ya ci ubansu, dama a wuya yake da su, suna son kashe mashi ƴar uwa ɗaya tilo, duk time da suka zo gidan idan suka tafi sai ta fi kwana uku tana fama da ciwon kirji, Allah ne kawai yake tsareta wani ciwon bai kamata ba, so a ƙule yake da su, idan ya biyewa zuciyarsa tsab zai sumar da su dukkansu biyu wlh.
Juyowa ya yi ya dawo gabanta. "Gani". Ya faɗa yana kawar da kallonsa gefe guda.
"Ba zaka tsugunna ba ka wani tsaya a gabana, so kake wuyana ya yi ciwo wajen ɗaga kaina na kalli fuskarka idan zan yi magana ne? Wannan ai rashin tarbiya ne, haka kake tsayawa a gaban mamanka gangan da kai ka sakata ɗaga kai sama dan ganin fuskarka kafin ta yi magana........."
Aikuwa bata kai karshen maganar ba ya dallah mata wani irin gigitattacen mari. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce. "Iskancinki ya tsaya a iya kan maman Zainab, dan itace kuka haɗa wani abin da ita, kuma ko ita ɗin ma idan kika sake kuna wani magana da ita kika saƙo mamarmu a ciki sai kin gane ke karamar maras kunya ce! Mahaifiyarmu ba sa'ar ki bace, idan baki ɗauki taki da daraja ba mu tamu tana da daraja.......".
Shi ma bai kai karshen maganar ba baban Zainab ya dalla mashi mari tas a kumatu.
Wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaura hannunsa ɗaya a kumatun nasa, nan take idanunsa suka yi jajir kamar jini, da alama ransa ya ɓaci sosai. A hanzarce ya sanya kai ya fice daga gidan, domin gudun kada abin ya kwaɓe masu sosai, yasan idan ya tsaya zuciya zata ɗebesa ya daki baban Zainab ɗin ma, idan ya yi hakan kuma sam bai kyauta ba, yana da halinki sosai, baya manta alkhari, ba irin Haidar bane shi ɗin, yanzu ma ba dan ya lura Hauwa na ƙoƙarin saka mahaifiyarsu a cikin rai'nin wayonta ba da ba zai sanya mata hannu ba, yasan idan bai dakatar da ita ba tabbas zata cigaba da kiran mahaifiyarsu a cikin maganarta, shiyasa ya yi saurin taka mata birki, ban da haka da zai danne zuciyarsa ya shanye walaƙancinta ko dan saboda baban Zainab ɗin.
Kafin baban Zainab ya yi wani magana tuni ya fice daga gidan da sauri.
Kukan munafurci Hauwar ta saka mashi, cike da makircin tana kukan munafurcin ta fara magana. "Wlh baban Zainab ni ba zan yarda ba, kana gani wani ƙato ya dakeni ina matsayin matarka, dole a bi mun hakkina".
(Matarsa kuma?🤔 Yaushe aka yi hakan?🤔 Dole su yi mana bayani)
Hakuri ya fara bata tare da gaya mata to ba ga shi ya rama mata marin ba. Kafewa ta yi a kan ita fa ba zata yarda ba, wannan marin da ya yi masa ya yi mata kaɗan, idan yana son ta hakura dole ya karɓi komai nasa daga hannun Sadiq ɗin, ya karɓi keys ɗin shagonsa da komai nasa, sannan Sadiq ba zai bisu sabon gidan da ya gina ba, maman Zainab kawai zasu ɗauka, Sadiq ɗin ya koma gidansu. Tirƙashi da alama da biyu ta takali Sadiq ɗin da faɗa, da alama tana da manufa sosai a kan dukiyar baban Zainab ɗin, so ta lura Sadiq ɗin zai kawo mata cikas shiyasa ta takalo faɗar, ga shi kuma da alama burinta zai cika, wanna Hauwar anyi makira wlh.
"Duk yadda kike so haka za'ayi, zan karɓi komai na, shikenan?". Ya yi maganar yana goge mata hawayen munafurcin da take zubarwa.
Kai ta gyaɗa mashi alamar e hakan ya yi mata. "Tom shikenan mu je cikin ko?".
To ta amsa mashi da shi tare da wucewa gaba tana mai tambayarsa to yaushe zai karɓi keys ɗin daga hannun Sadiq ɗin. Amsa mata ya yi da duk lokacin da take so. Tana ƙoƙarin shiga cikin parlourn ta yi saurin amsa mashi da yau take so. Babu damuwa ya amsa mata da shi tare da shigewa ciki.
Maman Zainab tana zaune a in da take bata tashi ba, already ta jiyo wannan shegiyar muryar Hauwar mai kama da muryar babanin akuya, jin muryar ma yasa bata motsa daga in da take ba, ta cigaba da zamanta kawai, dan yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani ganin fuskar Hauwa a rayuwarta.
"Ana sallama maman Zainab ba zaki amsa mana ba sai kace ba musulma ba? Ko dai kin manta da muhimmancin sallama ne? Ina karatun islamiyar da kika yi? Ko dai ya zube ne?". Cewar Hauwar, ta yi maganar tana ƙoƙarin zama a saman sofa, cike da iyashege da shakiyanci tare da son ganin ta bakantawa maman Zainab ɗin rai ta yi maganar tata.
"Kada ki kuskura ki zauna mun a saman kujera Hauwa, idan kuma kika zauna wlh zan yi maki ɗanyen aiki, kin san halina!". Maman Zainab ta faɗa tare da miƙewa tsaye.
Kallon baban Zainab Hauwar ta yi ta ce. "Honey waye ya sayi kujerar ne? Kai ne ko kuma daga gida ta zo da su?".
Zama ya yi a saman kujerar mai zaman mutu ɗaya. "Ni na saya Hauwa'u na".
Wani irin shu'umin murmushi ta saki kafin ta ce. "To maman Zainab ashe kujerar na mijinmu ne ma ba naki ba, to ki bari sai kin sayi naki sai ki hanani zama, amma wannan ai nima nawa ne tun da mijinmu ya saya!".
Wani irin murmushi wanda ya fi kuka ciwo maman Zainab ta yi, ƙoƙari take yi ta ɓoye ɓacin ranta, saboda ta lura burin Hauwa ne kullum taga ta cusa mata baƙinciki, in kuwa haka ne to bai kamata ta bari Hauwar tana ganin ɓacin ranta ba, hakan yasa ta yanke shawarar fito da nata makircin na mata, ai ba Hauwar ce kawai ta iya makircin ba, kowa ma ta iya.
"Hauwa kenan, to ki zauna a kai ki ga ɗanyen aiki, idan kika zauna ne kuma zaki san ainahin wanene mamallakin kujerar". Ta faɗa tana mai cigaba da ƙaƙalo murmushi dole, daga ta ciki kuma zuciyarta kamar zai fashe, barema da ta ji Hauwar ta ambaci baban Zainab da sunan mijinsu, hakan ya tsaya mata a rai sosai, sai dai taki yarda ta fitar da ɓacin ran a fili bare ma Hauwar ta gani ta ji daɗin ta ɓata mata rai.
Kasancewar Hauwar ta san halin ƙawar tata sarai, sai bata zauna a saman kujerar ba, sai ta fake da jan magana, irin kada ace ta tsorata ta ƙasa zama a saman kujerar, ta fake da kananan maganganu tana ta soki burutsu tana ƙoƙarin ta cusawa maman Zainab ɗin ɓakin ciki ta hanyar nuna mata cewa ai baban Zainab yanzu mijinta ne, har da wani cewa kila ma yanzu sun sami ɗan tayin ciki da bai wuce sati ɗaya ba.
Ba yake maman Zainab ɗin ta gama fahimtar dan ta ƙuntata mata ta zo gidan, sai bata nuna kamar ta damu ba, sai ma murmushi da ta saki tare da cewa. "To ai dama shi namiji mijin mata huɗu ne, me a ciki dan ya aureki? Yanzu ma ai akwai sauran gurbin mata biyu a tattare da shi, so yana iya cike gurbin ya rufe kofa kawai, idan ma bashi da ƴan matan da zai cike gurbin da su ba sai mu samo mashi ba, ki samo mashi ɗaya in samo mashi ɗaya ya kara ya rufe kofa me a ciki?!".
Sam sam Hauwa bata so hakan ba, ta so maman Zainab ɗin ta tada balli dan su ji daɗin yi, ko kuma ta hau kuka burinta ya cika, amma ina maman Zainab ta gwada mata cewa ai ita ma ta iya makircin, ta shanye ɓacin ran tsab ta ɓuye kayanta.
Meyake faruwa a tsakanin Hauwa da kuma baban Zainab ne? Nasan kowa tana son sani, to ku matso ku kasa kunne. Hauwa dai sara ce ta zo mata a kan gaɓa, dama already ta kashe aurenta saboda ta auri baban Zainab ɗin, zaman idda take yi a gidan mijinta da ta mayar da shi wani soloɓiyo, dama tana can tana shirin yadda zata yi ta mallaki baban Zainab ɗin cikin sauki, ta kai sunansa wajen wannan bokan nata na kan dutse, sai bokan ya ce mata aikin ba zai taɓa yiwuwa ba dole dole sai da wani abinsa da ya taɓa amfani da shi, ko dai single ɗinsa ko short ɗinsa, ko wani abin nasa, to tarasa taya zata yi ta sami wannan, tana ta tunani, kwananta uku da gama idda ta sake komawa wajen wannan boka, a nan ma ya sake jaddada mata aiki ba zai yiwu ba dole sai ta kawo abin da ya gaya mata ɗin nan. Hakan ta kwaso jiki kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta dawo, kwananta biyu da dawowa daga wajen bokan maman Zainab ta kirata a kan matsalar da take ciki, ta yi matuƙar farinciki da jin hakan, domin ta samu damar da zata cinwa burinta, hakan yasa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen bawa maman Zainab ɗin shawarar su je wajen wannan boka, ta kuma zagaya ta gayawa bokan nata ga abin da take son ya yi mata zasu zo a tare da maman Zainab ɗin, kada ya nuna kamar ita zai yi wa aiki, ya nuna cewa maman Zainab ɗin zai yi wa aiki, idan ya yi mata hakan komai ya tafi dai'dai zata bashi maƙudan kuɗaɗe.
Da yake bokan mutuminta ne sun saba, ba yau ya fara yi mata aiki ba, shi ya yi mata aiki ta mayar da mijinta soloɓiyo sai abin da ta ce zai yi, ya kuma yi mata aiki ta mallake dangin mijin nata basu da bakin magana a kanta, so sun jima a tare da bokan, hakan yasa ya aminta da wannan aiki da ta kawo mashi, cikin sirri suka shirya komai ta munafurci maman Zainab. Bayan sun zo an yi aikin ne sai Hauwar ta kwashe kayanta daga gidan mijinta ta koma gidan iyayenta a garin Kaduna garinsu maman Zainab ɗin kenan, dama already ta gama iddarta da tsawon sati ɗaya ma kenan, burinta ya cika da samu kan baban Zainab, so a Kaduna baban Zainab ya je ya nemi aurenta, dama na gaya maku ƙanin babanta da take a hannunsa mayen son kuɗi ne, sai abin da Hauwar take so yake yi, dan ita take ɗaukar nauyinsu, dan haka bai wani ja ba da Hauwa ta ce ga mijin da zata sake aura, a takaice dai yanzu sati guda kenan da ɗaurin aurensu, shi baban Zainab iyayensa basu sani ba, ita ma maman Zainab bata sani ba, shi kuma kanin baban Hauwa kuɗi kawai yake so ba ruwansa da tambayar daga ina Hauwar ta samo miji ko ya halinsa yake ko kuma ina iyayensa, shi dai kawai ya bi umarnin Hauwar gudun kada ta cire masu tallafi ya shiga uku, zuciya ta mutu ba zai fita ya yi sana'a ba, Allah ka rabamu da matatciyar zuciya. In short wannan shi ne abin da ya faru a tsakanin Hauwa da baban Zainab, yanzu maganar da nake maku sun tare a sabon gidansa, shi ne fa tsabar mugunta irin na Hauwa, dan son ta kuntatawa maman Zainab ne yasa ta cewa baban Zainab ɗin lallai dole dole su zo su ɗauki maman Zainab su koma sabon gida a tare. Da alama so take ta kashe maman Zainab da bakinciki, wato su koma sabon gida a tare dan ta je ta cigaba da cusa mata kayan takaici, wannan Hauwa tamkar green snake under green grass take, shegiya silent killer, ta san ta kan duniya, cikin ruwan sanyi zata dama mutun.
To mata ina fatan wannan yazama darasi a garemu, duk wanda zata ce maki ki je wajen boka wane kaza, ko kije wajen wane ya biya maki bukatunki, hakan yana nufin tasan bokan kenan, sun jima a tare, idan baki ji tsoron Allah kin koma ga Allah mahaliccin kowa da komai ba kika biye mata ta kan iya yi maki irin ta Hauwa, ni labarin gidansu Zainab yi mun yake yi kamar true life story wlh, kamar gaske haka nake jinsa, dan mata dayawa suna tabka irin wannan babban kuskure, yaushe zaki yarda bawa mai kafa biyu! Hannu biyu irin naki, mai yin kashi da fitsari, mai cin abinci kamar yadda kike ci, mai kwanciya ya yi barci ya kuma tashi ya yi tafiya, yaushe zaki yarda mutun kamar ke zai iya biya maki buƙatar da ke ba zaki iya biya ba?! Wannan magana hankali zata ɗauka kuwa?! Mutun ne fa kamar ki! Komai da yake da shi kina da shi! Amma kike yarda da cewa shi ne warakar matsalarki?! To dai ga Hauwa ta nuna maku aya, idan baku kuji bin shawarar kawaye domin Allah ba, zaku guda dan gudun cin amana, bare ma ace kinfi kawar komai, kin fita jin daɗi da morewar rayuwa! Ai abin da kuka ga Hauwa ta aikata wlh kaɗan ne ma a kan wata idan ta tashi tabka maki nata son zuciyar, babu mai sanin mutun sai Allah, Allah shi kaɗai yasan ɗan adam in and out, ko shekara ɗari kika yi a tare da mutun baki isa ki ce kin san shi in and out ba, dan a kowani rana, a kowani lokaci zuciyar ɗan adam tana juyawa tamkar juyin agogo, dan haka mata gareku sai ku kiyaye, kun dai ga aya ƙarara, babu mai yi sai Allah, kuma babu mai hanawa sai Allah, ki miƙa lamuranki ga Allah ki jira ki ga ikon Allah, ba wai ki dogara da wani ƙaton banza mai kashi da fitsari ba!!!. Allah yasa mu fi karfin zuƙatanmu.
Mu koma kan labarinmu tun da kunji menene yake faruwa a tsakanin Hauwa, baban Zainab da kuma maman Zainab da yadda aka yi waɗan nan abubuwa suka faru, dan haka mu koma kan cakwakiyar domin ganin ya wasan zata kaya.
Gyara tsayuwa Hauwar ta yi, ta dai kasa iya zama a saman kujerar, dan fa ba karya tana tsoron maman Zainab sosai, tasan halinta sarai, macece mai hakuri da kawaici, amma kuma idan ka kureta, dama ance mai hakuri fa bai iya fushi ba, so a gaskiya maman Zainab tana da zuciya over, faɗarta kuma babu daɗi idan ta fara shi, hakan yasa Hauwar bata zauna a saman kujerar ba, sai ta ce. "Allah ko maman Zainab, gaskiyarki haka ne, namiji mijin mata huɗu ne, to amma fa banda honey, shi daga ke sai ni mun ishe shi".
Sake sakin murmushi wanda ya fi kuka kuna Maman Zainab ta yi kafin ta ce. "A'a ki barshi ya cike huɗun kawai zai fi, ko dai kina jin tsoron yin kishi da su ne idan suka shigo? Kada ki damu ai ni zan tsaya maki". Ta yi maganar tana jefa mata wani irin kallo mai wuyar fassaruwa. Yau fa ake yinta a wannan gida, kowacce ashe ba tayar baya bace.
Ajiyar zuciya Hauwa ta sauke. "To ai ni bana kishi, nafi karfin na yi kishi da mace, ke baki gani bane, yanzu duk bama wannan ba, munzo ɗaukarki ne ke da yara mu koma sabon gida, mu je mu haɗu a can mu zama cikakkun family ai yafi, nasan kuma kina kewar honey sosai, bai kamata ya barki a nan kina ɗaukar kwanaki baki sanya shi a idanunki ba, shi ne naga ya dace na zo na ɗaukeki mu koma can tare, at least a kowace rana zaki sanya shi a cikin idanunki ko sau ɗaya ne kam". Cike da mugunta sosai ta yi maganar, ta kuma yi maganar ita ma tana wurgawa maman Zee ɗin wani irin kallo na nuna tsantsar isa da rai'nin wayo. So take dole dole sai ta kuntatawa maman Zainab ɗin, burinta kawai taga bacin rai ya bayyana a saman fuskarta.
"Allah ko?". Maman Zee ta faɗa tana binta da kallo. Wannan shi ne idan mutun yana son ganin kukanka to kada ka yarda ka bari ya tafi ba tare da ka nuna mashi dariyarka ba, sai dai bakin ciki ta kashe shi!.
Hura chewing gum dake a bakinta Hauwar ta yi kafin ta ce. "Yeah hakan naga ya dace, ai bai kamata mu barki kina zaman kaɗaici tare da gauranci ba, dan haka ki shiga ki ɗauko mayafinki kawai mu tafi ko honey?". Ta kai karshen maganar tare da juyo da kallonta a kansa. Shi dai ya zubawa wayarsa ido yana aikin latsawa, da alama ma hankalinsa baya a kansu.
A takaice ya ce mata. "Yadda kika ce hakan za'ayi".
Wani irin tauna chewing gum ɗin nata ta yi sai da ya bada sautin kas kas tare da sakin wani shaiɗanin murmushi. "Tom maman Zainab kin ji honey ya ce yadda nace haka za'ayi ba sauran ja, to na ce ki shiga ki ɗauko mayafi mu wuce, waɗan nan tsofaffin kayan ɗakin naki duk ki barsu a nan ko kuma ki turawa mama Kaduna ta yi amfani da su, akwai komai a sabon gida an zuba, so bamu buƙatar tsofaffin kaya".
Haƙiƙa a wannan gaɓar maman Zainab ta kulu da bakinciki, ta zo har wuya, kiris take jira ta fashe, amma sai ta kara daurewa, duk da ta rasa me zata sake cewa da Hauwar, hakan bai hana ta ƙaƙalo murmushin dole tare da sauke ajiyar zuciya ba. Sannan ta sanya kai zata wuce izuwa cikin ɗakinta.
"Kiyi sauri, kada ki bata mana lokaci, dan ba zan iya jimawa a wannan gidan ba, zafi ya yi yawa babu Ac, kuma yanzu lokacin cin abincin honey ya kusa". Cewar Hauwa.
Tamkar maman Zee bata ji ta ba, sam bata juyo gareta ba, ta nufi cikin ɗakinta kawai zuciyarta na tafasa tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje.
Tana shiga cikin ɗakinta Zainab ta fito daga nasu ɗakin zata nufi waje.
"Ke Zainabu abu zo nan". Hauwa ta faɗa, har lokacin kuma tana tsaye, ta kasa iya zama a saman kujerar, da alama tana mutuwar tsoron maman Zainab, kawai dan taga baban Zainab yana bata goyon baya ne ma yasa ta tsaya har ta iya gayawa maman Zee ɗin magana, ban da haka tana tsoronta sosai, alamu sun nuna a lokacin kuruciyarsu Hauwa ta sha kashi a hannunta sosai.
Wani irin matsiyacin kallo Zainab ta wurga mata kafin ta sa kai ta wuce waje, taki zuwa, dama fa ita Zainab kun san ba kamar Khadija take ba, bata