x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 36 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 105001 words
  • 108000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 383

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ya zauna tare da fara gyara abin. Yana yi suna hira da Sweetien sama sama. Ita kuma Pretty ta zauna a saman wani ɗan madaidaicin dutse dake bakin ruwan da yake taruwa a ƙasar ƙoramar, ta zura kyawawan fararen kafafunta a cikin ruwan, har da wani ɗaga kai sama tana jin daddaɗar yanayi, ga ruwan ƙoramar yana ɗan watsuwa mata a face nata, ga kuma iska mai matuƙar daɗi, sai ta ji duniya na yi mata daɗi.

Abin busa shi kuma Kamran ya gyara da waɗan nan abubuwan ayaba guda biyun da ya ciro ɗin, ya miƙawa Sweetie guda ɗaya ya ɗauki ɗaya ya nufi wajen da Pretty take zaune. Har ya kai wajen sai kuma ya dawo ya ɗauki kwari da bakarsa. A gefenta ya zauna ba tare da ya kalli in da take ba ya sanya wannan abin busar a bakinsa ya fara busa mai bala'in daɗin ji.

A hanzarce ta juyo da kallonta haɗe da fuskarta a kansa, yana ganinta ta wutsiyar idanun, amma yaki yarda ya juyo su haɗa ido, saboda baya son ta sanya shi ya rikice.

"Kamran waye ya koya maka wannan abin?". Cewar Pretty sarki kin gani a kyale, bata ganin abu ta yi shiru, sai ta tambaya.

Ita ma Sweetie dake zaune a bayansu sai da ta ce. "Kai amma ta yi daɗi waye ya koya maka?".

Sai a lokacin ya ɗan juyo da face nasa, kaɗan ya kalli face ɗinta ya ɗan kawar da kallonsa izuwa kan Sweetie kafin ya amsa mata da. "Mammata ce ta koya mun, amma bana yi, yau ma saboda ku kawai na yi".

Matsowa kusa da shi Pretty ta yi sosai, cikin zumuɗi ta ce. "Zaka koya mun? Bani ma dai na gwada yi, zan iya ba sai an koya mun ba, ina hurawa ne kawai?".

Ɗan bakin nata kawai yake kallo, ba dai magana ba kam, ga kauɗi.

"Why not?". Ya faɗa yana mai miƙa mata abin da nufin ta busa ya ji.

Sarkin kauɗi, a hanzarce ta karɓa kamar wata kwararriyar, ta ɗauka hura iska ake yi sai ya bada sauti mai daɗi, da sauri ta kai ɗan bakinta ta fara hurawa.
Kash babu abin da ta iya, ko da ta busa iskar bakinta ne kawai yake fitowa ta ramin dayakamata ace sautin busa ta fita, ina nata ai iska ne kawai yake fita kamar ana sace tayar mota.

Turo ɗan bakinta ta yi tare da cire abin daga bakin nata tana bin shi da kallo.
"Kamran abin ya dai'na yi, ina ga ya lalace ne, sai ka sake haɗa mun wani".
Ta faɗa tana turo baki, bata yarda cewa bata iya bane, sai dai ya lalace ne, ita irin kwararriyar nan!.

Duk abin da take yi yana ganinta ta wutsiyar idanuwansa, dama yasan ba iya busawa zata yi ba, ya dai bata ne kawai dan kada ta ce ya hanata ko kuma ta ji babu daɗi, shi ne yasa ya bata, kunga idan ta gwada yaki yi ai ba zata dai ce ya hanata ba.

Guntun murmushi ya saki, hakan ba ƙaramin kara bayyanar mashi da kyansa ya yi ba, wannan da a cikin gari yake ba makawa da wannan murmushin nasa zai sa ƴan'mata masu ji da kansu, masu class dayawa su fola mashi, bashi da fara'a, amma time to time yana murmushi kaɗan kaɗan idan suna yin hira da Mammarsa, kuma ba ƙaramin kyau murmushin take yi mashi ba, sai ka ji kamar ya yi ta yi kana kallonsa ba gajiyawa.

Sosai ya yi matuƙar burge Pretty da ya yi wannan murmushin, kun san ta bata gani ta yi shiru, dan haka sai ta ce.
"Kamran ka yi kyau sosai da ka yi wannan murmushin".

Ɗan kara sakin wani murmushin ya yi yana faman sanya kifiya a jikin kwarinsa. "Da gaske murmushin ya yi maki kyau?". Ya tambaya

A hanzarce ta gyaɗa mashi kai tana faɗin. "Ka yi kyau sosai".

Juyo da waɗan nan kyawawan fararen eyes ɗin nasa ya yi a kanta, ya kalleta ido cikin ido yau kam.
"In dai ya yi maki kyau to zan rinƙa yi, amma sai kina yin abin da zai sakani yin murmushin, dan yanzu ma ke ce kika sakani yi ai".
Har ya kai karshen maganar bai kawar da kallonsa daga cikin kwayar idanunta ba, ita ma kuma bata ɗauke idanunta daga kallon nasa idanun ba.

"To yanzu me na yi da na saka ka yin murmushin?".
Ta faɗa tana mai cigaba da kallonsa sosai.

Ji yake yi kamar ba zai iya jure kallon cikin idanun nata ba, amma kuma yau ya kuduri niyyar sai ya kure kansa, sai ya kalli cikin kwayar idanunta sosai ya gani ko zata dai'na rikita shi.

"Da kika ce abin busar bata yin aiki mana, shi ne ya sakani yin murmushin, naga dai yanzu fa ina tsaka da busa tana yi na cire na baki ita, amma daga gwadawarki ɗaya ki ce mun ta dai'na aiki? Ai dole ki sakani yin murmushi".

Ɗan kara turo ɗan bakin nata ta yi kafin ta ce.
"To ai naga na busa iskace kawai take fitowa daga ramin da naka sautin busar take fitowa".

Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, sai Allah kaɗai yasan me yake tunani a cikin zuciyarsa.
"Ni yanzu ba busa nake son fara koya maki ba, ki koyi harbi da kifiya zai fi, idan kika koyi harbi da kifiya zaki rinƙa rakani yin farauta".
A wannan karon ya kai karshen maganar tare da ɗan yin ƙasa da idanunsa daga cikin nata, ya mayar da kallonsa izuwa samar wannan haɗaɗɗen gurun wuyar tata da yake cike dam dam.

(Yo bata wasa da cin abinci ba dole wuyarta ta cika dam dam ba fisabilillahi 🤌😅)

Ba ƙaramin kyau wannan tsokar gurun wuyar tata take yi mashi ba, ya kara mata kyau over, yana ɗaya daga cikin abin da yake burgesa a tattare da yarinyar, sai kuma wayonta da shegen son tambaya a kan abu, bata ganin abin da bata sani ba ta yi shiru, sai ta tambaya dan ta kara ilimi, kuma tana da gaskiya, duk abin da baka sani ba ka tambaya.

"To ka koya mun mana, ni komai ma ka koya mun ina so".

"Komai kuma?".
Ya faɗa tare da kai hannunsa ɗaya samar wuyar tata, wani ɗan kwaro da ya sauka a wuyar tata yanzu ya cire mata.

"E komai zaka koya mun".
Ta bashi amsa tana kai hannu zata karɓi kwari da kifiyar dake hannunsa.

Ita dai Sweetie tun da ba ganinsu take yi ba, sai kawai ta yi shiru tana sauraron hirar tasu, abin gwanin ban tausayi, rashin gani akwai matukar ciwo wlh, Allah mun gode maka da ka bamu idanun gani, ya Allah ka hana waɗan nan idanun namu ganin saɓonka ko kuma su haske mana izuwa wajen aikata saɓonka, kamar yadda ka yi mana ni'ima ta gani ya rabbi kasa iya aikin alkhari kawai zamu rinƙa yi da ita.

"Pretty kina nufin na koya maki har da faɗa zaki iya yi? Zaki iya koyan duk abin da Mamma ta koya mun?".
Ya yi maganar yana dawo da kallonsa cikin kwayar eyes ɗin nata tare kuma da sakar mata kwari da bakar.

"E zan iya, yanzu ma ka nuna mun ya ake amfani da wannan abin? Ga abin busar kuma ka ajiyeta a wajenka". Tana magana tana miƙo mashi abin busar.

Karɓa ya yi ya ajiye a gefen dutsen, sannan ya sanya hannunsa a saman shoulder ɗinta ya zagayo da shi ta gaban face nata, ya riko hannunta ɗaya da yake rike da kwarin nasa, sannan ya sanya ɗayar hannunsa ya kama wannan hannun nata dake riƙe da bakar.

Da kanta yasa ta haɗa kwari da bakar waje guda, duk da yana rike da hannayen nata amma bai tayata yin controlling nasu ba, ya bari ta saita da kanta, sannan suka ja kifiyar baya a tare suka saki ba tare da saita komai ba.

Sai dai ko da suka sake kifiyar sam bata yi nisa ba, sai ma ta sauka a kusa da su, hakan kuma ya samo asali ne sakamakon sake kifiyar da wuri da Kamran ɗin ya yi, ya rigata sakewa, da ya sake mata kuma kunga ya saki gudun karfin jan da ya yi, so ita bata da karfi hakan yasa da taga ya saki sai ita ma ta saki daga baya, kifiyar ta ki yin gudu mai nisa, shi kuma ya kasa iya ce mata su sake a tare ne, ya kasa iya magana, saboda wani irin yanayi da yake ji a tattare da shi, shi da kansa bai san wani irin yanayi bane bawan Allah, ga Pretty da shegen son jiki, da ta ji ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman shoulder ɗinta sai ta saki jiki ta kwanta mashi a gefen chest ɗinsa, dama can yaya, rikita shi take yi, bare kuma ta kwanto a jikinsa? Hakan yasa ya shiga yanayin da shi kansa ba zai iya sanin menene bane, duba da in da ya taso, da ni da ku dukka mun san ba zai sani ba dama, dan ma dai wani abin ba sai an koyawa mutun bane.......🥱😅

Ɗauke hannunsa daga saman shoulder ɗin nata ya yi, duk sai ya ji wani irin sanyi ta rufe shi kamar mai jin zazzaɓi, tunani ya fara yi anya Pretty zata iya koyar abubuwan da zai koya mata kuwa? Anya shi kansa zai iya cigaba da koya mata kuwa? Saboda a duk lokacin da ya haɗa jiki da ita tana sawa ya ji sanyi ta rufe shi kamar mai jin zazzaɓi, so ya fara tunanin ba lafiya yake ba, dole idan ya koma yau ya tambayi Mammarsa meyasa idan ya taɓa jikin wata ba ita Mammar tasa ba yake jin sanyi ta rufe shi? To amma jikin waye zai cewa Mammarsa ya taɓa? Shi ne tambayar da wani ɓangare na zuciyarsa ta yi mashi, To fa Kamran yana tsaka mai wuya wlh. (Bawan Allah bai san me ake nufi da........🤐😅 Na dai yi nan, bari na koma KINGDOM OF POWER, wata kila kafin na dawo Kamran ya nemawa kansa mafita😅 Mamma baki kyauta ba da baki koya mashi soyayya ba😅 wai baki san zai girma bane?🤔 25 years fa😒 gaskiya da sake😌 amma ba komai, Pretty zata banbance mashi me yake ji ai🥱 shi ma ɗan kaniya idan ha taɓa Sweetie baya jin komai sai dai Pretty😒😅)

KINGDOM OF POWER💪🔥

Baki ɗauke da sallama Yah Jawad ya shiga cikin bedroom ɗin Akka.

Akka bata a cikin ɗakin, Gimbiya Chuchu ce kawai take kwance a saman katafaren bed ɗin Akkar, daga ita sai kayan barcin jiya a jikinta, bata ciresu ba, da alama ma ko wanka bata yi ba, tana kwance ruf da ciki ta wani rungumo pillows kamar zata mayar da su cikin kirjinta.

Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kallonsa, a saman bedside drawer ya zauna tare da ɗaure fuska sosai.

Ita kuma jin sallamarsa yasa ta ƙara nutsuwa tsit tare da haɗe malaman jikinta waje guda, nan take wani sabon tsoronsa ya dira mata a ranta, gabaɗaya ta rasa me zata yi, sai ta fara ƴan kame kame.

"Good morning Yah Jawad".
Ta faɗa murya na sarkewa.

Bai amsa mata gaisuwar tata ba, sai ma kara ɗaure fuska da ya yi ya ce.
"What are you doing here da baki je kin yi shirin zuwa school ba?".

Kara tsorata ta yi, dan tasan yayyun nasu basu wasa da batun karatu, basu yi masu ta sauki in dai a kan makaranta ne.

Shagwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka, ga tsoro cike fal a ranta ta fara magana.
"Dama bana iya tafiya sosai da kafafuna ne, my legs is paining me to much, shi ne yasa na kasa iya........".

Kasa karisa maganar ta yi saboda wani irin kallo da ya wurga mata da waɗan nan idanun nasa masu rikitarwa.

"Baka gama da wancan case ɗin ba kake shirin kara yin wani laifin ko Jawad?."
Cewar Akka dake tsaye a bakin kofar toilet, ta yi magana cikin harshen larabci.

Harara ya wurgawa Akkar kafin ya ce.
"Wani case kuma? Ke wannan tsohuwa kwata kwata baki son zaman lafiya ko? Ni yanzu da sassafen nan me zaki wani kirani?".

Ita ma harara ta wurga mashi da waɗan nan farare tas ɗin idanun nata, da alama sun saba, ba yau bane farau.

"Me Jannat ta yi maka da ka ci zalinta har bata iya taka kafafunta? Anya Jawad kai kam akwai wadda zata soka kuwa? Anya muguntarku zai barku ku sami abokan rayuwa kuwa? Mutane ne sai mugunta, ina ɗaya mai mugun halin kuma yake? Ai tare na ce kuzo, dan na ja maku kunne a kan azabtarmun da kishiyoyi da kuke yi, ni ba kishin zamani nake yi da kishiyoyina ba, na da nake yi, dan haka zan iya tare masu faɗa".
Ta kai karshen maganar tare da ƙarisowa wajen nasu. A bakin bed ɗin ta zauna kusa da shi.

"Jaish kam ai kin san daidai yake dake, ni wai Akka me ma ya hanaki komawa wajensu mai rankarfe ne? Sune suke buƙatarki mu mun gaji dake gaskiya". Cewar Yah Jawad ɗin kenan.

"Innalillahi kun gaji dani, to ubanninku basu gaji da ni ba, kuma ni nan da kake gani na takalmin karfe ce mai take maza, kai ni ma kake cewa kun gaji da ni ko? Wlh nasan maganinka, maza kira mun Abbas a waya, yanzu ba sai anjuma ba ya zo ya yi mun maganinka".

Shiru ya ɗan yi mata na ƴan sakani kafin ya ce "Ina wayarki take? Ni bani da number daddy, ki kirashi da kanki".

Nan fa ta fara sababi wai dama da Jawad da Jaish sun rainata. Da dai yaga da gaske take yi sai ya fara lallaɓata dan sun rabu lafiya, kada ta je ta gayawa daddynsa ko kuma daddynsu Jaish, tasa su ɓata masu rai a banza, wannan tsohuwa ta iya tsiya ita ma!.

"Shikenan Akkarmu ta ƴan gayu, yanzu dai gaya mun meyasa kika kirani? Kin ga dai zan je wajen aiki ko farincikin Familyn ABDUL MALIK?".

"Ba in da zaka je har sai ka ɗauki Jannat ka kai mun ita asibiti an duba mun lafiyarta dana kafarta, dan na lura so kake ka mayar mun da ita gurguwa ka cuci mijin da zata aura, to wlh baka isa ba, kai ka je ka auro tsaleliya mai kafa ita kuma ka cuceta ko? Wane kai, idan ta zama gurguwa kai zaka aureta, ni ka tashi maza ka kai mun ita asibitin a duba mun ita".

Girgiza kai kawai ya yi, rigimar Akka babu mai iyawa da ita sai ƴaƴanta su King kenan, sune zasu iya biye mata.
Miƙewa tsaye ya yi yana faɗin. "To ta tashi muje asibitin a dubata ɗin, ba shikenan ba?".
Ya kai karshen maganar tare da nufar hanyar fita waje.

"Ai dawowa zaka yi ka ɗauketa, kafafun nata sun kumbura basu iya takawa, dan haka dawo ka ɗauketa har izuwa asibitin".

Dafe kansa ya ɗan yi, wannan tsohuwa gara mashi ya rabu da ita lafiya, idan ba haka ba yanzu zata kira daddynsu Jaish a waya ta ɓallo masu ruwa, ta ja mashi wani aiki, dan haka gara ya yi abin da ta ce kawai su rabu lafiya.

Dawowa ya yi kusa da gadon. Da sauri Gimbiya Chuchu ta runtse idanunta saboda wani irin kallo da ya wurga mata, kallo ne na zamu haɗu ne, irin zai kamata ɗin nan, ta ja Akka ta ɗaura mashi wahala, kuma dole ya yi idan yana son zaman lafiya, dan haka ita ma ba zai barta ba, sun saka kafar wando ɗaya kenan, ba mai kwatarta a hannunsa........ E mukam zamu ga wannan wasa ya zata kaya, namu eyes...... 👀😅

Ɗaukarta cancak ya yi, cikin sauri ya nufi waje da ita, yana jiyo Akka tana sababin tare da masifa a kan ya kula mata da Chuchunta sosai, kada ya bari wani abin ya sake samunta, kuma ya tabbatar an duba mata kafafun nan nata da kyau anyi mata abin da ya dace, sannan ya dawo mata da ita har saman gadon nan kamar yadda ya ɗauketa, sai surfa masifa take yi, ai kuwa ko sannu bai ce mata ba, sai ma sauri da ya kara ya bar room ɗin.

Suna shiga cikin elevator ya sauketa ƙasa, cikin bada umarni ya ce maza ta taka da kafafunta, kuma anjuma da daddare ta same shi a cikin part ɗinsa, zata gane kurenta.

Kuka ta saka mashi, saboda har ga Allah kafafun nata suna yi mata zafi, bata taɓa yin kneel down ba sai jiya, shiyasa suke yi mata ciwo.

"Rufe mun baki ko kuma na karya kafafun mai gabaɗaya ki huta, da kafarki zaki taka har izuwa cikin hospital".

Zaro dara daran idanunta ta yi, duk da cewa katafaren hospital ɗin a cikin masarautar take, amma tana da nisa sosai da part nasu, idan za su je sai sun shiga mota, shinfiɗaɗiyar mikekiyar titi ne daga part nasu har izuwa cikin hospital ɗin, asibitin masarautar ne, harta school ɗinsu a cikin masarautar take, sai dai ita ma tana da nisa da part nasu, sai sun shiga mota, sannan akwai manya manyan masu faɗa aji a kasar da suka sanya ƴaƴansu a school ɗin, ƴaƴan manya ne kawai suke karatu a cikinta, malamai daga manyan ƙasashe masu faɗa a ji a duniya aka ɗebosu suke karantar da yaran, from nursery one ne two Ss3, daga nan sai su fita waje karatu, haka suke yi, akwai komai a cikin KINGDOM OF POWER, ba masarauta ce ta wasa ba, ba ta kananan kai bace ba, masarauta ce da idan bata zo ta farko a duniya ba to zata zo ta biyu!, ga bala'in girma duniya guda!.

"Please Yah Jawad i can't walk with my legs, zafi suke yi mun, na tuba ba zan sake gayawa Akka ba, kuma yanzu ma ita ce fa ta tambaye ni me ya sami kafafuna, shi ne na gaya mata, amma please for give me".
Tana magana tana ruwan hawaye, wani na bin wani!.

Tamkar babu shi a cikin elevator, ya yi banza da ita, sai ma wayarsa da ya ciro ya fara latsawa abinsa.

Durkushewa kasa
End Ads