"Jawad akwai wasu ayyukan ginin gidan marayu guda biyar dana fitar, companynka ta shirya karɓar aiki, ku yi mun aiki da sauri, kuma a ƙawata mun shi kamar yadda na fitar da zanensu, bari dai na kammala tsare tsaren zan nemeka". Cewar King.
JAISH dai ya yi shiru sai Allah kaɗai yasan me yake tunani. Shi kuwa Jawad haka suka cigaba da hira cikin tsantsar so da kauna shi da King, kai kace abokai ne ba uba da ɗa ba, wani lokaci King ya zolaye shi yana murmushi, dan gaskiya King yana da son zolayar ƴaƴan nasa idan suna hira, barema manyan yana sakewa su yi wasa da dariya kamar abokai, duk kuma hiran da suke yin nan King yana ta aikin act design ɗinsa abinsa. Daga karshe dai Jaish wayarsa ya fitar ya fara aikin latsawa, dan shi hirar King da Jawad ma bata shiga kunnensa, baya jin me suke faɗa, gara ya yi abin da ya saba, wato latsar waya!.
Sai wuraren karfe 10 ne Yah Jawad ya miƙe hannunsa rike da envelopes ɗin.
"Daddy am feeling sleeping, bari na je na kwanta, have a wonderful night our hero". Ya kai karshen maganar tare da ɗan rungume King ɗin yana manna mashi sumbata a goshi.
"Have a great night my son, don't forget to pray before sleeping".
In Sha Allah ya faɗa tare da juyar da kallonsa izuwa kan Jaish da kwata kwata baya a tare da su, hankalinsa ta yi nisa, ya tafi can duniyar latsa waya.
"Bro am feeling sleeping, see you tomorrow morning".
Ya yi maganar yana taɓa shoulder ɗin Jaish ɗin, dan yasa idan ba taɓa shi ya yi bama ba jinsa zai yi ba, ya yi nisa a duniyar latsar waya.
"Take care my bro and good night".
Shi ne abin da Jaish ɗin ya faɗa, sai dai daga jin yadda voice nasa ta fita in a low sosai ya nuna cewa yana jin barci shi ma, jikinsa duk a mace sosai.
Wucewa Yah Jawad ya yi ya nufi waje abinsa. Shi kuwa Prince Jaish juyo da kallonsa a kan daddyn nasu ya yi.
"Please dad you have to be sleep now, dare ya yi sosai fa".
Ya kai karshen maganar tare da kai kyawawan fararen hannunsa ya ɗauke laptop ɗin dake a gaban King ɗin. Kasheta ya yi tare da ɗurata a saman bedside drawer, sannan ya maido da kallonsa izuwa saman fuskar daddyn nasa.
"Daddy i don't want to see you suffering your self to much like that, please our hero dad ka rinƙa samun hutu".
Nisawa King ya yi kafin ya ce. "My god bless you my son, ina alfahari daku dukkanku ƴaƴana, amma da ka bari na ƙarisa aikin ai, saura kaɗan ne".
"No dad gobe zaka ƙarisa, now dai ka kwanta ka yi barci".
Ya kai karshen maganar tare da mannawa dad ɗin sumbata a goshi cikin so da kauna tare da miƙewa tsaye.
A zahirin gaskiya King yana matuƙar kaunar ƴaƴan Gimbiya Rahilarh fiye da dukkan sauran ƴaƴansa, domin suna da tarbiya na wuce misali, ga hankali da sanin yakamata, suna kuma kaunar iyayen nasu sosai, barema ita auta da ta ɗauko irin halin King na taimakon bayin Allah, shiyasa ta fi kowa farinjini a gidan, dukka ƴaƴan Gimbiya Rahilarh ba'a cikin kingdom ɗin suka girma ba, hasalima Gimbiya Rahilarh bata haihuwa a cikin masarautar, tun da ta yi haihuwarta ta fari a ciki, daga nan idan ta sami ciki ta kusa haihuwa Dubai take komawa wajen iyayenta, a can take haihuwa, dan a cewarta bata yarda da gidan ba, a duk lokacin da take da ciki tana yawan mugayen mafarkai, ga yawan tsoratata da ake yi, wani lokaci ta rinƙa ganin jini a cikin toilet ɗinta da abubuwa mabanbanta da suka yi kama da tsafi ko makamancin haka, abubuwa dai kala kala, wani lokaci har danneta ake yi a cikin jacuzzi idan tana wanka, a danneta a shaƙa mata ruwa har kamar zata mutu, duk kuma hakan baya faruwa sai idan tana da ciki, wannan dalilin yasa bata taɓa yarda ta haihu a cikin Masarautar, dan fa a haihuwarta ta fari ansha gwagwarmaya, bata yi tunanin abin da ta haifa zai rayuwa ba, tun da ta haihu take cikin masifa ita da ɗan har sai da ta koma Dubai na tsawon shekara biyu, a can ta reni yaron har ta yayesa kuma ta dawo ta barshi a can, saboda tana gudun wani abin ya samesa, a lokacin da take da cikin auta mutuwa ne kawai bata yi ba, amma ta azabtu iya azabtuwa, bata samun barci, bata iya cin komai, da ta fara cin abinci zata fara ganin wasu hayaniya suna yi mata yawo a kai, babban abin damuwar kuma da zarar ta fara addu'a sai ta ji ana karisar mata da addu'ar tata ko kuma an shaƙe mata maƙoshinta ta kasa iya cigaba da karanto addu'oin, abin dai ba'a magana, KINGDOM OF POWER idan ka kalli masarautar ta wata fuska masarauta ce mai zaman lafiya da kuma son kwanciyar hankali, ga kuma taimakon jama'a, amma kuma ba kowa bane yasan ainahin menene a cikinta, duk yadda kuke tunaninta ta wuce nan, amma lokaci ne zai gaya mana menene a cikinta, yanzu na ɗan fara gutsira maku labarin ne, sai mun afka ciki zamu ji menene yake gudana!.
A takaice dai duk ƴaƴan Gimbiya Rahilarh harta auta a Dubai suka taso, ba kunji auta tana cewa Yah Omar ya kammala secondary school zai dawo ba? To haka ƴaƴanta suke, sai sun kammala secondary school nasu a Dubai sannan suke dawowa, auta ce kawai ta dawo bayan kammala primary school ɗinta, dan King ya kasa hakura ya barta a can, yana kaunarta fiye da kowa a gidan, so yana son ganinta a kusa da shi, yanzu tana jss one, Obaid da Omaid ma ba'a nan suke karatu ba, hutu kawai suke zuwa, yanzu haka suka Ss 1, saura masu shekara biyu su kammala su dawo masarautar mai gabaɗaya, hakan yasa tarbiyar ƴaƴan Gimbiya Rahilarh ya babbanta dana sauran familyn, daban suke, shiyasa King ya fi kaunarsu fiye da kowa, amma yana ƙoƙari wajen ganin ya ɓoye son nasu da yake yi, baya nuna banbanci a tsakanin ƴaƴan nasa. Sai dai fa da Yah Omar ɗin auta da kuma twins Obaid and Omaid a wajen kakansu mai rankarfe suka girma, shiyasa kuka ga Omaid and Omaid basa jin magana, kunsan girman kaka, hmmm ba'a magana sai dai kun gani da idonku, su Jaish and auta kuma a gidan yayan gimbiya Rahilarh wanda yake matsayin Secretary to government of federation suka girma.
Cikin so da kauna Jaish ya yi sallama da daddyn nasa, amma kafin ya tafi sai da ya tabbatar da King ɗin ya kwanta, sannan ya lulluɓe shi da duv ɗinsa mai kyau da laushi, ya rage mashi gudun Ac tare da janyo mashi kofar bedroom ɗin, sannan ya wuce nasa part ɗin abinsa, bawan Allah yana ji da iyayen nan nasa sosai da sosai.
Yana zuwa bedroom nasa ya ajiye takardun da King ya bashi a saman table dake a tsakiyar bedroom ɗin gaban wata sofa mai bala'in kyau da laushi, bayan ya ajiyesu ne ya nufi saman katafaren king bed ɗinsa, addu'a ya yi bayan ya haye, sannan ya kwanta tare da jan duv zuwa dai'dai cikinsa, ya ɗauko remote dake a saman bedside drawer, wutar ɗakin ya kashe, nan take duhu ta mamaye ko'ina, a hankali ya lumshe idanuwansa ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi!. ASUBA TA GARI!.
Washegari da safe shirye cikin wasu shegun tsadaddun suit Jaish and Jawad suka fito domin zuwa office nasu, companynsu daban daban, Jaish shararren ɗan jarida ne na gaske gaske, babba ne sosai wanda ake ji da shi, shi kuma Yah Jawad civil engr ne, so kowa da aikinsa.
Sun fito sosai abinsu, kayan jikin nasu ma iri guda ne, sun yi masifar yi wa kayan kyau, Jaish yana sanye da black glass a idanunsa, while shi kuma Jawad yana sanye da white glass ɗan siriri kamar medicated, sun fa haɗu iya haɗuwa.
A babbar parlourn King suka ci karo da su Gimbiya Zunaira, Fanan, and Aneesa suna shirye cikin uniform nasu na makaranta mai bala'i kyau, riga da sket ce sai ɗan hijabi da bata wuce kirjinsu ba, sket ɗin navy blue ne, kuma bata kai masu har ƙasa ba, dai'dai singalalin kafafunsu ta tsaya, rigar kuma fara mai doguwar hannu ce, sai hijab fara, sun je sun gaishe da King ne sun fito.
Suna ganin su Jawad suka hau zuba masu gaisuwa cikin girmamawa, auta ce kawai ta zo ta rungumi Yah Jaish tana murmushi.
Shi ma rungumarta ya yi ba tare da ya yi magana ba.
"Where's Jannat?".
Cewar Jawad, ya yi maganar yana kallon auta, dan yasan ita ce mutuniyar Gimbiya Chuchu, kullum suna tare.
"She's not feeling fine, and dama Akka ta ce na kira mata kai, wai kaje da sauri, Aunty Chuchu ɗin ma tana ɗakinta".
Ta bashi amsa tana raba jikinta dana Jaish, dan ta bi bayansu Fanan da suka wuce izuwa part na Mummy dan su gaisheta kafin su je wajen mama ma su gaisheta sai Momma, daga haka sai su wuce a kaisu school, ita kuma Sarina yanzu tana two hundred level a jami'a, ba secondary take ba!.
Jinjina mata kai Jawad ya yi yana tunanin yadda zasu kare da Akka, dan yasan cewa tabbas Chuchu ce ta kai kararsa a kan kneel down da ya sakata jiya, dama kuma ita Akka wlh ko su Sarina ya bawa punishment idan ta sami labari ya rinƙa shan ruwan masifa kenan, tsohuwar akwai rigima, bata bari a taɓa ƴan'matan, shiyasa ya kafawa su Sarina doka a kan idan suka kuskura dan ya basu punishment suka gayawa Akka sai ya ɓallasu, to yanzu ga Chuchu ta je ta faɗa, yanzu idan tsohuwar nan ta sako shi a gaba da bala'i sai ma ta ce mashi ai haka ubansa ya rinƙa yi mata rashin ji da yana ƙarami ta rinƙa hakuri da shi har ya girma, to shi waye da ba zai hakura ba dan kannensa sun yi masa ba dai'dai ba? Akka duniya ce, kada ka yarda ka bari ta kamaka ka yi laifi, zaka sha surfar masifa.
"Jaish ka ƙarisa ku gaisa da dad bari na amsa kirar ƴar tsohuwar nan, zan sameka a nan".
Cewar Jawad ɗin kenan, ya kai karshen maganar kuma tare da wucewa wajen elevator dan ya nufi part na Akkar ya ji me zata ce mashi kuma.
Da okey Jaish ya amsa mashi kafin yasa kai ya wuce izuwa wajen King ɗin.
To bari dai mu leƙa su Kamran, kafin mu dawo mu ji ya Jawad zai kare da Akka da kuma Chuchu!.
🕊️🔥🕊️🔥🕊️🔥🕊️🔥🕊️🔥🕊️🔥🕊️🔥🕊️
🏞️FOREST🏞️🔥
A wannan rana dai da kyar su Pretty suka iya raba jikinsu da juna har suka samu suka haɗa abin da zasu cinwa cikinsu. Wani irin ɗan ƙaramin dutse mai masifar haske Pretty ta ɗauko ta fara daka masu kayan biya a saman wani dutse mai ɗan faɗi, wannan dutse da yake a hannunta tana dakar da shi haskensa sai ya bawa mutun tsoro, yana da haske sosai mai kashe idon mutun, design of star ne dutsen, kamar kuma ba dutse bane ba, to ga dai shi nan, sai Allah ne kaɗai ya san daga ina suka same shi, da shi suke daka abubuwa, ya zama kamar taɓaryarsu kenan.
A haka dai cike da tsoro Pretty ta haɗa masu abin da za su ci, suka ci, ko da lokacin kwanciya ya yi yau a manne da juna sosai suka kwanta, alamar suna tsorace sosai kenan.
Kamran kuma bai sake dawowa wajensu ba sai washegari da safe rana ta ɗan ɗaga, kamar yadda ya yi masu alkawari haka ya dawo tare da kwari da bakarsa, sai dai yau a tare da Rocky suka zo, Rocky ya zauna a bakin kofar shiga cikin ramin, dan idan baku manta ba jikinsa ba zata iya shiga cikin ramin ba, ya yi girma, so a baki ya zaune. Shi kuwa Kamran ya shigo ciki.
Zaune a saman bed kamar kullum ya isko Sweetie, ita kuma Pretty tana wajen kayan sakawarsu tana aikin gyarawa. Jin motsin shigowa yasa ta yi saurin juyar da kallonta izuwa kan hanyar shigowar.
Ganin Kamran ne yasa ta ɗan saki cool murmushi wadda sai da yasa dimples nata suƙa lotsa, sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, hankalinta ya kwanta, ta samu nutsuwa, dan idan Kamran yana nan to fa tana jin kwarin gwiwa sosai.
"Pretty who's here?".
Cewar Sweetie wadda ta jiyo motsin mutun a kusa da ita, ba kowa bane kuma face Kamran, takardar addu'oin da yake a kusa da ita wadda Pretty ta ajiye yake son ɗauka.
"Sweetie it's Kamran, yanzu ya zo". Pretty ta bata amsa tana mai dawowa kusa da su.
Ajiyar zuciya ita ma Sweetie ta sauke jin cewa Kamran ne, hankali ya kwanta.
Shi kuwa takardan da ya ɗauka ya fara buɗewa yana dubawa, kamar wani wanda ya iya karatun larabci, dan ma dai akwai English translation a jikin littafin.
"Kamran wai yaushe zamu je neman wancan mutumin ne?". Cewar Pretty sarkin rawan kai da giggiwa.
Ɗan satar kallonta ya yi ta ƙasar ido dan yaga shin tana kallonsa ne ko kuma, idan bata kallonsa sai ya kalli face nata, idan kuma tana kallonsa sai ya hakura, dan ba zai iya kallon cikin kwayar idanunta ba, suna rikita shi.
Aikuwa shi ta kafe da idanu tana ta kallo, dan yana burgeta, a cewarta yana yi mata kyau, haka zalika ita ma Sweetie duk da bata gani bata san ya kamannin Kamran ɗin yake ba, amma har cikin zuciyarta yana burgeta, bata da burin da ya wuce idanunta su buɗe ta kalli face ɗinsa. E to akwai kura dai kam!.
Ganin cewa shi take ta kallo ne yasa bai ɗago idanu ya kalleta ba, sai ma ya kara yin ƙasa da kansa, cikin sanyin muryar nan tasa ya ce. "Yanzu zamu tafi, ku zo mu fita waje ko?".
Da sauri Pretty ta miƙe tana murmushi kamar baki ba zai rufu ba, dan ta ƙosa taga sun gane wannan mutumin da mamarsu ta ce su nema, dan mamar nasu ta gaya masu in dai suka ga wannan mutumi zai kula da su sosai, hakan yasa ta ji duk ta ƙosa su gansa ta kuma bashi saƙon da mum ɗin tasu ta basu su bashi.
"Sweetie kawo hannunki mu tafi, zaki fita waje kema yau".
Cewar Kamran, ya yi maganar yana rufe littafin tare da mayar masu a in da ya ɗauka ya ajiye.
Ba musu Sweetie ta miƙa mashi hannunta, dan tana jinsa har cikin ranta, ta kuma yarda da shi. Ita kuma Hajiya Pretty sarkin rawan kai, tuni ta yi gaba.
Sanin cewa Rocky yana a bakin kofa ne yasa Kamran ɗin ya ce da Prettyn ta dawo su jera a tare, dan yasan halinta da tsoro, yanzu idan taga Rocky sai ta haukace masu.
Ba musu ta dawo suka jera, sai satar kallonta yake yi, ta yi matuƙar kyau cikin shigar wata doguwar riga zuwa gwiwanta, rigar mai kyau ce sosai, daga gani kuma tana da tsada sosai da sosai, kasar rigar a buɗe kamar umbrella, yau ta sanya wani irin hula mai kyau ta rufe kanta da shi, hular ce mai gashi gashi a jiki, ta yi kyau sosai, shigarsu iri ɗaya da Sweetien, amma shi Kamran a iya jikin Pretty ne kawai shigar suka yi mashi kyau.
Kamran ɗin ne ya fara fita daga cikin ramin kafin ya sanya hannu ya fito da Sweetie, ita kuma Pretty ta fito da kanta. Lokacin da suka fito Rocky baya a wajen, da alama ya ɗan kewaya wani wajen ne, dan shi ma ya iya yawo........ Yo dama da kafarsa da lafiyarsa gasas me zai zaunar da shi? Ai sai yawo kawai abinsa, ya nemi nama ya ci, idan ba haka ba kuma ya cinye Kamran da Mamma........🥱😅💔
Suna fitowa waje Rocky ya dawo wajen da ƴar gudunsa, dama ashe bai yi nisa ba. Ai kuwa Pretty tana ganinsa ta daka wata uwar tsalle tare da kurma ihu mai razanar da ƙwaƙwalwar mai sauraro tana ƙoƙarin guduwa ta bar wajen, ita sam ta manta Kamran ɗin ya taɓa gaya maya Rocky abokinsa ne kuma ba zai cinyeta ba.
Ai kuwa tana zunduma wannan ihun shi ma Rocky ya zunduma nasa ihun, habawa kara haukacewa suka yi daga ita har Sweetie da bata gani kuma bata san ya girman Damusar take ba, ta dai ji kurnaninshi da kuma kukanshi mai tashin kan duk wata halitta mai rai.
Da sauri Kamran ya riƙo Pretty dake ƙoƙari zundumawa a guje ta bar wajen, ya rikota ne kuma saboda yasan wlh tana gudu Rocky zai rufa mata baya ya damkota ba fashi, dan haka sai ya yi saurin rikota tare da jawota jikinsa yana ƙoƙarin yi mata magana akan ta nutsu babu abinda Rocky zai yi mata. Dama already yana rike da hannun Sweetie kam, suna neman haukasa bawan Allah.
Ai kuwa bai kai ga yi mata magana ba Rocky ya iso wajenta ya fara bin jikinta da shinshina kamar wani tsahon maye. Habawa wani irin mahaukacin ihu ta sake zundumawa tana faɗin. "Shikenan ya cinyeni na shiga uku na gama yawo! Wayyo ya cinye mun kafata! Laa shikenan ya fara cin kun kafata, wayyo Allah nazama mara kafa, ya cinye dukka, wayyo na mutu na mutu mummyna".
Wayyo cikina, Pretty zata kashe ni da dariya,😅 ga abin tausayi ga kuma abin dariya, to ni kam dai na shiga aljanna naki fitowa ne, sai dai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu, yau Rocky zai cinye Pretty mayyar tsoro...🥱
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘