x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 349

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
gwanin burgewa, har wani shining yake yi.

Duba da dara daran idanu farare kal kal tamkar audiga, kwayar idanunsu bakin kirin har yana wani walwali, eyelashes nasu zara zara sosai like gashin doki. Ita kuma ƙaramar cikin nasu kwayar idanunta ba baki bane, hazel eyes ke gareta, kasancewar idanun nata fari ne tas, hakan ya bawa launin kwayar idanun nata damar kara fitowa sosai.

Wasu shirga shirgan dakarun yaki masu ji da lafiya da karfi ne a tsaye a ɗan nesa kaɗan da waɗan nan ƴan'matan, da alama bodyguards nasu ne, dan kamar yadda suke su huɗu a wajen, dakarun yakin kuma su uku ne a wajen, da alama kowacce jarumin sadaukin dakare ɗaya ne yake gadinta duk in da zata je, saboda yanayin yadda dakarun suka tsaya tamkar wasu saƙaguna, kowannensu yana fuskantar mace ɗaya, hakan ce zai baka tabbacin cewa kowanne da wadda yake gadi, sai ita kuma karamar cikinsu babu wani dakare da ya fuskanceta a wajen, da alama nata dakaren baya wajen ko kuma wani abin makamancin haka.

Sai hira ƴan mata ukun nan suke yi cikin harshen larabci, ita kuma ƙaramar tana zaune rike da wani hoto a hannunta tana kallo, ta ƙurawa hoton idanu sosai, kome take kallo a ciki?. Daga karshe ma sai ta sauka daga saman throw pillow da take zaune, ta koma saman carpet ɗin ta zauna, tare da kishingiɗa a jikin pillown tana mai cigaba da kallon hoton.

Wani cikakken gwarzon namiji ne ya shigo cikin wajen, sanye yake a cikin kayan yakinsa shi ma, baka iya ganin face nasa saboda hular kayan yakin nasa dake a kansa, yana tafiya ne irin na cikakkun gwarazan maza, ga tafiyar tasa cikin wata iriyar nutsuwa da kamala, sam babu hayaniya a tattare da shi, sai wani irin dake a tare tattare da shi, yana buƙe kamar wani zaki.

Hannunsa na rike da wata kyakkyawar kwando mai ɗauke da fruits a cike a cikinta, fresh fruits ne mai matuƙar kyan gani a idanun. A gaban ƙaramar cikin nasu ya zo ya tsungunna tare da ajiye mata kwandon fruits ɗin a gabanta, cikin girmamawa ya ce.

"Ranki ya daɗe ga shi nan".

Ƴar yarinya da bata wuce 11 to 12 years ba, kanta ta ɗago daga kallon hoton da take yi tare da sauke dara daran Hazel eyes nata a kansa.

Cikin sauri ya kara risinar da kansa ƙasa alamar girmamawa.

"Banace maka ka daina ce mun ranki ya daɗe ba? Ka kira su Aunty MieMie da ranki ya daɗe, ka kira su Aunty chuchu da ranku ya daɗe, nima da nake ƴar yarinya sai ka wani ce mun ranki ya daɗe? To ni bana so, kawai kace mun auta ta ko kuma ka kirani da baby kamar yadda uncle Taheer yake ce mun".

Ta yi maganar cikin kwararriyar laraɓcinta, ga ta da zaƙin murya sosai, voice nata gwanin daɗin saurara.

"Kiyi hakuri ranki ya daɗe, zan gyara". Ya bata amsa da yaren da ta yi mashi magana, ya yi maganar a sanyaye cikin nutsuwa.

"Ba zaka gyara bakam, ga shi yanzu ma ka sake ce mun ranki ya daɗe, to shikenan tun da ba zaka canza hali ba".

Ta kai karshen maganar tare da ɗaukar ƴar wukar da yake a cikin kwandon fruits ɗin da kuma Apple guda ɗaya da nufin ta fara yankawa ta ci.

Waɗan nan ƴan mata guda ukun da suke wajen har suna rige rigen karɓar wukar daga hannunta tare da Apple ɗin, shi ma wannan dakaren nata ya yunkura zai karɓi wukar ne sai ya ga ƴan uwanta sun riga shi, hakan tasa sai ya koma ya nutsu.

"Ke auta so kike yi ki yanke hannunki uncle Taheer da daddy su bamu hukunci ko?".

Cewar ƴan matan, sun yi maganar har suna haɗa baki.

"Kai Aunty Chuchu ni fa yanzu na iya yanka fruits, baki ji uncle Taheer ya ce yakamata nima na fara koyan takobi bane? Ya ce na girma yanzu".

Miƙewa tsaye dakaren nata ya yi tare da tsayawa a ɗan gefenta kaɗan, kamar wani mutun mutumi, kun san haka dakarun yaki suke tsayuwa dama, cike da jarumta sosai, musamman idan aka basu kula da mutun mai mahimmanci, ai sam basu zama, Auta tana da matuƙar mahimmanci sosai ga kowa da yake gidan, ƴa ce ga Gimbiya Rahilarh, wato amaryar King Zuhair kenan, ƴar ta ce, shi ne yasa ma ta fisu kyau, dan ita gaba da baya dukkan jinin larabawa ne babu mix, kada ku manta mamanta ƴa ce ka sarkin Dubai, King Zuhair ma nasan baku manta tushensa ba, so ita auta bata da mix ko kaɗan, suna ji da ita, suna sonta sosai, shi ne ma yasa King Zuhair ya wakilta assistant commander mayakansu wato HOORAIN da ya kula da ita, ya zama shi ne mai bata tsaro, tsabar son da yake yi mata ne ya yi mata wannan gata, duk sauran ƴaƴansa normal mayaka ne suke tsaronsu, amma banda ita auta, ita assistant commander da kansa ne yake tsaronta, da da dama ma da commander za'a sanya ya yi tsaronta, duk wani motsin da zata yi ya kula da ita sosai, idan ta yi koda tuntunɓe ne zai sha hukunci.

(Kai irin wannan soyayya haka, to Allah muma ka yi mana arzikin da zamu yi wa ƴaƴanmu fin haka ma🤲)

"Ba wani girman da kika yi, ki bari mu yanka maki ko a kira kuyangu su yanka maki ki sha".

Cewar ɗaya daga cikin ƴan'matan, wadda aka kira da Aunty Chuchu kenan.

Ɗan turo baki ta ɗan yi kafin ta ce. "Amma Aunty Chuchu kin san ni bana son na kuyangu ko?"

Gyaɗa mata kai Aunty Chuchu ɗin ta yi alamar e ta sani

"Tom shikenan, ni bari ma na je wajen daddy a faɗa kafin ku gama yankawa, dama nace mashi zan je hutu wajen Mai rankarfe, this time Dubai zan tafi, bari na je na tuna mashi da batun hutu nawa, dan gobe nake son a kai'na". Still cikin harshen larabci ta yi maganar tata, da voice nata na yara mai shegen daɗi.

Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye, tana da tsawo dai'dai gwargwado, ba gajera bace ba, kafarta na sanye da cover mai bala'in kyau launin gold color miƙewarta tsaye yasa tsananin kyanta ya kara bayyana sosai, kyakkyawa ce ajin farko.

Wucewa gaba ta yi HOORAIN ya rufa mata baya, yana taku na kikakkun jarumai waɗan da jininsu yake a tsananin tafashe, Hoorain baya magana, tamkar wani kurma haka yake, sai iya cika aiki cikin zafin nama.

Da kallo su Chuchu suka bita da shi har ta fice daga cikin wajen.

Duk in da ta zo wucewa sai manya manyan dakarun yaki sun sunkuyar da kansu ƙasa alamar girmamawa a gareta, idan kuma bayi ne sai sun zube gwiwowinsu a ƙasa haɗe da sunkuyar da kai dan girmamawa, ba zasu ɗago kansu ba har sai ta wuce, gata wata ƴar firitu a wajen, amma haka ake bata wannan girma dan dole, kun san yadda gidan sarauta take, musamman sarauta mai cike da girma irin haka, girmama ɗan sarki dole ne ga bayi, koda kuwa jariri ne.

Tafiya take cikin nutsuwa har izuwa kofar tampatsetsen babban fadar mahaifin nata, wasu jiga jigan zataran matasan dakarun yaki ne suke gadin kofar shiga fadar, suna shirye cikin kayan yakinsu, tsayawa zayyana maku haɗuwa da kyan kofar shiga cikinta kawai ma ɓata baki ne, dan ba zata faɗu a baki ba.

Fada ce irin na hamshaƙan sarakuna masu faɗa aji a duniyar mulki, sai dai kuma wannan fada ta fita daban a duk cikin fadojin da kuka sani a duniya, saboda fada ce ta manya.

Tun da auta ta saƙo kafarta, da Sallama ta fara cin karo, Sallama wani bawan sarki ne wanda kamar matsayin PA yake, duk wani mai son ganin sarki in ma a cikin gida ko kuma a waje or a fada to dole sai ya bi ta hannun Sallama, idan ba haka ba ba zai sami damar ganin sarki ba, kun dai san yadda matsayin PA yake ko?, To haka matsayin Sallama a cikin fadar sarki yake.

Ganin Gimbiya auta ce tasa Sallama ya fara washe baki tare da fara zuba mata kirari.

"Takawarki lafiya ƴar sarki jikan sarki, mace mai farar aniya tare da farar zuciya, farar mace alkyabbar mata, tauraruwa a cikin taurari, ƴar gata kuma ƴar lelen kowa dake a cikin masarautar nan, Queen Zunaira taka a sannu masu kasar Dubai da kewaye".

Yana zuba mata kirarin ne tare da ɗaga hannunsa ɗaya sama alamar jinjina, ya kuma sunkuyar da kansa kasa alamar girmamawa.

Duk wanda yake son zaman lafiya a cikin KINGDOM OF POWER to ba shakka dole ya kaunaci Gimbiya Zunaira, dan King Zuhair ya fi kaunarta sama da yadda yake son kansa, hakan tasa sallama ya zage yake ta zuba mata kirari babu kakkautawa, dan ya faranta ran sarki.

Da yake kamar yadda Sallaman ya faɗa, ita ɗin macece mai farar zuciya, ga kyauta kamar babanta, ga san jama'a da saukin kai, duk ƴaƴan KING ZUHAIR suna da masifar jiji da kai haɗe da izza ta gidan sarauta, kunsan yadda jikin sarauta suke, iya fadanci, nuna tsantsar isa da takama, izza da nuna fifiko, to duk haka ƴaƴansa suke except auta, ita kaɗai ce mai saukin kai tare da ɗaukar mutane da daraja a cikinsu, sai kuma Gimbiya Chuchu wadda ita sam bata da wata matsala, bata da jiji da kai, bata ma da yawan magana, in kaga tana magana to da su Gimbiya Zunaira ɗin ne, ban da haka ita bata kallon mutane ma bare ta yi masu walaƙanci, ita kuma auta tana tsayawa ta saurari mutane ɗaya bayan ɗaya, yanzu ma tsayuwa ta yi tare da kai kallonta cikin ainahin fadan, sannan ta furta cewa a bawa Sallama kyautar kujerar Makka, daga haka ta wuce ciki abinta, da sauran ƴan uwanta ne ko kallon arziki sallama ba zai samu ba bare har su yi mashi magana, akwaisu da izzar bala'i, musamman ma wata yar autar mai suna Gimbiya SAREENA, ta fi kowa iya jiji da kai tare da nuna izzar sarauta, isa da taƙama, kamar ba zata mutu ba

Kai tsaye saman stage da mahaifinta yake auta ta nufa, sai faman duƙar da kai ƙasa duk wasu mayakan dake a matsayin bodyguards a cikin fadar suke yi, alamace ta suna girmamata.

A saman wajen stage da sarki yake daga ta bayansa akwai wasu dakarun mayaka guda biyu wanda ake kiransu da sunan sarakan Figini, su ne masu yi wa sarki firfita da maficin gashin jimina, sai fifita suke yi mashi da wasu tampatsetsa tampatsetsan maficin gashin jimina.

Daga ta can gefen kujerar sarki da iyalansa kuwa, wasu hamshaƙan sofa sets ne a wajen, su kuma kujerune waɗan da aka ware na zaman malam liman, wato limamin Fada, sai Galadima, yana cikin majalisar sarki, Madaki, Yana daga cikin ƴan majalisar sarki shi ma, sai Sarkin Dawakin tsakar Gida, ko ban faɗa ba kun san shi ne mai jagorantar masu kula da dawakan gidan sarki.

Daga kasar stage ɗin ma akwai wasu sofa sets tantsama tantsama, wasu daga cikin manyan fada ne suke zama a kai, irinsu sarkin gida, mai jagorantar masu shige da fice na cikin gidan sarki kenan, sai sarkin hatsi, mai kula da wajen ajiye kayan abinci, shi ne kuma mai fitar da zakkar sarki idan lokaci ya yi, duk wata sadakar kayan abinci da za'ayi dole sai da saninsa, komai dai da ya danganci abinci shi ne mai kula da shi, ko in ce jagoran ma'aikatan da suke kula da su, akwai ɗan iya, mai rerawa sarki waƙa kenan, yana da zazzaƙar murya, dan mai murya sosai ake nemowa, mai kuma ilimi sosai, sannan akwai sarkin bayi, ko ban faɗa ba kun san shi ne mai kula da duk wasu bayi da suke a cikin wannan Masarauta, sai Kasheka, wanda shi ne yake kasancewa a tare da sarki kullum, duk in da sarki zai je dole Kasheka ya kasance a tare da shi, sai amintattcen sarki, wanda wannan muƙami ne da ake bawa wanda sarki ya aminta da shi sosai, still akwai kilishi, kilishi wani bawan sarki ne wanda alhakin yi wa sarki shimfiɗa ya hau wuyansa. A duk gurin da sarki zai zauna, to kilishi ne yake yi masa shimfiɗa, imma a cikin Masarauta ko a wajenta, sai sarkin mayaƙa wato commander ZAFAR, shi ma a cikin fada ya fiya yawan zama, domin idan za'a fita yaki ko wani abin ya sani.

Akwai dai muƙa mai da dama a cikin fadar sarki, amma waɗan nan sune manyan muƙaman, na kawo maku su ne kuma dama dan ana karatun littafi ne domin a samu karuwar ilimi, so ko baki taɓa shiga fadar sarki ba idan kika karanta littafin nan zaki san abubuwa da dama da suka danganci sarauta, shi ne amfani karatun dama, shi ne kuma yasa nake ƙoƙarin ganin na faɗaɗa maku komai dan ku sani ku sami karuwar ilimi.

Kasancewar wajen zaman sarki waje ne da kowa ya sani na daban ne, tampatsetsan kujera ne na alfarma mai zaman mutun biyu, sai kuma na iyalansa dake a gefe da gefen nasa, wanda idan sun zo cikin fada zasu zauna a kai, babu wanda ya taɓa zama a saman kujerar sarki sai sarkin, koda kuwa matansa ne basu zama, shi kaɗai yake zama abinsa, amma saboda son da yake yi wa Auta, idan ta shigo a gefensa take zama, saman kujerar tasa.

Yanzu ma da ta shigo a gabansa ta zo ta tsugunna, cikin girmamawa tare da ladabi da biyayya ta sunkuyar da kanta ƙasa, cikin sanyin murya ta yi mashi barka da hutawa, while shi kuma Hoorain yana waje bakin kofar fadar yana jiran fitowarta, dama baya binta ciki idan suka zo, a waje yake tsayawa abinsa.

King Zuhair duk da yana jikin naɗin farar RAWANIN sarautarsa, ya sha alkyabbarsa mai bala'in tsada, hakan ba zai hana ka ga madarar kyau ba, kyakkyawar gaske ne shi ɗin, namiji mai cikar haiba da kamala, ya hakince a saman kujerar nan tasa yana gudanar da mulki bisa gaskiya da amana tare da adalci.

Ƙasa ƙasa ya yi magana ta yadda ko masu yi mashi fifita na bayansa ma basu ji me ya ce ba, duk da cewa yana cikin naɗin RAWANIN mai kamar nikaf. Auta dake a gabansa ne kawai ta iya jin abin da ya faɗa, dan haka sai ta miƙe cikin nutsuwa ta koma kusa da shi ta zauna tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya.

"Me yake tafe dake Mamana?". Ya sake yin magana ƙasa ƙasa cikin nutsuwa, harshensa akwai kaifi sosai, maganarsa tana da kaifin da idan ta ratsa dodan kunne sai ganganjiki ta amsa, dama akwai masu irin wannan murya a cikin jama'a, sai dai ba kasafai aka cika samunsu ba, mutun ne da zaku ji muryarsa mai kaifi, idan ya yi magana koda cikin nutsuwa ne sai masu sauraronsa sun shiga taitayinsu, koda kuwa raha yake yi da su, saboda kaifin harshensa sai kaga suna tsoron yin magana da shi, ko da ba mafaɗaci bane, bare kuma shi King Zuhair da ya kasance jinin Modarawa, ai kunsan faɗa dole, zafin rai dole, dan a jinin Modarawa dai babu rago mara zuciya, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa KING baya magana da ɗaga murya, dan tsaro, shi kansa yasan yana da kaifin harshe, so ɗaga muryarsa ga al'umma haɗari ne babba, zata iya sa wani da bai ji ba bai gani ba ya mutu saboda tsoro.

"Daddy dama na zo ne na gaisheka".
Ta faɗa a nutse.

Ba tare da ya kalli in da take ba, dan suna jere ne wajen guda, cikin sanyin murya ya amsa mata da.

"Anya kuwa autana gaisuwace ta kawo ki?".

Ɗan guntun murmushi ta yi wadda sai da dimple nata suka lotsa, fararen hakwarantan nan suka bayyana, ga wani ɗan siriri wushirya a tsakanin hakwaran nata, kyau iya kyau ya kara bayyana dalilin wannan murmushin.

"Kai daddy shi na zo yi mana". Ta faɗa a ɗan shagwaɓe.

"Ai nasan halinki ne, haka kawai rana tsaka baki zuwa wajena, keda wani lokaci ma sai na sanya an nemo min ke, to yanzu dai gaya mun kawai me kike so kika zo a dai'dai wannan lokacin?".

Ɗan kwanto da kanta a saman shoulder ɗinsa ta yi tana mai cigaba da murmushi, daddyn ya gama ganota

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI.








🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 6/7/2024.....✍️📚🌹






🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️






E____________8🔥





Ɗan kwanto da kanta a saman shoulder ɗinsa ta yi tana mai cigaba da murmushi, daddyn ya gama ganota.

"Daddy dama batun zuwana wajensu mai rankarfe ne fa".

Ta yi maganar kamar wata mai in'ina.

"This time kuma can kike son zuwa?". Ya faɗa yana fitar da hannunsa ɗaya dake a cikin alkyabbar tasa, lallauran kumatunta ya fara shafawa.

"Daddy ba Mummy ta ce Yah Omar zai kammala secondary school ɗinsa this time ba? Kuma ta ce yanzu zai dawo nan da zama idan ya kammala, shi ne zan je mu dawo a tare da shi ai".

"Ya kammala dai ba zai kammala ba mamana, shirye shiyen dawowa ma yake yi, sai dai ki je ki tarosa ku dawo a tare".

Shiru ta ɗan yi kafin ta sake cewa. "To daddy yanzu a nan zai cigaba da karatu ko?".

Jinjina mata kai ya yi alamar e, da alama bai cika son yawan magana sosai ba, dan daga yanayin amsa mata ɗin da yake yi zai nuna maka cewa sam baya son motsa bakinsa, dan ma ita ce, ba dan haka ba da ba amsawa zai yi ba.

Wani dakakken jarumin mayaki ne ya shigo cikin fadan, cikin girmamawa ya duƙa dan gaisuwa ga sallama, sannan ya sanar da shi cewa Sarkin yammaci
End Ads