiq da ya je ya ɗauko su suka sami baban nasu.
Hajiya Zainab sarkin raki tun daga harabar gidan take kiran sunan maman tata, sai kace wata tsohuwar makauniya, sai kwala kira take yi, sai da Khadija ta ce.
"Ni kam ke kam Zainab yaushe zaki yi hankali ne? Wai ba cikin ɗakin zamu shiga bane? Ki bari mu shiga mana sai ki gaya mata duk abin da zaki faɗa mata, amma kin wani tsaya daga tsakar gida kamar wata makauniyar da sandar dogarawarta ta ɓata kina kiran neman taimako?".
Turo bakin nan tayi kamar biro, sannan ta wuce izuwa cikin parlourn fuuuu kamar wata kumfa a saman ruwan teku, Khadija ta cika shisshigi a cewarta.
Tana shiga da ta ga babanta a kwance a saman kujera bata san time ɗin da ta saki school bag ɗin nata ya faɗi ƙasa ta ƙariso wajensa da gudu, kamar wata under 10 years tana ambatar sunansa.
"Baba, baba ya aka yi yau ka dawo da rana? Da muka tambayi kawu Sadiq ina kake ya ce mana kana kasuwa fa, ashe kana gida".
Khadijah tana ƙoƙarin cire takalmar makarantar tata a wajen ajiye takalmarsu ta tsinkayo muryar Zainab tana faɗin baba, baba, ai a ɗari ta yi maza ta ƙarisa cire takalmar ita ma ta faɗo cikin parlourn, bayin Allah suna matuƙar kaunar baban nasu sosai, dan uba ne na gari shi ɗin, yasan ciwon kansa dana iyalansa, yana koyi da fiyayyen halitta sosai da sosai.
Jin muryar Zeezeensa yasa ya buɗe idanuwansa da suke jajir da su kamar wuta.
Ɗan zaro idanu Zainab ta yi kafin ta ce. "Baba baka da lafiya ne?".
"Kai'na ne yake mun ciwo Zeezeena, shi ne yasa kika ga na dawo kasuwa da wuri, jeki ki cire uniform kuyi wanka kuzo mu ci abinci a tare, yau a gida ma zan ci abincin rana".
Da yake har yanzu yarinta sosai yana a kanta, sai ta miƙe cike da murna yau zasu zauna da babansu da rana su ci abinci, ɗakinsu ta nufa tana yi mashi addu'ar Allah ya sawwaƙa mashi ciwon kan nasa.
Khadijah dake a tsaye a bakin kofar shigowa tana kallonsu ne ta ƙariso cikin parlourn, a ƙasa saman carpet ta zauna kusa da baban nata, gaisuwa ta fara ɗaga mashi cikin nutsuwa kafin ta ɗaura da cewa.
"Baba ka dai'na sakawa ranka damuwa, zai iya taɓa lafiyarka, ni nasan kana damuwa ne a kan ni da yaya Haidar, to na yi maka alkawari zan zauna da shi kuma na yi hakuri, amma sai ka dai'na damuwa ka ji?".
Khadijah ba dai hankali ba, akwai shi kam, ga nutsuwa, bata shiga harkar kowa, kawar da kai da kawaici duk ta haɗa.
Miƙewa zaune ya yi, cikin sanyin murya ya fara saka mata albarka kafin shi ma ya ɗaura da cewa.
"Mamana ba zaki auri Haidar ba In Sha Allah, saboda ba shi ne irin mijin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce mu zaɓawa ƴaƴanmu ba, dan haka ni ba zan aura maki shi ba, ina jiran ne kawai ki rubuta Exams naki ki gama sai na san abin yi, dan haka ki kwantar da hankalinki ki rubuta Exams kuma ki ciyo mun first class kamar yadda kika saba kin ji ko?".
Haƙiƙa ya gaya mata hakan ne kawai domin ta nutsu ta rubuta Exams nata na karshe a secondary school da kyau, tabbas bashi da mafita a kan aurenta da Haidar, amma kuma baya taɓa sarewa wajen cewa ba zai aura mata shi ɗin ba, a kullum yana da kwarin gwiwar cewa Allah zai kawo mashi mafita ya kawo sanadiyar hana auren, amma for now dai bashi da wata hanya ko wata zaɓi, kawai gaya mata yake yi ba zata aure shi ɗin ba dan hankalinta ya kwanta.
"To baba ta ya za'ayi na dai'na damuwa na kwantar da hankalina bayan kai da kanka da kake cewa na dai'na damuwar kana cikin damuwa? Ni nasan yanzu haka damuwar ce ta ja maka wannan ciwon kai da har ka dawo gida da ranar nan bayan baka saba dawowa da rana ba, hankalina ba zai taɓa kwanciya ba matuƙar iyayena suna a cikin damuwa".
Tana magana idanuwanta a cike tab da kwallah.
"Mamana kada ki damu, muma daga ni har mamarki mun dai'na damuwa a yanzu, kema ki kwantar da hankalinki, yanzu dai jeki ki cire uniform ki yi wanka kuzo muci abinci a tare, na yi maki alkawarin ba zaki sake ganin damuwa a saman fuskata ba kin ji ko?".
Jinjina kai ta yi tana mai ƙoƙarin goge hawayen da suka cika mata idanun.
"Baba kafin na cire uniform ɗin bari na sayo maka maganin ciwon kai ɗin, idan mun ci abinci sai ka sha ka kwanta ka yi barci zuwa la'asar zaka ji sauki ko?".
Kamar zai ce mata ta bari, sai kuma ya tuna Khadija ba kamar Zainab take ba, Zainab ne zai cewa ta bar abu ba zata tambaye shi dalili ba zata bari, ita kuwa Khadija yanzu idan ya ce ta bari ma wani sabon rigima ne, dan sai ta ce mashi lallai sai ya sha magani ko kuma ta tsayar mashi da kuka, zaman lafiyar dai kawai ya barta ta je ta sayo ɗin, baya son fitarta, amma da yake lallaɓata yake son yi yanzu ta kwantar da hankali ta yi karatu, sai ya kyaleta ta je ta sayo ɗin, tun da shagon babu nisa, idan ya ce ta bari ya sayo ma zata ce a'a ya kwanta kansa na ciwo, su Zainab kam an tafi wanka, sai murna take yi yau zata ci abinci a tare da babanta da rana. Hmmmmm Allah ka bamu ƴaƴa waɗan da zasu iya fahimtar farincikinmu da kuma bakincikinmu ba sai mun gaya masu ba!.
Har ta kai bakin kofa zata fita sai kuma ta juyo tana faɗin.
"Baba ina mama kuma?".
"Mamanku tana ciki tana barci".
Ya bata amsa yana ƙoƙarin ciro kuɗi daga aljihun dakakkiyar shaddar jikinsa.
Shiru Khadija ta ɗan yi tana tunanin, hakiƙa zuciyarta ta gaya mata ba lafiya ba, ace babanta ya dawo mamanta tana cikin ɗaki tana barci? Bata taɓa ganin hakan ba, idan ma barcin ne wlh a tare suke yi, dole dai akwai abin da yake faruwa, dan mamanta da zarar babanta ya dawo to tana tare da shi, duk