ya ce da Aunty MieMie ko uppan ba. Yana fitowa suka haɗu da Gimbiya Chuchu da ta fito daga cikin elevator a yanzu, ita ma wajen Momma zata je, dama renon Mommar ce ita, shiyasa kuka ga ta fi shaƙuwa da Gimbiya Zunaira sama da kowa a cikin gidan, a part ɗin Momma ta saba zama time da take karama, da ta girma ne ta koma part ɗin Akka, sam bata son zama a wajen mummy wato mamarta sosai, baiwar Allah da alama zama da Momma mace mai farar zuciya ne yasa ita ma take da saukin kai duk da bata kai Zunaira ba.
Kamar dai kullum aikin da aka saba, tana fitowa daga cikin elevator ta fara ɗaukar kyakkyawar fuskarta a hoto da wayar Fanan da yake a hannunta, idan baku manta ba Yah Jawad ɗin ya kwace nata wayar, hoto dai ba zata fasa ɗauka ba, abin ya bi jininta, ita da ko barci ta tashi sai ta kashewa kanta hotuna kala kala bare kuma ace ta yi wanka ta yi kwalliya, ai abin ba'a magana, shi ne har da aro wayar Gimbiya Fanan.
Tana aikin ɗaukar hoto tana tafiya, sai turo ɗan bakin nan take tana canza style kala kala, sam bata lura da mutun yana zuwa ba, da yake yanayin takalmar kafafunsa smooth shoes ne, irin na yawo a cikin gidan nan, suna da laushi sosai ta yadda sam basu kara idan mutun yana tafiya, hakan yasa sam bata ji tahowarsa ba.
Shi kuwa tun da ta fito daga cikin elevator yake kare mata kallo, ta canza shigar da yake a jikinta ɗazun izuwa wasu haɗaɗɗu kuma tsadaddun kayan, dama ita ƴar wanka ce, ga masifar san kwalliya, kamshi da kuma gyaran jiki kamar me.
Sai tinkarosa take yi kallonta na a kan screen ɗin wayar, sam bai kauce mata daga hanya ba kuma bai yi mata alamar tasan mutun yana gabanta ba.
Karo suka yi ta bugu da faffaɗar kirjinsa a in da wayar Fanan ɗin ta faɗi ƙasa saman beautiful tiles ɗin, ji kake tas karar wayar.
A razane ta ɗago da kallonta izuwa kansa, dan taga wanenen?. Shi kuwa ɗaure fuska sosai ya yi tamkar bai san me ake cewa sakin fuska ba bare murmushi.
Ganin shi haka yasa ta yi wani irin ja da baya, murya na rawa ta fara cewa. "Kayi hakuri Yah Jawad wlh ban ganka bane, kuma......".
Bata kai karshe maganar ba ta dakata sakamakon wani kallo mai kama da harara da ya watsa mata, shi dai bai san ya zai yi da Chuchu da Sarina a kan waya ba, su biyun nan idan suka rike waya sai sun baka haushi, bare ma ita chuchu mayyar hoto da videos, kana zaune baka sani ba sai dai kaga ta ɗaura maka camera a fuska tana yi maka video kamar ka aiketa, ita kuma Sarina mayyar chatting ce, shi ne yasa Yah Jawad ɗin ya kwace wayoyinsu ɗazun, sai kuma gata dana Fanan ta karɓo, kai Allah mai iko, yanzu haka idan ya karɓi na Fanan ɗin ma anjuma na Mummy ko Momma or Akka zata ɗauko, na Akka kuwa bai isa ya kwace ba, dan bala'in tsohuwar nan ba iya ta zai yi ba! Zaman ka lafiya kada ka bari Akka ta kamaka ka yi laifi, idan hakan ya faru ka shiga talatin, ta in da take shiga ba ta nan zata fita ba, ta iya faɗa. Irin dai faɗa na normal tsofaffi da jikokinsu.
Shiru ta nutsu tana muzurai kamar wata maras gaskiya, sai wani ƴan kame kame take yi. Shi kuwa ya kafeta da ido yana tunani wai me zai yi ya raba yaran nan da cutar waya ne? Dan wayar ta zama cuta a garesu.
Kunsan idan ana kallon mutun duk sai ya rasa nutsuwarsa, ko da kuwa kallon mutunci da soyayya ake yi wa mutun yana rasa nutsuwarsa bare kuma kallon neman kalar hukucin da za'ayi wa mutun, ai kunsan dole Gimbiya Chuchu ta tsargu ta rasa nutsuwarta sosai.
"Wayar waye wannan?".
Ya tambaya calmly kamar mai ciwon baki.
Miƙa mata hannunsa ya yi akan ta bashi wayar ba tare da ya sake yin magana ba.
Jiki na kerma ta tsugunna kasa ta ɗauko mashi wayar tare da miƙo mashi ita.
Bai kai ga karɓa ba call ya sake shigowa wayarsa da take a cikin aljihunsa, kira ta ɗaya da ta biyu duk sun katse, yanzu na uku ne ya shigo.
Burus ya yi da call ɗin da ta shigon ɗin, ya kai hannunsa ya karɓi wayar da Chuchun take miƙa mashi, sannan ya ce. "Anjuma ki sameni a bedroom ɗina".
Yana gama faɗar hakan yasa kai zai wuce ta.
A hanzarce ta matsa ta bashi hanya. Wucewa ya yi ba tare da ya sake kallon in da take ba.
Tsayuwa ta yi tana bin bayansa da kallo ranta a cike tab da takaicin abin da yake yi masu na kwace masu wayoyi ya hanasu sakata su wala, ji take kamar ta je ta ja kunnen nan nasa ko zata huce takaicin da yake a cikin ranta.
"Allah Yah Jawad ɗin nan ya iya mugunta".
Ta faɗa a fili tare da murguɗa baki kafin ta wuce ta nufi kofar shiga parlourn Momma. Shi kuma Jawad elevator ya hau zuwa second step.
A ɓangaren Jaish kuwa, ɗan bakin nan nasa a ɗauke da sallama kasa kasa ya shigo cikin bedroom ɗin na Momma.
A wannan karon bata a saman bed nata, ta sauko kasa samar shinfiɗin alfarma da ake yi wa gimbiyoyi a cikin bedroom nasu dan hutawa, yanayin shinfiɗin kamar da gashin ɗawisu ake yinsu, amma kuma ba gashin ɗawisu bane, carpet ne na alfarma da ake kyarasa haka kamar da gashin ɗawisu, ga bala'in laushi, sai tashin kamshi yake yi, sannan an zuba mata throw pillows manya manyan a saman shinfiɗin, dan kishingiɗa aka zuba mata su idan zata kishingiɗa sai ta yi amfani da su, ta fito a ainahin cikakkiyar gimbiyarta, alkyabbar yana kara fitar mata da kyanta sosai.
Kusa da wani throw pillow dake a gabanta Jaish ya ƙariso ya zauna a saman shinfiɗar da take ɗin kenan.
"Sannu da hutawa Momma".
Ya faɗa kansa na'a ƙasa yana kallon shinfiɗar, dama na gaya maku muguwar kunya ke gare shi, sam baya son haɗa idanu da mutane.
Gyara zamanta ta yi a in da ta kara dakewa a cikin alkyabbar.
"Jaish ka dawo lafiya? Ya gajiyar hanya ya kuma ka baro mun su Abbana?".
"Kowa yana lafiya Momma, and suna gaisheki sosai".
Bawan Allah ko part nasa bai leƙa ba, yana dawowa kawai iyayensa ya fara buƙatar gani, sune sama da komai a garesa, baya wasa da su kuma bi haɗasu da kowa ba, idan ba ya zo ya gansu ba ko wanka ba zai iya zuwa ya yi ba, shi ne yasa ya fara da fada ya duba daddynsu sannan ya taho wajen Mommansa, a kullum idan ya dawo daga tafiya haka ko daga office sai ya bisu ɗaiɗai ya fara duba suna cikin aminci kafin ya tafi ya je ya yi abin da zai yi.
"Ina amsawa ina Omar?".
Ta yi maganar tana kai hannunta saman kyakkyawar bakin gashin kansa, a hankali ta fara shafa kan nasa tana saka mashi albarka.
"Baka je part naka ba ko?". Ta sake jefo mashi wata tambayar tana mai do da kallonta a saman kyakkyawar face nasa.
Nisawa ya yi kafin ya bata amsa da. Omar yana gidan uncle Rahab babban yayanta kenan, sai ku ya ɗaura da cewa. "Ban je part nawa ba, ai kinsan ba zan iya zuwa ko'ina ba har sai na zo na ganki".
"Allah ya yi maka albarka my son, ina alfahari da ku".
Da amin ya amsa mata kafin ya ce. "Momma kina lafiya ba wata matsala in wuce part nawa?".
"Lafiyata lou Alhdulillah nake, amma da ka je gidan Yah Rahab ya kasami su Jannat?".
Shiru ya ɗan yi na a kallah one mint kafin ya ɗago da kallonsa ya ɗan kalli face nata kaɗan, sannan ya sake sunkuyar da kan nasa ƙasa, sai ƙoƙarin tuna su waye kuma su Jannat a duniyar nan yake yi? Amma ina ya kasa tuna su waye su, dan bai ma san da su ba a duniya, ƴaƴan uncle ɗin nasa ne da shi bai ma san da zamansu a duniya ba, su kuwa sun san da shi, har ma sun saka shi a cikin zuciyoyinsu, dan muguwar farin jinin ƴan'mata ke gare shi sosai, duk in da ya shiga sai ya shiga can cikin zuciyoyinsu, amma shi sam baya kula kowa. E babbar magana kenan, lallai Jaish ka cika cikakken ɗan duniya, ƴaƴan uncle ɗin nasa ne ma bai sansu ba.
"Ba dai su ma su Jannat ɗin baka sansu ba kam?".
Ta yi maganar tana aikin kallon face nasa da ya wani sunkuyar da kai ƙasa.
"Momma i don't know them". Ya bata amsa yana kai hannunsa ya riƙo nata guda ɗaya a cikin nasa.
Shiru ta yi a kan maganar su Jannat ɗin, dan tasan fin haka ma zasu aikata, dama ta yi sa'a suka san uncle Rahab ɗin kenan, kaɗan daga aikinsu su ce basu san sauran uncles ɗin nasu ba.
"Mommana zan iya tafiya?".
Yana magana ya ƙoƙarin cire mata wani dankareran tsadadden diamond ring da yake manuniyar yatsarta, zoben ya kama mata yatsa sosai ne, har ya fara cin namar jikinta.
"Meyasa zaka cire mun? Zoben Ummiee na ne fa".
"Ummm shi ne yasa kika ki cirewa har ya fara cin maki namar jikinki ko? Tom ni dai ba zan iya ganin shi yana ƙoƙarin cutar mana da ke na barshi ba, zan cewa Ummiee ta aiko maki da wani, dan nasan nata daban ne".
Ya kai karshen maganar tare da zare ring ɗin a hankali cikin dabara ta yadda ba zai yi mata zafi ba, tamkar ma bata san an cire ba, duk da kuma yake ya kama jikinta.
Murmushi kaɗan ta yi a cikin zuciyarta tana ƙara godewa Allah da ya bata ƴaƴa masu matuƙar kaunarta har haka, sun san farincikita ko bata gaya masu ba, haka zalika sun san bakin cikinta ko bata bayyana masu ba, sun san abin da take so da wadda bata so.
"Momma zan je na yi wanka na ɗan yi barci, inason gobe na fita office da sassafe, kinga almost 2 weeks bana nan, so yakamata na je office gobe dan naga me ake ciki".
"Jaish barci yamman nan fa bashi da kyau, idan ka yi shiri yanzu zaka tashi da ciwon kai".
"In Sha Allah zan kiyaye, but now am feeling to much of sleeping, zan yi kaɗan kin ji mommata?".
Ya yi maganar in a low voice sosai!.
"Tom shikenan, ka kula sosai Allah ya yi maku albarka".
Da Ameen ya amsa mata kafin ya miƙe tsaye rike da ring ɗin nata, sannan ya nufi kofar fita da wannan taku nasa cikin nutsuwa haɗe da fadanci. Da idanu ta bishi har ya fice daga cikin ɗakin, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana mai kara godiya ga Allah a cikin zuciyarta.
Yana fitowa ya iske Aunty MieMie da Gimbiya Chuchu and Zunaira suna ta hirarsu, Yah Jawad baya wajen, tamkar zai tambayi Aunty MieMie ina Jawad yake? Sai kuma ya fasa tambayar yasa kai kawai ya wuce ba tare da ya bi ta kansu ba.
Ita ma Aunty MieMie bata ce mashi ko uppan ba, dan tasa da wuya ya amsa mata, Gimbiya Chuchu dama saboda ance mata yana cikin ɗakin ne yasa ta nemi waje a parlourn ta zauna, dan haka yanzu yana fita ta yi maza ta miƙe ta nufi cikin ɗakin da murnarta. A hanzarce auta ta miƙe ta rufa mata baya, suka bar Aunty MieMie ita kaɗai, gyarawa ta yi ta kwanta a samar sofar tare da fito da wayarta ta fara latsawa.
Dai'dai Jaish zai shiga cikin elevator wasu kyawawan ƴan samari suka fito daga cikin elevatorn, kyawawa ne sosai, da gani ba tambaya ƴaƴan Gimbiya Rahilarh ne, wato Momma. Ƴan samari ne da basu fi 13 years ba a duniya, kana ganinsu kaga twins, saboda tsannin kamannin da take a tsakaninsu ta yi yawa, ba zaka iya banbantasu ba, idan ka gansu ma zaka ce mutun ɗaya ne, dan fa komai sak suke kama.
Suna ganinsa suka ɗan ja da baya suna mai risinar da kai.
Tsaresu da idanu ya yi ba tare da ya yi magana ba. Nan take suka sha jinin jikinsu suka fara ƴan kame kame.
Obaid ne ya ce. "Wajen momma zamu je dama". Sai kace an tambaye shi, tsabar tsarguwa ce kawai, da gani sun aikata wani abin da ba dai'dai ba, dan wlh idan kana neman ƴan rigima ƴan haɗa cakwakiya fitinannu marasa jin magana idan ka samesu kai kam ka gama komai, su ɗin number one ne a harkar rashin jin magana, sam basu son zaman lafiya, idan ƴaƴan sarakuna suka zo neman auren Gimbiya Sarina da Fanan, to da su Gimbiya Sarina take haɗa baki su kulla munafurci su kori ɗan sarkin, yanzu sau uku ƴaƴan manya manyan sarakuna daga masarautu daban daban suna zuwa neman auren Sarina ɗin, amma duk ta haɗa baki da su Obaid ɗin ta kori samarin, a cewarta babu class nata a cikinsu, suna da wani uncle mai suna Taheer kanin Mama wato matar king ta biyu, wannan uncle Taheer ɗin mutun ne mai izza da ji da kai bala'in girman kai na wuce misali, tun yana ƙarami yake cikin masarautar, yana nuna isa da zafin rai, ga jarumta, amma duk da haka sai da ranar su Obaid suka kusa saka shi kuka, kuma har yau babu wanda ya gane su suka yi mashi wannan ɗanyen aikin, kuma Sarina ce ta saka su, dan uncle Taheer ɗin yana bata haushi, yana takura mata da faɗa akan ta yi sallah ta dai'na taɓa waya, shi ne nan ta je ta sanya wata kuyanga daga cikin masu yi mata hidima ta ɗebo mata wani irin azabbabben mai mai zafi da aka rubuta rob a jikinsa, ɗan iskan zafi ke gare shi, haka ta kawo mata, saboda rashin imani ta saka su Obaid suka san ta yadda suka yi suka zubawa uncle Taheer ɗin wannan rob ɗin a towel da zai goge fuskarsa idan ya yi wanka, haka kuwa aka yi, dama ga shi jajir da shi kamar tsada, ai kuwa yana goge fuskarsa da towel nan ya kara yin wata uwar ja fuskar tasa, nan take face ɗin nasa ta yi ruɗu ruɗu kamar wadda ya sha marika a hannun maza irinsu commander ZAFAR, kan ka ce me idanuwansa sun yi jajir kamar jini, fitsari ne kawai bai saki a wando ba ranar, saboda azaba, sai da ya kwanta a gadon asibiti, saboda rub ɗin tana da azaba sosai, ga shi sun zuba dayawa a jikin towel ɗin.
Ƴan albarkar ƴaƴa har yau ba wanda ya iya gane su suka yi wannan aika aikar, sun iya haɗa sharri kamar ba jinin gimbiya Rahilarh ba su kam, babban abin haushin kuma muguwar shiga rai ke gare su, wlh idan ka gansu sai sun yi mugun burgeka, ka ji duniya kana kaunarsu, ga shi kuma idan suka yi laifi aka kamasu to fa ba za'a taɓa iya banbance wanene ya yi laifi a cikinsu ba, saboda tsananin kamar da suke yi, sai su yi ta rai'nawa mutane wayo, wannan ya ce wannan ne, wannan ma ya ce wannan ne, haka suke ruɗar da mutane.
"Me kuka aikata?".
Shi ne tambayar da Yah Jaish ya wurga masu.
Kallon juna suka yi, a tare suka haɗa baki wajen cewa.
"Yah Jaish bamu yi komai ba, daga part ɗin mummy fa muke"
Sam bai yarda da maganarsu ba, dan yasan hali, yasan basu zama shiru, basa ji, auta da take kanwarsu 11 years ma tana nan nutsatsiya kamar wata waliyiya, amma banda su, ba dan ba dan ba da na ce waɗan nan renon shaiɗan ne.......😅
"Idan na ji kun aikata wani abin Allah sai jikinku ya gaya maku".
Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya shiga cikin elevator abinsa.
Tsayuwa suka yi a wajen har sai da suka ga tashin elevator, sannan suka kalli juna suka kwashe da dariya a tare kamar wasu munafukai, tamkar masu aljanu a tsakar ka.
Dariya harda rike ciki suka yi, tamkar basu ne yanzu suke muzurai a nan ba. Sai da suka yi mai isarsu sannan Omaid ya ce.
"To mu idan ma mun yi laifi za'a iya gane mu ne? Ai ƙwaƙwalwar Star ne da mu, ba tunanin boss muke da shi ba, dan boss ne yake da ɗoɗaɗɗen ƙwaƙwalwa, a film kullum cikin rashin nasara yake saboda tunaninsa na banza, kullum shi ake kashewa ba actor ba, kafin mu yi abu sai mun yi tunani irin na actor, sai mun nemo hanyar da baza'a taɓa gane mumuka yi ba".
Dukar wasa Obaid ya kai mashi a shoulder ɗinsa yana faɗin.
"Amma kasan dai Yah Jaish and Yah Jawad they're acting like actors ko? Suma ba tunanin boss suke da shi ba, tunanin actors ke gare su, wlh tun da sun dawo sai mun kara dogon tunani ta yadda zamu rinƙa zulle masu".
(Ka ji wani zance, wai masu 13 years ne zasu yi wa mai 25 years wayo😂 kai jama'a su Obaid basu da kirki, kaɗan fa suka samu gadon kaifin ƙwaƙwalwar King Zuhair, amma har suke ƙoƙarin yiwa manyan kai waɗan da su suka gaji ƙwaƙwalwar da gaske wayo fisabilillahi 🤌😂 lallai kuna ruwa, mu muna gefa idan suka riƙeku zaku san cewa tunanin actors kuke yi, amma fa da gaskiyarsu, suna da kaifin basira sosai wlh, sun iya saka mutun a tarko su zulle su barshi)
"Kai Obaid mu wuce ciki hai, kada Yah Jawad ya isko mu a nan, kasan dai tun da ka kalli Yah Jaish ya wuce to Yah Jawad yana bayansa, dan kasan basu rabuwa, kullum suna a tare".
Ya kai karshen maganar tare da wucewa izuwa wajen kofar shiga cikin parlourn Mommar. Da sauri Obaid ya rufa mashi