karo da shi before ki iso nan? And ina ɗankwalinki? Kin kalli irin dressing da yake a jikinki kuwa?".
Kasa jure neel down ɗin ta yi, saboda zafin da gwiwowinta suke yi mata, hakan yasa idanuta suka ciko tab da kwallah, ta kuma kasa iya dakatar da kwallar daga zuba mata a saman lallausan kumatunta, tana ji tana gani suka fara zubowa wani na bin wani kamar an buɗe fanfo, ita yanzu me zata ce mashi? Shi ne abin da take tunani, tsantsar danasanin zuwanta part ɗinsa ne a cike a cikin ranta, ji ta yi gabaɗaya haushinsa ma take ji.
"Am i not talking to you? Amsa me, tell me the reason why kika fito da kayan barci and without ɗankwali?".
Ya faɗa still kallonsa na'a kan screen ɗin wayarsa.
"Am so sorry Yah Jawad, na manta ne na fito a haka, amma ba zan sake ba, na tuba".
Yadda ta yi maganar daga ji kasan a kule take har wuya da haushi.
Jin yadda ta yi maganar ne yasa ya dawo da kallonsa a saman fuskarta. Ganin hawaye suna bin saman kyakkyawar kumatun nata ne yasa ya ɗan..............
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
Jin yadda ta yi maganar ne yasa ya dawo da kallonsa a saman fuskarta. Ganin hawaye suna bin saman kyakkyawar kumatun nata ne yasa ya ɗan zaro dara daran idanuwansa waje.
"Bana ce kada na kara ganin hawaye a saman face naki ba? What are you crying for?".
Jikinta na kerma ta nuna mashi wajen gwiwowinta da suke yi mata raɗaɗi tare da zogi.
"Yah Jawad am tired for this kneel down, my kneel and my all leg's is paining me, please for give me, ba zan sake ba fa".
Tana magana hawayen suna mai cigaba da bin kuncinta.
Shiru ya ɗan yi na tsawon a kallah 1 mins, ganin hawayen nata na kara tsananta ne yasa in a low voice kamar mai raɗa ya ce.
"Firstly tell me da su waye kika haɗu before you reach here?".
Cikin kuka ga voice ɗin nata baya fita sosai ta ce.
"Only uncle Taheer ne kawai".
Shiru ya ɗan yi na a kallah two mins kafin ya ɗan kawar da kallonsa daga kanta, sannan ya ce mata.
"Okey start up, ki zauna a saman bedside drawer nan".
Ai tun bai kammala kai karshen maganar ba ta yi maza ta miƙe, gwiwowin nata sun yi jajir da su, saboda hasken fatarta, ga shi luwai luwai, ba zata iya jurar wahala ba komai ƙanƙantarta.
Da kyar ta iya ƙarisawa wajen bedside drawer ta zauna tare da yin ƙasa da kanta tana mai cigaba da ruwan hawayenta.
"This tears for what again?".
Ya faɗa ba tare da ya kalli in da take ba, da alama ta wutsiyar idanu ya saci kallonta har yasan bata dai'na ruwan hawayen ba.
Kyawawan fararen tafukan hannayenta ta kai saman face ɗin nata, share hawayen nata ta farayi tana mai jin haushinsa sosai a ranta, ya wani zo ya saka mata kafafunta suna yi mata ciwo a banza dan mugunta.
"I will going to give you your phone now, but idan kika bari na sake kamaki a kan this case babu mai karɓarki a hannuna, kin sani ai, kinga irin punishment da nake bawa su Sarina ba? Irinsa zan yi maki kema, now ki wuce ɗaki kada ki kuskura ki sake fitowa sai da safe".
Ya kai karshen maganar tare da miƙo mata wayar tata.
Hannunta sai karma yake yi ta kai hannu ta karɓi wayar tare da faɗin.
"Thank you, In Sha Allah I won't do it again".
Shiru ya yi bai sake yin magana ba, haka zalika bai sake ɗago idanu ya kalli in da take ba, sai dai yasa hannunsa ya yi mata nuni da hanyar kofar fita, alamar zata iya tafiya.
Duk da kafafunta suna yi mata zafi hakan dai ta daure ta miƙe a hanzarce dan ma kada ta kara yi mashi wani laifi, dan tasan halinsa sarai, baya yi wa su Gimbiya Sarina ta daɗi idan ya rikesu, idan suka yi laifi yana azabtar da su dai'dai gwargwado, dan haka tasan muguntarsa sarai a kan wasu, ƴaƴan King Zuhair ɗin ne dai basu taɓa shiga hannunsa ya basu punishment ba sai yau ita Chuchu ta shigo hannunsa, kuma da alama tana da sa'a ya yi mata hukunci sassauƙa.
Kofar fita ta nufa a hanzarce, tana tafiya tana jan kafafu tare da ɗan ɗingisasu. Ta wutsiyar idanu ya bita da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa, har sai da ta fice daga cikin ɗakin ne ya mai da kallonsa full a saman screen ɗin wayar tasa ya cigaba da abin da yake yi, daga karshe ma sai ya miƙe ya fice daga cikin bedroom ɗin izuwa na JAISH, dan wani lokaci ma a tare suke kwana, so sai ya tattare wayoyinsa dana Fanan and Sarina ya fice da su gabaɗaya.
A bangaren JAISH ɗin kuwa, bayan sun kammala cin abincin daren, wanka shi ma ya shiga ya yi kamar yadda Yah Jawad ya yi, sannan ya shirya cikin wasu kaya na shan iska masu bala'in kyau da tsada, ya fito izuwa wajen daddynsu.
Haɗaɗiyar elevatornsu ya haye izuwa part na King, dan daddyn nasu ne ya kira shi a kan ya zo part ɗinsa ya samesa, ya yi matukar kyau sosai, sai tashin daddaɗar kamshin yake yi kamar anyi ɓarin perfume a jikinsa.
Ƙasa ƙasa ya yi sallama a bakin kofar shiga babbar parlourn King, in da su Momma suke haɗuwa kenan, a baƙin kofar da akwai wasu jiga jigan zataran warriors guda biyu da suke tsaron kofar.
Babu kowa a cikin parlourn, sai wani fitinannen kamshi da ya bule ko'ina a cikin parlourn, ta ko'ina tsab tsab tamkar babu wanda ya taɓa taɓa komai dake cikin parlourn, da alama masu yi wa part ɗin hidima kwararru ne sosai wajen iya gyara.
Kai tsaye wata siririyar stair case ya nufa, ita kanta wannan stair case ɗin abar kallo ce, ta haɗu iya haɗuwa! Ga wasu kwayayen lantarki dake bada wuta mai haske a jikin duk wani step ɗaya, hakan ba ƙaramin kara fito da golden color pentin da yake wajen ya yi ba, sai ya yi tamkar ginin ɗanyar gold, abin ya ƙayatar matuƙa, ga wasu decoration na wasu haɗaɗun tsararrun flowers dake a manne a jikin bangon wajen stair case ɗin, abin dai sai wanda ya gani, amma fa ba'a magana wajen haɗuwar part ɗin King.
A bakin kofar karamar parlourn sama ya yi sallama. Ita ma parlourn ta ƙawatu da kayan alatu na more rayuwa wadda baki ya yi kaɗan ya zayyanosu. Ɗakuna ukku ne a cikin parlourn, sai dai da alama ɗayan ɗakin ganawa da baki masu matuƙar mahimmanci ne, duba da yanayin tsarinsa ɗauke da luntsuma luntsumar sofas set uku launika daban daban, ash, golden and milk, ga wani shegen rug a tsakiya, hakan yasa ya yi kama da ɗakin ganawa da manyan baki, biyun kuma bedrooms ne.
Ɗakin dake a tsakiya ya nufa, yana taku cikin jarunta tare da nuna izzar sarauta, da alama hakan a jinunsu take.
Sallama ya yi wa daddyn nasa a bakin kofar shiga bedroom ɗin.
An ɗauki a kallah two mins kafin daga ciki king ya amsa mashi sallamar tare da yi mashi izinin shigowa.
Shiga cikin ya yi bakinsa a ɗauke da siririyar sallama again. Hmmmm bedroom na King aljannar duniya kenan, ga shi ya sha gyara, iya katafaren King bed ɗinsa ne kawai a cikin bedroom ɗin, sai wasu tsala tsalar shinfiɗu na alfarma da suke har guda uku ta kowani ɓangare a cikin bedroom ɗin, da yake ɗakin yana da bala'in girma sosai, hakan yasa akai mashi shifiɗu na wasu shegun tsadaddun Turkey carpet masu bala'i laushi, kyau da kuma tsada har guda uku, tiles na floor ɗin bedroom ɗin kamar glass yake, sai kyalli yake yi fari kal da shi, dressing room na King glass ne mai kama da transparent, daga ciki shi zai iya hango na waje wanda ya shigo cikin bedroom ɗin, wanda yake a cikin bedroom ɗin kuma ba zai iya ganinsa ba, haka yanayin tsarin dressing room ɗin yake, ya tsantsaru iya tsantsaruwa, curtains for windows and doors ma kawai ya isa ya sanya mutun ya wuni yana kallonsu ba tare da ya gaji ba, saboda haɗuwarsu.
Kusan yanayin design na bed ɗin nasa iri ɗaya dana Momma, sai dai nasa ya fi nata girma sosai, da kuma banbancin colors, nasa color dark navy blue ne sosai, idan ka gansu ma kace bakakene, so haka shinfiɗun carpet dake a tsakiyar room ɗin ma yake, kana taka saman carpet ɗin nan kafarka zata lume ciki lausasan gashin da aka kawata kwalliyar carpet ɗin da su, tamkar gashin jimina, da yake mafiya yawan shinfiɗun gidan sarauta dama da gashin jimina ake yinsu!!. Kofofi biyu ne a cikin room ɗin, daga na balcony sai na bathroom! Sai drawers dake gefe da gefen bed ɗin wanda aka ɗaura wasu ƙayatattun lamp masu kyau da kuma hasken gaske, babu dressing mirror a cikin room ɗin, da alama yana cikin dressing room.
King na zaune a tsakiyar katafaren bed ɗinsa, sanye yake da kayan barci, da alama ya yi shirin kwanciya ne, da kamshin perfume ɗin jikinsa da kuma daddaɗar kamshin perfume na room ɗin sai suka haɗu suka bada wani irin kamshi mai kwantar da hankali, ga kuma sanyin Ac mai sanyaya zuciyar mai shaƙa. Sanye yake da wani haɗaɗɗen siririn farin glass a face nasa, ya tasa wata shegiyar tsadaddiyar laptop a gabansa yana aiki, dama idan baku manta ba na gaya maku shi King architecture ne, so da alama wani aiki yake fitarwa a cikin laptop ɗin, ga kuma wasu envelope wadda a kallah zasu kai guda ashirin a saman bedside drawersa ta kusa da in da yake zaune.
A kusa da shi Jaish ya zauna yana ɗan yamutse fuska kamar wadda yake jin barci, hannunsa ya kai tare da ɗauko pillow babba guda ɗaya daga cikin pillows da suke jere a bayan King ɗin, ya ɗaura a saman laps ɗinsa yana mai do da kallonsa a saman laptop ɗin na daddyn nasu.
"Good evening my lovely dad". Ya faɗa a sanyaye.
"Evening my pleasure". King ya bashi amsa cike da so da kauna!.
"Daddy what are you doing by this time around? You have to be sleep ka hutawa ranka, since morning you're working like watch, yanzu dare kam ka huta mana, and da sassafe kuma zaka sake fita fada ka yi attending mutane fa, gaskiya ka kwanta ka huta, koma wani aiki kake yi ka barshi ko kuma ka kawo na yi maka".
Nisawa ya yi kafin ya ce. "Jaish i can't sleep now, a duk lokacin da naga al'umma cikin damuwa da tashin hankali bana iya barci har sai naga abin da zan iya yi a kai".
"But daddy hakan zai yi affect na lafiyarka, at least ka rinƙa samun 12 hours kana barci".
Wasu envelope guda goma King ɗin ya kwaso daga saman bedside drawersa, miƙa mashi su ya yi yana faɗin.
"Take this envelope, na ƴaƴan talakawa guda goma ne, ka nutsu ka duba takardun da kyau, naka ne, ina son ka bawa biyar daga cikinsu aiki a companynka, biyar kuma karatun surgery dr suka yi, so ka miƙawa Raj su ya sama masu aiki cikin gaggawa, bana son su ɓata lokaci basu fara aiki ba, dan mu duk ɗan talakan da ya kawo kukansa gabanmu da izinin Allah ba zai tashi daga gabanmu ba sai mun saka shi dariya, dan haka a sama masu aiki cikin gaggawa, aiki kuma mai matuƙar kyau sosai wanda zai sa su ji suma masu gata ne a duniya".
Ya kai karshen maganar yana mai cigaba da zanen da yake yi, wani katafaren ginin gidan marayu mai haɗe da kamarantar boko da islamiya a kusa da gidan yake zanawa, ga kuma masallaci ta gefe guda, duk na marayun ƴaƴa ne da yake son gina masu, domin marayu sun yi yawa ba wajen zama, a kallah irin wannan zane sun kai biyar yanzu ya yi, kuma kowani gida zata ɗauki yara marayu sama da 500, ga ingantaccen abinci da wajen kwana mai rai da lafiya da zai sama masu, makaranta kyauta, suma zasu yi karatu kamar sauran ƴaƴa masu iyaye kuma masu gata, komai a kyauta, abin ban sha'awa kuma dukka filayensa ne ya sadaukarwa da marayun dasu, King Zuhair ba dai farar zuciyar taimako ba, yana kaunar jama'arsa, shiyasa suma suke kaunarsa kuma suke kaunar mulkinsa, shi ɗin baya ne goya marayu, aiki yake yi tukuru ba dare ba rana duk domin yaga rayuwar jama'arsa ta inganta, idan aka ce maku farar zuciya ma ai an rage, King Zuhair ya wuce haka, baya kyaman talaka! Kowa nasa ne sai wanda ya kawo mashi wargi, dan baya ɗaukar raini! Yanzu zai haɗawa mutun jini da majina! Ga shi idan ya kamaka ka yi laifi babu sonkai babu komai a nan take zai yanke maka hukunci ba tare da ɓata lokaci ba, kamar yadda jininsa take a tafashe haka yake wajen zartar da duk abin da zai yi babu ɓata lokaci!.
Sallamar Yah Jawad ce ta sanya suka mayar da hankalinsu a kan kofar shigowa. Prince Jaish ne ya amsa mashi sallamar yana mai dawo da kallonsa a kan King ɗin, domin ya ji me zai ce, shin Jawad ya shigo ne ko yaya?.
Kyakkyawar gerarsa ɗaya king ɗin ya ɗaga mashi alamar ya ce da Jawad ɗin ya shigo. Ba ɓata lokaci ya sanar da shi hakan.
Sake kwankwasa siririn sallama Yah Jawad ya yi kafin ya shigo ciki. A kusa da King ta ɗayan bangaren shi ma ya zauna, sai yazamana king yana a tsakiyarsu.
"Barka da dare daddynmu, ya hutu?". Shi ne abin da Yah Jawad ya faɗa.
"Barka dai my son, ya aikin barci?". King ya faɗa yana gyara glass dake a face nasa!.
"Daddy barci kuma? Mu ɗin?".
Jinjina masu kai ya yi yana faɗin. "Kuɗin fa, ku gaya mun aikin da kuke yi idan ba barci ba? Kai Jaish rabonka da office naka tun yaushe, ka wuce wajensu Akka ka yi zamanka ko? Duk na zuba maku ido ne ai ina son in ga gudun ruwanku".
"Kai daddy Allah kaiko, to mu me zamu yi da ya wuce hakan?". Cewar Jaish kenan, ya yi maganar kuma yana ɗan satar kallon Yah Jawad, while shi ma Jawad ɗin shi yake kallo.
Sauran envelope da suke a saman bedside drawersa ya kwaso tare da miƙawa Yah Jawad yana faɗin.
"Zan sama maku abin yi ai nan bada jimawa ba, sai ku rage yawace yawacen ƙasashe da kuma barci, yanzu dai Jawad ga wannan, takardu ne na haziƙan student masu ilimi da mayar da himma a makaranta, ga fasaha, na duba result ɗinsu da suke a ciki dukka, yara ne da samun irinsu cikin al'umma ba karamar nasara bace, amma kai ma ka nutsu ka duba komai da kyau zaka gani, akwai guda biyu da suke da master a ciki, sauran dukka degree certificate ne, and takwas daga cikinsu ne civil engineers, biyun akwai computer engr ɗaya, sai kuma business, so su waɗan nan civil engineers ɗin idan akwai fili ka basu aiki a companynka, saura takardu biyun kuma ka bawa Abbas su ya sama masu aiki cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba".
Duk wannan magana da yake yi hankalinsa na'a kan laptop dake a gabansa, aikin da yake yi kawai ya ƙurawa waɗan nan dara daran idanun nasa irin na su twin's Obaid and Omaid.
Karɓar takardun Yah Jawad ya yi yana mai kara jinjinawa King, kullum burin daddyn nan nasu yaga ƴaƴan talakawa cikin farinciki da annashuwa, yaga marayu suna farinciki kamar sauran kowasu ƴaƴa masu iyaye kuma masu gata, ƴaƴan talakawa da yau aka mayar da su marasa galihu a duniya, su sha wahala da kyar da suɗin goshi, iyayensu su hana kansu abincin ci duk dan su samu su biyawa waɗan nan ƴaƴan kuɗin makaranta, amma sai dai kash, yaran zasu gama karatu babu aikin yi, babu mai tallafa masu ya nema masu aiki saboda sun fito daga gidan marasa galihu, ko sun nemi aikin ma babu wanda yake basu, babu ma wanda yake kulasu, wani ma su bada result nasu a wajen nema aiki ko kuma wajen wani babba mai muryar faɗa aji a kasar dan ya nema masu aiki, a haka wannan result ɗin take ɓacewa, saboda ba kulasu ake yi ba, amma shi King Zuhair muddin result na ƴaƴan talakawa zai gifta ta gabansa dan neman aiki, to da izinin Allah ba'a kwana ɗaya sai ya sanya an basu aikin yi a koma ina ne a kuma kowani irin caurse suka karanta, shiyasa da wuya King ya yi kwana uku ba tare da buƙatun ƴaƴan marasa karfin ta gifta ta cikin fadarsa ba! Haka yake bawan Allah mai farin zuciya!.
"Okey daddyn angama In Sha Allah". Cewar Yah Jawad kenan, yana magana yana kuma bin takardun da kallon. Karfi da ya ji King ya koya masu taimako dan dole, saboda dayawan ayyukan marasa karfi ko marasa ghalihu su yake sanyawa su yi, basu isa kuma su ce